← Book details Zanyi Biyayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 60

Sashe 46

Zanyi Biyayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saurin riko hannun momyn nashi yayi " momy ya sadiq zata Aura? "Eh, Hmmmm, ok ya fada yana sakin ta ya fita a dakin kawai jikin shi a sanyaye, a zuciyar shi yace "relax meenal kinsamu zabin zuciyar ki Amma ni sai hakuri, and am happy for you, yafada yana komawa dakin shi, zaiyi iya yinshi ya goge tunanin ta, anyway yasan ta fi karfin shi don haka Zai tayata murna da farin ciki,

*******************

Shirin biki sukeyi sosai Auren Y'an gata ta ko ina, HAJARA da kanta ta dage tana gyara Meenal, farin ciki ne a zuciyar ta fiyeda tunani, Allah kadai yasan me ya boye a cikin mukaddarin rayuwar su don haka dole ta godewa Allah bata Auri Al Ameen ba yau ga ya'yan su zasuyi Aure, Allah mai girma,
Koda yaushe cikin kukan zuci Meenal take domin kukan ma yadaina fita mata, gashi bata fita konan da can saboda mai gyaran dake musu itada kannen ta ko kawayen ta bata fada mawa ba don gani take ba Auren farin ciki zatayi ba mezatayi da wasu kawaye, kannen ta dai Fati suke shiryawa na fitar hankali wanda tace bata ciki,

Gefen Ango Sadiq kuwa aiki ma yataso mai suna bakin border kwana biyu baya zama duk shirin da akeyi bai sani ba, Su Husna dai sun karbi kudi dole a wurin shi, da aka tsantsara mata lefe na kece raini, grandma tace sai Anyi set Biyar Auren sadiq dinta, akwuwa an narka dukiya,
Ga dalleliyar mota Y'ar yayi ta mata Y'ar karama dall a leda, daga Al Ameen,
RAHAMA kuwa gold ta zuba masu shegen tsada don tace Y'ar tace ko badon zata Auri sadiq ba,

Sai Ana saura two days ya dawo, yayi mugun mamakin ganin yanda gidan su ya cika makil da mutane, sai a lokacin ya tuna da wani zancen Aure, don haka juyawa yayi kawai yayi gidan shi a GRA, yayi matukar mamakin ganin an gama tsara komai an shirya dakunan shi da gadaje masu tsada komai Italian,
Imagining yayi dama Ace wata ce za a Auro mai ba wannan yarinyar da sam baima san yanda zai iya sarrafata ba,
Wallahi da ya more sadakin da baban shi ya biya mai, a daren farko Amma shi yazaiyi da ita karshe ma raini zai shiga tsakanin su tana ganin they are age mate, mtswww tsaki yayi, "nida keson Aure zasu hadani da wanna dama banfada ba na bari sha'awar ta kashe ni,

Yasan yau ma inyace zaiyi bacci a gidan nan zai yi kwanan wuya don kwana biyu don yana busy ne yasa ba abinda yadame shi Amma yau yanda suka kawata gidan nan dole yafara tunanin samun wurin da zai juye ruwan jarabar shi,

Wanka yayi ya canja yayi gidan kakarshi kawai, can ma yasamu tanata hada kayanta domin dole zata koma gidan nasu saboda biki, "wai ina zakije ne haka? "Gidan ubanka zanje wurin Aure ko kar inje? "Hmm grandma please ni fa am not happy about this marriage at All amma ke sai wani rawar jiki kikeyi nifa dama kunfasa meye Amfanin Auren da ba biyan bukata,

Zama tayi ta zuba mai ido, " fadamin me kake nufi? Gyara zaman shi yayi ya falle idon shi don akwai rashin kunya tsakanin shi da ita yace" nifa ko wallahi bansan wace irin rayuwa zanyi da sa'ata ba, and secondly kinsan ra ayina banason babbar mace, ni nafisan undergraduate wadda zan juya ta, yadda nakeso, but wannan cewa zatayi ma may be am too young for her,
"You are mistaken, yarinyar na sonka sosai couse Nasir yafada min dazu she is crying batason Aure saboda she is Already in love with you,tana tunanin wani ne na daban zata Aura bakai ba, kaga zakaji dadin zama da ita saboda Already ta rayu da soyayyar ka,

Wani irin kallo yayiwa grandma, " she loves me? How? Abin yajishi wani iri yazata soshi bayan bai taba koda minti biyu tareda itaba? Yasaba jin Y'an mata na fadamai suna sonshi but bai taba jin Kalmar wani iri ba sai yau da aka fada mai the girl he is going to Mary is already in love with him, this is strange yafada domin wani irin strange feeling yakeji a zuciyar shi shidai yasani, duk yaran family dinsu bai taba tsayawa da kowa kona minti biyu ba impact wasuma ko a hanya zai iya wucewa su wuce he don't really no them, ita kanta bazai fadi how she look ba,

Kawai tsintar zuciyar shi yayi tana sakewa tareda jin wani irin feeling na girman kai tana sonshi har tana kuka, Hmmm so yake yaga yazatayi if tasan shi zata Aura? Wow Abin zai matukar kayatar dashi sosai Allah yasa kar Afada mata shine, kawai yaji yanaso yaga how she is going to react Abin zai mugun burgewa, he is eager to see that,

"Idan ka gama tunanin tashi ka kaini gidan naku, grandma dinshi ta fada,
Zabura yayi yace suje, don he is already lost, thinking of some one loves him deeply har tana kuka because of him, makes him feel proud, shi baida lokacin kowa mata ma tun tashin shi baya harkar su da wuya ya fita shikadai yaje wuri saboda his father is very protective about him tun yana yaro ma lokacin da ya girma ma baida lokacin shirme friends ma saidai na school he is like his father baida kwashe kwashen friends,

Shiyasa yake jin wani iri akan abin mata kuwa masu binshi wasu a wurin aiki ne wasu a Instagram duk da bawai yana advertising kanshi bane but ansan waye shi,
Sannan yanzu aikin shi da koda yaushe yana yawo baida lokacin all that stuffs,
Sha'awa kuwa is his nature wanda yanaji bakaramin wuya zaibawa mace ba inta shigo hannu, but what about this one?

Har yakai grandma gidansu baice komai ba yana faman tunani, yana tsayawa tace "Alhmdulillah tunda ka kawoni lafiya saika wuce ace mutum yayi shiru yana tunani ayita magana ba Amsa tunanin ma me kakeyi?
"Nothing bari inshiga ingaida momy dazu nazo nakasa shiga saboda mutane, don haka bayanta yabi tareda daukar jakar ta suka shige,

RAHAMA ta taso da sauri tana tsakiyar kawayen su da kuma husna itama suka taresu, gaida su yayi Husna ta hade rai, "kai wane irin ango ne kamaje wurin Amaryar taka kuwa? Dukar da kai yayi " no momy yanzu fa nadawo garin, " ok kaje kabasu kudin lalle, ", Hmm tom yafada ya na barin gidan, bayajin zai iya zuwa gidan Amma shiba marowaci bane don haka wani yaron gidan ya kira ya cire dubu hamsin ya ce yaje gidan mama HAJARA yabata yace kudin lallen Amarya ne,

Gefen meenal duk da bata farin ciki amma ta gyaru in and out har wani sheki fatar ta keyi saboda gyara ga wani laushi ita kanta sai shafa jikinta takeyi saboda laushi, tafi kannin ta kyau nesa ba kusa ba saboda ita kama take da maman ta harma tafi maman ta komai,
Kallon jikinta takeyi sosai "ina ma yaya Sadiq ne zata Aura da tasan dole taja hankalin shi don tasan ita din ba macen da namiji zai kibace da garaje,

Kannin tane suka shigo "Aunty Anjima fa akwai dinner angwaye zasuje don Allah ki kira brother inlow shima yaje, kallon banza tayi musu tareda yin shiru don bama tason dogon turanci,
Haka suka gama naci suka fita,

Karfe bakwai na daren kowa yagama shiri ana jiran da anyi isha a wuce wurin party ita kadaice kwance ba ta shiga sabgogin su,
Mama HAJARA ce ta shigo, "ke tashi ga mai kwalliya tazo kishirya kema kije,
"Mama don Allah kibarni wallahi zazzabi ma nakeji, "banson shirme kitashi nace ko ranki ya baci kinji,

Ba musu ta mike tuni taji ma zazzabin yazo da gaske Allah yagani batason zuwa ko, ina impact she is not ready to meet who ever he is,
Amma dolenta ta shiga ta tsaro wanka ta tsane jikinta tunda bata salla ta zauna aka tsara mata ado na daukar hankali, wata doguwar rigar material kamar wedding gown sky blue kamar French less ta hadu ga bayanta najan kasa ta saka make up artist din ta daura mata silver head ga purse da takalmi suma siver saman rigar net ne kana ganin yanda kirjin nan kamar suyi Amai saboda cikowa da turowa fadin kyanta bata time ne gashi anzubo Sumata da tasha gyara har baya, fuskar tace kawai ba fara'a Amma ko ina masha Allah,

Tana kammala wa mama ta shigo tayi tasbihi tareda riko hannun ta suka fita har waje tasaka ta a wata mota itakadai sai kawar ta da batasan ma tazoba driver yaja suka fita, "Amma meenal bakida kirki ko ki hayyace ni? Ai gashi yanzu mama ta kirani nazo, Gaskiya Angon nan zaki haukatashi idan yaganki babe,
Matse fuska tayi "Hmm am not happy fa bakya gani" kekika sani dai ni baruwa na mama tace inkula dake,

Gefen Ango ma momy Husna ta kirashi tasa ya shirya dole ya tafi shida drivern shi yana imagining yanda zai kalleta so yake yaga reaction dinta ma don haka ya matsu suyi two eyes ya kara jan Ajin shi, gashi cikin farin yadi mai tsada yayi matukar yin kyau kanshi da hula Y'ar gaske yana buga kamshi da sheki gemun nan na gayun yanzu yasha gyara,
Wayar shi yake matsawa a natse....... 🖊

*Matar Soja*
2/28/21, 6:17 PM - Q: 🌻🌻
*ZANYI BIYAYYA*
🌻🌻

*By FENERH*

6⃣7⃣&6⃣8⃣
Chapter 46 · 0% Book details