← Book details Zanyi Biyayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 60

Sashe 35

Zanyi Biyayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ranar kuwa da ya kammala medication dinshi ta yabawa aya zaki, domin yanzu tasan waye shi duk da marar ta na yawan ciwo bai raga mata,
Yau ma suna kwance ya gama abinda yafi so ya nannade ta tamau a jikin shi yana maida numfashi, yace " hmm baby Ashe da rayuwa kawai nakeyi a duhun kai da cutuwa "Alhmdulillah ba Abinda yakai rayuwar miji da mata dad'i, wallahi ji naki dama duk rayuwa ta ta baya ace tare dake nayi ta da nafi kowa morewa,
D'an tura baki tayi kadan na gajiya, "ai nidai yanzu a daga min kafa yau da dare,
Kodan babyn ka please, "wayau zaki min ko a hadani da yaro na aa naki wayon yarona ma yanaso in more, do you no yanda nake jinki yanzu? Wallahi kamar wani kogin zuma ne nake linkaya a ciki,
Kinada wani irin gardi da baki bazai iya furtawa ba baby, kodai harda baby na yasa nake jin ki kullum kamar ana kara miki d'an dano,
Kunya maganar shi tasa taji ta yi saurin cusa kanta cikin kirjinshi,
Yayi dariya tareda rada mata wata magana a kunne,
Saurin dukan kirjin shi tayi cikin shagwaba, haka dai suka ci gaba da more rayuwar su tareda kuma renon cikin su, wanda bayan ya gama ganin likita suka fara yawon ganin kasar state daban daban sun zagaya a India, wanda RAHAMA ta kara bude ido tareda waye wa,
Idan kaganta kamar ka taba jini ya fito tsabar hutu da jin dadi ga kudi Al Ameen ya sake mata komai jidowa takeyi saboda tsaraba kullum tanaji daga Husna da kuma yaya HAJARA, wanda tayi musu siyayya sosai a India irin kayan su, daga nan Makka suka wuce domin yin umara,
Wanda da yafada mata zasuje harda kukan ta,

Lokacin da ta tsinci kanta a bakin dakin Allah kuwa tuni ta manta komai ta rungumi ibada duk da tana jin kasalar kar fafa jikin ta tayi ta maida hankalin ta wurin bauta da neman dacewa duniya da lahira,
Wanda Al Ameen ma ya jinjinawa kokarin ta wajen ibada, duk kasalar ta bata wasa da lokacin sallah,
Bare yanzu da ta ganta gaban Alkibilar ai sai godiya, Al Ameen yaga farin cikin ta sosai lokacin da suka isa kasar mai tsarki wanda shima abin ya mai dadi har yana cewa da nasan zakiyi irin wannan murna tuntuni da munzo, Amma Karki damu idan kin sauka lafiya zamuzo muyi aikin hajji,
Tayi godiya sosai tareda yimai Addu'a mai yawa da kuma fatan Allah ya sauke ta lafiya,
Daga makka ya wuce da ita China domin wasu harkokin su na shigo da kaya wanda nan ma sun kusan kwashe wata biyu domin har cikin ta yafara fitowa wanda Al Ameen ya dauki son duniya ya dorawa, momy kullum sai ta kirasu sama da uku domin jin lafiyar ta tana kara jadda da mata ta kula da kanta,

Wasa wasa saida suka kwashe wata shida cur suna zagaye kasa she saida momy ta fara fada su dawo haka ya ishe su, shi kuwa ba komai yakewa ba sai zancen kar azo ana rike mai mata shiyasa yafison haka kullum suna like duk wani business dinshi ma a online yake komai Abinka da zamani,
RAHAMA tayi wani irin cika da kuma budewa ga kyau da jindadi kamar ba Y'ar kauyen RAHAMA ba,
Tundaga jikinta suturan ta zakasan matar wani ce domin ta taka matakin ci gaba a rayuwa Kala Kala,

********************
HAJARA ta saba sosai a rayuwar gidan mijin ta, yanzu kokarin take ta gyara mai yanayin rayuwar shi yasan yanda zasu inganta zaman su wanda ta samu shawara daga FENERH tafara dora shi akan hanya yanda zasuji dadin Auren su wanda tuni yafara hawa kan layi,
Bata sa damuwar komai a zuciyar ta ba wanda take ganin Amfanin BIYAYYA don da ta bijire da tana cikin bakin ciki kila a yanzu, amma da tayi hakuri yau gashi tana zaune da kowa cikin mutunci bata rasa komai ba domin irin kula da kuma ingan ta rayuwar Bello da takeyi tuni yasa ya sakar mata ragamar komai nashi har ma da kudin da yake samu kullum yakan iya damka mata domin Ajiye, kuma duk Abinda takeso dai dai iyawar shi yanayi,

Yau a zaune take tsakar gidan suna hira a tsakanin su uku wanda sanadin ta, zaman gidan ya gyaru sosai ba kamar farkon zuwan taba da ba wani zaman fahimta, yanzu kuwa sun gane kansu suna zaman fahimtar juna,

Sallamar Su Ladidi ne da wata kawarta irin ta Y'ar duniya yasa ta dago daga kitson da takewa kanwar bello,
Suka shigo suna yatsina fuska da baki, d'an sakin fuska tayi ta musu barka da zuwa, suka gaida surukan ta dake wurin a dage kafin ta mike ta musu iso cikin dakin ta,

Ganin yanda HAJARA ta murje ba wani damuwa a tare da ita ya mugun sosa ran ladidi, jikin ta bai Kara yin sanyi ba saida ta shiga dakin taga irin kayan da ke ciki,
Cikeda kyashi da rashin jin dadi tace " tab HAJARA kin fado wallahi zama cikin gidan gandu irin wannan gaskiya wallahi dai tom nayi shiru,
Tafada bayan ta zauna, tana kallon KO ina, dariya HAJARA tayi ta takaici,
"Hmmm Ladidi ai ni a yanzu rayuwa ta jin ta nake kamar ina gidan sarauta domin ba duk mace ke samun baiwar samun mijin ba ma bare gidan gandun wata ma a gantali da kokarin tarwatsa rayuwar mutane zata kare. .......... 🖊

* akwai mata da yawa dake ganin bazasu iya gyara rayuwar mazajen su ba yanda suke son su kasan ce, Y'ar uwa fito ki koya wa mijin ki halin da idan bake ba sai rijiya kawai idan bakya duniyar shi duk zai damu don haka mata kufito ku gyara gidajen ku ku Gina shi da rodi ba ginin kasa ba kifito ki fafata a rayuwar Auren ki ta wayayyar hanya ba wai ta bin Boka damalam ba, Y'ar uwa kissa, tafi Magani *

*Matar soja*
2/28/21, 6:17 PM - Q: 🌻🌻
*ZANYI BIYAYYA*
🌻🌻

*By FENERH*

*ga masu bukatar biya ku hanzarta kar Abaku labari ku biya ku karanta cikin Aminci,katin Airtel 200 zaku turo normal vip 500 kuturo katin ku ta wannan numbar 09011251444 ko ta Asusun banki na 7304736012 nafisa sani Fcmb don Allah vip Kudaina turomin kati idan kana son vip kutura min ta banki katin nayimin yawa sosai in bakuda Account kibayar a pos don Allah sucire charges dinsu a ciki, Y'an Niger 🇳🇪 masu bukatar biya ku nemi wanna number +225 48 15 39 03*

4⃣9⃣&5⃣0⃣

Wani irin uwar Ashar ta lailayo, " ke banza mara wayau dakikiya, ni zakiyi wa gorin Aure? Wallahi ki zauna ki zuba ido zakiga mijin ladidi, "a ina zai zo? Ai da zaizo da tuni kina dakin miji domin nasan yanzu haka kishi kike da wannan gidan ma da nake ciki,
Sannan rashin wayau da kike kirana dashi da dakikan ci Alhmdulillah da kam banda wayau yanzu kuwa ko beran birni sai ya barni, to yama bazanyi wayau ba nayi rayuwa dake Ladidi inbanyi hankali ba sai yaushe,
"Nasani kinyi min fanfo da yawa na shiga ruwan yanzu kuwa na dawo daga rakiyar kawa irin ki mai bakin cikin da mugun nufi, saboda ke har kuka iyaye na sunyi, Allah yasa iyaye na mutanen kirki ne da sunyi min mugun baki irin naki da yanzu ina nan ina bin kawa irin ki,
Alhmdulillah ala kulli halim, rayuwa ta tayi kyau yanzu ko banza iyaye na sun yafe min Amma kefa? Har yanzu kina yawo ne da tsinuwar uwa da uba da kuma Al ummar gari,

Kije ki natsu ki gani ko gidan gandun ki samu ki labe irin nawa don nasan yanzu ma ba haka kika so ki ganni ba, bellon da kika nunawa wayau kika turashi gidan mu da motocin gyara kullum saboda yaja ra ayina ya fayyace min komai saboda yana min son fisabillahi, don haka yanzu dai bakida ciniki a nan ki tari wani sarki,

"Amma ki sani Ladidi bazan yafe miki tsanar da kika cusa min ta kanwata gudan jini na mai yim biyayyar iyaye, ga kuma hangen nesa duk Abinda nayi mata ko ince kika sani nayi mata bata taba mayar min da martani ba ko ta raba sharri akan sharri, yanzu fa tana ina? Taci gaba nima yanzu ina karkashin inuwar Aure ina cin Albarkacin wa innan igiyoyi masu matukar daraja guda uku,

Ta shafa cikin ta sannan mai yafi komai dadi sama da samun rabo, ina dauke da gudan jini NA a marata wanda duk uwa ke Addu'ar samu,

Shekewa da dariya ladidi tayi "badai haka rai yasoba HAJARA a kare a, gidan gandu to bari kiji da dai in shigo gida irin wannan gwara mutuwa a budurwa...... "Wait kice gwara mutuwa a bazawarar kan titi domin ke ba budurwa bace, ina sane da duk yawon ta zubar da kike yi, ni Allah ya kare ni duk rawar kaina zuciya ta bata taba hango min fasikan ci ba, ki rike wannan, indai iyaye nagari ne to ko Allah na tsare musu mutuncin ya'yan su a duk inda suka shiga, zina Y'ar aike ce waya sani ko tsoho yayi ne shiyasa duk kuke bin titi,,

Zaburowa tayi zatayi cikin ta, " akul tadaga mata hannu, tabani kamar kin kai kanki ne yanzu min rataye batareda hukunci ba, domin rai biyu ne a nan, nida d'an baba,
Chapter 35 · 0% Book details