← Book details Waye Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 29 OF 84

Chapter twenty eight: I love you

Waye Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

𝑊𝐴𝑌𝐸 𝑆𝐻𝐼?(𝐵𝑒ℎ𝑖𝑛𝑑 𝑡ℎ𝑒 𝑚𝑎𝑠𝑘)𝐵𝑦 𝐴𝑢𝑡𝑢𝑚𝑛 17


https://chat.whatsapp.com/ITRS0D9vLpo1uGMEvTahfs?mode=wwt


𝐶ℎ𝑎𝑝𝑡𝑒𝑟 𝑡𝑤𝑒𝑛𝑡𝑦 𝑒𝑖𝑔ℎ𝑡: 𝐼 𝑙𝑜𝑣𝑒 𝑦𝑜𝑢....


Ganin idan har suka cigaba da kasancewa a haka bazai haifar musu da ɗa mai ido ba yasa Ahmad tashi daga jikin Samha data wani ƙame ƙam, jiyayi towel ɗin shi ya kwance da sauri ya sake komawa kanta duk da cikin duhu ne bai yarda da cewa bazata ganshi ba after all shi yana ganin ta " Washhh Allah na" Samha ta faɗa jin yanda ya buge mata ƙirji wani irin zafi taji, a ɗan rikice Ahmad yace '' mai ya faru?" Yayi maganar with a husky voice hannun sa na lalubar ta cikin duhu jiyayi hannun shi ya sauka saman wani abu mai laushi, ihu Samha ta saki ta ture shi daga saman ta ta nufi ƙofa cikin duhun tana cin karo every now and then, Dr Ahmad ko ihun Samha ya sa shi gane Abinda ya taɓa it was her chest! Koda ya juya ya kalli ƙofar har Samha ta fita. Komawa yayi ya kwanta yana sauke numfashi mai huci, he felt so weak he was aroused. Ya ɗauki lokaci a wurin kafin ya miƙe ya koma toilet wanka ya sake yi sannan ya fito ya kunna wuta, ya nufa gaban mirror duk da Ac'n dake kunne wani irin zafi yake ji ga idanun sa dake lumshe wa suna buɗe wa. Mayukan shi ya shafa, ya taje sumar shi ya shirya cikin wasu navy blue pajamas ya ƙara fesa turare Sannan ya nufi gado ya kwanta facing down wards. Wani irin ciwo marar sa ke masa, bedside drawer ya buɗe ya ɗauko wani magani ya cire 2 tablets ya miƙe ya fita daga ɗakin, ɗayan palorn gefen Amreesh ya nufa ya ɗebi ruwa from the dispenser ya haɗiye maganin, wuri ya samu ya zauna ya jingina kanshi da headrest ɗin kujerar ya lumshe idon sa, ji yake kamar ya shanye maganin duka, buɗe idanun sa yayi da suka canja launi da sauri, yana ɗan jan tsaki, abinda ya faru tsakanin shi da Samha just flashed.'' Ba sha'awar ta nake ba'' ya faɗa a ɗan fusace kamar yana faɗa ma wani.
Samha ko sai Safa da marwa take idanun ta azare,what just happened? Ga wata irin zufa da ta wanke ta duka da sauri ta cire kayan jikin ta ta faÉ—a toilet tayi wanka sannan ta fito ta sa wasu kaya, ta kashe wutar É—akin ta kwanta bata so tayi tunani akai.

10:00pm

Amreesh ne ke tafiya cikin wani wuri kamar Beach, wurin zagaye yake da itace da flowers gefe da gefe hakukuwa, amma akwai pathway
Wurin yayi shiru ga iska mai daÉ—i da sanyi dake kaÉ—awa, tafiya kawai yake amma bai ga single soul a wurin ba it makes him wonder ko dai address É—in ta turo was wrong? Amma duk da hakanan ya cigaba da tafiya.
Bayan wani lokaci ya kawo fili wato babu itace zagaye da wurin illa Teku da yake gani, daga gefe kuma anyi setting É—in table for two anyi decorating É—in table É—in da red roses, sai cake da wine bottles da aka jera sama neatly,

Kujerun da kansu lulluɓe suke da farin yard, daga gefe da gefen su kuma wasu red roses ne da candles masu yawa surrounding them,candles ɗin sun sa wurin haske sosai sai wata romantic song dake tashi a wurin

The sight was absolutely breathtaking and romantic, ƙarasowa Amreesh yayi idanun sa searching for her.

har ya kai kusa da kujerun bai ganta ba ya ɗauko wayar shi zai kira ta yaji foot steps bayan shi juyowa yayi and their eyes met, her beauty swept him off his feet, sai ido daya kafe da shi she looked like a piece of artwork. Saye take da baƙar riga body hug da akayi ma adon flowers baƙaƙe, rigar tayi mata kyau ta zauna jikin ta ɗamas outlining her shape especially her *cleavage* da suke kamar zasu zubo. Gashin ta anyi wavy hair style sai aka sa white pearls da yake haska gashin, fuskar ta ba kwalliya amma ta shafa kwalli that *accentuated* her almond eyes lips ɗinta sunyi ja kamar ta shafa jan baki amma gloss kaɗai ta shafa, murmushi mai kyau wanda yasa dimples ɗinta lotsawa kwance a fuskar ta, ta riƙe wani candle ɗaya da ya haskaka fuskar ta making her look so *ethereal* . Ƙafafun ta sanye da wasu heels baƙaƙe that added to the look ' Masha Allah ' ta kowa ta cigaba da yi her hips swaying effortlessly tun kafin ta ƙaraso ƙamshin turaren ta ya cika masa hanci, tana tafiya iska na kaɗa gashin ta, ganin yanda Amreesh ya kafe ta ido ko ƙyafta wa bayayi yasa Murmushin ta ƙara faɗaɗa.

Dab dashi ta tsaya cikin yin ƙasa da murya tace '' welcome my king '' lumshe sexy eyes ɗin sa yayi tare da sake buɗe su akan ta, Ajiye candle ɗin dake hannun ta tayi sannan ta dawo gaban shi placing her hand on his shoulders tace '' wurin yayi kyau?do you like my surprise?" Hannayen sa yayi wrapping around her waist yana kallon ta yace '' eh '' sai kuma yakai hannunsa haɓar ta lifting her head idon su ya haɗu in a sexy voice yace ''but you look even more gorgeous '' murmushi Salmah tayi tana ƙara ƙasa da kanta, matso da fuskar shi yayi on the nook of her neck taking in her sweet scent,ita ma ta lumshe ido turaren sa na cika mata hanci. After a while they disengaged ya riƙo hannun ta ya zaunar da ita, shima ya zauna yana ƙara ƙare mata kallo kasa ɗago kanta tayi, cake ɗin da aka rubuta *congratulations* *Amreesh* ya kalla sannan ya kalle ta, '' You made all this for me?" Ya tambaya his eyes roaming on her,gashin da ya faɗo gefen fuskar ta tayi brushing tana gyaɗa kai, sai yanzu take jin wata irin kunya na rufe ta, especially Saboda kayan da tasa musamman idan ta kalli ƙirjin ta da yake buɗe,miƙe wa tsaye tayi tazo ta tsaya bayan shi ta ɗan ranƙwafowa tare da ɗaukar wuƙar yanka cake ɗin, shima Amreesh ya tashi yazo ya tsaya bayan ta bayan ta ɗauki wuƙar ya riƙe hannun ta, tunda ya tsaya bayan ta taji ta kasa aiwatar da komai saboda yanda zazzafan hucin sa ke sauka saman fatar ta,ga hannun shi da ya saƙalo a ƙugunta, sniffing her '' let's do it '' ya faɗa yana hura mata iska a kunne sanyi da taji lokacin da hucin nasa ya sauka a kunnen ta yanzu,bata jisa ba tuntuni da take wurin. Numfashi ta sauke sannan ta yanka cake ɗin da ƙyar Amreesh was busy doing things to her.
Juyowa tayi tana fuskantar shi ta kai cake ɗin saitin bakin sa tace '' Congratulations Amreesh '' tayi maganar kanta ƙasa,ta kasa kallon shi, idon sa *_fixated_*on her ya riƙe hannun ta har yanzu ɗayan hannun shi on her waist ya juyar da cake ɗin zuwa bakin ta yana faɗin '' after you my Queen '' yanda yayi maganar yasa taji wani irin sanyi na ratsa ta,buɗe bakin ta tayi taking a bite from the cake kafin ta miƙa masa, still holding her hand shima yaci inda taci, wani irin blushing Salmah keyi tana sinne Kai. Zama suka sake yi Amreesh ya zuba musu wine, yana kallon ta, bayan ta shanye nata ta ɗan ɗago taga ita yake kallo,ƙasa tayi da kanta tana cigaba da blushing sai kuma ta miƙe tazo dab dashi ta miƙo hannun ta tare da faɗin '' wanna dance?"
Idanun Amreesh suna wani sparkling yace '' absolutely my Queen '' yayi maganar tare da miƙe wa hannun sa cikin nata, jawo shi tayi zuwa fili tuni waƙar ta canja into a more romantic one, couple dance suke yi hannayensa a ƙugunta nata a kafaɗar sa, suna kallon juna cikin ido with unspoken words cike da begen juna

Waƙar ta kawo ƙarshe displaying fire works irin wanda ake a new year ko Christmas, Amma wannan daban saboda da fire works ɗin yayi sama it turned into different colors juyar da kansu sukayi daidai fire works ɗin yana rubuta '' I love You Amreesh '' juyo da kansa yayi yana kallon Salmah data ƙara matsowa kusa dashi hannun ta a wuyan shi tana shafa gefen bakin sa da yatsanta tana kallon green eyes ɗinsa tace '' , Ina matuƙar ƙaunar ka, kuma ina so in kasance da kai Ako da yaushe. You mean alot to me.....I love you so much Amreesh '' ta ƙarashe maganar kissing him passionately, Amreesh kissing her back fiercely. At the moment yanda yake ji, was indescribable but he was sure about one thing,zai kare ta and he will keep her with him that's it.

Babu abinda wani zai ce that will make him leave her. Cire bakin sa Amreesh yayi yana kallon fuskar Salmah da taƙi yarda su haɗa ido, shima yana so ya faɗa Mata he feels the same amma zai yi confessing ɗin feelings ɗinsa in an even more grand way.

Matsawa Salmah Tayi ta ɗauko wani ƙaramin box navy blue Mai shegen kyau dawowa tayi gaban Amreesh ta buɗe ta ciro wani zobe mai bala'in kyau da ɗaukar ido, hannun Amreesh ta riƙe tasa masa zoben kissing it after wards, jawo ta Amreesh ya sake yi crashing his lips on hers the kiss more intense than before. Bai iya faɗa Mata yana son ta ba amma zai iya nuna mata atleast. And he promises to keep the ring with him.....

Sun cigaba da sha'anin su batare da sanin what future had in store for them.

Washegari...

Samha ce tsaye a kitchen tayi dame dame da flour ita ala dole sai tayi pizza, fuskar ta da gashin duk sun ɓaci kitchen ɗin ma duk yayi kaca kaca her brown pajamas too.

Ga wayar ta ajiye agefe tana duba tutorial ɗin, '' kai ya Salam abun in anyi anba mutum sai yaga kamar ba wuya amma wurin yi sai mutum yasha baƙar wahala '' tayi maganar tana jan tsaki tare da kallon fulawar ta da tayi ruwa sosai.
Ahmad ya sauko daga stairs ɗin cikin green ɗin riga da wando jeans baƙi fuskar shi ba walwala sai ƙamshi yake zuba wa, tun kafin ya ƙaraso ƙamshin sa ya riga ya sanar da wanzuwar sa a wajen, Dr Ahmad zuciyar shi duk ba daɗi he was worried kada samha taga kamar he took advantage of her yesterday, shigowa kitchen ɗin yayi sai dai Samha ta juyo suka haɗa ido her heart skipped a beat tuna abinda ya faru jiya da sauri ta kauda kanta shima Ahmad did the same

Har ya juya zai tafi tayi saurin zuwa gaban shi, kallon ta yake tun daga tsakiyar kanta har ƙasa duk tayi buɗu buɗu, murmushi me kyau tayi sannan tace '' Yaya Ahmad ina kwana ka tashi lafiya Allah ya ƙara mak....'' shidai Ahmad yayi shiru Yana Binta da ido, yanda take maganar he was sure she wanted something katse ta yayi da faɗin '' what do you want?" Zaro ido Samha tayi holding his arms tace '' nasan ka iya abinci mai daɗi, you're a good chef, pizza zaka haɗa min kaji yayana mai sona'' tunda hannun ta ya riƙe nasa ya dena fahimtar abinda take faɗa his brain was rebooting har tagama surutun ta,taja shi gaban gas bai san abinda take faɗa ba.
His body was feeling something else....

Sakin hannun sa tayi ta ɗauko apron ta miƙa masa,karɓa yayi jiki ba ƙwari ya ɗaura sannan ya dawo da idon sa kanta yace '' clean up the mess'' jinjina kanta Samha tayi sannan ta fara goge wa da wanke abubuwan da ta ɓata shi kuma Ahmad ya shiga fara haɗa ingredients ɗin da suke buƙata.
Samha sai surutu take Dr Ahmad na jin ta ya taɓe baki 'the girl is so cunning ' ya faɗa a ransa.
Amreesh ne ya fito sanye da Kayan Bacci ash color, idanun shi sai sparkling suke, and he looked so handsome ƙarasowa kitchen ɗin yayi da sauri Samha ta juyo tana kallon shi, kallo guda yayi musu su biyu ya ɗauke kai. Wurin kayan shayi ya nufa, sai wurin asuba suka dawo jiya he had the best moment of his life

Ahmad ya bishi da kallo kafin yace '' su zakee abin ba magana?" Yi Amreesh yayi kamar bai ji abinda Ahmad ya faɗa ba, taɓe baki Ahmad yayi yana cigaba da abinda yake, Samha ta sa hannu cikin aljihun wandon ta ta ɗauko wata flower da tayi yaushu har ta gaji ta matso kusa da Amreesh tana miƙa masa flower tace '' congratulations best CEO of the year'' Dr Ahmad ya kalli abinda Samha ke ba Amreesh wata irin dariya na cinsa juyo wa Amreesh yayi ya kalli Samha from head to toe sannan ya kalli flower da take miƙa masa ya ɗauki tean da ya haɗa looking at her smiling face yace '' flower tayi datti tayi ƙajin ƙajin kamar ke'' yayi maganar tare da barin wurin, Samha ta saki baki da ido tana kallon shi Dr Ahmad ko ya tuntsire da dariya....


WAYE SHI?(Behind the mask) By Autumn 17
Chapter 29 · 0% Book details