← Book details Zanyi Biyayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 60

Sashe 11

Zanyi Biyayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A falon ta kasa daurewa suna shiga ta fisge hannun ta tareda, cewa "ke banza ki Amsani gidan nan NA uban waye, tafara Zaro idanun ta duka waje ta matsu bataji Amsar taba wanda yayi daidai da fitowar Al Ameen daga dakin shi daman he want to see if she is ok don ya dade bai gantaba, yaga fuskar HAJARA dake facing dinshi and he no she is that annoying girl dake bibiyar shi, "what is she doing here, ganin yanda take ma RAHAMA masifa yasa yaja ya tsaya inda sam basa ganin shi,

Cikin Hajara bai kada ba saida ta hango tangamemen hoton Al Ameen dake manne a karshen falon yana miskilin murmushi a jikin Paris high tower 🗼 ta dafe kirji bakinta na rawa ta ce "shi sh sh shsh ne mijin ki???? Kallon hoton RAHAMA tayi tareda dauke kanta domin sam bata kallon hoton sau biyu saboda kwarjinin da yakeda shi ko a hoto, tace "muzauna yaya HAJARA, " bazan zauna ba don ubanki Kifada min shine mijin ki?
Gyada mata kai tayi tareda cewa " eh shine mai gidan,

"Kutumar uban can shine baki fadamin ba kafin adaura Aure Amma RAHAMA bakya kaunata namijin da nake kwakwar so saboda shi na guji Auren hadin da baba yamun nabar gida yanzu you are telling me shi ne mijin Aurenki, I hate you RAHAMA you are not my sister yanzu namijin da nake ra ayin Aure kika Aura,
Magan ganun ta sun sosa mata zuciya sosai tace dakata Yaya HAJARA, cikin muryar ta mai sanyi tace " me yasa zakiyi min haka, bayan ke kika ja komai kece sanadin komai me yasa kika kiyiwa baba BIYAYYA lokacin da yake rokon da ki karbi Auren nan meyasa kika zabi ki tozartasu kibar gida saboda Auren nan, sanadinki Aka gutsure min karatuna aka kawoni nan gidan kinsani Am not ready to get marry, bayan guduwar ki baba ya mayarda Auren a kaina wanda kinsani banason Auren bana son mijin, bana bukatar duk wainnan Abubuwan kinfi kowa sanin halina Amma yanzu you are blaming me Aunty HAJARA why,

"Idan har da gaske kikeyi bakyason Auren leave this house ki barmin A yabo shine zabin zuciya ta I love him so much bazan iya rayuwa Bashi ba don't take my happiness away My sister,
Tafada tana rungume ta, wani irin mugun tausayi taji ta bata, ta fara bubbuga bayan ta, "am sorry yaya HAJARA nayiwa su baba Alkawarin komai wuya zanyi BIYAYYA bazan iya watsa musu kasa a idoba, tureta tayi ta tafi luuuu zata zube tajita fada a jikin mutum,
Wanda ya gaji da jin magan ganun HAJARA da kuma kalma mafi muni itace nima banason Auren banason mijin, shine ake wa wannan hayaniyar she suke rejecting ita har tana barin gida And now she is following him, dole ya saita ta kuwa shi A yabo,

A zabure ta gyara tsayuwar ta tareda kokarin barin jikin shi cikin Sauri domin ta gama gano komai, ya rike tafin hannun ta da yakejin shi kamar kad'a mugun karfin hali yayi ba karamin namijin kokari yayi ba lokacin da ta fado kirjin shi da bai tsaya da kyauba yanda yaji wani irin shocked da sun zube, a karkace yake kallon ta tana sanye da hijab din like always, saidai she look pretty,

"A yabo HAJARA tafada jiki na rawa ganin sam kamar baiganta ba ya kwakume Hannun RAHAMA yana bata wani irin kallo masu ma'anoni, "why are you like this? You are too cool you are good heated, you obedient, you are religious, karshe kuma she is wonderful,
RAHAMA dai a mugun tsorace take domin fargabar ta ta farko shine kar yaji magan ganun su, secondly the result,
"Are you Alright wife? Ya tanbayeta cikin wani irin salon murya tareda Kara matsowa jikin ta, batareda ya rungume taba, duk ta rude "please take care of yourself for me karkijamin Asara you no you are pregnant with my baby right? Gaskiya am happy sati biyu har doctor ya gano Ajiyar dake cikin ki, I must give you something as gift, wace kalar mota kikeso in canja miki wadda aka kai a lefe is too small for my wife, and aikin gidan nan NA hana dole kibari a kawo house girl banson ki wahala "or zandauke ki muje Paris kihut...... A yabo, HAJARA ta buga mai tsawar da saida RAHAMA ta boye bayan shi,
"Cin fuskar yayi yawa basai ka fadamin ka tale kanwata ta kwanta da itaba I can see everything kaga karamar yarinya dole ka cuceta ke kuma dakikiya jaka kinsake wannan turmusheshen ya na danneki wawuya mara wayau, and kisani sai kinyi kuka tunda kika boyemin gaskiya, yanzu kika gama fadamin bakyason shi Amma jiki munafuka kin makale a jikin shi a gabana,

Kuka Mai cin zuciya RAHAMA tasa domin tozarcin da HAJARA keyimata a gaban Al Ameen wanda ya nade hannu a kirji yana wani irin murmushin mugunta saida HAJARA tayi shiru yace "am sorry yayar mu banganki bane sannu da zuwa "sweetie kin bata drinks kuwa? nuna mata gidanki yakamata kiyi kizagaya da ita taga cikin gidanki,

A fusace ta hankade RAHAMA ta wuce fuuuu tana kuka ko zama batayi ba a gidan, RAHAMA data kusa kifewa taji ya fisgota domin All this while bai saki tafin hannun taba HAJARA na fita ya tureta tareda bata fuskar shi, yanajin wani radadi duk shirmen HAJARA bai dameshi ba what hurt him is that tana fadar bata son mijin da take Aure,

"So you are rejecting me a gaban yayar ki ni Al Ameen kike cewa you don't want to be with me, really? Who the you think of yourself, yafada yana buga mata tsawa, "how could you, how dere you reject me, yafada har jikin shi na rawa, ya dunkule hannu tareda naushin iska,
"Oh kema wani kika hango like your sister wanda yafini ko shiyasa kikeda gut ki bude baki kice wai ke bakyason mijin da kike Aure,

Cikin karaji yake Maganar kamar zai tashi sama idanun shi sunyi mugun ja his heart is burning deep down, shi ne aka jewa neman Aure har ake gudun shi, and the second one itama she don't like him, "ni Al Ameen Shuaibu Yabo kike rejecting nida mata kebibiya suna neman ko friendship muyi dasu Amma bana kula su you got me free of charge as your husband amma kina fada ma wata dakikiya wai bakyason Aure na, ni banyi rejecting dinki ba kece zakiyi rejecting dina, yafada yana matsawa gaban ta kamar zai mareta,

Saurin ja baya tayi a tsorace jikinta na rawa ga tsoron shi ga kunyar Abinda HAJARA tayi mata a gaban shi, wani irin kallo kawai yake binta dashi ganin hawayen dake zarya a kumatun ta duk tabi ta kankame jikinta saboda firgita da lamarin shi gani take kamar zai hadiyeta,
Bazama ta iya cewa komai ba, to me zama tace, sai kuka kawai,
Wanda yake shakar dashi domin zaiso ta karyata Kalmar batason Auren shi yaji Amma she is not going to talk don haka ya buga mata tsawa " if you are not going to say anything leave, kafin inyi kwallo dake,
Ai kuwa da gudu tayi dakinta, wanda he can see how her body is shacking,

Zarya yakeyi a cikin falon zuciyar shi NA Azal zalar shi, wanda yarasa dalili da ya kasa sukuni he don't care about that crazy and lunatic girl, he is worried deep down, wanda baisan me yake tunani ba, don haka ya zura key kawai yabar gidan,
Gidan su ya nufa kai tsaye, momyn shi ya samu zaune a falon tana duba wasu kayan siyar warta da aka kawo mata samples tagani a gida, Husna na tayata,
Ko sallama shi kadai yaji kayar shi,, zama yayi gefen momy tareda riko hannun Husna, kana ganin shi kasan yana cikin damuwa da kuma takaici,

"Kai lafiyarka zaka shigo min gida ba sallama? "Nayi momy, ina wuni, "lafiya, ta Amsa tareda cigaba da aikin ta, Husna tace "yadai my lovely brother? "Baby me mace take nufi intace she don't like her marriage? What was that means,
Kai tsaye batareda tunanin komai ba tace "that's means she don't love the husband at all,
Zabura yayi ya zauna kamar wanda aka watsawa barkono yace, "koda mijin irina ne? "Yeah ra ayi riga ne ai yaya daina ganin mata na binka akwai wadda sam baka gabanta ma,
Kalmar ta cimai tuwo Akwarya tamai zafi ta cakeshi idanun shi kamar wuta, ya kalli momy " wai don Allah meye dalilin daura min Aure da wadda bazata soni ba meye Amfanin Auren hadin, da Anbarni na nemi love da kaina da yafimin leaving with the person who don't care about you is unfair, wani irin mugun kallo momy ta watsa mai kafin ta bude bakinta tace " don't worry zanyi maka maganin matsalar ka baban ka kawai nake jira kuma insha Allahu Jibi zai dawo komai zai dawo normal,
"Momy wane magani zakiyi bayan is too late kunriga kun kakaba min Auren da ban shirya ba wallahi an takuramin rayuwa da zuciya kawai an hanani sakewa a cikin gidana,
"Kashh ka rage gajen hakuri zanyi maka naganin Abun tashi kaje indaina ganin ka,

Husna ya kalla" muje gidana sister please, yafada duk yayi wani irin sanyi,
"Ba inda zaka kaimin yarinya, "please momy ina bukatar ganin tane a gidana kibari muje don Allah, "kasan Allah katafi kawai Amma ba inda ya' ta zataje,
Mikewa yayi tareda cewa shikenan natafi'
"A sauka lafiya, inji momy,
Ya fita kawai, duk jikinshi ba kwari,

****************************
HAJARA da kuka ta shiga gidan lokacin baba ya shigo da kayan miya zai fita, tundaga farkon shigowar ta kurma ihun da saida inna ta fito daga daki da zani a hannu, tana Allah ya jisheni Alkhairi me yasamu ya' tagari, domin duk tunanin ta tasamu RAHAMA cikin mawuyacin haline shiyasa take kuka,
Burgima ta fara yi tana wayyo Allah ba a kauna ta ba a sona agidan nan,
An muna funceni,
Muciya inna ta dakko a kitchen mukekiya tace "yi min shiru ko in ji miki rauni don kinga ba yayanku a gida shine kike mana zanbarwar bori a gida ko, uban me akayi miki,
Chapter 11 · 0% Book details