← Book details Zanyi Biyayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 60

Sashe 60

Zanyi Biyayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read

Haka akayi washe gari yadawo da wuri sukaje gidan su momy harda gidajen kannin ta duk ta zagaya ta Kara musu dabaru tareda Kara musu haske kafin ta tafi gidan maman ta can ma itama ta Kara mata nata nasihohin inda tace tayi koyi da halayen zaman Auren su ba fada ba yaji, nan ma tasamu karin kayan harka kafin su koma gidan su RAHAMA, ita daki tasata ta mata Nasiha sosai, kafin taje dakin Grandma da suka hanata komawa gidanta sunce tadawo kenan ba inda zata koma, suna zaune suna zuba hirar su harda Al Ameen, suka zauna gidan har karfe tara kafin su tattara suyi gidan su,

Dakin su suka koma RAHAMA da Al Ameen bayan sun salami grandma, tasa musu Albarka zuciyar ta fess meya fi wannan dadi a zuri'a kaga bakada wani baragurbi itakam tayi zufan Arziki,

Rungume RAHAMA Al Ameen yayi tareda cewa "madam kinkusa zama grandma kema very soon domin nasan yarona jarumi ne kina ganin har wani sheki yakeyi, dariya tayi " badole ba yasamu yata yanata murza,
"Zomuje nima in murji mamanta da bata tsufa, yafada yana fisgota zuwa gado,
Binsu naso inyi ya dago kai yace " toh Hajiya fenerh kije tsegumin ki ya isa haka kinbimu kinbi ya'yan mu shiyasa bazan baki kujerar hajjin ba saboda kin cika jin kwakwab da tsegumi,....... .🖊

"Bakomai lokacine ai Al Ameen idan Allah yakirani sai naje don haka a nan nake cewa Tammat bihamdillah, godiya ga sarki Allah mai kowa mai komai da ya kawoni karshen wannan labarin
Ina rokon Allah ya sa a Amfana da duk Wani Abun da yake na karuwa a cikin shi sharrin dake ciki Allah ya gafartamin
Godiya mara adadi ga my but groups normal and my very best special people wato vip Allah yasaka muku da Alkhairi da kauna da soyayyar ku agareni yasa idan na kasa kuke saya Alkhairin Allah ya kaiwa duk masoyana na duniya tundaga kasar mu har ma wainda suke ketare,

*Sai kun Kuma jina a cikin sabon littafina mai suna MUK'ADDARI(Auren soja) that' is another Army love story kunsan inda mutum yake kullum bai rasa ganin sababbin Abubuwan da zai rubuta zakuji dadin labarin fiyeda bariki Auren soja Akwai ilmantar wa akwai fadakawar wa akwai Kuma soyayya mai taba zuciya don haka sai kunjini*

Takuce dai

*Matar Soja*
Chapter 60 · 0% Book details