← Book details Waye Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 17 OF 84

Chapter fifteen: First day at school

Waye Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 11 min read

𝑊𝐴𝑌𝐸 𝑆𝐻𝐼?
(𝐵𝑒ℎ𝑖𝑛𝑑 𝑡ℎ𝑒 𝑚𝑎𝑠𝑘) 𝐵𝑦 𝐴𝑢𝑡𝑢𝑚𝑛 17

𝐶ℎ𝑎𝑝𝑡𝑒𝑟 𝐹𝑖𝑓𝑡𝑒𝑒𝑛: 𝐹𝑖𝑟𝑠𝑡 𝑑𝑎𝑦 𝑎𝑡 𝑠𝑐ℎ𝑜𝑜𝑙


Ta daÉ—e tsaye a wurin har Saida taga rana ta faÉ—i sanyi ya fara sauko wa kafin ta goge hawayen ta, ta juya walking slowly ta fara tafiya wani irin kaÉ—aici na fisgar zuciyar ta, har tayi rabi ta kusa kai hostel taji ance '' hey '' kamar bazata juya ba sai kuma ta juyo a wani irin slow motion she instantly recognized the girl, it was Zeenah yarinyar da suka haÉ—u a restaurant har ta zauna akan cinyar Ahmad. Maida kallon ta Samha tayi zuwa ga abokan ta dake biye da ita they were all together that day, yanzu ma sai wani cika suke suna batsewa.

Itako Zee kallon Samha take, yarinyar kyakkyawa ba makusa wani irin tsanar Samha ya shiga ranta.
Ganin suna ɓata mata lokaci yasa Samha yin gaba ta fara tafiya,da sauri Zee ta wani finciko ta '' ke wace ce banga ma magana ba zaki tafi?" Kallon ta Samha take, she was dumbfounded yanzu ita meye haɗin ta dasu, sauran ƙawayen Zee ko sai zuga ta suke hakan yasa ta tsaya ɗan da Samha sannan cike da gargaɗi tace '' stay away from him'' tana gama faɗar haka ta tura ta sannan ita da tawagar ta sukayi gaba. Bahaka suka so ba, sun so Zee tayi ma Samha duka ko su duka su taru su bata kashi....Zee tafiya take tana ƙara ji aranta dole tayi maganin Samha, tun lokacin da suka sauko daga mota Zee ta gansu suna tafiya tare,da farko ta ɗauka yan uwa ne hakan yasa take binsu abaya ba tare da sun sani ba,anata tunanin idan an gama ma Samha komai they will become friends and with their relationship,tafi samun dama da Ahmad, sai da aka tafi office ɗin principal take jin labari daban
Take zuciyar ta tafara tafasa dan ita da gaske son Ahmad take.
Haka ta cigaba da binsu bayan sun fito daga office ɗin to be sure and she saw them both hugging ji tayi kamar taje ta wawwanka ma Samha mari even right now she wished she could damage her beautiful face!! Fuskar Zee tayi ja saboda fushi, ƙawayen ta na biye da ita suna gaya mata ways to make samha's life miserable

Samha ta ɗau mintuna tsaye wurin still trying to process what just happened,sai kuma tayi wani murmushin mugun ta tace a fili '' yara kun taro match, i love this '' ta ƙarashe maganar licking her lower lip.
Barin wurin tayi zuwa hostel ɗin su, koda tashiga room mates ɗin ta duk sun dawo unlike ɗazu da basu nan. Binta suka yi da idanu ita ko directly wurin kayan ta, ta tafi ta cire veil ɗin da tanaɗa tare da ribbon ɗin da tana ɗe gashin ta, sannan ta sa hannu ta warware gashin allowing air to enter. Waro idanun su room mates ɗin ta sukayi ganin yawan gashin ta, magana suke ƙusƙus wata yar siririya cikin su ce ta fara tashi ta tafi wurin samha that was arranging her clothes in the cupboard,ji kawai tayi ana taɓa mata gashi, swiftly ta juyo, fuska ɗaure take kallon yarin yar, murmushin tsoro yarin yar tayi sannan ta miƙo hannunta '' Hi I'm fateemah'' kallon hannun yarinyar samha tayi sannan tace'' dan sunan ki Fateemah sai aka ce ki taɓani?" The other two girls exchanged glances kafin yarinyar nan data buɗe ƙofa ɗazu ta ja tsuki tace '' mutum kamar biri amma sai jan ajin tsiya, damar abun ma mun san gashin kanti ne'' ɗaya yarin yar dake zaune kusa da wadda tayi maganar tace ''haba Na'ema ai ke daga ganin wannan gashin kinsan bana kanti bane'' har zuƙowa Na'ema tayi tace '' ke Ra'esah ki shiga taitayin ki, badai dake nake ba ko to wallahi ki fita daga idanuna in rufe toh'' a tsorace Ra'esah tace ''Allah ya baki haƙuri'' Daga nan taja tayi shiru ita dai Samha sauraren su take but she didn't say anything,ita ko Fateemah taƙi tafiya tayi tsaye tana cigaba da yaba gashin Samha ,jin har yanzu yarinyar na tsaye bayan ta yasa ta sake juyowa da sauri Fateemah tace '' can we be friends '' ''A'a'' samha ta faɗa tana ɗaukar wata doguwar riga loose fitted tashiga toilet ɗin dake ɗakin, ɗan turo baki Fateemah tayi determining Bazaa ta haƙuri ba till they become friends with Samha. Komawa tayi saman gadon ta da yake kusa da ɗayar windown ta zauna, kowa nada gadon sa in a corner, sai rug shimfiɗe a tsakiyar ɗakin, samha ta ɗauki blue, Fateemah nada pink, Ra'esah green sai Na'ema purple. Truly ɗakin ya haɗu. Bayan Samha ta shiga,sake fitowa tayi ta kwashi toiletries ɗin ta,ta jera su a bayen kafin ta shiga wanka. Koda Samha ta fito yanda ta barsu haka ta same su, Ra'esah reading her text book, Fateemah tana nan tana jira ta fito ita kuma Na'ema tana danna wayar ta. Gaban madubin dake manne da wardrobe ɗin ta ta tsaya,ita sai yanzu ma tayi noticing. Kwaso su turarunkan ta da originally ta shirya su a wardrobe tayi ta mai da su saman dressing table ɗin sannan ta zauna ta shafa mai ta fesa turare, zata fara gyara gashin ta sai ga Fateemah tazo da murmushi '' can i help you?" Kafin samha ta amsa har ta ɗau mashaci ta fara shace mata gashin ta gently, Samha ta ji daɗin yanda Fateemah tayi mata hakan yasa ta lumshe idanun ta sai kuma ta tuntsire da dariya cikin ranta tana faɗin da gida ne saidai ita tayi ma salmah haka ganin tana dariya Fateemah tace '' now can we pls be friends? Dan Allah'' the girl was so persistent and she looked cute not bad jinjina kanta Samha tayi sannan tace '' amma idan kika yi offending ɗina, that's it'' da sauri Fateemah ta jin jina kanta cike da farin ciki tayi ma Samha alƙawarin bazata bata haushi ko wani abu ba... Komawa saman gadon ta samha tayi Fateemah ta biyo ta tana bata labarin makarantar sosai samha ke sauraren ta with full attention ''kin San me? Akwai wani bad boys gang a makarantar nan wai 'dark flames' ana matuƙar tsoron su. It's a group of bad boys nima wallahi tsoron su nake'' waro ido Samha tayi tace meyasa ake tsoron su'' ganin Samha was listening yasa Fateemah ƙara ƙaimi wurin faɗin ''saboda iyayen su politicians ne, I'm worried for you, idan yarin ya tana da kyau ko,they will be after her until they sleep with her and idan taƙi? Zasu yi gang raping ɗin ta ko sukashe ta! Babu wanda ya isa yayi wani abu, saboda students ɗin tsoron su suke both male and female!" Sosai Samha ta girgiza da jin wannan labari,
Ra'esah ce ta taso tazo ta zauna saman gadon Samha ta dafa kafaɗar Samha cike da damuwa tace '' zai fi,idan kika sa wani abu don ɓoye kanki domin tsira da mutun cinki '' jinjina kanta Fateemah tayi alamun ta yarda da abinda Ra'esah tace, ajiyar zuciya Samha ta sauke sannan tace'' i appreciate your care nagode sosai'' murmushi suka yi mata. ''sunana Ra'esah Nasir, sai Fateemah Muhammad '' kefa?
''Sunana Samha Aliyu Sabo'' jinjina kansu sukayi they had become friends, soon lokacin sallah ne hakan yasa suka miƙe sukayi alwala '' Na'ema bazakiyi sallah ba?" Fateemah ta tambayi Na'ema that was lying on the bed
'' idan ke ake yima sallar kada ki karɓa'' ta faɗa tana cigaba da danna wayar ta ''she's so rude'' samha ta ayyana ranta. Jerawa sukayi su uku sukayi sallar su tare da azkar ɗin bayan sallah.
Abin ban sha'awa dukan su baza su wuce shekaru sha biyar ba kuma dukan su tsawon su guda with the same comolexion wato chocolate banda Na'ema da take baƙa kuma tana da tsawo da jiki za ta ɗan girme su. Bayan sun gama adhkar ɗin ne Samha tace '' toh waye leader ɗin wannan dark flames ɗin kuma su nawa ne?" Ra'esah tace '' wani mai suna Andrew bama musulmi bane, sai chibuke,sai Emmanuel sai kuma mathew.'' Fateemah ta ƙara da faɗin '' wasu lokutan yan matan fa ke kai kansu! Ba ko da yaushe ne ake yin fyaɗen ba'' duk abinda suke faɗa Na'ema najin su. And if only they knew itama tana cikin masu son koda sau ɗaya ne su samu dama da one of the boys,Amma ita Andrew take so. Taji yanda yan mata ke magana akan sa she wants to experience it too, gabaki ɗaya cikin boys ɗin babu na yar dar wa cuz ba ƙarya,sun haɗu iya haɗuwa. Tall,sexy, muscular and damn sexy ga kyau and charm. Tun tana SS 1 Na'ema take da wannan burin and she's going to fulfill it at any cost in ss2 ɗin nan.
Bayan sallar isha'i Fateemah da Ra'esah suka ce yunwa suke ji zasu tafi cafeteria, Samha tace ita ta gaji su kawo mata koma mene.
Bayan tafiyar su ta koma ta ɗauko wayar ta ta shiga contacts, scrolling tayi har ta kawo kan number sa, she stared for a while contemplating whether to call him or not,tana cikin tunani batare da tasani ba ta danna kira, waro ido tayi ta maza ta katse kiran amma har ya shiga ''wayyoni Samha '' ta faɗa lokacin da taga kiran Dr , numfashi taja ta tsare wayar da ido,sai da taga kiran ya kusa Katsewa kafin ta ɗauka ta kara a kunnen ta tayi sallamah amsawa yayi kafin yace in a sexy voice '' My lady'' runtse idanun ta samha tayi falling back on the bed ga wani irin Abu da take ji a cikin cikin ta '' uhm'' ta amsa da wata ƙaramar murya, thats not what she intended her voice betrayed her, murmushi mai sauti Dr yayi from the other end kafin yace '' har yanzu baki yi bacci ba?"
Tace ''uhm '' " me yasa?''
''Bakomai '' ta faɗa tana jawo duvet ɗin ta rufe rabin jikin ta '' ba komai ko tunani ya kasa barin ki? Kina ji ina ma ace ina kusa" waro ido Samha tayi tace ''kai ya Ahmad '' tayi maganar a shagwaɓe, sake lumshe idanun sa Dr Ahmad yayi ya jingina da head board ɗin gadon yanda ta kira sunan sa har cikin ƙwaƙwalwar sa. Saye yake da kayan bacci alamun bacci zai yi,but he couldn't tunanin ta ya hanasa. " To in bahaka bane why aren't you asleep?" Da sauri tace ''abinci fa zamu ci.''
'' okay'' ya faɗa after a while, ''kai kaci abinci?'' ta tambaye sa. Ya ji daɗin tambayar san da tayi cewa yayi '' talking to you alone has satiated my hunger'' ɓoye fuskar ta tayi cikin pillow tana blushing tace ''so you know how to flirt?" Yar ƙaramar dariya yayi sannan yace in a serious tone '' I'm stating the truth, I'm not flirting ''
Da iya gaskiyar sa yayi maganar '' okay '' ta faÉ—a, she felt so happy and at the same time shy.
'' Good night my lady'' Dr Ahmad ya faÉ—a
''Good night '' ita ma tace,though Bata so maganar ta tsaya nan ba. Ta daɗe tana kallon screen ɗin, turo ƙofar akayi it was Ra'esah da Fateemah hannun su rike da take away directly gadon ta suka nufa suka miƙa mata, godiya tayi musu before she dug in. Su kuma suka canja kayan su zuwa na bacci suka kwanta, itama Samha tana gama wa bayi ta shiga ta wanke baki sannan tayi alwala kafin ta zauna saman gadon ta tayi addu'ar Bacci ta kashe wutar gefen ta tayi hanyar garin su.....

*************
The next day Monday, bayan sunyi sallah komawa Samha tayi ta cigaba da bacci,sun yi ta tashi ta shirya taƙi hakan yasa sun tafi sun barta. Sai wuraren ƙarfe takwas da rabi Samha ta tashi, undies ta ɗauka Black color,bayi ta shiga tayi wanka tafito saye da ɓakin skin tight ko rabin cinyar ta be rufe ba,sai half cut ita ma bata kai ciki ba, mai ta shafa sannan ta taje gashin ta, ta shafa hair oil ɗinta, ta ɗan tsira ma kanta ido ta madubi, Samha nada hips sosai kawai dai ƙirjin tane da yaƙi fitowa koshi ba wani flat yake can can ba. Sannan she has the ladies shape, tsaki taja ta koma ta buɗe cup board ɗinta, papers ɗin da aka batane jiya suka faɗo, duƙawa tayi ta ɗauka ta buɗe RULES OF ELITE ACADEMY taga an rubuta ɓaro ɓaro

1. Students must attend classes on time
2. Students should not roam around during lectures
3. Illegal sexual behavior is not allowed
4. Wear your uniforms correctly
5. Bullying is not allowed t.....etc.
Taɓe baki Samha tayi bayan ta gama karanta wa ''kwaji da shi'' ta faɗa tana jawo uniforms ɗin da aka bat. Riga fara mai ɗauke da Black collars,sai Black tie, da Black blazers, sai kuma...sakin baki Samha tayi lokacin da taga wani figigin skirt ɗin da aka bata '' kam bala'i!! Wa zai sa wannan abun? Ina musulma za'a kafurtani? Wallahi baku isa ba!" Tana gama faɗar haka ta zaro wani zumbulelen hijabi daga cikin kayan ta tasa ta fita daga hostel ɗin duka , bayan ta fito left and right ta kalla kafin ta ɗauki left corner tana ta tafiya kafin ta iso boys hostel. Zata shiga mai gadin wurin ya kira ta ya tambaye ta ina zata,kame kame ta fara hakan yasa yace ta tafi ta bashi wuri girls aren't allowed, yi tayi kamar ta tafi, ta zagaya ta baya ta hau katanga ta dira ciki, samha da Salmah both bayan kasancewar su martial artists, sun iya gymnastics da acrobatics hakan yasa Samha ta iya hawa katan gar. She was lucky ta baya ta dira hakan yasa ta samu akwai shanyar kaya a wurin,ai ko ta duba ta ga ba kowa tayi gaba da wani falke ken wando, katangar ta sake hawa ta dira, bata tsaya ko ina ba sai hostel ɗin su. Wandon tasa da sauri ta ɗau rigar ta tasa,tasa blazer ta ɗauko wani karamin hijabi half sunna ta sa ta fesa turare, jakar ta baƙa ta ɗauka, tasa takalma baƙaƙe, duk waɗannan was provided by the school,turare tayi wanka dashi sannan ta kalli kanta a madubi,she looked dashing.
Except wandon looked too big for her and she liked it....


WAYE SHI?(Behind the mask By Autumn 17
Chapter 17 · 0% Book details