← Book details Zanyi Biyayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 60

Sashe 4

Zanyi Biyayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kiran babanta yasa ta fito cikeda nishadi, ta zauna, "yauwa Y'ar baba dama zancen Auren ki ne da d'an gidan Alhaji ina muka kwana? Tuni ta gimtse tareda cewa "wallahi baba nidai banaso Kudaina ma zancen nan haka kawai ni bazan Auri naka sasshe ba,
Cikin zafi Aliyu dake gefe yace "ke wai saboda kinga Ana lallashin ki kike iskanci ko to Wallahi ba wanda zai kuma lallaba ki a gidan nan ko kinki ko kin so sai andaura miki Aure in yaso ki mutu wawuya kawai,
"Bita a a hankali Ali, "Hajara Allah yagani nabaki hakkin ki na lallasheki nabiki duk yanda kikeso inbiki don haka yanzu lokaci yayi da nakeso in nuna miki ni ne mahaifinki na kuma isa dake, don haka daga yau kifara lisaafi sati na sama za a daura miki Aure, ki shirya ki cire komai a zuciyar ki,
Hakkin ki ne nariga na sauke shi Hajara da a ce yau kinada wani tsayayye ne da zan baki dama Amma bakida kowa don haka kiyi BIYAYYA zakici ribar Abin zakiyi Alfahari kinji,

Kuka ta kwantsama tareda tashi tayi daki, RAHAMA dake zaune taji sam zuciyar ta ba dadi sam baban su bai can canci butulci daga garesu ba ubane daya tamkar da dubu, tashi tayi ta nufi dakin nasu domin lallashin Yayar tata,
Tasameta ta sakawa wayar ta idanu itafa kawai Auren ne bata shirya ba ko shi wannan gayen kawai if possible suyi friendship ya isa kawai ya tsaya as her friend, don yanada kyau but he didn't deserve her,
Ita har yanzu mijinta bai isoba,

Zama RAHAMA tayi gefen ta ta riko hannun ta "yaya don girman Allah ki yi BIYAYYA zakici riba zabin iyaye shine zabin Allah nasani is painful I can understand your pain Auren wanda Bakaso baka sanshi ba and for that reason ma baida lafiya all is something Amma ki yarda iyayen mu kullum cigaban mu sukeso ba zasu tabo son mu fadi ba, bale ke kinsan baba na sonki sosai kullum yana kokarin faran tamiki ne domin yaga ya cika miki burinki, don Allah yaya kiyi hakuri,

"Wallahi baya sona tunda zai mun Auren dole, look at me Please ni za a hada da nakasashshe wallahi baya sona yafi sonki ke meyasa bazai Aura mai keba, ni Aurena wallahi Akwati sai ankawo dozen so nake a san zanyi Aure a Unguwar nan so nake masu ganin bazan taba samun mijin da nakeso ba inyi proving dinsu wrong, amma hakan bazai samuba baby sai na hada degree lokacin zan iya shiga villa ba,
"Yaya ki dauki komai da sauki king..... Yi shiru don Allah banza bagidajiyar kauye kibari ki shiga jami'a kigasan dadin duniya har yanzu kanki na cikin duhu, you don't know anything,

Wani haushin yayar tata taji, kullum kallon Y'ar kauye take mata tana mata kallon bagidajiya, bude baki tayi tace " gwara dai ki natsu Aure ba fashi tunda baba ya fito ya ce kinsan bazai taba canjawa ba, kuma in Allah yaso nima sai nayi karatu irin naku kafin inyi Auren, wayewa irin taki ta karya bana sonta, tafada tana gyara kwanciyar ta tareda janyo hisnul Muslim dinta tafara dubawa,

Kallon zanci ubanki ta bata, " zamuga wanda za a Aurawa wani banza a gidan nan ai. Bata kuma tanka mataba, don tasan inta Kara zata iya gwabzar ta,

*************

Shiri akeyi sosai domin malam bala ya Tara kudi harda adashi ya shiga domin yima Y'ar shi gata daidai karfin shi, inna kuwa tayi iya yimta domin ganin tafara gyarata Amma taki yarda kallon su kawai takeyi, RAHAMA dai bata Y'ar da da takunta ba domin tasan she is up to something shiyasa tadaina gardama da kuka Amma tasan bazata iya mata magana ba,
Yau tunfitar ta school shiru tun safe har la'asar ba labari gashi saura kwana hudu Auren ta, wanda tanajin jiya suna zancen kawo kayan lefe don haka sam bazata tsaya tasha kunya ba, in banda su matsiyata ne ace kayan Aure har saura kwana hudu sunkasa kawo kaya wannan yakara tabbatar mata da gagaruman matsiyata ne su basu jika a kudi ba,
Shiyasa ta shirya ta dinga kwasar kayan ta daya daya tana fita dasu saida ta kwashi Kala kusan Biyar, daman ta shirya bazata dawo gidan ba sai Anfasa Auren,

Wasa wasa har dare ba labarinta tun hankalin su inna bai tashi ba har ya fara tashi Aliyu yaje school din su sau biyu yau ance bataje ba, yaga babbar kawar ta ma ya tanbaye ta tace bata ganta ba, bayan tare suka shirya komai ta na boye a hostel din school dakin kawar tata,
Da aka fadawa baba kuwa tashin hankalin da ya shiga ba acewa komai zubewa yayi yana jan numfashi sama sama saboda tashin hankali,
Gashi ta kashe wayar ta,
Ranar sam basuyi bacci ba a gidan,

Gashi ankawo akwatuna saiti uku kowanne fadin dukiyar dake ciki bata bakine harda makullin Camry new morthen, Alhaji shuaibu da kanshi ya kai akwatunan domin bayason Y'an Uwan shi su ga inda zaiyiwa d'an shi Aure suzo suna jininita maganar, don haka yace shi zai kai kayan,
Domin yasan halin kannen shi mata sam basa son talaka musamman wadda ke Auren sultan of sokoto, tsabar tashin hankalin da suke ciki kota kan kayan basubi ba ranar, malam bala yayi kuka har yaba uku lada, RAHAMA ma kuka take tayi ganin iyayen su na kukan tozarcin da Y'ar uwar ta tayi musu Aure saura kwana hudu ta gudu me take nufi da wannan cin zarafin da tawa mahaifin su,

Gaba daya ya rasa ta inda zai bullowa lamarin washe gari ma haka suka tashi Aliyu ya bazama duk inda yake Sa ran zai ganta bai ganta ba, haka ya dawo gidan, jiki a sanyaye tareda Alkawarin idon shi idon HAJARA sai ya illata ta tunda ta Kunsa musu bakin ciki ta kuma wahalar dasu,
Zaune suke tsakar gidan sunyi jugum inna duk idanun ta sun kunbura saboda kuka haka RAHAMA dake gefe duk jikinta ya yi sanyi ganin iyayen ta cikin tashin hankali,
Aliyu ne yayi karfin halin bude baki yafara magana, " baba ina ganin ka cirewa kanka damuwa HAJARA kanta ta cuta ba muba, ku cireta a zuciyar ku zata dawo duk inda taje zata dawo duniya ce ai,
"Aliyu me nayiwa Ummi da zata yimin irin wannan sakamakon tozarcin, mutanen nan basu kyamace muba mune zamu guje su, duk gatan da ummi keso nayi kokarin bata Amma sakayyar da zatayi min kenan?

Share hawaye yayi tareda kallon su yace "Larai ki zama shaida ta ko HAJARA ta dawo gidan nan bani bata najanye duk hidimata a kanta,
Kuka mai cin rai da kuma tausayin Y'ar uwar ta yasa ta saka kuka tareda riko hannun baban ta tana gunji " baba don girman Allah karka juya mata baya don Allah ka yafe mata baba karta lalace don Allah, tafada duk ta birkice, tareda tsantsar kaunar Y'ar uwar ta da kuma tausaya ma rayuwar da ta jefa kanta,

"RAHAMA, yakirata cikin muryar bada umarni tareda kuma tsantsar damuwa da mika komai ga ubangiji yace " zakiyi min BIYAYYA? Zaki yi biyayyr da Y'ar uwarki ta kasa yimin?
Zabura tayi ta fara girgiza kai tana dafe kanta, " baba karka yimin haka shekaruna shatakwas fa yanzu nake shiga ko secondary ban kammala ba inaso nima inyi zurfi baba don girman Allah baba na kabari inyi karatu irin wanda nake da burin yi,

Cikin tsawar da tsawon rayuwar su basu taba gani ko jin yayi irin taba yace " inkema bazakayi biyayyar ba kibi Y'ar uwarki, duk in sallama ku Alhmdulillah inada magaji a tare dani ko yau zan iya mai Aure ya haifamin jikokin da zasu shafe min ku a zuciya ta,

Kuka ta Kara tareda riko kafar shi tana girgiza kai " ZANYI BIYAYYA wallahi zanyi don Allah ka yafe mana wallahi nayi biyayya bazan watsa maka kasa a idoba, ta matsa jikin d'an uwanta ta rungume shi "yaya don girman Allah kaba baba hakuri na yarda karyayi fushi dani wallahi na karba ZANYI biyayya,
Wani irin hawayen tausayin Y'ar kanwar tashi ne yasa ya rungume ta tareda bubbuga bayanta kadan yace " relax Karki damu baba na Alfahari dake Rahama ke ta daban ce,

Inna ta taso tareda dagota ta rungume ta tace "Allah yawa rayuwar ki Albarka RAHAMA, zakiyi Alfahari kinji kiyi biyayya wata rana sai zakici ribar Abin, Ajiyar zuciya take saukewa saboda kuka ta zauna gefen baba domin ganin sam har yanzu baida walwala domin ji yake ajikin shi itama guduwar zatayi kamar Y'ar uwar ta, don haka ya mike ya fice Abinshi batareda yace musu komai ba,

"Hajara ta cuce mu ta cuci kanta tsawon zama na da mijina bai taba fushi bai karfi ba yau ta Kunsa mai takaicin da ko Y'ar uwar ta bazai yarda da itaba,
RAHAMA ki sharewa ubanki hawaye ki wanke mai zuciya ta hanyar karbar Auren nan,
Hawayen da keta gudu akan fuskar ta ta sharce duk da basa tsayawa ta, "Inna insha Allahu na karba kuma koda zan mutu bazan taba baku kunya ba duk yadda Rayuwar gidan Aure na take zanyi kokarin yin biyayya bazan taba yin Abinda zai zubar muku da mutunci ba,
Tafada tana fadawa jikin inna,
"Nasani RAHAMA ni na haifeku duka nasan tunfarko dake akace baza asamu akasi ba, Allah ya miki Albarka kinji,

Aliyu yayi dariya ya riko ta" come here my lovely sister, ya rungume ta cikeda tausayin his hardworking sister, Am proud of you my sister............ 🖊

*Matar Soja*
2/28/21, 6:17 PM - Q: 🌻🌻
*ZANYI BIYAYYA*
🌻🌻

*By FENERH*

*ga masu bukatar biya ku hanzarta kar Abaku labari ku biya ku karanta cikin Aminci, 200 ne normal vip 500 kuturo katin ku ta wannan numbar 09011251444ko ta Asusun banki na 7304736012nafisa sani Fcmb sai najiku*

*Aslm ina mata masu sana'oi ko kasuwanci dake bukatar Ayi muku tallar kayan ku ta yanda zaku samu customers online, to ku garzayo domin kasuwancin ku ya bunkasa zamu tallata muku Hajarku domin samun cigaban kasuwancin ku,hajar ku zata zagaya ko ina ta fadin Arewacin Nigeria har ma da kasashen makotan mu*
Chapter 4 · 0% Book details