← Book details Zanyi Biyayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 60

Sashe 14

Zanyi Biyayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

HAJARA yau ta tashi da kudurin sai ta je gidan RAHAMA koda bada yardar inna ba so take taje kawai ta yi mata famfo tareda mata hudubar tsiya harta yi nasarar korata tabar mata gidan, don haka karfe goma ko wanka batayi ba ta zuba kayanta a jaka guda biyu ta sulale ta fice gidan,
Tana isa A yabo na fita, wanda she is happy zata samu damar yiwa RAHAMA wayau domin tasan batada wayau ko kadan,
Ta isa batareda matsalar komai ba, mai gadi ya bude mata ta shiga tana Kara kallon ko ina NA harabar gidan, motocin kawai dake parking space na Al Ameen, Kara ingiza zuciyar ta sukeyi bare ginin gidan,
Ko sallama babu haka ta tura kai falon tareda Ajiye Jakarta ta fasa kuka kamar wadda akawa sakon mutuwa domin ganin falon kawai yasa taji ina dole fa ta koka saboda bakin ciki domin ragewa zuciyar ta radadi, tsabar bakin ciki ke cin ranta wanda inzata samu dama wallahi shake RAHAMA zatayi, da sauri RAHAMA ta fito daga dakin ta jin kuka a falo, domin tasan ita kadaice a gidan A yabo ma ya fita,
Ganin HAJARA yasa ta rugo da gudu tareda cewa "subuhanallah yaya lafiya? Dago kanta tayi ta kalli RAHAMA idanun ta sharkab, idan ba gizo take mataba tana hango wani irin cika da kuma fresh da fatar RAHAMA keyi wanda ya tabbatar mata da lallai tanada cikin kenan,

Kara volume din kukanta takeyi kawai saboda bakinciki, gaba daya ta ruda RAHAMA, tace "bari inkira inna inji Meya sameki tunda kinki yin shiru kiyimin bayani, riko hannun ta tayi tana girgiza kai, cikin kissa da munafunci tace "kema korata zakiyi? Bayan inna ta koreni kema korata zakiyi, bari intafi kawai inshiga duniya kowa ma ya huta tunda bawanda ke kaunata, ta Kara kuka tareda tashi kamar zata tafi da gasken kuwa,
Rikota tayi tasa kuka "don Allah Karki tafi bari inkira inna inbata hakuri ki koma gida don Allah Karki tafi,

Saurin riketa tayi "inkin kira inna kinfada mata wallahi zankashe kaina zan kona kaina kowa ya huta, yanzu bazan iya zama a gidan ki na kwana biyu ba sai kin koreni, bakomai ni nasan bazaki so in zauna a gidanki ba saboda mijinki, bari intafi Allah ya sada fuskokin mu da Alkhairi,

Kuka RAHAMA tasa tareda rungume Y'ar uwar ta, "aa don Allah yaya karkiyi haka don dai kwana biyu wallahi ki zauna nidai Karki yi kokarin kashe kanki banason ki mutu kafira don girman Allah karkiyi Abinda zaki daga Hankalin su inna da baba,
"Bazan yiba inhar zaki taimake ni, "eh I promise, Karki fadawa inna ina nan gidan kota kiraki, "ok bazan fada ba, ko yaya Aliyu ko baba Karki fadawa kowa, bazan fadaba, muje ciki, ta dauki jakar ta tanufi dakin da take kwana a ciki ta ajiye mata, bin bayan ta tayi tareda ya tsine Baki,

Yanzu duk girman gidan nan kika zabi wannan akulkin dakin? "Banason wanda aka bani ne yamun girma,, Hmmm muje inganshi, tafada, " aa yaya muyi zaman mu a nan yafi,
"Oh rowar ganin gidan naki kike min kenan? "Aa muje kigani, ko zakici wani Abu? "Eh mufara ganin dakin baccin naku tafada tana gyara zaman rigar jikin ta,
Bataso taje dakin sam saboda ya mata warning tunfarko don haka batason ta yasamesu ciki,

Tundaga farkon shigowar tabuga ashar saboda ganin tsaruwar dakin ga gadon kamar kwallo cycle, karewa dakin kallo takeyi komai na dakin ba a magana idanun ta suka sauka kan akwatunan da aka jera masu Biyar Biyar saiti uku, tuni ta waro ido "buro uba "RAHAMA waincan na uban waye? "Kayan lefen ne" jar uba, bari ingani tafada jikinta narawa, tace "kije ki shirya min Abinci kafin ingama gani,
Ba tason haka Amma dole tace tom tana Allah Allah tayi ta gama ta fita dakin kar yadawo domin ta lura yanzu bayajin wuyar shigowa gidan,
Kitchen ta tafi domin hadawa Hajara special dishes,
Saida ta bude kowacce akwati ta ga kayan ciki babu karami ba na Y'ar wa kana ganin kayan kasan ba na Nigeria bane ga uban gwala gwalai, tashi tayi ta kulle kofar tareda duba ko ina ta ga kofar bathroom, kwabewa tayi tas ta shiga a nan ma kusan suma tayi Domin ganin irin tsaruwar shi, duk shige shigrn ta gidan masu kudi bata taba cin karo da irin wannan bayin ba, cika ruwan zafi tayi tareda sheka turaren wanka ta zuba ruwan sabulai masu kamshi da tsada ta shige tayi wanka, tana tsinewa munafuncin RAHAMA shegiyar yarinya dole ta lafe tana fresh irin wannan daular,

Har RAHAMA ta kammala tafito falon tareda ganin kofar a garkame, ta buga "yaya me kikeyi kika kulle kofar?
Budewa tayi, taci Ado cikin wani fitinannen less daya daga cikin akwatin, ta baza d'an kareren gwal ta zuba ado up and dwan kamar matar gidan, RAHAMA ta bude baki kawai takasa magana,
"Ki kalleni na hadu? Kinga telan kila yasan measurements dina gaba daya sunyi min cif cif, kinsan komai saboda ni akayi,
Gaskiya daga A yabo yasan kalar matar da zai Aura daga farko,
Kalmar ta caki RAHAMA ranta ya baci sosai Amma bazata iya cewa komai ba, "tace muje ki ci Abincin na kammala,
Ta ce muje kinuna min kizo ki gyara kayan duk na bazasu a tsakar dakin,
Tafada tanayi gaba,
Haka ta bita saida ta baje mata komai kan dining ta koma dakin domin batason yazo yaga dakin a haka tayi laifi, cikin sauri tafara tattara komai ta mayar tareda gyara duk Abinda ta bata a dakin,

Da Sallamar shi ya shigo falon, daidai HAJARA ta kammala zata mike ta ji muryar shi, tuni taji wani irin dadi tareda tasowa cikin Sauri tana rangwada, tsayawa yayi cak tareda zuba mata ido yana mamakin hali irin nata na dakikai, kayan da ya dade yana tsara yanda zaiga RAHAMA a ciki shine tazo ta ciro tasaka don iskanci da dakikanci, kusan kullum sai ya bude kayan yagani haka kawai yake imagining ganin ta cikinsu tun ranarda tasa red dress din nan yake kwadayin kuma ganin ta cikin wani Adon Amma yau gashi wanna banzar ta saka, tuni kayan suka daina burgeshi ya hade rai tareda gimtse duk wani farin cikin dawowar shi gidan, she spoil his mood,

Da wata irin kwarkwasa tana juya dry body dinta da sam baiyi kamada na RAHAMA ba, ta iso kusa dashi, "hy handsome welcome back, tafada tana zuba fari da kuma motsa baki cikin salon jan hankali da kuma nuna cewa ita ta waye,

Nade hannun shi yayi ya zuba mata ido yace "unbelievable,
"How did you see me!? Beautiful hum not like your village wife, just give me one chance zan tureta in maye ma gurbin ta domin nasan nice kalar ka nice matar da ta dace da gidanka,
Kaima kasani samun mace kamar ni sai mai sa'a,

Wani irin kallo yake mata mai cikeda rainuwa da kuma tsanar halinta,
Yace cikin kwantar da kai, " tank you baby, Yafada cikin wani irin salo, RAHAMA da tafito tundazu ta zuba musu ido tana kallon komai batareda sunganta ba domin yabada baya,
Wani irin kwarkwasa ta karayi jin yace mata tank you baby, wato yaji dadi zata rabashi da Y'ar kauye,
"Mention not sweetie, tafada kamar tafada jikinshi,
"Tank you for runing away, Yafada cikin wani irin murmushi na rainin hankali, wallahi you really help me, sanadin guduwarki I found my perfect match,
Gimtse fuska tayi tareda cewa bangane ba,

"Yes da baki gudu ba yazanyi insamu someone better,? Da kin tsaya aka daura mana Aure da kin cuceni, marrying someone like you is diserster to my life, tank you for saving me.
"Al Ameen kai d'an wulakanci ne, " kece babbar Y'ar wulakanci da zaki tako har gidan kanwar ki kina kokarin yi mata snatching, ko a tarihin hikayoyi bantaba ji ko ganin jahila irinki ba, ina tantama ba ciki daya kuka fitoda wife ba,
"Karka manta am fighting for my right ne, nice yakamata ka aura ba itaba,

"That's means ita keda right akaina bakeba don haka before I loose it leave my house right now,
Rage murya tayi tana kokarin rikeshi, " um um don't even think of touching me,
"Al Ameen ina kaunar ka yau nafada maka I love you so much , wallahi inka bani dama zan share maka hawayen ka,

"Hawaye kika gani a idona? Ni hawaye na a share suke, and now I understand kinzo Kiga rayuwar da mukeyi ne domin kisamu hanyar shigar da kanki "you are too late baby, kin makaro kanwarki is Amazing,
If you are here too see ne you are highly welcome,
Juyawa yayi tareda yin murmushin mugunta a zuciyar shi kuma yana aiyana he is going to use her to get closer to RAHAMA zata sha ruwan mamaki sai tabar musu gidan su da kafar ta bibbiyu da shi Al Ameen take zancen........ ... 🖊

My opinion RAHAMA is fool fans ko me kuka ce????
Ruwan comment 💃💃💃💃💃💃

*Matar Soja*
2/28/21, 6:17 PM - Q: 🌻🌻
*ZANYI BIYAYYA*
🌻🌻

*By FENERH*

Free page

*ga masu bukatar biya ku hanzarta kar Abaku labari ku biya ku karanta cikin Aminci,katin Airtel 200 zaku turo normal vip 500 kuturo katin ku ta wannan numbar 09011251444 ko ta Asusun banki na 7304736012 nafisa sani Fcmb don Allah vip Kudaina turomin kati idan kana son vip kutura min ta banki katin nayimin yawa sosai in bakuda Account kibayar a pos don Allah sucire charges dinsu a ciki, Y'an Niger 🇳🇪 masu bukatar biya ku nemi wanna number +225 48 15 39 03*

Free page

1⃣5⃣&1⃣6⃣
Chapter 14 · 0% Book details