← Book details Zanyi Biyayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 60

Sashe 38

Zanyi Biyayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daki suka shiga duk ta rude saboda murnar ganin Y'ar uwar ta a gidan ta tace ina Al Ameen?
Yana waje yace inyi sauri ne ma zamuje gidan Yaya Aliyu, "naga ku yanzu ai kinzama manya RAHAMA, don Allah ki yafewa yayar ki kinji, saurin matsawa tayi jikinta ta rungume ta tareda share kwallar tausayi,
" wallahi ba komai Yaya ni bantaba rike ki da wata manufa ba saboda ke jini nace,
Sun dan taba hirar bayan Rabuwa kafin Kiran Al Ameen ya shigo, bata daga ba ta mike " yaya zamu tafi kayan da aka shigo dashi tsarabar kice, ta bude jakar ta ta zaro kudi yakai 20k ta mika mata " gashi ki rabawa Y'an gidan ku da yara, ta kuma mika mata wata, "ungo wannan ki rike naki ne,

Wani irin kukan dadi yaya HAJARA tasa tareda rungume Y'ar kanwar tata tana kara godiya, ta share mata hawaye " kiyi hakuri zakiyi farin ciki insha Allahu,
Ta fita tareda Sallamar mutanen gidan,
Daga sasan suka rabu tana daga mata hannu domin batajin zata iya fits su hada ido da Al Ameen, koma wa tayi cikin gidan tana murna ta ciro kudin da aka basu ta mika musu " gashi ku raba inji kanwa ts,
Ai jikin su har rawa yakeyi wurin rigen rigen dafe kudin, suna zabga godiya da shi Al barka,

Fitowa tayi jikin ta a sanyaye,
Wanda Al Ameen tuni ya gane damuwar ta yasan ta akan Y'ar uwar tata, shi kanshi ya tuna gwagwar mayar HAJARA A rayuwa duk bata wuce ta shiga daula ba sai gata a irin wannan katon gidan gandu, Allah mai yanda yaso, ace the classy Hajara ce a gidan kasa,

Bai ce mata komai ba har suka je gidan Husna, wadda tayi fushi domin natsuwa da son ganin su da tayi,
D'an rungume ta Al Ameen yayi " sorry little sis gamu munzo munfara zuwa gidan su inna dasu Momy ne, yanzu ma daga gidan HAJARA muke, "wato nice karshe tafada tana turo baki,
"Ayi mana Afuwa my Aunty Husna,
A nan gidan kam sundade sosai har dashi bindin sukaci sukasha, gidan nata ba laifi duk da NA hayane anasa ran watara na, zai mallaki nashi inda rai da rabo,

Sai kusan magrib suna bar gidan Husna bayan sun ajiye mata nata tsarabar, yayan ta ya bata na sa mai ta rakosu suka koma gidan momy,
Yana Tsayawa tafita shikuma ya wuce masallaci, ta shige cikin gidan,

Momy tace ai Nadauka bazaku dawo ba,? "Muna can muna yawo gidan Husna muka dade, toh kije kiyi sallah kafin babanku sudawo masallaci,
Tsohon dakin Husna ta shiga saida tayi wanka tayi sallah tareda mayarda kayan ta ta fito, ba Abinda take kauna sai kwanciya, don haka yanzu burin ta bai wuce suzo sutafi ba,

Saida sukayi isha'i suka shigo, ta gaida dady shima ya Amsa cikeda farin ciki,
Suka baje dining suka kwashi girkin momy suna yi suna hira dady farin ciki kamar yayi me ganin d'an shi ya samu kwanciyar hankali ga lafiya yanzu, ba Abinda yafi wannan dadi a wurin su domin Ada ciwon shi shine babbar damuwar, yanzu kuwa harda rabo,

Ba nakasar da tafi kowacce tashin hankali a wurin da namiji sama da rashin lafiyar mazakuta, domin inhar bakada wannan lafiyar tofa kayi mutuwar tsaye, shi kam Alhmdulillah iyayen shi sunyi iyakar kokarin su da lokacin da zai san Amfanin ta bazata yi mai aiki ba,
Sai kusan tara suka bar gidan,
Sai gidan su, ranar kam dole ya daga kafa domin yaga Alamar gajiya a tattare da ita,

******************************

Bayan wata uku lokacin Cikin Rahama yakai wata uku, zama dakyar tashi da dabara Al Ameen yagama shirya komai saboda zumudi dakin yara ma antsara shi sosai anzuba gado da kayan wasanni Kala Kala,
Anata fama yabarta zuwa wankan gida ya murzawa idanun shi toka, kuma wani lokaci ba komai iyaye kewa gudu ba, idan har baka samu wankan farko mai kyau ba to daga baya kana iya fuskantar matsala, amma fir yaki Dady ma yaki bari su hadu domin yasan neman shi yakeyi,
KO gidan momy ya yanke zuwa saboda kullum zancen ta daya ne, ita kanta RAHAMA tafison taje gidansu domin itace damar ta takarshe da zata je gidan Inna ta zauna,

Tana matukar son ta saka baki Amma tasan fushi zaiyi idan ta rokeshi yabar ta zuwa wankan zaice dama batason shi shiyasa ta ke son ta gudu tabar gidan shi, domin wannan gorin rashin so bai daina fadar shi ba har gobe,
Idan ya tuna da zancen ta da HAJARA na cewa itama bason zaman gidan shi takeyi ba, wanda a lokacin tana cikin fargabar zama a gidan shi, ga fitinar HAJARA a lokacin na son Al Ameen dole tasa ta fadi Kalmar,

A zaune take a falon ta mike kafar ta tunanin ta yayi nisa ya shigo har saida ya zauna a gefen ta ya shafo fuskar ta tayi saurin juyowa tareda Ajiyar zuciya ta sakar mai murmushi,
"Me ake tunani maman Y'an biyu? Yafada yana kai hannun shi kan katon cikin ta, bata rai tayi " kadaina yimin fatan biyu mana, ko yanzu fa a mugun tsorace nake wallahi inna tuna dole sai wannan abin ya fito,

Dariya yayi tareda zama a kasan gab da ita " sosai kuwa tunda na saka dole yafito, Amma kuma tare zamuje haihuwar zantaya ki, " ai da zaka iya taya ni mika maka zanyi saika haifeshi, "Haka Allah ya tsara mu mu saka ku ku kenkyashe,
Now fadamin me kike tunani? Nasan ba wani haihuwa kike tunani ba, " yes ina tunanin zuwa gidan Inna ne in haihu please karka fassara ni kaga kowa haka yakeso domin ba wanda zai iya tsayawa dani kuma haihuwar farko ce,

Gyara zama yayi batareda ya bata raiba yace " kina so kije? Daga mai kai tayi tareda marai rai cewa, " ok mufara hada kayan ba damuwa bayan haihuwar zanyi Tafiya zuwa China oder wasu kayan company na da na dady don haka no problem, Amma sai kin haihu zan iya daurewa na sati daya bakya tare dani Amma ana gama suna zan gudu,
Cikeda farin ciki tace godiya nakeyi,

Sun shirya komai na Tafiya wankan ya fadawa momy ya yarda taje wankan gidan momy tayi matukar mamakin canjin Al amarin, wanda sai daga baya ta gano akwai Tafiya a gaban shi shiyasa yayi saurin sakkowa,
Yau kamar anyi ma RAHAMA wahayi da yin aiki tunda safe ta tsiri sanitation din gidan ta harda gyara tsarin dakin baccin ta wanda ta dade batayi aiki irin wannan ba, saida ta gama tsab bayan ta yafara Amsawa tuni ta samu wuri daya ta zauna tana cije lebe, koda mai akin ta ta leko taga yanda take gumi taji tsoro tareda matsowa cikin rawar jiki, " hajiya dama aiki kikeyi baki kira na tayaki ba gaki da nauyi kika hau aiki irin wanna?

Dakyar ta ke daga kanta a yanzu Domin ciwon da gaske yakeyi, wani irin rikewa marar ta keyi kafin taji d'an shin wani irin ruwa na bin ta, cikin karfin hali tace bani waya ta, da sauri ta dakko tace duba min number mijina itace farko a dial call,
Kiran shi tayi yana dauka yafara magana " gani a kofar gidan ki habibty, ya datse call din domin ya shigo gidan shi,

Zamewa tayi tareda nunawa mai aiki ta fita, ta fara murkusu su tareda juyi so take ta mike tsaye Amma wani Abu ya tokare ta ya hana ta mike,
Da fara'ar shi ya shigo tareda cewa ina maman biyun..... Saurin karasowa yayi da gudu yana lafiya? Domin tun shigowar shi ya hango halin da take ciki, kokarin daga ta yakeyi, "please ka kaini Asibiti haihuwar ce ruwa na zuba tafada mai cikeda dauriya,
Saida yayi kokarin tsayar da ita yaga yanda ruwan kebin kafafun ta, tace ya cire mata pant din jikinta yana damun ta,
Saurin daga doguwar rigar tata yayi ya zame pant din da yariga ya jike ya nufi wurin da take Ajiye hijab din sallar ta, cikin tsananin rudu da tausayin yanda take cije lebe,

Yana juyowa yaga ta na kokarin durkusawa, da gudu ya wurgar da hijabin ya rugo " baby daure mu wuce Asibiti kinji Allah zai sauke ki lafiya kinji,

"Abu zai fito.... Tafada da karfi cikin fisgo da zancen domin tanajin yanda Abun ke kun no kai wanda dole ta ware duk da batasan yanda akeyi ba, ganin yanda take numfashi da nishi yasa yasa duk ya furgice, kafin ma ya nemi mafita yaji kukan jariri,

Gashi tsaye kamar gunki, kasan ya Kalla yaga katon jariri yayi saurin zubewa gaban ta yana ware ido, tareda sungumar dan da cibiya da jini da komai bakin shi na rawa " kin haihu baby????? Allahu Akbar yafara jerowa batareda sanin Abinda zaiyi ba, Allah ya taimake ta mabiya ma tafado ta baje a wurin tana maida numfashi,
"Ka kira momy kafada mata kaga yanke cibi bamu iya ba,
Shi ina ma yasan inda hankalin shi yake yana cikin farin ciki........... 🖊

*Matar Soja*
2/28/21, 6:17 PM - Q: 🌻🌻
*ZANYI BIYAYYA*
🌻🌻

*By FENERH*

5⃣5⃣&5⃣6⃣

Shigowar mai aikin ta ne ya sa ya fara dawowa cikin natsuwar shi, da yake ba yarin ya bace ta ga Alamar nakuda RAHAMA keyi don haka takasa sukuni koda ta sauka dole tasa ta dawo saman, kuma ta na shigowa taji kukan jariri, shiyasa ta karasa dakin da gudu taganshi zaune dumu dumu cikin jinin shima ga jariri a kan jikin shi duk ya rude saboda farin ciki, sai surutai yakeyi,
Da gudu ta karaso tace "masha Allah hajiya kin sauka cikin sauki akwai reza a yanke cibi?
Nuna mata drower tayi ta ruga ta ciro sabuwar reza ta dawo tareda cewa "ranka ya dade kawo jaririn mugani saika je ka gyara jikin ka, karbar yaron tayi tubarkallah dashi katoto mai hasken ubanshi ta yanke cibiya shikuwa ya matsa gaban RAHAMA ya na shafa kanta,
Chapter 38 · 0% Book details