← Book details Zanyi Biyayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 60

Sashe 29

Zanyi Biyayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ummi gaki gani ga mahaifiyar ki nan, larai ki zama sheda, in har ummi kika tare kika dakko kafar ki daidai da kwana daya kika dawo gidan nan da sunan yaji ko wani tashin hankali, banyafe miki ba duniya da lahira kuma kinfita a cikin ya'ya na, domin tun farko da kike iya shegen ki nasa miki ido banbari wani ya kyareki ba a gidan nan ga maifiyar ki nan nasha yima ta kashedi akan karta ce miki komai zaki dawo hanya,
Alhmdulillah ki godewa Allah bello yaron kirki ne duk da baiyi karatu ba Amma yasamu shedar Arziki a wurin kowa tundaga bakin aikin shi har gidan su, don haka innaji wani Abu to daga wurin ki ne,.
Kuka tasaki mai cin rai tana girgiza kai " karku yimin baki don girman Allah baba ku yafe min nagane nayiwa kaina a rayuwa ina neman yafiyar bijire muku da nayi a farko ku yafemin iyaye ne wallahi koda zanje inci tuwon kasa a gidan bello baba ZANYI BIYAYYA bazan kuma yin Abinda zai bata muku raiba insha Allahu, tafada cikin tsananin tausayi na iyaye suka ce shikenan sun yafe mata Amma duk Furucin su akan gidan Auren ta basu janye shiba,

Daki ta koma ta zabga tagumi, waye zatayi tadi dashi ko ta rage bakin ciki, RAHAMA, wata irin kunyar ta takeji me zata fada mata, wane zance zatayi da ita, ta mugun sakin damar ta tunfarko, yanzu batada wanda zata fadawa taji sanyi,

A haka aka fara shirin Auren su Aliyu da Husna wanda su baba suka roki Alfarmar Bello ya bari a yi tarewar baki daya, baiyi musu ba ya Amince don haka dole a haka inna ta fara shirya ta irin na Amare, wanda a gefen su RAHAMA dai tana gidan momy Hankalin ta kwance koda yau she Al Ameen na zarya Abin shi wata rana sai momy ta kada shi ya matsu ba a gama Auren ba su gudu India wanda yana kan shirya mata visa,
Tanason zuwa gidan su domin Abu ya kasu mata kashi biyu itace gefen Ango kuma da gefen Amarya domin yanzu husna kamar RAHAMA ce ta zamo babbar kawa a wurin ta ba matar yaya ba,
Komai RAHAMA ke tsarawa, duk da tsakan kanin satikan tanajin wani irin canji a tareda ita, ga zazzabi dake tashin mata duk dare zuwa safiya kuma tajita garau,

Ba wanda ya ankare da yanayin ta har ya rage saura sati guda Auren su Husna, ta shirya domin zuwa gidan su taga nasu shirin saidai kullum tayi waya da inna, yau so take taje taga kayan kafin akawo,
Al Ameen tafada ma zata fita, yace ta jirashi yazo suje, ta ce aa yadai barta ta tafi domin batason ya ce zai kaita anguwa zai iya kwana domin kwanan nan rigima suke tayi akan yana bukatar ta, taki yarda su hadu ko yazo gidan,
Don haka dole ya hakura ta tafi ita kadai a cikin dalleliyar motar ta ta tafi wannan karon Husna ba zuwa gidan surukai,

Tun dosowar motar ta baba ya gane ita ce ya saki fuska cikeda farin ciki yana cikin mutane, ta faka cikin Sauri ta fito cikin shigar ta ta mutunci hijabi har kasa ta dakko jakar ta, ta nufo su cikin girma mawa ta gaida su baba, ya amsa cikeda farin ciki yace ta shiga ciki yana zuwa, ta wuce cikeda dokin ganin inna itama, saidai tundaga shigar ta jikin ta yayi sanyi ganin Y'ar uwar ta tana wanke wanke duk ta kode duk da bata cikin damuwa yanzu Amma ta canja kamar ba HAJARA sarkin gayu ba, ita tafara yima RAHAMA sannu da zuwa wanda Abun ya mugun taba mata zuciya,

Tace "yaya HAJARA lafiya kalau kike kuwa? Inna ce ta fito ta tare ta tace "kalau take Amarya ai duk tare za ayi tariya dole ta rame ana fargabar Aure, tafada tareda cewa "kin tsaya nan karaso daga ciki Kiga kayan duk da gidan ku za akai,
Tafiya takeyi tana waigen yaya HAJARA, rabon da su hadu tun ranar da sukaje gidan ta da safe itada ladidi,
Dakin inna suka shiga inda taga lafiyayyun Akwatuna saiti biyu masu Biyar kaya shake masu Aji, da tsada dai dai gwargwado Yaya Aliyu yayi kokari wajen fitoda Amaryar shi, sai gefe daya taga ganah must go din Hajara suma, tace " wannan fa? "Kayan Auren Y'ar uwar kine, ki bude kigani yaron yayi kokari sosai, shiru tayi kafin tace "wai inna wane Aure? Anan ta fada mata yanda baba yayi,
Bataji dadin hukuncin baba ba Amma ya zasuyi yariga ya daura an wuce wurin don haka cikeda tausayin Y'ar uwar ta ta mike ta fita lokacin har ta gama wanke wanke ta na share tsakar gidan, tace "yaya zo muyi magana, ba musu ta Ajiye tsintsiyar tabi bayan ta zuwa Dakin su, suka zauna kamar ba HAJARA sarkin fada da kuma gudun raini ba yau ta tsaya jin maganar kanwar ta da ta raina,

"Yaya me yasa baki kirani kinfada min maganar Auren ba? Dago kanta tayi cikin wani irin sanyin halin da bansan daga ina yafito ba, tace " mezan fada miki RAHAMA meye Abin fada A ciki Aure ne dai baba ya daura kuma RAHAMA koda bana son Auren nan zanyi biyayya in zauna da bello, ina kwadayin samun RAHAMA, ina kwadayin samun dacewa irin wadda kikayi RAHAMA ke kam kingama sa'a a rayuwar ki, biyayyar ki ta janyo miki cigaba a rayuwa, wanda ni kuma taurin kai na ya janyo min koma baya Kala Kala, karatun da nake takama nayi zai kare a gidan makanike,

Wani irin tausayi RAHAMA taji na Y'ar uwar ta, tuni hawaye suka wanke mata fuska, tayi saurin matsawa ta rungume ta, "Karki damu yaya ta insha Allahu zakiyi farin ciki zakiyi Alfahari, Kawai kamar yanda kika fada ne, biyayya ga iyaye tana tattare da riba, ki godewa Allah da har kikeda da sauran damar da zaki gyaro kuskuren ki,
Don wasu zasu tafka kuskuren Amma basa taba samun damar gyarawa Har Allah ya sa su koma ga ubangiji, don haka have faith, komai zai wuce zakiyi farin ciki kema da izinin ubangiji,

"Tom tace badon tana hangowa kanta wani sauran jin dadi a duniya ba, haka ta rage murya ta nemi yafiyar Y'ar uwar ta itama........... 🖊

Kuyi min Afuwa banda Enough charge wlh mu tari gobe idan Allah ya tashe mu lfy,

*Matar Soja*
2/28/21, 6:17 PM - Q: 🌻🌻
*ZANYI BIYAYYA*
🌻🌻

*By FENERH*

*ga masu bukatar biya ku hanzarta kar Abaku labari ku biya ku karanta cikin Aminci,katin Airtel 200 zaku turo normal vip 500 kuturo katin ku ta wannan numbar 09011251444 ko ta Asusun banki na 7304736012 nafisa sani Fcmb don Allah vip Kudaina turomin kati idan kana son vip kutura min ta banki katin nayimin yawa sosai in bakuda Account kibayar a pos don Allah sucire charges dinsu a ciki, Y'an Niger 🇳🇪 masu bukatar biya ku nemi wanna number +225 48 15 39 03*

4⃣1⃣&4⃣2⃣

Iya kokari tayi domin ganin ta karfafa jikinta zuwa yamma, Amma ita kadai tasan me takeji a jikinta, shirya wa sukayi cikin jallabiyu masu Aji da kuma haduwa Nata kusan iri daya da Amarya, da kuma yaya HAJARA, ta nada farin gyale akanta domin d'an kwalin baida girma,
Kuma ita matar Aure ce dole ta tsare kanta, don haka ta suturce jikinta da kyau, wanda duk da haka kana ganin irin haduwar da tayi da wani irin kyau na mai sabon shiga,
Makullin motar ta tabawa drivern momy tace shi zai kaita itada wasu friends domin Amarya Ango zaizo su tafi tare,
Kusan ma duk an wuce harda wasu Y'an Uwan momy ma, daga ita sai wasu guda biyu suka fito, takalmi da pos dinta silver suna shekin stones, ta fito cikin takun ta cikin natsuwa, ta shiga bayan motar itada dayar tana duba lokaci kusan karfe Biyar na yamma wanda tasan taro yayi nisa,
Ga miss call din Husna rututu,
Da yaya HAJARA,
Dialing number HAJARA tafarayi " yaya ina zuwa yanzu muna motor, "kin faya sanyi RAHAMA tundazu kowa yagama hallara, harda mijinki na nan,
Tuni taji wani irin farin ciki tace, tom ina zuwa, driver ta kalla tace yayi sauri don Allah, Suna isa harabar giginya hotel din da jerin motocin Al Ameen ta fara cin karo, murmushi tayi kawai tarasa dalilin ds yasa yake kaunar " convoy dinshi suna binshi kamar wani d'an sarki ko gwamna, duk motocin shi uku yake siya iri daya,

Ko Wacce akwai A yabo a jikin lambar jitayi kawai she wanted to feel as his wife in public don haka tuni ta gyara walk domin ta nunawa Y'an matan sokoto nata ne fa,
Aikuwa tun shigowar shi hole din gaba daya ya gama siye hankalin matan dake ciki, don ko Ango da Amarya dake ciki basa kallon su kamar shi,
Duk da cikin farar jallabiya yake shima kamar duk sauran samarin dake wurin saidai nashi ya fita daban dana kowa wankan ga wani bakin glass da ya kwama a ido labcece gaba daya he is worried, baiji dadin zuwa wurin ba as he came bata zoba and he came only because of her duk kwanakin nan kewar tace take neman kassara mai karfin jiki da kuma lafiyar ruhin shi,

Itace akan gaba lokacin da suka shigo duk da tanajin nauyin idanun mutane akansu baisa ta bada kanta ba as she no yana wurin sam so take ta nuna mai she can act like Mrs Al Ameen A yabo,
Tafiya take tana rausaya, batayi Aune ba taji mc na kodata tareda yi mata maraba,
"Barka da zuwa zuciyar Al Ameen Shuaibu Yabo muna miki barka da zuwa matar d'an gatan sakkawata, takawar ki lafiya mace mai sa'a,
Wani irin dagowa yayi tareda zare glass a idanun shi ya mike tareda nufar hanyar domin taro shi don ta gama Tafiya da ruwan kwakwal war shi, ta mugun haduwa ga wani irin haske da sheki da takara na gyaran da sukasha ga kuma kyallin sabon boyayyan Ajiyar su,
Chapter 29 · 0% Book details