← Book details Zanyi Biyayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 60

Sashe 42

Zanyi Biyayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tangamemen falon dauke yake da Y'an mata da samari kyawa wa su kusan bakwai maza Uku Y'an matasa mata guda hudu a kewaye suke da wata mata dattijuwa mai cikeda hutu da jin dadi idanun ta dauke da glass sai surutu suke zuba mata banda mutum daya datake gefe rikeda littafi tana karatu,

Dattijuwar ce tace " kunga ku tashi don Allah kuyi gidajen ku kubarni da meenal ita kadai ce zan iya zama da ita , ita rayuwar ta akwai dadin zama kamar ta gwaggon ta Rahama, Amma ku kunzo duk kun cikamin kunne da ihu, harda ku mazan da ba cefane, saidai kuzo Abinda ubanku ya siya ya Ajiye min ku cinye,

"Kai wallahi ku tashi mutafi kullum sai munsha gorin grandma a gidan nan saboda Kawai muna zuwa tayaki hira, dama munsani kinfi son yaya Sadiq miskili da baya bari mutun yasha ruwa ya Ajiye cup in yana nan,

"Ai wallahi banason gayen nan yadawo ya takuri rayuwar mutane gwara ma da yafara aiki kowa yasamu lafiya, cewar dayan, "ai kuma infada maka Dady mugun sonshi yakeyi sam baya laifi mune dai yanzu kaji dady na hakilo a kanmu,

"A kul na kumajin hakan , baban ku na sonku duka kar inkuma jin irin wannan, "dole akwaba muku saboda kuzama nagari nan gaba, don haka karku sa wani Abu a zuciyoyin ku, Sadiq da yanzu yakama aikin shi koda baya aiki ai da company shi da kakan ku ya mallaka mai tun yana raye kunga aikin da yakeyi saboda yana ra'ayi ne,

Kuma in kun dage kun kammala karatun ku zaku samu naku shear a wurin ubanku, don haka nidai kutashi kuyi gaba,
Y'an matan guda biyu ne sukace " kina korar mu grandma, bakomai zaki nemo mu ai kuma Aunty meenal baban ta bazai taba bari ta zauna a nan ba kinsani, don haka mudai mune dole kuma ki lallaba mu,

" in lallabawa kaina aiki dai kuda baku moruwa ita kuwa akwai son aiki da gyara ku sai shegiyar kuiya a wurin ku,
Zabura sukayi "ku mutafi mudai bazamu dawo ba daga yau, " kai tafi nono fari a sauka lafiya, komawa sukayi suka zauna, " mun fasa yanzu KO munkoma momy na Asibiti bakowa a gidan don Allah grandma ki koma gidan mu wai me kikeyi a nan ke kadai ko dai kina tuna mijinki matsoraci da ya gudu bai jiramu ba,

"Naji kuma zaku hanani tuna uban yaya nane? "Ya'yan guda nawa ne BIYU fa kacal, suka fada suna dariya, "Alhmdulillah gasu a yau sun cika min gida daku nan gaba kuma zaku zama one big family idan kukayi Aure, yau Al Ameen yaran shi Hudu Husna uku to me yafi wannan kuma zamu samu wasu karin a wurin ku zuri'a ta yi yawa da Albarka

Meenal ce ta mike tareda kallon su tace " nidai zan tafi gida Baba zai neme ni idan yadawo gida, Nasir muje ka sauke ni, grandma zantafi tafada tana saba gyale da jakar ta ta Y'an mata mai kyau Mai cycle

"Toh Amina ki gaida Hajara tunda ke bakya iya zama gidana, " aa wallahi baba ne ko family house baya bari muna kwana, " toh Badamuwa " nasir jeka sauke ta, tashi yayi yana jin dadi domin gaskiya yana son dama su jera akoda yaushe da ita yarinyar ce akwai kyau na fitar hankali gata fara tas irin uwar ta kirar ta kuwa ba a cewa komai, da biyu take yawan son zuwa gidan kakar su sadiq din,
Saboda tasan kullum yana zuwa gidan kuma Allah ya Dora mata mugun son yaya Sadiq din duk da bawani girman ta yayi ba impact yan watanni ne ma a tsakanin su,
Tariga tasan bazai taba sonta ba don ko kallo bata ishe shiba impact bata ma tunanin zai sota domin shi miskilancin shi har ya wuce gaban kwatance, Abubuwa da yawa sunsa tana shakkar shi domin yanada kudi sosai mahaifin shi nada kudi momyn shi babbar likitace a Asibitin Uduth dake sokoto ita kuma iyayen ta a kar kashin inuwar su suka ginu domin sunada labarin komai duk da akwai zumunci mai karfi a tsakanin s, tana kokarin goge wannan tunanin a kwakwal war kanta, tanada samari da yawa domin Allah ya bata farin jini Sosai saidai zuciyar ta naga Abubakar Sadiq da baisan tanayi ba,

Tana fara tafiya Nasir na bayanta, sukaji Sallamar shi cikin wata irin murya mai Amo da kuma taushi ga wani uban kamshi mai shegen tsada da kuma tafiya da hankalin Y'an mata, ya musu sallama, jitayi jinin jikinta ya tsaya cak take takasa motsa kafafun ta tafara shakar kamshin mai tafiya da imanin Y'an mata, dakyar ta iya bude kwayar idon ta ta sauke akan kyakkyawar fuskar shi dakuma surar jikinshi, zatasha workout,

A cikin kakin custom yake wanda kana gani Kasan ba wai karami bane yataki matsayi babba kuma mai girma ya hadu karshen haduwa gaba daya haibarshi da kwarjini shi sungama cika ko ina nafalon,
Kanshi ba hula hannun shi daure da Rolex watch ga wata katuwar tab a hannun shi kana ganin fuskar shi Kasan yarone d'anye sharab sai dai kudi da suka sa ya girma a idanun mutane don yataso cikin su,

Kasa motsawa tayi har saida nasir ya taba ta, " muje ko? Saurin dawowa tayi hayyacin ta tace" toh dakyar take iya daga kafar ta Allah yasani bata son ta tafi yanzu da yashigo Gashi yau taganshi cikin kaki bata taba ganin shi a cikin shigar ba sai taga kamar donshi a aka fito da kalar kakin, wani irin bugu kirjinta keyi saboda soyayayr shi, son Sadiq zai kasheta idan ba ayi wasa ba, gashi yayi kamar bai gantaba, don haka hartasa kafar ta zata fita tace wa nasir " am coming bari mugaisa kar yace bangaida shiba, " no kizo mu wuce kinsan halin shi zai iya gwaleki, " bari dai inzo tafada tana komawa, Wanda tuni duk sauran sun watse a falon dodo ya shigo,

Muryar ta na rawa ta karasa tareda cewa "ina wuni ya sadiq, dakyar ya daga halshe kamar wani sarki ko kallon ta baiyi ba yace lafiya,
Taji muryar shi kamar wata sarewa duk da bawata doguwar magana yayi ba Amma tasani tana mugun son jin maganar shi don har recording muryar shi tayi a wayar ta tana saurare idan tasamu kebewa ita kadai,

Tsawar da ya buga mata tadawo da ita, " uban me kikeyi anan please get lost zanyi magana da grandma dina, zabura tayi tayi waje da gudu tana dafe kirji, grandma ce ta kalle shi " meye haka Sadiq bana hanaka irin mugayen halin nan ba bakyau wulakanci fa kuma inba kaiba kaida Y'ar uwar ka kuma ma ai ba wani girman Aminar kayi ba wata baifi shida ba kaga ko ba wani son girma da zaka nuna mata,

"Wallahi ima mata kallon yarinya ce kamar su Aisha dasuke kanni na, "toh naji me kadawo yi yau kuma?
"Grandma dole indawo please kifadawa Dady Aure nakeso nama fara searching mata ina son Aure nan da karshen watan nan,

Wani irin kallo take aika mai, "ikon Allah shekarar ka Ashirin da hudu fa sadiq, "aa da Biyar fa grandma, kuma ai na isa Aure gani da business ga aiki dana samu kuma Alhamdulillah nafito da matsayi mai girma, don kunga kunki yiwa Y'an matan ku Aure da wuri ni Zanne mo sweet sixteen ne dai dai dani in Aura,
Bawai katuwa Y'ar shekara Ashirin ba,
"Toh me yakawo wannan zancen? 'Kune ai kun tara yara har sun wuce misali waisu karatu nifa inyarinya ta cika wayewa I dont like her duk sungama zubarda mutuncin su a university nifa nasan me sukeyi wasu ma kokarin yimaka fyade sukeyi a school, duk mungansu ai, shiyasa I hate graduate, " toh d'an wulakanci Aure lokaci ne kuma ba duka aka taru aka zama daya ba, don haka kayi musu kyakkyawan zato,

"Hmm ayidai shuru kawai please grandma back to our conversation please kifadawa dady Aure nakeso wallahi ko infara bin yaran mutane don inada lafiya nidai,
"Toh Allah ya shiryeka d'an banza tashi katafi ko insaba maka inka fasa bin matan mudai zuri'ar mu ba wanda yayi hakan don haka da izinin ubangiji bawanda zai janyo mana tozarci,

Mikewa yayi " nakoma bakin aiki sai nadawo inji yanda kukayi , yafita yana dariya kasa kasa irin ta miskilayen maza,
Wani irin tashin hankali grandma taji, ta janyo wayarta ta fara latsawa takira d'an nata, yana dauka tace " idan kun dawo kuzo gidana kaida matar ka ina son magana daku,
Tafada tana datse kiran,

****************
Meenal meenal aketa kwala mata kira bataji ba tun shigowar ta ta fada dakin su itada kannen ta ta kulle kanta ita kadai tasan yanda takejin zuciyar ta "Sadiq bazai taba samuwa agareta ba, fadan maman su yadawo da ita ta yi saurin goge hawayen fuskar ta ta zabura ta bude kofar,

Macece da, girma yafara nunawa atareda ita ta cika wuri tana nan yanda take da kyau saidai girma da yazo mata wato Hajiya Hajara kenan, wanda kana gani Kasan hutu ya zauna gata cikin gidan Alfarma da kuma ni'ima, fada tafara yimata,

" ke don iskanci kindawo gidan ma koki leko Kifada, min gaki ishashiya ko, to sannu mandiya, idanun ta ta Kalla taga yanda sukayi wani irin ja da kunburi saboda kuka,

"Meyasame ki? Au iya shegen ne na koke koken ya motsa, zaki fada muji intayi wari, kuma kifito babanki na kiran ki kuma ki gyara fuskar ki kafin yafara tuhuma ta ehem, tafada tana juyawa tabar dakin, ............... 🖊

*korafi ya karbu masoya zanci gaba da tsara wannan labari ta wani irin salo da zai kayatar daku kuci gaba da biyoni insha Allahu zaku nishadu fiyeda salon farkon don haka muje zuwa masoya*

*Godiya agareki kawata sa adatu matar Soja ina miki fatan Alkhairi a duk inda kike Allah ya baki Abinda kike nema duniya da lahira, jinjinar bangirma ta wajena*

*Matar Soja*
2/28/21, 6:17 PM - Q: 🌻🌻
*ZANYI BIYAYYA*
🌻🌻

*By FENERH*

6⃣1⃣&6⃣2⃣
Chapter 42 · 0% Book details