← Book details Zanyi Biyayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 60

Sashe 37

Zanyi Biyayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Assalamu Alaikum, inaso inyi wani bayani kadan akan kuskuren da nayi a farkon littafin nan, ta gefen gidan su Al Ameen da nayi zancen rashin Auren shi bayan kanin shi yayi kuma daga nan bankuma zancen ba, nabi labarin a natse daga baya domin akwai labarin da nabi nayi typing dinshi naga akwai kuskure sai na canja salon labarin daga baya, saidai akasin da na samu da natashi posting sai nayi posting wanda nayi typing da farko ba wanda NA gyara ba, A yau ne wata ta ankarar dani ta hanyar tanbaya ta, wai shin ina labarin kanin nashi da aka faro kuma basu kuma jin labarin ba? Eh akwai kuskure a ciki amma inaso inkara fahimtar da readers, typing is not easy Abinda ma zaka kirkira ka rubuta ba sauki bane koda kinada labarin akanki, Matsalar itace ta yaya zaki tsara shi ya bada ma'ana yaja hankalin readers labari akan fuskanci tauraron littafi ne ba mutanen ciki ba kuma ts wata fuskar don haka za a iya kafa labari da mutane da dama daga baya a saki a fuskanci taurarin da Abin ya shafa, ?, secondly akwai kura kurai musamman ma mu yanzu da muke littafin kudi kayi typing da safe kayi da dare, wane lokaci zaka samu ka tsaya editing? Wane lokaci kabawa gidan ka da ya'yan ka? Don haka ina rokon readers inda duk kukaga kuskure ku rika ankarar damu tun ba ayi nisa ba domin mu online writers ba kamar masu publishing bane da sai an tsaya an tace an rairaye shi sannan kowane d'an Adam na kuskure domin mu tara muke bamu cika goma ba don haka Ina baku hakuri da kuskuren da akasamu afuwan*

5⃣1⃣&5⃣2⃣

Tunda suka kule ciki sai sallah kawai ke sa ya fita, momy dai Kiran ta sukayi sukace sai gobe zasu samu shigowa, tace bakomai RAHAMA ta huta Abinta,
Sai washe gari suka shirya cikin ado na kece raini ta zura wata doguwar shaddar da ya dinka musu maroon tata doguwar riga taji capet design da stone, kana gani kasan dinkin yaja kudi sosai,
Ta yafa katon farin gyale shi ma haka yafito cikin dinki na maza lafiyayye,
Domin oder yabayar akayi musu dinki Kala yakusa hamsin hamsin shida ita kafin ya dawo, suka fita Abinsu cikin motar su ta Alfarma daga shi sai ita domin tana Mai complain batason convoy din nan kamar wani gwamna ko sarki,
Idan bazai iya driving ba ita zata jasu,
Haka dole ya tukasu suna tafe cikin nishadi da farin ciki tareda kwanciyar hankali, shi kanshi idan kagan yanda yadawo kasan baida wata matsala,

Suna fakawa a cikin gidan ya zagayo ya bude mata tareda rufe motar yariko tattausan hannun ta sukayi cikin gidan,
Momy da ta matsu tagan su ai kuwa da sauri ta taro su tana kallon heavy load din da RAHAMA ta zama, domin ta cika sosai irin na mata masu ciki kafafun ta sunyi luwai luwai suna sheki da hasken hutu da kuma ciki,

"Oyoyo momyn mu, nayi kewar ki tafada tana rungume ta cikeda jin dadi, Taja ta kan kujera tana Amsa gaisuwar Al Ameen, tareda cewa " nifa bana ganin ka kawai jikana nake hango wa kai Allah dai yaraba lafiya inga Nasamu Abokan hira,
Amen Al Ameen yafurta yana cewa hope
Momy ba shirin kwace min yaro ko yarinya kikeyi ba? "Sosai kuwa kawai ku Haifa shine aikin ku, dariya RAHAMA tayi tareda mamakin yanda momy sam ba ruwan ta da kunya ko kara akan cikin nan, inaga d'an ko Y'ar sin fito? Sai kallo Ashe,

Sundade sai tattalin RAHAMA takeyi komai kafin ma ta furta an ajiye mata birjik kamar bakuwa, "inkinga kina shan wahalar aiki kiyi zamanki nan kinji, karkije kina faman wahalar da jikin ki,
Wani irin saurin kallon momy yayi "haba dai tadawo nan ita shikenan bazata tsuguna a dakin taba sai yawon gidan mutane, "Au mune mutanen? yayi kyau kaji bari cikin ya tsufa kasan dole taje wanka gida ko Al adar mu ta sokoto,

"Tab Ashe akwai rigima , yafada yana kallon momy "Babba kuwa Amma ina fatan kafin lokacin ka fara hada kayan yajin ka na fushi da gudun hijira ko, domin ko bakawa Allah dole kabarta taje gidansu wankan farko,

"Tashi muje kinji gidan su Inna rana tayi yafada yana mikewa domin bayajin za a gama lafiya da wani zancen zuwa wankan gidan nan haka kawai bazai yuwu ba gaskiya, "tashi ki bishi muna gaida su laran tafada, domin ko ajikinta kafin tace "kuma dole kudawo kugaida baban ku domin yana gari kasani,

Tayi gaba tana yata sai kun dawo, bata rai yayi, ya fice tabi bayan shi, har suka hau titi fuskar nan tashi ba fara'a juyawa tayi tareda riko hannun shi daya mai dauke da agogon Gucci mai kyau na fata ta ce "ya akayi ne my dear?
"Ai dole kice ya akayi tunda baki damu da damuwar da nake ciki ba kinajin zancen momy amma kinki ki ce mata aa kinyi shiru dama basai kinyi shiru zansan kin gaji da daukar dawainiya taba, kuma balaifin ku bane laifina ne da na dawo dake Nigeria da muna can ai naga yanda zakije wani wankan gida, kuma idan kina so mu shirya Karki yarda fa zancen su na wani zuwa wankan gida,

"Toh kayi hakuri tafada tareda kissing hannun shi "ni ina tareda kai dear akoda yaushe nafi son mukasan ce tare rana da zafi ina son zama a karkashin inuwar ka, karkace na gaji dakai wace mace ke gajiya da Aljannar ta? "Ina sonka dear Ina son mukasan ce tare rana da dare,

Ajiyar zuciya yasaki tareda janyo hannun ta zuwa lips dinta ya basu kiss, " tank you baby I feel relief,
Kofar gidan su suka faka, ita tafara budewa cikeda farin ciki da jin dadi ta fito tareda nufar hanyar cikin saboda zumudi da kewar inna, saurin taro ta yayi '' haba Ajiya ajira mu shiga da tsarabar mana, sai yanzu ta tuna ta dafe goshi tareda cewa " kaga fushin ka yasa mun manta bamu bawa momy nata ba,

"Ina sane sai munkoma, yafada yana fitoda wata katuwar akwati suka shiga da Sallama, inna ce kawai itama zaune da Abokin hirar ta redio tana sauraren radio sokoto taji Sallamar su, da d'an gudun ta Rahama ta karasa gurinta Al Ameen kamar ya rikota yaji ganin yanda take mai gudu da ciki har wani bugawa kirjin shi keyi, karta fadi taja mai babbar hasara a rayuwa,

Maraba inna tayi musu tareda bazamai katuwar tabarma a tsafta taccen tsakar gidan ta da ba rana, ya zauna kanshi a kasa yana gaisuwa, inna ta Amsa itama cikin kunya tana cewa "yanzu ko baban ku zai shigo insha Allahu ku gaisa don yanzu yakirani yana zuwa,
Mikewa RAHAMA tayi ta shiga dakin inna tana kallon yanda aka tsara shi da kayan da akayi mata na Aure, inna ce tabiyo ta tace "kinga mujin ki yasa andawo mana da kayan dakin ki ko wai insa sun bar mana,
Dariya RAHAMA tayi tace "inna yaushe? "Ai tunbayan tafiyar ku da kwana biyu mota takawo su,

Saidaga baya yakira yake fada wa babanku wai kar abar kayan a jiye gwara ayi Amfani dasu,
Dadi RAHAMA taji sosai domin ita kanta taji dadin sauyin da kullum rayuwar su take samu Albarkacin wainnan bayin Allah don haka batada Abin fada sai godiya ga ubangiji,

Fitowa tayi tana kallon yanda ya natsu yana latsa wayar shi, kafin ma tayi wani motsi wayar ta tayi kara budewa tayi taga sakon shi, "let go baby, Allah yagani taso ya barta ta d'an yi hira da Inna Amma ya kasa ya tsare ya zatayi, dolen ta ta bishi yanda yakeso domin gudun fushin shi da yayi a gidan momy ya kuma yimata shi yanzu,

Inna tafada ma wa zasu tafi domin tana son su leka gidajen su yaya HAJARA,
Tace tom bazaku jira baban naku ba? "Zamu kuma dawo wa mugaida shi lokacin da yake gida, ya fada yana mikewa yayi hanyar waje bayan ya Ajiye mata kudi saman akwatin da suka shigo ds shi , yayi gaba yanawa Inna Sallama, tayi godiya sosai tareda sanya Albarka,
RAHAMA ta Kara yi mata Sallama suka ta tafi.

Daga nan gidan yaya HAJARA suka nufa,
Mugun sanyi jikin RAHAMA yayi tundaga kofar gidan da suka tsaya wanda da taimakon Husna suka san kwatancen,
Shi kanshi yaga reaction din ta da yanda fuskar ta ta nuna damuwa,
Ba abinda ya tsaya mata a zuciya sama ga burin Y'ar uwar tata nason zama gidan Alfarma da jindadi saidai ga inda Allah kuma ya kaddare ta da zama,
Tsayawa yayi a mota bayan ya fito mata da nata tsarabar ta bawa wani yaro ya daukar mata ta nufi cikin gidan tana tanbayar shi Hajara,

Yaron yace " matar bello? "Eh tace, "mutai, yana gaba har sasan su lokacin tana wanke wanke jibgi na gidan suna zuba hira da surukan nata, tajiyo Sallamar RAHAMA ,
Zabura tayi jikinta narawa ta kalleta cike da rawar jiki " RAHAMA!

Kokarin maida kwallar idanun ta tayi tace "na am yaya HAJARA. "Yaushe kika dawo tafada tareda nufota cikeda zumudi da kewar ganin Y'ar gudan kanwar tata mai kama da matar gwamnan sokoto,

Matan gidan ma sakin baki sukayi suna kallon wannan classic lady din da duk kamshin ta ya cika gidan, ta gaida su cikeda mutun tawa tareda sakin fuska, HAJARA baki har kunne tace " kanwata ce,
Duka rika mamaki duk da dai ko HAJARA ba baya ba wajen kyau da haduwa amma RAHAMA yanzu tasha gaban ta.... 🖊

*Matar Soja*
2/28/21, 6:17 PM - Q: 🌻🌻
*ZANYI BIYAYYA*
🌻🌻

*By FENERH*

5⃣3⃣&5⃣4⃣
Chapter 37 · 0% Book details