Sashe 8
Zanyi Biyayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
*ga masu bukatar biya ku hanzarta kar Abaku labari ku biya ku karanta cikin Aminci, 200 ne normal vip 500 kuturo katin ku ta wannan numbar 09011251444 ko ta Asusun banki na 7304736012 nafisa sani Fcmb don Allah vip Kudaina turomin kati idan kana son vip kutura min ta banki katin nayimin yawa sosai in bakuda Account kibayar a pos don Allah sucire charges dinsu a ciki, nagode masoya sai najiku*
9⃣&🔟
Saida taji yunwa na neman kasheta ta mike tareda kallon ko ina a dakin, ba laifi akwai gado da komai a ciki saidai dakin shine daidai zamanta dama, cikin sa'a ta hango d'an karamin mini prige a dakin, tayi saurin matsawa ta bude takoyi sa'a akwai drinks cike harda holandia, ta janyo jikinta na rawa, domin tun rana rabon ta da cin wani Abu, ta kafa kai saida ta shanye tas ta ajiye kwalin zufa ya karyo mata, kofar dakin ta garkame gudun kar wannan mugun ya dawo ta cire hijabin jikinta ta ga dakin baida matsalar komai yama fi mata kwanciyar hankali akan wancan dakin da yake kamar ba za a kwanta kabari ba, shiru tayi tana tuno maganganun shi,
Allah ta mika wa Al amarin ta tareda kudurta duk runtsi bazata taba bari tayi laifin da zai korata gida ba, domin komawar ta na daidai da bacin ran baban ta wanda sam bata fatan shi damara ta daura domin tasan bautar Allah zatayi, da daura damarar yin biyayya duk runtsi duk wuya daga yau bazata taba bari yaga bacin ranta ba ko hawayen ta duk ukubar da ya shirya bata,
Don haka Bathroom ta shiga taga wannan madaidaici ne daga sink sai shower daidai irin wadda tasaba gani ta dauro alwala ta fito, sallloli ta gabatar tareda rokon Allah yabata ikon cinye wannan jarawabar,
Taso ace Qur anin ta na dakin ta karanta Amma tasan ko tana hauka da nad'e nad'e bazata fita waje ba taci karo da beauty but beast, sunan da ta Bashi kenan,
Hayewa gadon tayi tareda kudundune wa cikin hijabin ta, sai bacci,
A ranar tayi wani irin bacci mai cikeda natsuwar da bata tabayin irin shiba duk da rayuwar ta na cikin matsala zama gida daya da namijin da baya kaunar ganin ka,
Gefen Al Ameen kuwa wani daki ya nufa kamar irin nata, yana tunanin dama wannan yarinyar da yake ta nema Y'ar gidan baba bala ce, duk da yasan mutuncin mutumin bai fasa kudurin shi akanta ba ya riga ya gama shirya duk ukubar da zai bata,.
Asubar farko ta mike saboda ta saba ta gabatarda nafila kafin sallar farilla tayi Addu'oin ta, ta mike ta kakkabe kan gadon da ta kwana ta duba ba Abinda zata gyara, ta bude kofar ta fito falon tana lellekawa taga wane aikin zatayi domin ita tariga jikin ta ya horu da aiki batajin zata iya zama ba wani aiki,
Wata kofa tagani can karshe harda labule ya ratsa ta nufi hanyar domin ganin ko kitchen ne a wurin, takoyi sa'a dining ne da kitchen a hade, tundaga kofar kitchen din tayi Hamdala tareda tasbihi ganin na urori daban daban kitchen din ya gama haduwa, tana hango wata kofa ta ci ta matsa ta bude store ne cike tab da Abinci ga manya manyan prige ta bude, daya, namomi ne Kala Kala dayan kuwa kayan miya ne tab da kayan lambu a basket,
Tuni taji tana son ta girka wani Abu da safen nan ko zataji nauyi a cikin ta domin sam bawai ta Koshi bane,
Rayuwar ta kab ta kare ta ne a sonyin duk Abinda ya shafi kitchen, duk littattafanta na girke girke ne wasu domin ita girki is her hubby, fagen kayan wuta ta iya kunna gas domin idan sunje gidan kanwar Inna tanada ire iren wasu Abubuwan amma ba irin wa innan ba, don haka bata sha wahala ba ta shirya indomie sharp sharp taji kayan lambu ta daba ruwan Lipton da yaji kayan kamshi ta soya kwai guda daya domin batason kwai yayi kauri,
Cikin minti kadan ta gyare inda ta bata tsab tareda zama nan taci tayi nak ta wanke komai tareda saka mopa ta goge tiles din kal, tana jin wani irin nishadi,
Kuma duk wannan aikin hijabin dai na nan a jikinta,
Tana gamawa ta dauki abin mopa din tayi falon duk girman shi ta mope shi tas tareda komawa ta nemo towel duk wani Abu saida ta goge shi a falon duk da ba datti,
Tana kammala wa ta koma dakin da aka jefata tayi wanka, Amma tarasa yanda zatayi, kayanta takeson canjawa Amma tana tsoron zuwa wancan dakin kar ya ganta, haka dai ta kuma mayarda na jikinta ta zauna gefen gadon tareda zabga tagumi, yanzu haka ne Auren yake? Haka zata cigaba da rayuwar kadaici ba abokin debe kewa ba wanda zaiji koda muryar ka, wayarta ta tuna tana can dakin a cikin Jakarta, dole ta mike domin tanason waya da inna da kuma ya Aliyu,
Fitowa tayi tana Kara kallon dukiyar falon, kawai taji ta gabza karo, kafin ma ta dago kanta tajita a kasa tim ya hankadata yana kakkabe jikinshi da ta taba,
Saida bayanta ya Amsa saboda unexpected tajita a kasan, ta ce washhh tareda dago kanta ta kalle shi, tayi saurin saukewa domin kayan geming ne a jikinshi yana diga saboda jugging yadawo, cikin tsawa yace
"Are you blind? Kina tafiya kamar makauniya next time kika kuma bari jikin ki ya shafe nawa sai na lahira yafiki jin dadi, kazama kawai tunjiya, kina yawo da kaya daya bana son datti a cikin gidana ki kiyaye and ki wuce ki wanke min bathroom before inyi wanka bana wanka kullum sai an wanke shi, tashi tayi dakyar domin bayanta da ya rike ta nufi hanyar dakin ta domin wankewar ya buga mata uwar tsawa, " bakiji magana ta bane zaki wuce,? "Da Banji muryar rashin kunyar kiba da zance ke kurma ce Amma bakin ki cike yake tab da manyan kalamai kina kwailar ki dake, don haka bina muje ki mun aiki oya,
Yanuna mata hanya, dole tayi gaba tanayi tana hardewa yabi bayanta, kofar datagani ta tura tashiga, komai na cikin dakin irin na wancan ne don haka saida gabanta ya fadi ta ina zata fara?
Jin motsin shi yasa ta wuce hanyar bathroom din ta tura, hijabin ta ta nade saman west dinta ta daure tareda daukar bucket ta Tara a fanfo ta debo ruwa ta fara wanke wurin da baida datti ko kadan, tsab ta wanke ta fito yana zaune da laptop a cinyar shi yana duba sakonnin da ya dade bai duba ba, hotunan da yafara cin karo dasu ya kurawa idanu domin yagan su kusan hamsin yanzu kusan sati biyu ana turamai kullum bai taba dubawa ba,
Tsaki yaja " classless ya fada tareda delete gaba daya ya rufe ya mike batareda ya kalleta ba " clean this mess yafada domin ko ina dakin ya watsar da kayan da ya cire da ma wa inda batasan ina suka fito ba,
Dukawa tayi ta fara kwashe kayan ta gyara tsab ba musu ta duba closet ta mayarda sauran tareda mamakin ina zaikai sutura duniya, cikin Sauri ta rufe ta dawo kan cycle bed din da yayi kamar Anyi dambe akai ta kakkabe tareda gyara bedsheet din cikin Sauri domin tafita kar ya fito,
Da sauri sauri ta gama zata fita taji yace "wait, tayi saurin juyowa, tuni ta Dukar da kanta kasa ganin yanda ya fito da kirjin shi a bayyane d'an guntun towel ne a jikin shi gaba daya kirar shi tsoro ta bata namiji ne da baka iya kallon shi sau biyu saboda cikar zati da haiba, uwa uba kwarjini da kyau, yanda ta Dukar da kanta kasa yabashi haushi yasa ya matso dab da ita,
"Dago kanki yafada cikin tsawa, ba shiri ta dago, "me kike gudun kallo a jikina? Inada muni ne da zaki kasa kallo na? " ok I understand saboda karkisa ran zan dora miki shi ko never this chest is precious, ko yatsan ki ba zai taba shiba bare banzan busashen jikin ki,
Wallahi an cuceki nima an cuceni da za a min aure da premature sai uban rashin kunya da kika iya, ko gaisuwa ma bakisan yanda akeyin taba,.
Muryar ta na shaking tace " ina kwana? Hold it bana bukata out of my room, yafada yana nuna mata hanya da hannu da gudu ta fita,
Tana dafe kirji, " iya Abinda yake tunanin zaiyi min kenan da sunan horo? Murmushi tayi domin wanna is not a punishment, aikin tane kuma zata iya har karshen rayuwar ta,
Shikuwa kallon dakin yakeyi yanzu duk Abinda ya baza ta gyara cikin lokaci kadan kamar injin, domin yasan aikine mafi wahala a wurin Husna idan tamai laifi horon da yake bata domin batason aiki,
Shiru yayi yana tunanin aikin da zai bata next da zata wahala,