← Book details Zanyi Biyayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 60

Sashe 36

Zanyi Biyayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ke HAJARA Karki manta da waye kike shirmen ki nice ladidi shedaniya kinsani kowa yasani ni nafi karfin ki idan kikace zakija dani sai na daidaita rayuwar ki, indai da Boka da kuma malamai basu kare ba,
"Kai ai bokayen har yau basuyi miki rana ba don basu baki Abinda kike nema ba a duniya shine kudi da kuma miji na nunawa duniya, nikuwa kinsani samari ba kalar wanda bangani ba Ashe koremin kikeyi saboda bakin ciki da hassada, to ki saka a ranki Arzikin mutum najikin shi watarana indai da rai da Aron rayuwa zaki gani ladidi don haka ayi gaba ki kwashi wannan kawar taki mai siffar Aljanu kuyi gaba,
Kuma ki rubuta ki Ajiye Bokayen ki, munfi karfin su mu jinin kebbi ne baki isa ba don haka muke ....... Wani irin uwar Ashar ta dura tareda zabura tayi cikin Hajara wanda tasa Kara domin taji shakar,
Da gudu surukan ta sukayo dakin domin jin Meke faruwa, ganin yanda Ladidi ta cukui kuye Hajara kawarta na kokarin cireta " ke ladidi gidan mijin ta fa mukazo keda zaki bari a hade a hanya kisa mota tabi ta kanta kizo kina so ki janyo muna bala'i, tafada tareda kokarin cire hanun ta a makogoron HAJARA,

Da mugun gudu suka fado dakin suna salallami ganin Meke faruwa, kishiyar maman bello dake a tsaye take ta fisgo ladidi kamar sanda ta watsa mata Mari, uwar shi na sababi tace " ku gane min mugun Abu ki biyomin sarakkuwa har daki ki ce zaki bugunta wallahi yau karyakki ta kare ko, kai ku kiromin d'an ga ku gane ta fadawa yaran dake tsaye curko curko suma,

Dakyar numfashin HAJARA ya tsaya domin taji shakar, maman bello tace " ke mi kinyi mata? Ta gyara makoshi tareda cewa " wai inna dole inkashe Aure na tazo sai kokarin take inbita inbar gidan nikuma nafada mata ina son mijina,
Nafada mata shine ta shake ni,
Salati sukasa ladidi ta fara zare idanun ta ganin yanda suka tsare ta sun hanata ko hanyar fita

Daga gani zataci ubanta yau, kawar ta dai tafita tsurewa, Dariya HAJARA tafarayi kasa kasa,
Sababi suketa yi tana gumi "Ai yau sai ke gsni gidanga indai bakida mutunci kitsko ki isko macce har cikin gidan Auren ta ki buga bayan kokarin kashe Arme, Auren da dana kajin dadi nai yayi sa'a don tunda tasshigo ko Abinci bamu koma saye ba yanzu kikaso ki kore muna ita don bakin ciki to Allah ya hiki,

Sallamar bello ne yasa innar ta tareshi tareda fadamai abinda sukayi ma HAJARA, ai ko k'irewa yayi tareda bankawa cikin dakin yana "Ina munahuka Allah take yau bane kacinki gareni, matata kika shigowa har cikin gida ki buga wallahi yau kina ganewa,

Wani irin trumbling cikin ladidi yafara yi kafin ma ya karaso kishiyar inna ta fisgo ta tareda kawar ta,
Wani irin wawan hambari yayi Mata tareda yin kwallo da dukansu, kunsan basakkwace da zucciya ai ko bugun fulawar gidan burodi yayi musu ligis su inna na taya shi, ga HAJARA da ke gefe, dataga zai daina sai ta sa kuka tana rike wuya, tuni zuciyar shi zata sake dugun zuma yaji sabon karfi,
Saida aka shigo aka kwace su jini hanci baki goshi ido ko ina ya kunbura saboda masga,

Yace kuma sai ya maka su kotu idan cikin matatai Ya zube, wanda sai a lokacin mutanen gidan ma ke sani suka fara murna da farin ciki,
Tuni aka watsa su ladidi waje sukuma suka zauna jin dadi, ko banza sunsan idan ta haihu zasu kwashi wata gara domin kowa yasan Al adar sakkoto da bidi'ar gara ta Aure da haihuwa,

****************

A yaune Su RAHAMA suka duro Nigeria cikeda samun nasarori daban daban ga cikin ta yafito sosai tana Tafiya irin ta takama na masu ciki ga kuma gwarzon mijinta a gefe, idan ta bude baki zaka hango dallelen hakorin ta na gold yana sheki fadin kyau da takara bata bakine

Driver ya kwashe su suna makale da juna sai gidan su da aka gyara shi tsab ga masu aiki yanzu ta ko ina da momy ta zuba domin bataso a wahalar mata da jika,

Husna Amarya ce tazo gidan ta shirya musu girkin tarba tareda jiran isowar su tunda Aliyu baya gari, itama tayi shar da ita kana ganin ta kasan oga Aliyu na bata madara yanda ya kamata,

Lokacin da motarsu ta tsaya da gudu Husna ta fita tareda bude motar jikin ta NA rawa ta rungume RAHAMA " Oyoyo sister inlow nayi matukar kewar ki, tafada cikeda zumudi da kuma farin ciki,
Dariya Al Ameen yayi musu kafin yace "hy sister Karfa ki matse min yaro ya fito da guntun hanci irin naki,

Sakin ta tayi tareda kallon cikin d'an kimanin wata shida dayayi girma ta shafa tana tsallen murna "babyn mu ya kusa fitowa yaya, kafin ta tura baki ta kalle shi " Amma kuma ai yaya na fika hanci kake zagin nawa bayan ni da hancina kamar biro ko RAHAMA? Tafada tana kallon ta,

Harara ta watsa mata " hmm bakiji da kyau ba kece kikafi mijina kyau? Lallai ma kije ki kara duba madubi,
Nice dai kinsani nafi naki mijin ko?
Bata rai tayi tareda karbar hand bag din RAHAMA ta juya tana magana " kuzo muje kafin ki tabo zuciya ta " don mijina zuciya tane uhm,

"Lallai Husna bakida kunya a gabana kike zancen mijinki? " to yaya ita ba a gabana take kushe min mijiba, RAHAMA dai dariya kawai tayi tana Mai jin dadin ta dawo kasar ta,

Wanka suka farayi tareda shiryawa, ita tafara fitowa domin tana jin yunwa sosai ta matsu bataci Abincin kasar ta ba,
Zama tayi taci ko jiran Al Ameen batayi ba saida tayi kat kafin ya fito, ya zuba mata ido" baby wanna sauri haka ba jira? "Wallahi yunwa nakeji and kuma naga tuwon shinkafa da miyar sure dole inkasa jiran ka,

Zoka zauna kaci tafada tana daukar plate ta zuba Mai tareda saka Mai spoon, zama yayi gab da ita yana kallon cikin shi yayi murmushi, " my baby is growing domin tana samun enough taki yanzu his\her father is fine now,
Yafada yana shafawa tareda narke idanuwan shi cikin nata wanda tasan salon kallon me yake nufi,

" um um fa dear karka fara nagaji fa yanzu ina gama cin Abinci zan kwanta inyi bacci, gobe maje gidan momy inmun huta da gidan su Inna da yaya HAJARA,
Langabe kanshi yayi tareda ture Abincin yace "to zan zauna da yunwa kuwa, domin gwara kibani wanna da ki hanani tuwon,

Dariya zancen shi yabata ta matsa dai dai kunnen shi tace " ai Duka dole kaci domin nakane mallakin ka ne sai yanda kayi da ni da kuma gidanka banaso mijina na rara gefe bayan yanada gidan hutu, rungume ta yayi yana godiya tareda cewa " insha Allahu baby sai na faranta miki kamar yanda kike kokarin faranta min, "bana bukatar komai mijina nidai soyayayr ka ma ta ishe ni da kulawar ka gwarzon mijina,
"Bakya bukatar komai a duniya? Yafada yana kallon ta, "kabani komai mijina saura Aljannah ka yarde min kawai in wuce,, "na daga kafata tuni har kin shige da izinin ubangiji don haka ki kwantar da hankalin ki matar Aljannah ta nasan kina bukatar wani Abu kuma Zanbaki shi insha Allahu inda rai da rabo,

Fitowar Husna yasa suka yi shiru tareda
Ci gaba da cin Abincin su, " tace ni natafi gidana, sai kunzo inba haka ba bazan kuma zuwa gidan kuba, tafada tana fita.
"Haba Aunty Husna kibari in kammala in rakaki kuma saurin me kikeyi haka? Bayan yaya baya gari,

"To me zanyi muku ku huta Kawai in ku kammala akwai masu aikin ki mata zasuyi miki wanke wanke da shara suna dakin kasa da kika taba zama, ni na tafi,
Tashi RAHAMA tayi bari ni in raka matar babban yaya dole na, tana biye da ita shikuwa wani irin murmushin jin dadi yakeyi yasan baida matsalar fadan kanwar miji da matar yaya a gidan shi,

Motar da tagani dalleliya Husna ta bude da sam bata ganta ba farkon isowar su sai yanzu ta lura
tace sai matar yaya wannan sabuwar fa?
"Wedding gift from oga tawa ya karba yabani sabuwar nan,
"Wayau dai yayi miki wedding gift ko wayau? " to zuga zugi wanna motar kudinta yayi biyun tawa yace bazai hau babbar mota ni inhau karama ba don haka malama maida wukar gulmar, tafada tana fadawa motar ta,
RAHAMA ta kwashe da dariya tace "wai tsaya, asiri kika wa yaya na ne haka? " eh ke kika kaini inda kika kai nawa yayan ai,
Dariya Duka sukasaka tayi mata godiya tareda daga mata hannu Mai gadi ya bude mata kofa tayi waje,

Hamdala tayi tana godiya ga Allah domin tasan Aliyu yasamu daukaka cikin lokaci kadan yana aiki yana business tareda baba don haka basuda sauran wata matsala a rayuwar su,

Ciki ta koma tareda samun shi har ya kammala ya kwashe kayan, ya kalle ta yana murmushi " kungama gulmar?
"Mu bama gulma saidai muyi gyaran Auren mu yanda zamu kara mallake ku,

"Hhhhh abarmu haka karmu kasa fita nemo muku na tuwo fa, amma kuma zankara kudi a kuma kaiwa wurinda ke karo dadi domin inkara morewa, yafada yana cirata sama yayi bedroom da ita....... 🖊

*Matar Soja*
2/28/21, 6:17 PM - Q: 🌻🌻
*ZANYI BIYAYYA*
🌻🌻

*By FENERH*

*ga masu bukatar biya ku hanzarta kar Abaku labari ku biya ku karanta cikin Aminci,katin Airtel 200 zaku turo normal vip 500 kuturo katin ku ta wannan numbar 09011251444 ko ta Asusun banki na 7304736012 nafisa sani Fcmb don Allah vip Kudaina turomin kati idan kana son vip kutura min ta banki katin nayimin yawa sosai in bakuda Account kibayar a pos don Allah sucire charges dinsu a ciki, Y'an Niger 🇳🇪 masu bukatar biya ku nemi wanna number +225 48 15 39 03*
Chapter 36 · 0% Book details