Sashe 20
Zanyi Biyayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kwance suke Husna na waya kasa kasa da ya Aliyu, RAHAMA na duba wani littafin Addu'oin ta, Husna tace "sister honey na gaishe ki fa, Cuna baki tayi tareda gyara zaman shimin dake jikinta data kamata dam kana ganin yanda kirjinta yakara wani cika da kyau, RAHAMA ba anyi over wise,
Ta diro tareda gyara falazo dinta tree quarter wanda baikai kasa ba tayi waje tana cewa " ni ai yanzu yaya tunda ya sameki baya tani nima kuma baruwa na dashi,
Dariya yayi, domin yajita, yace "please waya koyawa Sister tsiwa? Kece ko? "Kai baby wallahi ba ruwa na dama tanada kayanta a kulle yanzu komai ke fitowa,
Da coffee ta dawo rike tana juyawa, Husna ta mika mata wayar, "gashi yace sorry ku gaisa,
Ta karba, "nidai yaya ba komai badai ka share niba, "oh sorry sweet sister na kema kinsan ban isa in shareki ba aiki ne ya mun yawa, Amma gobe zan shigo am missing baby kema am missing you,
Buga kafa tayi tareda mikawa Husna wayar ta " karbi ke yake missing baniba kuma ko yazo ba zamu hadu ba ba ruwa NA dashi,
Saida suka gama hirar su ita tana sipping coffee dinta, bakomai yasa ta koya shan shiba sai don saboda Al Ameen, domin zaman da tadan yi dashi ta lura shine Abinda yafi rayuwa dashi itama ta koya yanzu,
Husna ce tace "wato kina jealous na kwace miki yaya, nikuma ince me? Kinsan duk duniya ba wanda ya Al Ameen yakeso yaji zancen shi sai ke, ", ya Al Ameen loves you more than yadda ya Aliyu kesona ya Al Ameen yana kewar ki yayi ta kokarin in hadaku momy ta hana tace inbar shi sai ya matsu yadawo da kanshi,
Cikin zakuwa tace "yanzu dama kuna waya dashi? "Sosai bari in kirashi ma kiji, ta fada tana dialing number shi,
Har wani rawa jikin RAHAMA yakeyi, tanaso taji koda muryar shine, "six month ba wasa ba kewar shi take na fitar hankali, "hello da yafada bayan yayi picking yasa ta lumshe idanun shi tanajin yanda zuciyar ta ke bugawa da wani irin sauri sauri,
"Husna ina Ajiya ta take? Yafada cikin wani irin yanayi domin mugun feelings yakeji akanta a lokacin ya matsu ya dawo nija wani uzurin business dinshi ya Sa ya tsagaita Amma duk runtsi dole cikin satin nan zai dawo,
"Yaya tana nan, "ok yace tareda katse kiran wanda ya mugun sosa ran RAHAMA, wato baida muba itace ta yi mugun damuwa dashi ko, Badamuwa, haka ta, koma tayi shiru tana tunanin wato ita kadai ke haukar ta shi ysnacan yana rayuwar shi da wasu kila a India,
Husna ma na mata magana shareta tayi taki kulata ta runtse idanun ta kamar tana bacci,
**************************
Yau ta tashi da kudurin zuwa gidan su domin duk watan nin nan bata taba yunkurin zuwa ba, yau tana tashi tafada ma momy zataje mabera, tace to su shirya taje itada Husna,
Sai kusan karfe sha daya suka kammala komai da suka saba Husna ta ruga bathroom tace " bazai yuwu ba kishige ki kwashe kusan hour ina jiranki ba ni bansan wane kyau kikeso ki Kara ba bayan wannan, ko so kike ki haukata yaya na,
"Ai yayan ki ma yanzu ji nake sai nayi shawara ma ko zan iya zama dashi ko aa, zaro ido Husna tayi tace "kaiiiii ki rufa mana Asiri kar kisa yayana hauka please,
Shareta tayi tareda murza sabulunta na dilka a fuska kafin ta shiga wanka, tace ai saikiyi nidai yi kifito na matsu banga Inna ba yau,, wai ma tsaya kina nufin bina zakiyi gidan surukai? "Watch and see ke ina kike? " ni akwai different ni Aure aka daura mana I m Mrs Al Ameen ko gobe kefa?
"Oh Abun gorine shikenan muma dai yana zuwa za a tsayar ki daina min gori kuma sai naje ai nima gidan mu ne, dariya ta mata tace "ai sai kijira a daura kafin ki rama,
Kusan hour biyu suka kwashe kafin su shirya cikin wata atanfa blue da ratsin fari an fitar musu da dinki na zamani riga da sket ya zauna dam a jikinsu RAHAMA kamar hips dinta da kirjin zasuyi magana saboda kayan cif jikinta ne, domin kowa yasan gwani fashion style sokoto wajen cire dinki,
Suka murza dauri tareda baza kamshi mai taushi da class, plat shoe suka dauka iri daya da jakar shi suka fito Rahama After dress milk ta dora mai fadin hannu taji stones kana gani kasan bakaramin kudi bace a wurin,
Dakin momy suka leka tace "sai yanzu mashiririta? Karfe daya tsakiyar rana zaku fita? To ko karkuyi dare dadyn ku na gari yau kun sani yana shigowa zai fara tanbaya hardai ke RAHAMA,
"Bazamu dade ba momy insha Allahu hour biyu sun ishe mu a gidan karfe hudu zamu dawo,
"Toh Allah yasa ga wannan ku kaima larai, ta mika musu katuwar leda mai dauke da turarukan wuta mayuka da kuma sabulai Y'an kasar waje,
Sukayi godiya suka fita,
Ni kaina mamakin wayewar RAHAMA nakeyi a yanzu,
Gata da saurin daukar Abu domin ko tukin mota kamar da wasa ta fara koya a wurin Husna kuma dayake mafi yawanci motocin Auto ne batasha wahalar iya tukasu ba,
Yauma ita ta tukasu har mabera,
Tundaga kofar gidan su tafara sakin Baki tana mamakin yanda ya zama morthern wato yasha gyara ta ko ina,
Husna taja gyalen da ta yafa tace "kunya nakeji zanga mother inlow, kuma baby na nan fa a gari, tafada tana dariyar shakiyanci,
Wani irin kallo RAHAMA ta bita dashi tace " kijira ni a mota to ai dama saboda kiganshi ne kika nace zaki biyoni, "wallahi ki rage sonshi karyazo yana ja miki Aji, "ba ruwanki ai shi ba irin ya Al Ameen bane,
Ledar Husna ta dauka suka fito motar daidai yaya Aliyu na fitowa zaije masallaci ya gansu, wani irin murmushi yayi mai kayatarwa na jin dadi, ganin RAHAMA ta zama classic RAHAMA ga kuma love of his life, Husna, sunfito kamar wasu taurari Rahama bazaka taba cewa kwalin secondary ne da itaba saboda wayewa da Ajin da ta hau saboda rayuwa da wayyun mutane datakeyi yanzu,
Cuna baki tayi kamar wata small baby ta ce "nidai banganka ba yaya, "ni Naganki lovely sister, and my baby yafada yana kallon Husna da wani irin kallo mai cikeda sakonnin soyayya, RAHAMA dai shigewa tayi tabarsu a wajen,
Da gudunta ta shiga gidan tana "Salamu Alaikum ina kike Inna ta? Cikeda zumudi da kewar ta tana tsugune bakin fanfo tana Alwala tace "gani nan Y'ar Albarka ai tunda naji zakizo tundazu nake kallon hanya,
Idarwa tayi sukayi cikin dakin ta rike hannun ta tamau kamar zata gudu, "tace to cikani inyi salla ko sai mu gaisa,
Toh tace tareda fitowa tana kallon ko ina na, tsakar gidan tasan yanzu baba na shago ta kalli kofar dakin su da shima angyara, ta taka a hankali ta nufi dakin taji muryar HAJARA na waya, da sallama ta shiga, ko dago kai batayi ba taci gaba da wayar ta saida ta zauna a gefe bayan ta ture kayan HAJARA dake tule ko ina na dakin, tace yaya HAJARA " juyowa tayi a yatsine, saidai gabanta ya mugun fadi da ganin yanda RAHAMA ta canja tayi cika tayi fresh fatarta na sheki da kyalli dama kuma Allah ya hore mata laushin fata dama, don haka yanzu da ta samu daula komai ya Kara canjawa, tashi tayi dakyau ta kalleta, "ke da mijin ki baya gari kikayi irin wannan canjawa? Tafada kamar wadda taga kashi, shareta tayi "yaya ya kike, "kalau yanda kika ganni ko kinga ina ciwo ne ko kina tunanin ina cikin wahala ne ke kina cikin daula? Toh ba haka bane gani garau kamar kullum HAJARA dai kika sani itace dai, don haka inkin gama munafuncin fitar min a daki banza,
Mikewa tayi kawai domin ba Abinda tazoyi kenan ba, kuma mugun hali bazata taba nuna ma Y'ar uwar ta shiba saidai cin kashin da ta mata a baya bazata daukeshi yanzu ba,
Har takai bakin kofa ta tsaya, "yaya HAJARA kenan ai ni kullum fatan Alkhairi ni nake miki ba sharri ba domin koma Meke tsakanin mu bazai shafi zumuncin mu ba don haka ina farin ciki tunda kina cikin koshin lafiya, ta juya tafita,
A can daki kuwa inna ta idar ta har Husna ta shigo itada Aliyu sungaisa ya kuma janyeta waje, RAHAMA ta zauna sukasha hirar bayan saduwa tareda tanbayar HAJARA fa yanzu? Inna tace "ai rayuwar Y'ar uwar ki sai du'a'i RAHAMA yarinya kamar shedan in anbullo nan ta fisge can akwai wani yaro yafito yana sonta wulakancin yau daban na gobe daban
Tana nan kamar likin fasashshiyar roba kullum aka like wani wuri wani wurin ne zai kuma bulewa Allah dai ya kyauta,
Haka suka sha hirar su sukaci lafiyayyan girkin inna sukayi kat la'asr nayi RAHAMA tace zasu tafi domin Dady zai dawo gidan yaga basa nan,
Inna ta kawo musu kayan gargajiya irin su kuka kubewa daddawar kauye da dakakkken kulin moya tabasu su kaiwa momy tareda godiyar Abinda suka kawo mata, Husna kamar karta tafi takeji
Saboda rayuwar gidan su RAHAMA simple tayi matukar burgeta don haka taji ta Kara son Aliyu da kuma muradin Auren shi,
Duk da sun samu zakka a gidan nasu Amma bata dsmuba itadai tana son Auren Aliyu koda baida Arzikin gidansu tasan zasu wadata domin yana karbar Albashin shi mai tsoka tunda yana aikin banki,
Sunji dadin ziyarar duk da Rahama taso taga baba Amma harta fito basu hadu ba saidai ta kirashi a waya suka gaisa, Aliyu kuwa saida yaga tafiyar su ya fita gidan suna likeda Husna tun zuwan su,