← Book details Waye Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 31 OF 84

Chapter thirty: Bring her home

Waye Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 12 min read

Bayan fitar su Amreesh wurin yayi shiru kamar anyi ruwa an É—auke sai kallon kallo ake kowa na al'ajabin maganar Amreesh,Aure? Yaushe yayi auren
Yan matan kuwa their faces turned pale ita Wadda aka kama sun ce ya aura ko wa? Fuskar Hajiya Maleeka matar papa was unreadable dama tunda kowa ke magana bata tofa yawu ba. Papa kuma har yanzu kansa na ƙasa har yanzu ya kasa ɗagowa

Tsaki Uncle T yayi tare da faɗin '' Aikin banza mu za'a raina ma da wayau? Wai yayi aure! To kai Yousuf da kake uban ja'irin ya faɗa maka zai yi aure?'' kowa ya kai duban sa ga Uncle T kafin su dawo da kallon su ga papa da yaƙi cewa komai abun duniya yabi ya ishe sa. Uncle Naseer yace '' ai yaron bai ganin kowa da Gashin ido dan haka ko uban nasa bai sani ba!" Uncle Naseer ya ƙarashe maganar cike da ƙunar rai. Kowa ransa ƙuna yake especially su Hajiya masu buri,yan matan ko zuciyoyin su kamar zasu yi bindiga
Miƙewa Old man Zakee yayi ahankali ya nufi hanyar fita, Uncle Ismael yace '' Alhaji bazaka ce komai ba game da y...'' ɗaga masa hannu old man Zakee yayi
Calmly yace '' mai zance? Ku dukan ku bakunyi magana ba? Ai yin maganar tawa bashi da amfani kun isa ai'' yana gama faÉ—ar haka ya fice wurin ya kacame da hayaniya and the blame was shifted to papa duk da kuwa ya girme su su duka

Tashi yayi ya fita walking slowly zuciyar sa ƙuntace yaga ɗansa and yet he couldn't even pull him in a warm hug,kowa sai zagin ɗansa yake yana tsine'' masa yet he couldn't defend him! Shin wai shi wane irin ubane? Mai yasa yake sakaci da ya'yan sa gashin yanzu babu ɗayan su dayake tare dashi. Tura ƙofar ɗakin sa da ya gaji da haɗuwa yayi ya shiga closing the door wutar ɗakin kashe hasken ranar da ta kusa faɗuwa ne kawai ya haskaka ɗakin, kusa da window papa ya tsaya yana dafe saitin zuciyar sa idanunsa sun ciko da ƙwalla in a whisper yace '' ya Allah '' ya zauna ya dafe kansa yana faɗi ciki ciki '' If hazel was alive,maybe...may be then...da yanzu family na would have been complete....me yasa Muhammad mai yasa?" Ya yi maganar baƙin ciki shimfiɗe a fuskar sa, he wanted to cry, yana so yayi ihu ko zai ji sauƙi but would that solve it?...

Bayan fitar papa kowa ya fara fita one by one magana ɗauke a bakin su kowa baƙin cikin sa daban amma tabbas suna cikin baƙin ciki.

Amreesh ya fito daga meeting hall ɗin yana tafiya cikin natsuwa fuskar sa idan ka kalla ba zaka taɓa sanin abinda ke yawo cikin sa dan babu wata alamar tashin hankali tattare dashi however,ga wanda yasan Amreesh idan ya kallesa zai ga his face is much more colder than usual, idan Amreesh ya saki fuska sai dai idan yana tare da matarsa ne kawai. His heart felt empty at the moment

Shigar sa mota yayi dai Dai da shigowar saƙo a wayar sa jawo wayar yayi bayan ya zauna a passenger seat ya duba saƙon

“𝐴𝑛𝑜𝑛𝑦𝑚𝑜𝑢𝑠”

_𝐶𝑜𝑛𝑔𝑟𝑎𝑡𝑢𝑙𝑎𝑡𝑖𝑜𝑛𝑠 𝑓𝑜𝑟 𝑢𝑟 𝑎𝑤𝑎𝑟𝑑 𝑒𝑛𝑒𝑚𝑦, 𝑖𝑛𝑎 𝑓𝑎𝑡𝑎𝑛 𝑢 𝑙𝑖𝑘𝑒𝑑 𝑚𝑦 𝑐𝑜𝑛𝑔𝑟𝑎𝑡𝑢𝑙𝑎𝑡𝑖𝑜𝑛𝑠 𝑔𝑖𝑓𝑡 𝑢ℎ𝑛,_

𝑌𝑜𝑢𝑟𝑠 𝑠𝑖𝑛𝑐𝑒𝑟𝑒𝑙𝑦 𝑎𝑛𝑜𝑛𝑦𝑚𝑜𝑢𝑠.

Bayan Amreesh ya gama karanta saƙon he realized that scandal ɗin dake yawo ashe wannan ne musabbabi dama ya zargi hakan....cije lips ɗinsa Amreesh yayi eyes icy cold. Dr Ahmad ne ya shigo motar ya zauna driver seat ya ɗan kalli Amreesh tada motar yayi suka fita daga family house ɗin, wayar sa Amreesh ya jawo yayi dialing ɗin Secretary Ayman bayan ya ɗaga curtly yace '' arange meeting with TBC news'' yana gama faɗar hakan ya katse kiran notifications sai popping suke News, business partners and social media.....
Har Amreesh zai mayar da wayar cikin aljihu kiran old man Zakee ya shigo Kamar kar ya ɗaga sai kuma dai ya ɗaga without saying anything from the other end old man Zakee zaune saman gadon sa with a calm voice yace '' Youg Zakee '' Amreesh yayi shiru bai amsa ba oldman Zakee ya ƙara faɗin '' Zakee my friend'' still Amreesh bai amsa ba,Dr Ahmad ya saci kallon shi slowly yace '' Zakee pls'' lumshe idanun sa Amreesh yayi from the other end har old man Zakee ya sadaƙar Amreesh ba zai yi magana ba yaji yace '' Old man '' kyakkyawan murmushi old man Zakee yayi tare da dafe saitin zuciyar sa jin Muryar Amreesh dramatically old man yace'' Wai harnaji sauƙi na ɗauka nima ta shafe ni'' Amreesh ya sassauta Muryar sa yace '' uhm'' kawai, Dr Ahmad yake glancing towards him once in a while yana ɗan murmushi jin yanda Amreesh da kakan nasu ke hira kamar wasu abokai duk da old man Zakee ke maganar all the times Amreesh kawai bai fi ya amsa da uhm,a'a ba.

After a while old man Zakee yace '' kawai sai naji kayi aure Muhammad,how is it done like that uhm? Nida naso inyi attending ɗin auren ka in zama cikin abokan ango sai kuma naji cewa har anyi auren babu Ni? Ban ji daɗi ba young Zakee'' Shiru Amreesh yayi bai ce komai ba sanin bazai yi magana ba yasa Ahmad fara ba oldman haƙuri dan dama wayar a speaker take.. oldman Zakee ya sauke ajiyar zuciya sannan yace '' when will you bring her home?" Idanun Amreesh dake lumshe ya buɗe yana kallon screen ɗin shima Dr Ahmad ya kalli Amreesh waiting to hear his reply,sanin da oldman yayi Amreesh na iya ƙi yasa ya fara lallashin sa akan ya kawo matar sa tasan dangin sa suma su santa ba'asan abinda gobe zata haifar ba, Dr Ahmad yace '' zata zo granpa '' wani kallo Amreesh yayi masa shiko yaƙi yarda ya kalli Amreesh ɗin '' yauwa na gode Dr Zakee '' yar dariya Ahmad yayi jin granpa ya kira sa da Dr Zakee


09:00
Tsaye take bakin window jikin ta sanye da wata rigar Bacci baƙa iya guiwa, hannayen ta naɗe a ƙirjin ta kanta jingine da frame ɗin windown, kanta saye da hula baƙa fuskar ta ɗauke da damuwa with a every ticking of time bugun zuciyar ta ƙaruwa yake, she was afraid idan pa dangin Amreesh suka ce Dole sai ya rabu da ita? Idan pa shima yace bazai zauna da ita? Lokacin da ya shigo Bayan sun dawo daga ko ina ma suka tafi he didn't even look at her. Wannan warmness ɗin datake gani a fuskar sa ako da Yaushe idan suna tare babu shi yau why? Itama taga Abinda ke trending a social media Amma ai ba laifin ta bane ko? Hawaye suka ciko idon ta,she felt tired she was depressed hawayen suka fara silalo wa suna jiƙa gaban rigar ta. Turo ƙofar Amreesh yayi ya shigo saye yake da gray pajamas sai ƙamshi yake zuba wa. Yanzu suka gama magana da board of directors it ended in tension wasu na faɗin zasu janye hannun jarin su idan har Amreesh bai fito yayi public speech yayi addressing ɗin issue ɗin scandal ba har directors ɗin sukayi Magana suka gama Amreesh baice komai ba. Abinda suke barazana ne kawai he owns 70 percent of the company 's shares and he made the company without him it will collapse. Tsayuwar sa taji bayan ta juyo wa tayi crashing herself into his arms tana kuka tace'' yanzu kaima zaka juya min baya ne? Abinda Ya faru ba laifi na bane why do I feel like you're also blaming me?" Ƙara rungumota jikin sa yayi haɓar sa akan ta with a deep voice yace '' ba haka bane Mahee,i was trying to settle things bazan taɓa juya maki baya ba.'' Salmah sai kuka take kamar ranta zai fita slowly yace '' I'm sorry '' yana patting ɗin Bayan ta. Sun daɗe a haka kafin ya zauna bakin gado sitting her up on his lap yana share mata hawaye yace '' kwanakin nan You cry too much I'm afraid you will fall sick'' yayi maganar cike da kulawa yana share mata gashin ta zuwa bayan kunnen ta, kwantar da kanta saman ƙirjin sa yayi as they listened to each other's heart beat. Jinsa tayi yana faɗin '' old man Zakee asked me to bring you home '' ɗago fuskar ta tayi daga ƙirjin sa tana kallon sa firgici a fuskar ta tana kallon Amreesh shima kallon ta yake baki ta turo hawaye na silalowa tace with a breaking voice '' nasan cewa za suyi ka rabu dani ko?" Ta ƙarashe maganar hawayen tana ƙara ƙarfi zuciyar ta na bugawa da ƙarfin gaske girgiza kansa Amreesh yayi holding her face yace '' babu wanda zai raba mu so calm down'' a rikice tace '' taya baza su raba mu ba? I don't have family I only have my sister idan suka tambayeni dangina nace bani da dangi they will definitely ask you to divorce me Taya hankali na zai kwanta Amreesh? I can't live without you Ina matuƙar son ka and I don't see my self without you ya zanyi?'" tayi maganar a mutuƙar haukace tana tashi daga jikin sa, hawayen ta knew no bound sai tsiyaya suke idanun ta sunyi jawur hankalin ta tashe, jawo ta Amreesh yayi tana ƙoƙarin ƙwace wa as she continues to analyze things da ƙarfi ya fisgota ta faɗo jikinsa ya haɗe bakin su kissing in a way that made her still itama ta fara kissing ɗinsa back and har lokacin hawayen ta zuba suke.... Cire bakin sa yayi ya riƙe fuskar ta cikin hannun sa looking into her eyes yace '' i assure you babu wanda zai raba mu'' tana sheshsheƙar kuka tace '' if they ask for my family...'' katse ta yayi da faɗin where are your family?" Ta kwantar da kanta a ƙirjin sa tana faɗin '' ba muda dangi '' shiru tayi kafin ta cigaba da faɗin '' they disowned our parents '' Amreesh yace "mai yasa?" Tafara bashi labari kamar yanda baban su ya faɗa musu before he passed away

Aliyu Sabo shine baban su, he's from the sabo family inda suke matuƙar ɗaukaka al'ada. Sannan basu yarda da auren bare ba sun fi yin auren haɗi. Yana da yayye maza uku Abdul Hakim,moddibo da kuma Abdullahi sai shi Aliyu. Duk cikin su baban su Alhaji dikko yafi son ALIYU suma kuma kowa a gidan na ƙaunar sa tunda shine auta ko a family idan an haɗu an dinga tambayar ina Aliyu kenan.

Lokacin da Aliyu ya kammala jami'a yan uwansa tuni su suna aiki a companyn familyn su bautar ƙasa aka turasa a garin inya murai anan suka haɗu da iyanu Bama musulma bace a lokacin Aliyu ya fara jan ta jiki yana koyar da ita abubuwa regarding Islam tunda itama lokacin bautar ƙasar take, kowa ya sansu tare Aliyu da iyanu ahankali alaƙar su ta koma daga friend ship zuwa soyayya amma there was a religious barrier tsakanin su. Bayan wani lokaci iyanu ta musulunta aka sama ta suna Salamatu Aliyu yayi farin ciki sosai

Gida ta kaishi tayi introducing ɗin sa matsayin wanda zata aura familyn su suma da suke riƙaƙƙun kafirai sannan kuma masu riƙo da al'ada lokacin da ta kawo Aliyu akayi musu chaaa ita dai ta turje ita shi take so korar kare akayi ma Aliyu da faɗin idan aka sake ganin sa wurin zasu kashe sa itako suka garƙameta kwana da kwanaki sai dai akai mata abinci, suka ce ƙo nan da ƙofar gida bazata leƙa ba kuma nan da kwanaki kaɗan za'a ɗaura mata aure da wani ɗan uwanta mai suna ebuka hankalin ta ya tashi ta ƙanjame ta bushe. Shima Aliyu ya rame ya fita hayyacin sa. Gida ya koma ya sanar da familyn sa Abin da yake ciki ki body supported him rather sai cewa da akayi za'a ɗaura masa aure da cousin ɗin sa mai suna kareema ai ko Aliyu ya tuɓure ya dinga zubda ruwan tijara duk wani efforts na convincing ɗin sa ya sha kara da Alhaji dikko yaga Aliyu na shirin jawo masu abin kunya cikin family meeting yayi announcing idan har Aliyu ya aure inyamura babu shi babu Aliyu yayi disowning ɗin sa kowa yayi na'am da wannan hukuncin na Alhaji dikko a tunanin su Aliyu zai yarda ya yi yanda suke so but to their surprise and disappoint ya tattara kayan sa yabar gidan duka. No one stopped him sai ma jadda da masa da suke babu shi babu su.

Hankalin Salamatu na kan Aliyu tana tunanin ko ina yake? Wane hali yake ciki? Does he remember her? Kwanaki kaɗan ya rage ayi auren Salamatu (Iyanu) da Ebuka sai shirye shirye ake kamar yanda al'ada ta tanadar Salamatu ta shiga yanayin ƙunci da baƙin ciki yet babu wanda ya damu sai cigaba ake da ƙoƙarin yimata auren dole

Ranar Aure aka fito da Salamatu after dressing her up like a bride sai kuka take tana turjewa maman ta tabiyo bayan su da muciya ta fara ɗibgar Salamatu, sai ihun neman agaji take wani Uncle ɗinta Mai suna Ebuza yazo ya ceceta yana ba maman ta haƙuri ya tafi da ita ɗakin sa yana lallashin ta. Kafin ya fita yabar ta da nufin anjima zai dawo ya ɗauke ta. Yana fita yasa security bakin ƙofar askin them to look after her. Tana zaune tana rusar kuka taji ana ƙwanƙwasar window mamaki ya kamata wa zai ke dinga ƙwanƙwasar window bayan ɗakin da take ciki was at the top most floor kuma dai babu stairs ta wurin window? Cigaba akayi da ƙwanƙwasa a ɗan tsorace ta tashi taje ta buɗe windown behold it was *ALIYU*duk ya rame kamar bashi ba ya fita hayyacin sa, ashe igiya ya kafe a ta wurin ya hawo har inda take which is the 5th floor idan mutum ya faɗo daƙyar yayi rai. Kallon juna suke cike da shauƙi kamar wa'yanda sukayi shekara da shekaru basu haɗuba jawo shi Salamatu tayi ya idasa shigowa ciki forgetting everything else suka rungume juna kamar zasu zama ɗaya cikin kuka tace '' you're so reckless Taya zaka biyo wuri irin haka '' yayi murmushi yace '' when there's love, there's nothing to fear.'' da sauri Salamatu tayi disengaging daga jikin Aliyu wasu zafafan hawaye na bin fuskar ta tace '' ka tafi kada su ganka zasu iya kashe ka '' tayi maganar tana tura shi akan ya tafi, hannun ta ya riƙo yace '' i will only leave with you'' girgiza kanta tayi tana kuka tace '' A'a bazai yiwu ba yanzu You have to leave pls'' daga ƙarshe she gave into his demands ya fara tura ta, ta tagar da ya biyo da tsoro ta riƙe igiyar going down slowly, bayan ta kai ƙasa Aliyu ya biyo bayan ta, yana sauka suka yanki daji....

Gida ya cika ana jiran Amarya ta fito a iyar da ɗaura auren ango yasha kyau har ya gaji, wacca aka tura taje ta kawo amarya came back tana faɗin Amarya ta gudu, lokacin da ta shiga ɗakin daidai Aliyu na kaiwa ƙasa. So taga lokacin da suka shige dajin
Mutane suka fara ƙus ƙus, wurin ya kacame da hayaniya ango Ebuka ya tashi jiki na tsuma yasa atattara masa sojin su, bayan an taro su ya basu order sukamo Aliyu da iyanu a mace ko araye suka amsa da Yes sir kafin su baɗu cikin dajin.....


WAYE SHI?(Behind the mask)By Autumn 17
Chapter 31 · 0% Book details