← Book details Waye Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 18 OF 84

Chapter sixteen: Andrew

Waye Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 13 min read

𝑊𝐴𝑌𝐸 𝑆𝐻𝐼?
(𝐵𝑒ℎ𝑖𝑛𝑑 𝑡ℎ𝑒 𝑚𝑎𝑠𝑘) 𝐵𝑦 𝐴𝑢𝑡𝑢𝑚𝑛 17


𝐶ℎ𝑎𝑝𝑡𝑒𝑟 𝑠𝑖𝑥𝑡𝑒𝑒𝑛: 𝐴𝑛𝑑𝑟𝑒𝑤

Wayar ta ta ɗauka ta fara hotuna,saƙo ne ya shigo wayar ta, her heart skipped when she saw the name, it was Ahmad buɗe saƙon tayi zuciyar tana bugawa

“ 𝑆𝑙𝑒𝑒𝑝𝑦 𝑒𝑦𝑒𝑠”
_ 𝑅𝑖𝑠𝑒 𝑎𝑛𝑑 𝑠ℎ𝑖𝑛𝑒,𝐺𝑜𝑜𝑑 𝑚𝑜𝑟𝑛𝑖𝑛𝑔 𝑚𝑦 𝑙𝑎𝑑𝑦, ℎ𝑎𝑝𝑝𝑦 𝑓𝑖𝑟𝑠𝑡 𝑑𝑎𝑦 𝑎𝑡 𝑠𝑐ℎ𝑜𝑜𝑙_💖

Cigaba tayi da kallon message É—in going over it again and again,gallery É—in ta tashiga ta tura masa one of the pictures she snapped,wani message me yasa ke popping up daga Mah-mah

“𝑀𝑎ℎ 𝑚𝑎ℎ”

_𝐻𝑎𝑝𝑝𝑦 𝑓𝑖𝑟𝑠𝑡 𝑑𝑎𝑦 𝑎𝑡 𝑠𝑐ℎ𝑜𝑜𝑙 𝑙𝑖𝑙 𝑆𝑎𝑚_😉

Murmushi Samha tayi, tayi typing É—in reply sannan ta sa wayar a aljihu.
She looked at herself one last time kafin ta fita daga hostel É—in,it was nine by then.
Tafiya take kamar ba wacca tayi lattin zuwa aji ba. She wished she could go back and sleep tayi tafiya mai tsawo before she reached her class,it was upstairs hawa take without looking at her front taji taci karo da mutum, ƙamshin turaren sa ne ya fara shiga hancin ta. Ɗago idanun ta tayi a wani irin slow and their eyes met, dogo ne sosai saye yake da uniforms ɗin sa da suka sha guga,ya naɗe hannun rigarsa zuwa guiwar hannu kasancewar long sleeved ne. Fari ne,irin farin igbo, dogo kyakkyawa, fuskar sa a matuƙar murtuke, daga gefen wuyan sa anyi tattoo ɗin 🔥 flame ga wani ɗan iskan aski dake kansa. Sannu a hankali abinda Fateemah ta faɗa mata game da dark flames ya fara dawowa ƙwaƙwalwar ta, he must be from among them, ta faɗa a ranta,tana sake ƙare masa kallo.
Kamar yanda Samha ke kallon sa haka shima ya zuba hannayen sa duka cikin aljihu yana ƙare mata kallo daga sama har ƙasa, yanda take kallon sa ba tsoro he wondered if she knew who he was? She must be a new student, tsofaffin ɗalibai idan sun gansa especially the females jikin su har ƙyarma yake, and here she is looking him straight in the eye. And her dressing....she really piqued his interest
Tsuke fuska Samha tayi sannan cike da tsiwa tace '' baka gani ne? Or your pretty eyes are only there for decoration?" Tana gama faÉ—ar haka ta galla masa harara tare da jan tsuki ta yi gaba. Binta da kallo Andrew yayi, who is she? Lallai dole ne ya koya mata hankali soon.
Shima juyawa yayi, ya wuce where he intended. Samha ta wuce several classes kafin ta iso nasu, and it was math.

'' Excuse me sir'' ya faɗa, da yake shiru aka juyo duk ana kallon ta, ganin how she was dressed yasa ajin aka fara ƙus ƙus,kallon ta math teacher yayi from head to toe, female student da wando?
Suma dai students abinda suke magana akai kenan and look at the time she showed up bayan second period is almost over '' how may I help you?'' math teacher ya faɗa yana haɗe girar ƙasa da sama
Samha batare da ta damu da kallon da ake mata ba tace '' I'm in this class '' tana gama faɗar haka ta kutsa kai, math teacher da kuma sauran students ɗin were astonished! Yanda samha ta wani kutso kai with being given permission ta samu seat kusa da window ta zauna, and what's more astonishing is the fact that math teacher Bai iya cewa komai ba. Kuma su sunsan idan har yana aji, then idan mutum yazo latti saidai yayi ta tsayuwa waje ko aturasa principal office ya karɓi punishment or worst be sent to detention, Babu wanda ke son zuwa detention why? Saboda gabaki ɗaya makarantar competition ake, its a survival of the fittest 'thus the name ELITE ACADEMY '' gabaki ɗaya idanu suka fara zarya from math teacher to Samba,ƙarfin halin Samha ya basu mamaki, while suna jiran math teacher ya juyo yace ta fitar masa daga aji,amma shiru har shuɗewar wasu lokuta.
Juyowa math teacher yayi zai cigaba da lesson wani ɗalibi mai suna Adrian Wanda da ka gansa kasan ɗan America ne saboda green eyes ɗin sa da kuma blond hair ɗin sa yace cikin American accent ɗinsa '' mr Salahu aren't you supposed to send her out of the class? Do you not see how unruly her behavior was? Bata da ɗabi'a, a matsayina na class captain Ina matuƙar tsoron kada ta ɓata sauran yan ajina,look at the way she is dressed, tayi kama da mara jin magana '' gabaki ɗaya yan aji sun gamsu da abinda Adrian ya faɗa especially matan, because obviously kishi ke damun su. Wata me suna Lucy taƙara da faɗin '' Ni body covering their hair why her? Wato ita kaɗai ta ɗau Musulunci ta aza akai Ko?" Sauran ma suka yi chaaa, Mr salahu ya idanun sa sun fara darting from Samha da tayi kamar bata San abinda ke faruwa ba zuwa yan aji, dake magana akan how unruly she was. Ya kama ta ta fara introducing ɗin kanta amma shine ta wani je ta zauna ignoring all this,she has broken way too many rules on the first day it self. Ajiyar zuciya mr salahu ya sauke sannan yace ''young miss come out pls'' sai da Samha ta ɗau kusan minti biyar kafin ta fito hakan ya ƙara tunzura yan aji, shiko the usual hot headed mr salahu found himself yana lallaɓa Samha '' introduce yourself pls'' ya faɗa yana nuna mata ta tsaya gaban yan aji ta fuskance su '' kallon Mallam salahu Samha tayi for 5 good minutes sannan ta juyo with a smirk a fuskar ta, she looked so damn pretty at the moment mafi yawancin mazan ajin shiru sukayi, suna bin Samha dana mujiya the girl is so pretty, matan kuma mafi yawancin su wani irin kishi ya tokare masu maƙoshi. Shiru ajin ya ɗauka kafin Samha cikin harshen Hausa tace '' bakuda wani hurumin son sanin suna na dan haka kowa ya kama kansa, sannan kai mai kan taliya'' ta faɗa tana kallon Adrian Wanda shima tunda ta fara magana da daddaɗar Muryar ta duk da bai san me take cewa ba ya tattara attention ɗin sa gare ta kamar sauran yan mazan,cigaba da faɗin '' Wallahi tallahi da kai da waccan mai fuska kamar an taɓe alala kan titi ku fita daga idona in rufe idan ba haka ba sai na yi muku rashin mutun ci toh'' ta ƙarashe maganar cike da tsiwa tana faman hararar lucy da Adrian. Masu jin Hausa cikin yan aji suka tuntsire da dariya jin an kira Adrian Mai kan taliya lucy kuma alalar da aka taɓe kan titi. Me salahu rarely smiles kullum zaka ga fuskar sa a murtuke Amma yau sai gashi yayi murmushi, yarinyar ta burgesa
Adrian was utterly confused,me yarinyar ta faɗa da yasa ake masu dariya? Ita ko lucy fuskar ta tayi baƙi ƙirin,ta gane duk abinda samha ta faɗa saboda tana jin Hausa and the girl just insulted her the assistant class captain what the heck!
Samha ta koma ta zauna daga inda ta tashi kamar ba ita tayi magana ba just now. The class was so noisy wasu na pressing É—in Samha wasu na condeming É—in ta

***********SAREESH****

Amreesh ne saye da suit black color, his hair was gelled, sai hannun sa sanye da wani tsadadden wrist watch, takalminsa sai wani shining suke, ga wani irin azababben ƙamshi dake tashi daga jikin sa, ajiye turaren yayi yazo ya zauna inda Salmah take, tayi tagumi tana turo baki kamar zatayi kuka,
Jawo ta Amreesh yayi, giving her a side hug yace ''if you want I can stay, Amma xamuyi wani abu in return '' ya ƙarashe maganar with a mischievous smirk ya kallon jikin ta daga sama har ƙasa, da sauri ta matsa tana rarraba idanu, miƙe wa Amreesh yayi still with the same look on his face ya nufi closet ɗin sa, few minutes sai gashi ya fito riƙe da wata baƙar kaka irin ta office, da sauri Salmah ta zo ta karɓa sannan ta saƙalo hannun ta holding his arm suka fita daga ɗakin sai shagwaɓa take zuba masa,gashi tana jin wani irin kishi aranta ganin yanda yayi kyau,yanzu duk sai an gama kallesa if she could da ta tsare sa gida wallahi. Bayan sun kawo ƙofar fita daga palorn tsaya wa Amreesh yayi ya miƙo mata hannu alamar ta basa jaka, miƙa masa tayi sannan tayi tiptoeing ta riƙe goshin sa ta yi masa addu'a before giving him kisses on each of his cheeks matsa wa tayi baya after wards yayi saurin riƙo ta kada ta gudu ya haɗiye lips ɗinsu giving her a hot kiss kafin ya rungume ta ajikin sa....'' I will be back soon '' ya faɗa saitin kunnen ta kafin ya sake ta, idanun ta sun ciko da ƙwalla hakan yasa ta yi saurin yin ƙasa da kanta. Ta share hawayen kafin da murmushi a fuskar ta tace '' i will be waiting '' jin jina kansa yayi sannan ya juya majestically ya fita, tsare entrance ɗin Tayi da ido as if hakan zai sa ya dawo....
Yana ɓacewa ganin ta ya wani haɗe rai, Secretary Ayman na ganin sa ya taso cike da girma mawa ya gaida Amreesh kafin ya buɗe masa back seat, har Amreesh zai shiga his eyes caught the sight of the body guards,ya tsane duk lokacin da zai tafi wuri a wani haɗasa da wayan nan abubuwan,ƙasa sukayi da kansu ganin kallon da yake masu. Shiga motar Amreesh yayi kafin Secretary ya rufe, sannan ya zagayo ɗayan side ɗin ya zauna carefully yanayi ma driver Alamar su tafi.

Tada motar Driver yayi suka É—au hanya, slowly Salmah ta bar terrace É—in ta koma ciki, tun lokacin da Amreesh ya tafi tayi sauri ta koma parlorn sama, ta fita ta tsaya a terrace tana kallon su, she missed him. Bayan tafiyar sune ta tuna da samha hakan yasa ta tafi tayi texting É—in ya
10:00 am
Salmah ce xaune tana kallon wani Chinese drama, she rarely watches drama Amma yau saboda kaÉ—aici,she had to and she enjoyed watching the drama.
Wayan ta ne yayi buzzing ta ɗauka taga saƙo ne daga Samha it read
“𝑆𝑎𝑚𝑚𝑦”
_𝑇ℎ𝑎𝑛𝑘𝑠 𝑠𝑖𝑠, 𝑖𝑛𝑎 𝑓𝑎𝑡𝑎𝑛 𝑘𝑜𝑑𝑎 𝑧𝑎𝑛 𝑑𝑎𝑤𝑜 ℎ𝑢𝑡𝑢,𝑖𝑛𝑑𝑖𝑛𝑔𝑎 𝑗𝑖𝑛 𝑘𝑢𝑘𝑎𝑛 𝑗𝑎𝑟𝑖𝑟𝑎𝑖_

Murmushi Salmah tayi,this girl....

Dr Ahmad ya ba zaune office ɗin sa aiki ya sha masa kai saƙo ya shigo wayar sa,sharewa yayi har lokacin da yagama aikin da kafin ya duba,it was from Samha,saƙo
It read
“ 𝑀𝑦 𝑙𝑎𝑑𝑦”
_𝑇ℎ𝑎𝑛𝑘 𝑦𝑜𝑢_
Sai kuma hoton da ta turo masa, full size lokacin da zata É—auki hoton timer tayi setting sannan ta matsa baya so it's full body sized photo. Tayi kyau sosai, wiping É—in screen É—in wayar sa yayi sannan yayi kissing É—in fuskar ta ''i love you '' ya faÉ—a in a whisper,tuna skirt ake sawa a makarantar tasu, lokaci É—aya mood É—insa ya canja, he felt jealous yanzu all the guys will be looking at his girl
Da sauri ya ƙara duba hoton ɗan waro ido yayi ganin ashe wando ne jikin ta da kuma karamin hijabi he didn't notice at first.

Murmushi yayi mai kyau, he felt relieved duk da yasan it's against the rule of the school the girl is so daring

**************
Ringing ɗin bell akayi signalling break time, bayan mr salahu ya fita da sauri ita ma Samha ta fita kafin kowa, Binta Adrian yayi da ido, the girl is something else, Lucy ganin yanda yabi Samha da ido, wani irin ya mutse fuska tayi,she had always had a crush on the guy kuma bai taɓa kallon ta ba and he's looking at this new girl? Kallon ta ɗaya daga cikin ƙawayen ta tayi tace '' Luciana ya za'ayi da yarinyar nan ne?" Shiru lucy tayi her heart was in rage wata mai suna Kathy tace '' kamata yayi mu nuna mata who rules in this place, she can't do as she pleases!! ''
Kathy ta faÉ—a, eyes burning with hatred ita wallahi taji ta tsani yarinyar.
Amarachi ta sake faɗin'' na tsani yarinyar nan, and the way Eddy(Adrian , Eddy Lucy ke kiransa) ya wani bita da kallo I'm afraid for you my friend " da sauri Lucy tayi mata wani irin sharp look hakan yasa tayi shiru. Tsuki lucy taja tace '' ba bi wata yarinya da ta isa Eddy ya so ta bayan Ni, duk wacca ta kuskure tayi wannan mafalkin wallahi saina kawo karshen ta a makarantar nan!!!'' lucy tayi maganar cike da ƙaraji, ƙawayen ta na ƙara bata ƙwarin guiwa akan hakan, the class was empty suka ɗai suka rage fita sukayi lucy a tsakiya Kathy da Amarachi gefen ta. Lucy itama yar America CE,tana da waist length hair da tayi dying blue color, fatar ta fara wanda yasha tsadadden mayuka hakan yasa ita glows, tana da matsakaitan idanun, with a model like body. She is curvy, skirt ɗin ta bayan kasancewar sa guntu,ita da ƙawayen ta sai da suka ƙara guntance sa. Butaran su nasama guda biyu a koda yaushe buɗe suke hakan yasa ana hango ƙirjin su. Kathy Yar Spain ce sai amarachi kuma yar Najeriya.
Duk inda suka wuce sai an bisu da kallo dan gaskiya ba ƙarya Allah yayi musu surah.

Cafeteria suka nufa directly,suna shiga wurin yayi shiru kowa akan su yake magana,boys wish to have them as girlfriends, Amma fa none of the girls were virgin 'dark flames sun yi aiki '
Zama sukayi bayan Kathy taje yi musu order abinci.

Dawowa tayi da abinda tayi musu order ta ba kowa nasa har yanzu ran lucy suya yake. Kathy da Amarachi na bata baki. Maza kuwa sai stealing glances suke yi. Har yan SS 3 some of them are crushing on them, Amma mafi yawan su suna yin shiru ne gudun embarrassment da kuma sun tabbatar mafi yawan matan makarantar 'dark flames sun cika aiki'

Bayan wani lokaci, sai gani sukai an turo ƙofar it was dark flames su uku suka shigo, two of which were from Italy ɗayan kuma wato chibuke ɗan Nigeria. Sun yi dying ɗin kansu red just like the name of their group dark flames 🔥
Kuma suma suna da tattoo irin na Andrew.
Shiru wurin ya É—auka, most of them tsoro be ya kama su, musamman matan da suka san they were beautiful and still virgins,maza kuma tsoro suke ji cuz this guys are the biggest bullies.
Kuma babu wanda ya isa yayi wani abu.

Ra'esah da Fateemah suma tsoro ne ya shige su, gashi suna ta neman Samha yet they couldn't find her.

Swiping ɗin gaze ɗin su dark flames sukayi across the cafeteria, wasu yan mata sai ƙara tattare kayan su suke, suna botsaro ƙirji, some looked scared, ga baki ɗaya dark flames wani smirk ne yayi foaming a lips ɗinsu suna jin daɗi a duk sanda suka ga ana matuƙar tsoron su.
Karɓar abincin su sukayi suka zauna dai dai table ɗin su Ra'esah, duk da basu kalle su ba, sai da Ra'esah da Fateemah suka kusan sakin fitsari a wando, especially Fateemah
Suna gudun su tashi, attention ya dawo kansu.
Wurin yayi tsit, kamar an yi ruwa an É—auke

Samha ta fito daga bayi ta kawo hallway É—in da zai sadaka da cafeteria ta kusa cin karo da Adrian daya dawo daga office É—in principal '' are you blind?" Ta faÉ—a tana yi kamar zata tsole masa ido. Baya yaja yana É—aga hannunsa sama in a surrending manner '' sorry'' ya faÉ—a curtly yana yin gaba, the girl...he doesn't have her time
Bayan sa tabi, sai gashi sun kawo cafeteria ɗin tare, suna shiga Andrew yana shigowa shima, wurin ya ƙara ɗaukar shiru an juyo ana kallon su ,all eyes on Samha the way she dressed,the way she walked confidently ba ruwanta mutane da yawa xaro ido sukayi....she is unaware of what she's in for.


WAYE SHI?(Behind the mask) By autumn 17
Chapter 18 · 0% Book details