← Book details Zanyi Biyayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 60

Sashe 18

Zanyi Biyayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wato ke tacewar ki takai ki dauki kafarki saboda kunyi hannun riga da kunya kitafi gidan kanwarki ki zabga mata karya wai ankoreki a gida, saboda kinsan ta da tausayi da hakuri sai zuba mata iskanci kikeyi a gidan ta na Aure kina matsayin yayar ta,
Wallahi da ki zubar mana da mutunci gwara inkasheki kowa ya huta da mugun iri, "salati inna tasa da salallami tace "oh ni larai yanzu HAJARA Abin kunya da zagin da zakiyi ja mana kenan? Yanzu a, Al adar bahaushe har ma dai mu sakkwatawa da mukasan yak'ana da kunya da Kara, ki dauki kafafunki kije har gidan kanwar ki ki share gindi ki zauna, innalillahi wa inna ilaihirraji un, Amma Y'ar nan kin cuce mu kin cuci Y'ar kanwarki da batasan komai ba,

"Inna da kinji dibar Albarkar da take mata ma da ranki sai yafi haka baci , Yafada ma inna komai sannan yace yanzu haka, Nasamu momyn su ta tafi da RAHAMA bansan wane tuggu ta hada musu ba har momyn shi ke kokarin kashe Auren,
Kuka tasa Amma bana nadama ba, "wallahi yaya ni bani nasa aka dauke taba dama ba kaunar ta yakeba cusa mai kukayi yanzu dole a...... Wani irin hambari ya kaimata, tareda Zaro belt,
Inna tace tsaya Aliyu kafin ka kasheta infada mata Kalmar da bansamu fada mata ba tun a farko kar in tabka asara,

"HAJARA bamu kika cutaba kanki kika cuta a rayuwa, munfita hakkin ki koda kika gudu kika dawo gidan nan ubanki hana yayi a duke ki, Amma saboda sharri kika kwashi kafa kika tafi gidan Y'ar uwarki kika shara mata karya mu mun koreki, kalma daya kawai zanfada miki yanzu "wallahi duk Abinda ya samu RAHAMA ko rayuwar Auren ta bamu yafe miki ba HAJARA duniya da lahira banyafe miki ba kuma duniya ce gata nan ta isheki riga da wando, wanda ma bai shigota ba jiran shi takeyi,

"Kai kuma inka kasa kasheta inada fiya fiya zan kanbada ma tanbadaddiya murage ire iren ta a duniya, ta shigewar ta dakin ta ta datse tareda kunna katon redion ta,
Ai kuwa dukan kawo wuka ya mata har saida ya ji bata motsi yajata dakin su ya wurga ta ya kulle ya fice, duk da haka baiji sanyin Abin da ya mata ba bai gama gamsuwa ba, saida ta dauki dogon lokaci ta farfado bakinta idonta fuskar ta ko ina ta kunbura saboda dakuwar da tayi, Aliyu mala'ikan daukar raine na duniya baida imani kona anini don ina kallon fuskar HAJARA nace Kuth dama Soja yayi kawai don suke canja kamannin mutum cikin minti biyu, don inka ga fuskar ta bazakace wannan hajon bace bai ji da kyau da kuma kwalliya,

Dakyar ta iya motsa kugunta tana Allah ya isa a cikin zuciyar ta domin bazama ta iya magana ba saboda kunburin bakinta,
Amma ta kudurta koda zai kasheta bazata taba goge kudurin zuciyar ta ba,

*****************
Yau RAHAMA ta kuma yarda da al marin Al Ameen dole yayi girman kai ganin irin gidan iyayen shi duk da ba irin nashi bane ta san cewa shi din d'an gatane da dole yayi girman kai, momy ta zaunar da ita tabata hakuri domin tasan ta tsorata ta da fada a, farko, "RAHAMA kiyi hakuri, ni na haifi Al Ameen nasan rayuwar shi, don haka kiyimin biyayya kamar yanda kikayi wa iyayenki zakici ribar Abin kinji,
Toh tace batareda ta nuna komai ba momy ta shinfida mata hujjojin ta tace nasan ke ya'ce mai biyayya da hakuri don haka bazaki tabema dole kiyi dariya kiyi farin ciki a rayuwar ki RAHAMA kema sai kin shigo gari yanda ba macenda zata nuna miki isa,

Dole sai kin daura damarar yaki da gidan Auren ki akwai kalubale a cikin rayuwar kowane zaman Aure don haka ki zage damtse ki koyi zaman gidan miji wanda koda Aure Al Ameen yakara kizama gwarzuwar shi a zuciya,
Haka momy keta tattalin ta, daga baya suka shige dakin Husna dake zaune tayi shiru, tana ganin RAHAMA ta zabura, tace yauwa sister in low ke nake jira, ta riko hannun ta suka zauna gefen gadon, tace "tell me About your brother, "me kike sonji akan shi? Labarin budurwar shi,
Murmushi tayi tace "ai yaya baida budurwa Amma Y'an mata nabin shi sosai, yace bazaiyi Aureba sai yaga ya wadata iyayen mu,

"Allah sarki shima yanada zuciya mai kyau, Amma haka yake baya magana da mutane? "Eh haka yake, kice halinku daya da yayanki sister inlow, tafada tana dariya,
RAHAMA tana cikin damuwar halin da Al Ameen ke ciki gashi har yanzu bai zoba she thought zai biyo bayansu, she is very worried, haka ta wuni sukuku a gidan duk da momy da Husna na iya bakin kokarin su,

Al Ameen kuwa yayi matukar daukar zafi don gani yake da RAHAMA ta nuna bazata bisu ba bazasuce zasu tafi da itaba, don haka ya nuna zuciya yaki ko zuwa gidan, Baban shi ya kira da shigowar shi kenan gari yace "Dady zan tafi gobe inga doctor, "to Allah ya kiyaye zaka iya tafiya Abuja yau gobe katashi you have everything, "yes dady Amma momy ta dauki RAHAMA yafada cikeda fatan Allah yasa dadi yace yazo ya tafi da ita
"Haka nada kyau ba damuwa nima yanzu na shigo zan fara duba office kafin intafi gidan if you like zaka iya zuwa mu hadu a office din sai ka wuce, in kuma kana sauri sai ka dawo ko ince sai munyi waya, ya datse call din, batareda ya jira cewar Al Ameen din ba,

Don haka yasan cewa koma meye yasan da yardar shi momy keyi don haka yasan ba wani Amfani da zuwan zaiyi mai gidan,
Kayan shi ya hada ya tattara ya fito tareda kudurin bazai dawo ba sai sun gaji sun nemo shi,
Yaron shi Amintacce ya kira tareda damka mai komai ya mika mai wani envelope yace ya kaiwa RAHAMA ya fada mota ya dauki hanyar Abuja zuciyar shi kamar transformer saboda zafi.......... 🖊

*Matar Soja*
2/28/21, 6:17 PM - Q: 🌻🌻
*ZANYI BIYAYYA*
🌻🌻

*By FENERH*

*ga masu bukatar biya ku hanzarta kar Abaku labari ku biya ku karanta cikin Aminci,katin Airtel 200 zaku turo normal vip 500 kuturo katin ku ta wannan numbar 09011251444 ko ta Asusun banki na 7304736012 nafisa sani Fcmb don Allah vip Kudaina turomin kati idan kana son vip kutura min ta banki katin nayimin yawa sosai in bakuda Account kibayar a pos don Allah sucire charges dinsu a ciki, Y'an Niger 🇳🇪 masu bukatar biya ku nemi wanna number +225 48 15 39 03*

2⃣1⃣&2⃣2⃣

A kwance take a dakin Husna, takasa bacci ba abinda take tunani sai Al Ameen da daren su na jiya, wani irin kewar shi takeji, gashi yaki zuwa ta ganshi, wani irin sanyi ke bin ko ina na jikin ta idan ta tuna da duk Abinda ya shiga tsananin su, a gaskiya rayuwar Aure na tattare da ni'imomi daban daban, domin tasan yau ma da suna tare haka zai shayar da ita madara mai wuyar mantawa, moment dinta da Al Ameen jiya was unforgettable, ya shiga cikin tarihin rayuwar su,
Tunawa tayi da ciwon shi, tuni taji wani irin tausayin shi, yanzu All this years Abinda yake fama dashi kenan,?
Tunawa tayi da lokacin da ake fama da HAJARA ta yarda da Auren shi taki, tana cewa ai nakasashshe ne, yanzu wannan ciwon ne HAJARA ke kira nakasa? Ai wanna Abun a tausaya mai ne domin kowa kallon mai lafiya yake mai ita dai bataga ciwon da zaisa ta kasa zama dashi ba koda kuwa gurgu ne, mutum ne mai halin kwarai idan ka fahimce shi,

Tunda taje gidan shi bai taba yi mata iyaka da wani Abinci ba sai dakin da ya turata wanda ita a wurin ta yafi mata saukin zama matsayin ta na Y'ar talaka,
Murmushi tayi tunawa da lokacin da yace zai horata, da aiki sai taga ma shi baiko iya shirya mugunta ba tunda bai iya daukar hannu yace zai daki mace,
Kwana tayi juyi tareda kewar Al Ameen sosai wanda batasan ta Ina takejin wani bakon Al Amari ba,

HAJARA dai wasa wasa kafarta ta kunbura saboda targadata da Aliyu yayi da duka dakyar take taka kafar ta, koda baba ma yazo yaji labari dakin ya, leka yace "ummi Allah ya shiryeki domin bamu yi miki bakiba ma kina ganin rayuwa bare kuma mun biki da mum munan lafazi, Amma kisani baki kyauta mana ba baki kyauta wa Y'ar uwar ki ba, kema baki kyautawa rayuwar kiba, kibi a hankali ummi ke ya' mace ce duk kuskuren da zakiyi zai zama cikin tarihin rayuwar ya'yan ki ne mai kyau ko mara kyau, yau bakya Alfahari da yanayin rayuwar yar uwar ki, RAHAMA ta gama dacewa, kina nan kina kokarin ruguza mata rayuwa Allah nakara daukaka ta,

Karatun nata da aka kutsire mata tana can zataci gaba saboda biyayyr iyaye, karkiga mun zuba miki ido HAJARA, wallahi ko infada ko kar infada sai duniya ta koya miki darasi ko yau ko gobe don haka Allah ya kare ki daga fadawa halaka,
Ya juya ya fita,

Wanda da kanshi ganin yanda take fama da kafar ya gyara mata cike da tausayi na mahaifi da kuma tsantsar soyayyar HAJARA da har yanzu tana nan domin soyayyar iyaye ta daban ce duk wanda ya rasa su yayi kuka wallahi duniya su din gatan mu ne jigon mune garkuwar mu ne su, duk da inna tayi fushi da ita Amma ta tausaya mata ganin yanda duk ta koma abin tausayi,

Amma Abinda basu sani ba sam rayuwar HAJARA babu nadama kudurin ta na nan na inhar bazata samu Al Ameen ba RAHAMA ma bazatayi farin ciki ba,
Daga zaune ta kira kawar ta mai zugata Ladidi wata irin yarinya ce masu irin yawon nan da son Abin duniya itama ba wai Y'ar masu kudi bace Amma tsabar son Abin duniya yasa ta zage damtse take yawon ta zubar domin ta rika karya,

Kawancen su da HAJARA ya samo Asali ne a school tunfarkon shigar su, d'an fodio, kusan halin karyar su yazo daya da HAJARA shiyasa suka dunke ko yanzu ita ta ke zuga HAJARA akan duk Abinda takeyi,
Chapter 18 · 0% Book details