← Book details Waye Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 75 OF 84

Chapter seventy Four: Na'emah

Waye Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

Cigaba da yawo Samha tayi a asibitin tana kallon wards zuciyar tana karyewa musamman data zo A&E (Accident and emergency) wani irin rauni ne taji ya lulluɓe zuciyarta,it reminded her of her parents duk da basu taɓa zuwa asibiti ba don jinyar ko ɗaya daga cikin su ba! Tsayawa tayi a ƙofar wurin tana ganin yanda aka tangale ƙafar wani a sama fuskar shi was bandaged duk yaji jiki,ga nurses attending to him daga gani Bacci yake sai daga gefe ga wata mata ta zauna sai kuka take slowly take faɗin '' Yace na jira shi yanzu zai dawo,kuma i had wai....'' Samha bata tsaya da ji ƙarshen abinda matar zata faɗa ba saboda yanda zuciyar take tsananin duka,jikin tana shaking ƙafafunta sunyi rauni, idon ta suka ciko da hawaye ba abun da ya faɗo mata face last words ɗin Aliyu it sounded the same,shima a lokacin cewa yayi ' Ku jirani yanzu zan dawo ' wani murmushin baƙin ciki Samha tayi tana tafiya a hankali yan ƙaramin hawaye ya sauko saman fuskar ta slowly in a whisper tace

'' But you never came Papa! You never did!!"
Hannu tasa ta share hawayen ta more memories na ƙara faɗowa cikin ƙwaƙwalwar ta haka ma zafafan hawaye suka shiga bin kyakkyawar fuskar ta '' Damn! I hate being so emotional,Amma...na ƙasa... Na kasa jurewa! Nayi kewar ku...i missed everything!" Tayi maganar tana cije leɓenta at the same time wiping away her tears da suke cika mata ido har bata iya ganin gaban ta,wani ward ta kawo daidai ana buɗe ƙofar saura kaɗan tafaɗi cuz bata gani,da sauri aka riƙe ta '' You' okay? Guess yau kowa na cikin baƙin ciki...Black Wednesday! Haha!" Shiru samha tayi tana sauraren muryar it sounded familiar kuma ta gane Muryar,ko acikin mafalki zata gane wake da wannan Muryar amma meyasa muryar ta take ɗauke da ciwo her laughter sounded empty kamar irin dariyar da mutum keyi idan yana cikin baƙin cikin da baisan yanda zaiyi expressing ba, yarinyar ta cigaba da kallon Samha duk da bata ganin fuskar ta, sai ta kalli hijabin dake jikin samha taga irin nata ne pink 🩷 jinjina kanta tayi kafin tace '' idan kinaso kiyi kuka ko ki gaya ma wani damuwar ki... I'm here duk da Bamu san juna ba!" Ra'esah tayi maganar with sincerity,tana Dan ware kyawawan idon ta don jin how foolish she sounded Taya daga ganin mutum kawai sai ka shiga gaya masa damuwarka? Ta faɗi hakan ne kawai don itama da kanta tana cikin damuwa sosai!
Miƙewa Samha tayi a wani irin slow their eyes locked! Ra'esah ta saki baki tana kallon samha from head to toe like she just couldn't believe it, ita kuma Samha tayi murmushin gefen baki da sauran hawaye maƙale a gefen idon ta tana kallon Ra'esah da duk da tasa hijabi ramar ta bata ɓuya ba sai kuma ta ƙara kyau sosai!

'' Sam!" Ta kira in disbelief, rungumeta Samha tayi itama tana jin farin ciki sosai cike da sanyi tace '' Eysah!" Ƙanƙameta Ra'esah tayi trying so hard not to break down '' wallahi faɗar irin farin cikin danake ciki is a waste of words Samha...our very own Samha a gabana kamar a mafarki!" Ra'esah tayi maganar cike da farin ciki which couldn't be hidden daga muryar ta,yan mutanen dake wucewa nata kallon su, disengaging sukayi suna kallon juna cike da ƙauna da bege, Samha couldn't help but notice how slim she looked

'' naga kin ƙara kyau kin ƙara haske and kin ƙara ƙiba Sam!" Ra'esah tayi maganar da murmushi a fuskar ta hannun ta cikin na Samha suna tafiya yar dariya Samha tayi '' no seriously da gaske nake..and kin ƙara iya moves ɗin Nan naki na martial arts? Kin tuna yanda kike dukan dark flames? Samha inaso nima ki koya mun self defense ɗin nan pls it's so cool! Musamman idan kana faɗa dana miji You just kick them and that's all, I love it Samha Dan Allah ki koya mun....'' Ra'esah went on and on,tace wannan ta saki ta kama wannan sannan tayi reverse back to what she was saying, Samha ta bala'in yin noticing komai game da Ra'esah how she changed and all,harda wani scar tayi noticing a hannun ta But she didn't say anything... Can dai ganin yanda Ra'esah ke magana non stop yasa Samha faɗin '' Eysah!" Gently Ra'esah ta juyo '' what? Am i talking too much? Yi haƙuri farin cikin ganin kine Samha,ji nake kamar na kawo ƙarshen hutun mu koma makaranta Samha.... Oh yau 18th December just few more days I'm so..'' Maganar Ra'esah ta yanke ganin Samha ta tsaya cak tana kallon ta, itama Ra'esah tayi shiru tana kalle kalle she couldn't meet her gaze '' What's the problem girl! Something's up baki da yawan magana haka what's it Eysah?" Ƙin haɗa ido da Samha Ra'esah tayi rather tana kallon wani wuri tace '' you're over thinking ba komai fa! Me yasa ma kike kuka ɗazu?" Ra'esah maimakon ta bada amsa ta tambayi Samha, Unexpectedly sai ga samha gaban ta kafin Ra'esah tayi wani abu Samha ta ɗaga hijabin ta kafin ta cire shi duka don inda suke ba mutane sosai '' Ah!" Ra'esah gasped tana rufe ƙirjinta don wata yar ɓingilallar riga ce jikinta, Samha tabi jikin ta da kallo yarinyar ta tsuke ta ƙanjame ta lalace ga wasu tabo ajikinta ba kyan gani... instantly idon Samha darkened she knew it! Something was up da Ra'esah tun ranar da Na'ema tayi drugging ɗinta tasani! '' what's this Samha? Bani hijabi na!" Ra'esah tayi maganar tana miƙa hannu tareda turo baki,she felt embarrassed a yanda take '' meyake faruwa anan! Anything special?" Wata muryar ta sake faɗa, Muryar da Samha ta tsana fiye da komai,Muryar da ta yaudare ta, Muryar dake son kawo karshen ta! Idon Ra'esah suka ware ganin Na'ema saye cikin wasu matsatstsun kaya da basu ɓoye komai na surar ta ba

Swiftly Samha ta juyo tana kallon Na'emah from head to toe idon su cike da tsana towards each other '' Never knew, Trash Samha was into girls..." Na'emah ta faɗa with a sneer in her face tana kallon Ra'esah dake ƙoƙarin saka hijabin ta
Samha tayi murmushin gefen baki taÉ—an É—age gira tace '' It's actually trash Emah or traitor Na'emah don't you think?'' Wani murmushin basarwa Na'emah tayi tana kallon su su duka kafin tayi dariya daga baya '' So pathetic! It's a pity Samha! Naso ace ranar komai ya faru kamar yanda na tsara da yanzu kin muzanta, You won't be able to show your face to anyone! But no! It didn't...''
Samha tayi dariya tace '' nasan hakan ya kusa kai kiga committing suicide I bet!" Jinjina kanta Na'emah tayi kafin ta matso dan da Samha har suna shaƙar numfashin juna,itadai Ra'esah ido waje take kallon su,bata son faɗa ko kaɗan '' kin ci Sa'a the last time Samha,but I assure you wannan lokacin baxaki samu matai maki ba! No one would save you! I hate you!" Tana kallon ƙwayar idon Samha ta faɗi hakan,and she meant every word '' well you know...Babu wanda ke mutuwa a duniyar rabbi don an tsane shi! If you hate me so much kici tsanar ki kora da ruwa,amma kisani Samha tayi miki nisan da har abada baxaki kamota ba,like a star in the sky...you can see but not quite reach! Duk wani tuggun ki zai ƙare akan kine Na'emah!" Daga haka Samha ta riƙa hannun Ra'esah suka bar wurin leaving Na'ema standing alone zuciya na tafarfasa'' zaki sani Samha..You have no idea What's about to hit you!" itama tabar wurin
************

Da sauri suka fara fita ɗakin ido waje kowa na jinjina rashin kunya irin na Amreesh,wai agabansu yake kissing mace Kai! Turawa? '' Wannan daga gani da ace mutum zai iyayi a ƙabari ba abinda zai hanashi, ɗan iskan banza!" Hajiya zakiyya Cursed, Saudat da maraƙisiyya suke tafiya slowly kamar wa'yanda aka kyara ma ruwan sanyi,shiko khaleel his head was swirling with dirty thoughts...

'' idan privacy yake so ai sai yayi mana magana,he didn't have to be shameless!" Hajiya Turai ta cafe huci na fita ta baki ta hanci,haushi take ji sosai

Amidst all this Babu wanda ya kula da Mariya da fuskar ta tayi baƙi ta cika ta batse '' humph!!" Ta faɗa kafin ta ɗauki wani sashe daban walking on her own!

'' Why did you do that?" Salmah ta tambaya head down don wani irin blushing take tana wasa da yatsun hannunta,har yanzu cheeks ɗinta felt hot why would he do that?" Do what?" Taji Muryar Amreesh saitin kunnen ta wani irin yarrr taji all over, turo baki tayi kanta still a ƙasa taƙi yarda su haɗa ido tace '' abinda kayi yanzu!" Murmushi Amreesh yayi,yaso ya cigaba da teasing ɗinta amma sai kawai yajata suka kwanta yana faɗin '' Surutu suke...i didn't like noise,kuma inaso in kasance da matata!'' Da sauri Salmah ta rufe idonta jin Yanda yayi maganar looking into her eyes,wani ɗan ƙaramin murmushi Amreesh yayi har ya ƙara matso da fuskar shi wanting to kiss her aka turo ƙofar,da sauri Salmah ta miƙe zaune shiko Amreesh fuskar shi tayi baƙi kafin shima ya tashi zaune his ocean blue eyes looking displeased da koma wane ne ya shigo at this very moment

Samha tayi kamar bata ga abinda ya faru ba tana murmushi take kallon Salmah dake mazurai alamun rashin gaskiya daga inda ta tsaya tace '' Mahmah i have a surprise for you!" Amreesh jin haka couldn't help ya wani juya idon shi in circle kamar mace, Salmah kuwa ta saki murmushi tana jira taga surprise ɗin, juyawa Samha tayi ta riƙo hannun Ra'esah bringing her in, Da murmushi Ra'esah ta shigo shyly tana kallon Salmah,su ukun fuskokinsu ɗauke da murmushi except Amreesh daya wani ci magani an ɓata masa show just now!

Salmah tana ma Ra'esah murmushi tace su ƙaraso ciki,har sunyi rabin suit ɗin ta ƙyallara ido suka haɗa ido da Amreesh,his eye color instantly changed daga blue zuwa pale green,zuwa golden then multi colored,wani irin ihu Ra'esah ta saki kafin ta zura da gudu ta ɓoye bayan Samha tana shaking kamar kazar da ruwa ya buga

Amreesh ya ƙara tsuke fuska what the heck! Salmah da Samha were confused, tasowa Salmah tayi itada Samha suka shiga tambayar ta meya faru,'' Aljani ne wallahi!" Ra'esah ta faɗa ido waje tana nuna Amreesh ta cigaba da faɗin '' kalar idon shi ya canja, Samha let's go from here!" Ra'esah ta faɗa har da ɗan ƙaramin fitsari a wandon ta, Samha da Salman suka gimtse dariyar su, shiko Amreesh sai cika yake yana batsewa '' he's my husband!" Salmah ta faɗa gently tana jawo hannun Ra'esah suka ƙarasa itadai a tsorace take, Samha tana tafiya tana dariya

Amreesh kuwa instantly his mood brightened up jin an kira shi da kalmar 'Husband'....


WAYE SHI(Behind the mask) Book 2 na kuɗi ne ga duk wanda ke buƙata ya biya ta wannan account ɗin 9138091955 SALMA ALIYU Monie point shaidar biya ta wannan number+234 9138091955


WAYE SHI?( Behind the mask) By Autumn 🍁🍁
https://chat.whatsapp.com/ITRS0D9vLpo1uGMEvTahfs?mode=wwt
Chapter 75 · 0% Book details