← Book details Zanyi Biyayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 60

Sashe 5

Zanyi Biyayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*munada lases masu inganci da kuma quality munada atamfofi na yayi da kuma shaddodi domin sabunta mai gida ku fito kuyi odar cikin farashi mai rahusa,akwai masu saukin kudi akwai kuma manya, ku fito kuyi tanadin sallah mata masu Aji, ance mai kwamin ido da wuri yake fara kuka siyan nagari maida kudi gida, to place your oder just give us a call 0803 343 8895*

5⃣&6⃣

Kusan raba dare tayi a ranar takasa bacci, tsawon rayuwar ta bata taba kawo zatayi Aure nan kusa ba sai gashi yau saura kwana hudu wai A daura mata Aure, kokarin saita tunanin ta takeyi ganin bacci yaki zuwa haka ta fito tsakiyar gidan su tayi Alwala a bakin fanfo ta koma daki tareda tada salla, saida tayi raka'a biyu kafin ta janyo carbinta tafara istigifari, qur ani ta bude tafara rero k'ira'ar ta mai dad'in saurare,
Tana kan daddumar ta har Asuba, saida ta sallaci Asuba tadan kishingida kafin gari yayi haske ta taya inna aiki kamar yadda ta saba, saidai bacci yayi nasarar tafiya da ita saboda rashin bacci,
Koda safiya ta waye inna larai ta leko ta ganta kawai komawa tayi tayi aikin ta tana mai tausayawa Y'ar tata, tasan dagani batayi bacci ba daren jiya,

Karfe goman safe tayi salati tareda zabura ganin yanda gari yayi haske sosai, tafito tsakar gidan data tarar komai inna ta kammala, "kintashi RAHAMA? Eh inna ina kwana? Lafiya kalau, yau kinsha bacci, wallahi daga kishin gida gashi inada test, "ai kidaina maganar karatun nan malam ya dakatar, yace Karki kuma fita ko kofar gida,
Wani irin ras gabanta ya buga Amma tayi Alkawarin bata ba musu da iyayen ta, Amma kallo daya zakayi mata tabaka tausayi sosai,

Cewa kawai tayi tom inna, ta ce " me zan tayaki? "Ai na kammala komai kije kidibi ruwan zafi kiyi wanka,
Yau ki huta, ga abin karin kinan a kitchen, to tace ta koma daki tareda tubewa ta daura zanin ta tareda dora hijabi karami tafita wanka,

Kamar wasa Y'an uwa duk an hallara shiri kawai akeyi duk da lokaci ya kure a haka suke mata gyara sama sama kannin inna mata da sukazo, gyara irin nasu na gargajiya na lalle wanda keda sirri fiye ma da NA zamani, kokarin sakawa zuciyar ta walwala takeyi domin gudun batawa iyayen ta rai Amma sau da yawa tana kulle kanta taci kukanta sai ta Koshi,
Ko wanka ta shiga sai taci kukanta take fitowa, HAJARA kuwa tafara nadamar tafiyar ta domin jitake kamar ta dawo gidan Amma kawarta nakara zugata karta koma sai bayan bikin tareda nuna mata ita ba matar da za ayiwa irin mugun Auren nan bane, tana kodata da Kara mata dogon buri, ita kuwa haka takeso taga ana Yabawa kyanta a kullum,

********************
"Wai Al Ameen bazakaje kaga gidan ka ba an hada komai an zuba maka kayan ka yanda kakeso har kayan Amfanin ka nasa ankai maka can so ina so ka tattara ka koma gidan ka tun Amarya bata isoba,
Ya mutsa fuska yayi tareda goge gumin da ya ke tsiyayo mai a jiki da wani farin towel, daga gani daga geming ya fito, "momy please kubar ni a nan me zanje inyi mata a can? Nifa banso aka gyara gidan nan ba ba saboda ita na kashe shekaru ina tsara gini naba, haka kawai nayi gini saboda ina son in shiga in huta kunzo zaku saka min wata, yafada yana wucewa,
"Allah, to kaje kafadawa ubanka hakan, bani marainiyar wayonka ba, iya shege tun ranar da yafada maka ko tak baka ceba Amma ni saboda ka raina ni kullum sai ka kawon zancen banza, kabari in anyi auren kasake ta inbaka so,

Gaban mirror dake dakin shi ya tsaya tareda zubawa kirar jikin shi ido shifa bayajin wannan jikin zai iya shearing din shi da kowacce jaka, domin baijin matar da keda wannan matsayin ma an 'kera ta,
Ni kuma nace rainin hankali wanda ya haura talatin yace ba a k'era matar shi ba to sai ya tsufa?
Kara matse fuska yayi da ya tuno da yarinyar nan da tamai rashin kunya ranar because of that girl ya tsani duk wata mace dake cikin garin sokoto in aka cire momyn shi da sister shi saboda Abinda tayi mai ranar yayi ta neman ta harda drivers din shi yasa su koma su nemo ta domin baijin zai iya yafe mata Abinda tayi Mai so easily, Amma ba a gano gidan su ba he pray koda sau daya ne Allah ya aramai dama sai ya wulakanta rayuwar ta, yanda gobe idan taga ya'yan hutu irin shi zata kauce musu a hanya,

******************************

Shiru tayi tana kallon yanda kowa ke kai da kawowa a cikin gidan, wai Auren ta ake daurawa a yau, Abu kamar a mafarki, har yanzu jin Abun take kamar wasa, gashi taji ana ta maganar kai kayan da baban ta yayi mata sunje gidan ko ina a cike ba wurin Sa komai, dole store suka zuba mata nata suka dawo, suna santin RAHAMA kin gama sa'a a rayuwar ki Y'ar uwar ki tayiwa kanta bakin ciki a rayuwa, haka suketa sambatu ita kuwa zuciyar ta fal fargaba da tsantsar tsoro ga hudubobin da takesha da sam bata taba jin irin su ba,
Tsawon rayuwar ta batada shige shige ko kawa batada ko a school she is leaving a lonely life dayawa kallon miskila ake mata saidai su gaisa ba ruwan ta da cusa kai gashi garin sokoto ya Tara ya'yan masu kudi ita kuwa tasani ita ba Y'ar kowa bace don haka ta iya kanta,

Amma yanzu hudubar hakkin mijin nan da aka yimata tun daren jiya tasa ta a duhu, Allah yasa ni batasan komai ba duk da tana da zurfin ilimi a Addini dai dai gwargwado amma zuciyar ta sam bata hango mata Abinda aka fada mata jiya,
Hardai zancen wata kanwar Inna dake Abuja da yake wa yayya ce sosai,
"RAHAMA kiyi maintaining jikin nan naki bakisan baiwar dake tattare da halittun jikin kiba, karkiyi tunanin HAJARA tafiki kyau ko kusa kinfi ta komai,
Kyan hali jiki mai daukar hankali da kuma iya zaman duniya, wanda shine hakuri matakin nasara,
Ba duk namiji zai 'kikiba ba sakaran namijin da zaiyi Arba da halittar jikin ki ya kawar da idanun shi, kiyi Amfani da damar ki da kuma wayon ki na ya' mace ki riko zuciyar mijinki da kyau,

Wannan hijabin da yazamar miki jiki daga nan gidan ki Ajiye shi, idan ba baki kikayi ba ya kasance koda yaushe kina cikin gayu, kaya Alhamdulillah an zuba miki harda na zaman falo, ga motar ki nan sabuwa dal an mayar miki gidan ki mun shirya miki komai kayan suturun ki, na jera miki show glass dinki na kayan kamshi da kuma su hakin maye,
Ke jinin sokotawa ce, bama boranci a gidan miji don haka ki koyi dabaru na shirya miki littattafai da zaki karu a cikin drowar dakin ki,

Magan ganun ta nada yawa Amma wasu sunfi tsaya mata a zuciya, wanda tana bukatar kuka Amma wazata yimawa da zai lallashe ta, mikewa tayi tareda fita dakin ta nufi na yayan ta dataji ya shigo,
Tana shiga tagan shi cikin farin yadi daidai talaka Amma ya fito fes domin yayan su shima badai zati da kyau ba,
Sallama tayi tareda karasawa da gudu ta fada jikin shi ta saka mai kuka,

"Subuhanallah, RAHAMA, yakira sunan ta tareda rungume ta tsam saida tayi kukan ta ma ishi kafin, yana tsaye batareda ya hana taba, saida yaji tafara Ajiyar zuciya, ya zaunar da ita gefen katifar shi Y'ar dai dai, ya tsuguna gaban ta,
"Me yasa kike bata kyakkyawar fuskar ki RAHAMA, yakama ta kiyi farin ciki, saboda kinada sakamako mai girma a gobe daga yau zaki shiga kwarya mai girma mai kuma dumbin lada,
Am happy for my sister gaskiya, and kinsan me? Ta girgiza kai tana share hawaye, am jealous, saboda da ni mace ne nine zan yarda baba yamun Auren in samu lada Amma kanwata ta kwashe,

Yafada cikeda tsokana saboda ya sata dariya, takoyi taji tasamu sauki sosai, "yaya karatuna fa? " kiyi hakuri idan har kinada rabo zakiyi RAHAMA,
Nidai so nake kiyi hakuri ki kwantar da hankalin ki komai zaiyi daidai kinji, kinga ana gama Aurenki zan koma wajen service dina, yasa hannu tareda ciro waya Y'ar karama kirar techno ya bata, gashi ki rike zamu rika gaisawa kafin mijin ki yasiya miki Babba domin ke yanzu you are a big girl, RAHAMA da mota, yafada yana dariya, she feels ok duk da baison magana Amma he try, domin ganin ta saki jiki, kuma Alhmdulillah, godiya tayi mai tareda cewa" yaya zankwan ta a dakin ka mutane sun cika a namu,
"Ok ni fita zanyi zamuje mu dauro don haka relax,
Daukar wayar shi yayi da hula ya fita,
Ta kwanta, tana kallon yar karamar wayar da ya bata akwai layi akwai numbobin kowa harda na HAJARA, duk da bata taba rike tata waya ba Amma ta san kan waya don tana taba na HAJARA da na inna wata rana, duba balance tayi tareda ganin naira Dari biyu, ta gwada kiran HAJARA cikin Sa"a ya shiga, zabura tayi zaune jikinta na rawa,
Picking HAJARA tayi tace hello, kuka ta saka mata tareda cewa " haba yaya meyasa zakiyi min haka me yasa zaki jefa iyayen mu cikin damuwa wallahi har yau baba cikin fushi yake a gidan nan baida walwala tunda kika bar gidan nan ko dariyar shi ba wanda ya kuma gani,

"Ni kuma yaya bakiyimin adalciba guduwar ki ta cutar da Rayuwata Auren da kike gudu ni an lika min karatuna ya tsaya ta kowane gefe kin kyauta kenan?
"Yi mun shiru banza dama ai roko na kike in yarda to ke me yasa kike kuka kiyi biyayyr mana inda dani,
"Bakiyi nadama ba yaya? Bakiji rashin kyautawar Abinda kikayi ba?
"Ke Karki dame ni da sirutunki na banza wawuya kawai dakikiya ke dama haka kikazo duniya da duhun kai kuma dama you deserve that. Da nasan kece ma bazan dauka ba don haka asha Amarci lafiya Amarya nasan dai ba akawo ko Ghana must go ba saboda Auren cushe ne,
Chapter 5 · 0% Book details