← Book details Waye Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 53 OF 84

Chapter fifty two: Akwai Mayu a dangin ku Amreesh?

Waye Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 20 min read

Slowly ya fara saukowa daga stairs ɗin, Samha ta kafe sa da ido ko ƙiftawa batayi,and just then she realized how much she missed him,ya ƙarayi mata kyau sosai, shima Ahmad gani yayi Samha ta canja masa yan kwanakin da basu haɗuba.

Iska ya hura mata ya ranƙwafo with a smirk tare da faɗin '' Can't take your eyes off,my lady?" Matsawa Samha tayi tare da rolling ɗin idanunta, zuciyar ta running a marathon, yanda tayi rolling ɗin idanun yasa Ahmad yaji wani irin yarrr... Damn! If only she knew the kind of trouble she stirs idan tayi hakan....'' Ni gidan nake kallo ba kai ba!" Samha ta faɗa tana haɗe fuska,at the same time tana kallon ko ina na gidan, sosai ya burgeta,idanun ta suka faɗa saman wani aquarium mai ɗauke da ruwa kalar blue sai kifaye dake swimming aciki,she was utterly amazed.

Murmushin gefen baki Dr Ahmad yayi, ganin yanda samha ke wani wayancewa, '' I missed you'' Dr Ahmad ya faɗa stepping a bit closer idanun Samha suka ƙara girma jin abinda ya faɗa and su biyun suka wani tsura ma juna ido completely sun manta da mutanen dake zaune a parlor,it felt kamar su kaɗai ne and every other thing ya tsaya.

Murmushin gefen baki Itama Samha tayi,ta matsa kusa da Ahmad ya kasance space ɗin dake tsakanin su was very thin har suna shaƙar numfashin juna.

Their hearts beating in sync, zatayi magana taji ana Faman buga salati ana jan tsaki and all... Slowly idanun ta yakai ga mutanen dake zaune duka sun wani zubo masu ido kamar jira suke suyi Wani abu su rufe su da duka,

Idanun Samha suka sarƙe da na Azeezah that was giving her a killer look kafin na ummu,sai kuma judging eyes of the Hajiya's


'' wato karuwancin ne na waje bai isa ba har sai an shigo cikin gida ko?" Inji Hajiya zakiyya ido waje ta wani riƙe haɓa,sosai Ahmad yaji kalaman sun daki zuciyar sa,waye karuwa?

'' Kaima Ahamadu da ake ganin ka nan salihi ashe sheÉ—ani ne?" Inji Hajiya Turai.... Idanun Samha suka zama blank jin yanda ake aibata Ahmad..oh sorry ake ai bata ta,

Matasan gidan mata da maza kuwa sun wani tsare ta da ido,she could feel it har ƙarƙashin ƙasusuwan ta, Dawo da idon ta tayi kan Dr Ahmad da yayi saurin ƙirƙiro murmushi yaja akwatin ta yana faɗin
'' Muje ki huta My Lady '' gyaɗa kanta samha tayi tana biye da shi,with every step they took idanun mutanen sai ƙara binsu yake, Samha could feel the hatred their eyes bore amma ta rasa mawa!?

Sluggishly Dr Ahmad ke tafiya kamar wani marar lafiya, Azeezah ta cire idanun ta daga Samha ta mayar akan rabin ranta damn...she loves this guy kamar ranta,'' Baka da lafiya?" Muryar Samha ta shiga kunnen sa,'' Rashin ganin ki ne na yan kwanaki!" Ya faɗa kai tsaye,Yar karamar dariya tayi tare da faɗin '' Did you have a degree a likitanci or in flirting, cuz you're really good at it...'' shima Ahmad yayi ɗan guntun murmushi yace '' a likitanci nayi degree Amma ganin ki yasa my heart automatically learn how to say this words... My lady'' cheeks ɗin Samha suka wani yi ja, she was blushing jin yanda Dr Ahmad ke flirting da ita,duk wannan maganganun da suke a kunnen mutanen dake wurin, Sai Salati suke zabgawa, Hajiyoyin su kalli juna su mayar da idon su kan Ahmad da Samha,yan matan kuwa su ma dai ransu yayi baƙiƙirin, Azeezah idonta suka ciko da hawaye,ya Ahmad bai taɓa yima kowa cikin su koda murmushi bane yet yake flirting Dan wannan yar alhakin?

Samarin kuwa sun zauna suna kallon ikon rabbi,sun wani yi tagumi kamar suna kallon show, Hajiya Maleeka didn't utter a word itama ta barwa su Hajiya Turai suyi tayi, The ppl in the parlor were literally cursing su Samha under their breath, wato Amreesh yayi nashi shima Ahmad bara ya zuba nashi tijarar ko?

Suna tsaka da wannan tunanin dai dai Samha da Ahmad sun kawo wurin su, tripping Samha tayi zata faɗi,da wani irin reflex Ahmad yayi wrapping ɗin hannuwansa around her waist,their eyes collided, Samha kuma tawani gripping ɗin rigar shi,the buttons went off duka, his madly riped abs came into view, '' You' okay my lady?" Dr Ahmad ya faɗa not minding yanda rigar shi ta buɗe da kuma yan sa idon dake zaune wurin, hawayen dake maƙale idon Azeezah suka fara bin kuncin ta, loudly sultana tayi tsaki,itama idon ta sun ciko da hawaye, tana ji kamar ana yanka zuciyar ta,

Kabir ya É—an yi murmushi,he loves romance kuma abinda ke faruwa kenan yanzu a free show, sadeeq ya wani yi rolling É—in idanun sa kamar wani mace, Kowa a parlorn da reaction É—insa,and the hajiyoyi were utterly speechless....


Lumshe idanun ta Samha tayi in a way that made Dr Ahmad yaji wani irin yimmm... Her eyes are so seductive, kallon shi take without actually knowing baki buɗe, like....taga maza da yawa masu abs of course and ita bai ma taɓa damun ta ba...yet...Dr Ahmad hits differently..ganin kallon da take masa yayi a mischievous smile in a whisper yace '' I know I have a freaking hot body.... thanks for the compliment with your eyes... Amma idan kika cigaba da kallo na haka the.....'' Da sauri Samha ta ture shi,glaring at him tace '' Ni bansan haka kake ba Wallahi '' tayi gaba shiko Dr Ahmad yabi bayanta da kallo,sauke ajiyar zuciya yayi zai tafi yaji Hajiya Saude tana faɗin '' Ashe kai ɗan iska ne Ahamadu?" Tayi maganar idanu zare, suma sauran sukayi masa chaaa, murmushi Ahmad yayi dishelving his hair yace '' Ashe sai yau kuka sani?" Daga haka yabi bayan Samha yabar su da baki sake, tsaki sukayi kafin su fara barin parlorn cike da jin haushi,Abinda na suka zo su gani basu gani ba rather sai haushin da suka kwasa especially the ladies....

********

Amreesh na sauke Salmah saman faffaɗan royal bed ɗinsa da aka sama navy blue bedsheet,ya cire mata veil ɗinta sannan ya shige toilet,buɗe idon ta tayi bayan jin rufewar ƙofar,tashi tayi zaune tana kallon ko ina na ɗakin,faɗin wannan ɗakin yakai na gidan Amreesh, setting ɗin iri ɗaya, kawai dai nan akwai wani neon lights a head board ɗin, da kuma ceiling....the room is so beautiful.

Sauka tayi daga saman gadon tana jin wani *euphoria* engulfing her, walk in closet É—in Amreesh ta shiga ta É—auko wasu riguna farare guda biyu knee length da boxers suma guda biyu tana jin wani rush of excitement why? Itama batasani ba.

Fitowa tayi daidai Amreesh ya fito ƙugun shi ɗaure da towel,his hair dripping wet, idanun ta sunyi tracing ɗin beads of water dake ɗigowa daga kanshi zuwa ƙirjinsa till they disappear into the towel, Wani irin murɗaɗɗen jiki ne dashi daya ga gym har ya gaji, fatar shi ta ƙara wani fari, His face looked so *ethereal*kamar wani piece of artwork,his muscles bulging kamar zasu fashe, lips red, eyes white

Murmushi Salmah tayi kafin ta ajiye rigunan dake hannun ta,ta ƙarasa inda Amreesh hugging him tightly,Amreesh stiffened for a second kafin yayi wrapping ɗin arms ɗinsa around, yana share mata gashin ta to the side,
'' what's with the excitement?" His sexy voice pierced her ears,ƙara matse shi tayi,kafin ta ɗago fuskar ta,tana kallon shi kamar yanda yake kallon ta,jan kumatun shi tayi smiling cutely tace '' Babu, kawai dai ina farin cikin kasancewa tare da kai!" Ta ƙarashe maganar tare da matsawa baya tana kallon jikin Amreesh for the second time,gani tayi kunnen Amreesh yayi ja, fuskar da cheeks ɗinsa slightly burning,he was blushing.... Rufe bakin ta Salmah tayi tana dariya wai namiji da blushing,takasa gane Amreesh one minute he's being romantic the next second kuma je looks shy,Idanun Amreesh sai yawo suke from one side to the other,wata kunya na kamashi, so yake yasa kaya, perhaps he'll feel better, Tsalle Salmah tayi ta ɗane shi ta baya,tana dariya '' You're blushing Amreesh!!!" Tayi maganar repeatedly tana dariya, Amreesh dake zare zaren ido kamar wanda yayi ma sarki ƙarya yace '' A'a ba blushing nake ba fa '' yayi maganar sincerely and innocently,'' to meyasa fuskar ka tayi ja,and your ears too '' Amreesh was speechless, Bai san me zaice bama,tun bayau ba,he has always been a shy person kuma bai taɓa zama kusan tsirara ba sai gaban ta kawai,why does he feel shy? Twirling Salmah ta farayi a bayan shi,and they both fell on the bed, Salmah na cigaba da dariya,Tana ƙarƙashin Amreesh da ya riƙe towel ɗinsa gam jin ya kunce, what's with him? Ranar ba shine ya kawo ta bayi Ba and he even undressed her,can da baiji kunya ba why now? Yayi tambayar aranshi,his eyes looking everywhere, fuskar shi ta ƙara ja, juyowa yayi suna facing ɗin juna,
Salmah ta rungume fuskar sa, His pupils dilated itako Salmah she was having fun,yanda fuskar shi tayi ja da kuma yanda yake zare zaren ido ƙayarar da ita hakan keyi, Amreesh dai ta towel ɗinsa yake shikam, '' My.. towel '' Amreesh ya faɗa avoiding eye contact,zafin dake kumatun shi spreading to his neck, '' to ka kalle ni mana!" Salmah ta faɗa a shagwaɓe, '' and if the towel falls then....'' tayi maganar tana trailing ɗin ƙirjinsa da hannun ta, Lumshe idon shi Amreesh yayi why is he suddenly like this? Ji yayi ya kasa numfashi, Easily tayi flipping ya koma ƙarƙashi ita a sama '' Mm..Mah..ee'' ya furta a rarrabe, itama meyasa take acting haka? She never did!
'' Shhhh'' ta ɗaura yatsanta saman lips ɗinsa, yawu Amreesh ya haɗe losing his voice '' Kada kace komai... let's burn in this passion... together '' Salmah ta ƙarashe maganar da wani irin seductive voice,Amreesh yaji ya kasa komai,his heart beat quickned kamar yanda zuciyar Salmah ke bugu,Saukar lips ɗinta yaji anasa, lumshe idanunsa yayi hannun shi flying into her thick black hair,Ɗayan kuma on her waist holding her firmly,as their tongues collided,Wata Duniyar daban suka faɗa, Amreesh dake aga da towel tuni ya manta da wani towel can,they were both deeply lost in their romance kamar zasu cinye juna

'' Yunwa nake ji'' Samha da ta Kwankwaso kofar kamar zata cire ta faɗa daga waje,damn...! Da sauri Salmah ta sauka daga saman Amreesh dan ta ɗauka Samha ta shigo,tana mayar da numfashi ta miƙe ta ɗauki ɗaya daga cikin rigunan da ta ajiye ta shige toilet, Amreesh yaji kamar yaje ya shaƙo wuyan Samha,she just interrupted them, karamin tsaki yaja kafin ya miƙe ya ɗauki ɗayar rigar da Salmah ta bari,a natse yasa saman towel ɗin dake jikin sa,Buɗe ƙofar yayi fuska a matuƙar murtuke looking down at Samha hannayen sa naɗe a ƙirjin sa, Wani banzan kallo ya jefa ma Samha,if looks could kill da Samha ta mutu, matsawa baya tayi ganin how serious Amreesh was,har taji yar zufa na keto mata, smiling sheepishly tace '' Yayan mu....'' katse ta yayi da faɗin '' Idan kika ƙara zuwa nan,i will break your legs and feed it to you!" Yayi maganar cike da jin haushi yana hararar ta, Samha ta matsa baya,so take ta mayar masa da baƙar magana ko ranta zai yi sanyi amma sai ji tayi kamar an ɗaure mata harshe, Amreesh yayi mata wani irin kwarjini
'' kayi ha...'' kafin ta kai ƙarshe dai ji tayi ya banko ƙofar right on her face
Damn shiiit!!! Cije leɓenta na ƙasa tayi, what's even wrong with her? Wai ita Amreesh zai rufe ma ƙofa a fuska, kuma yayi mata baƙar magana and she couldn't reply!! Tsaki taja ta bar wurin tana ƙunƙuni ,ɗakin ta takoma ta buɗe akwatin su ta ɗauko wani biscuit data ajiye wurin intentionally incase of incases, zama tayi bakin gado tana cin abinta hankali kwance

Saye take da baggy pants baƙi sai riga baƙa mai guntun hannu,gashin ta neatly pa into a high ponytail Abinda Bata cika yankin ba kenan, her foxy eyes looking sharper, lips ɗinta more pinkish, jelar gashin ta faɗo har ƙirjinta. Sai ƙamshin turaren Dr Ahmad da take,'' sai na ƙara ɗauko wani turare wannan ya kusa ƙarewa...ko dai in tambaye shi?...nah ɗauka kawai zanyi,abinda ka ɗauka without permission yafi daɗin amfani '' tayi maganar tana ƙyalƙyalewa da dariya. Kafin ta jawo wayar ta suka hau chatting dasu Eysah,tana faɗa musu tsaruwar gidan roughly duk da bata wani kalla da kyau ba,amma parts ɗin da suka wuce kafin su iso na Amreesh and the spaces in between is worth writing on magazines.
*******
Fitowa tayi saye da irin kayan da ta ajiye ma Amreesh, Fuskar ta tayi wani kyau more than usual almond eyes ɗinta sai shining suke musamman da suka sauka akan Amreesh daya tsare ta da ido, something surging within him,kayan sun yimata yawa, farar rigar made her look slimmer eliminating her perfectly shaped hourglass figure, ƙafafunta dogaye neither fat nor slim tsaka tsaki kawai, Gashin ta da ta tsane rabi over her shoulders ɗaya kuma bayan ta, slowly take tafiya kanta ƙasa, Yanzu ita kejin kunya, miƙewa Amreesh yayi ya iso gabanta, hannuwanta ya riƙe yana kallon fuskar ta,kafin yayi brushing ɗin gashin da ya faɗo gefen fuskar ta '' you're so beautiful Mahee '' ya faɗa da deep voice his hands encircling her waist, gently pulling her close, yana shaƙar ƙamshin shower gel ɗinsa da tayi amfani dashu but it smelt better coming from her body, Murmushin kunya tayi her head facing down, ɗago fuskar ta yayi ta lumshe idanun ta,takasa haɗa ido dashi, Lowering ɗin kansa yayi going for her lips '' Mahma yunwa nakeji fa!''Kafin Amreesh ya haɗe bakin su, Salmah ta jiyo Muryar Samha daga waje, so fast ta matsa daga wurin Amreesh tana zaro almond eyes ɗinta,'' Samha tana jin yunwa '' ta faɗa awkwardly,kafin Amreesh ya sake faɗar wani Abu tayi gaba, punching ɗin iska yayi, yana ƙarajin haushin Samha, Why won't she listen?

Bin Bayan Salmah yayi,tana buɗe ƙofar har Samha zatayi magana taga Amreesh tsaye bayan Salmah haɗiye maganar tayi tana murmushin rashin gaskiya tare da matsawa baya,da sauri Salmah tace '' I'm sorry Sam,n....'' da sauri Samha ta katse ta da faɗin '' ba komai ai,bari in tafi wurin ya Ahmad'' Tayi maganar tana kallon Amreesh da ya haɗiye hannun shi baya idanun shi literally glaring at her dangerously, da sauri ta bar wurin... Salmah tabi bayan ta da kallo feeling bad. Jawo ta Amreesh yayi yana faɗin '' Karki damu,She won't be eaten..'' dariya Salmah tayi tace '' Akwai Mayu a dangin ku kenan?" Amreesh yayi ƙasa da murya haɓar shi a saman kafaɗAr ta yace '' da yawa ma, and there's one with horns like the devil ''
'' Toh AI samha zata iya dasu...and I have you!" Ta faÉ—a tana juyowa ta kalli fuskar shi, Shima ita yake kallo, suddenly yaji zuciyar sa ta wani irin bada dum,' idan fa tasani? What if someone tells her?" Yayi tambayar aranshi looking a bit tensed
'' Meya faru?" Salmah ta faÉ—a tana shafa fuskar shi, Rungumeta yayi yana faÉ—in '' na gaji ne, let's sleep '' gyaÉ—a kanta tayi and he led her to the bed, kwantawa yayi ya jawo ta jikin shi yana sauke ajiyar zuciya he has to let her know as soon as possible....

*******
Da ƙarfe takwas duka ahalin Zakee sun hallara a dining table,foods of different varieties were served,yan aiki sai kai kawo suke both yan Nigeria da turawa table ɗin ya cika,don harda su Uncle T da matan sune wurin,kowa ya hallara banda old man Zakee da Amreesh, Salmah da Samha, Ahmad sai kallon stairs ɗin yake wanting to see Ina Samha zata ɓullo.

Azeezah tazo zata zauna kusa da Dr Ahmad yace ta tashi the space wasn't meant for her,kowa ya É—ago yana kallon shi, Azeezah taji zafin abinda ya faÉ—a yet bata da wani choice sai ta canja wuri.

Samha ce ke saukowa daga stairs ɗin idanun ta akan gari gudan mutanen dake wurin, babu wani alamar tsoro ko baƙunta tattareda ita,rather kamar dama she belonged here, kallon ta suke su duka, she was totally unbothered sai ta cikin ta da take, kayan ɗasu sune saye a jikin ta sai ɗan kwalin da ta ɗaura kafin ta fito

Ganin yanda kowa ya tsareta da ido especially the young men, Ahmad yaji wani abu ya tsaya masa a maƙoshi amma sai ya danne kawai, miƙewa yayi yaja ma Samha kujerar dake gefen sa yana faɗin '' My lady '' murmushi Samha tayi a charming one,'' Thank you '' she said kafin ta zauna,
Shima zama yayi,aka bisu da ido, Uncle T ya dinga kallon tsakanin Samha da Ahmad,suma sauran da mamaki suke kallon shi, can Samha taga wani mai kama da Amreesh Sosai,Kafe shi tayi da ido kafin slowly tace '' Ina yini " Murmushi yayi ya amsa da ''lafiya '' zai yi magana suka haÉ—a ido da Hajiya Maleeka,gum yayi da bakin sa ya mai da hankali on his food, Itama Samha sai bata sake cewa komai ba.

'' ke dan baki da tarbiyya,baki iya gaisuwa ba?" Hajiya zakiyya ta faÉ—a tana zaro ido ma Samha, lifting kanta samha tayi meeting her gaze, kowa na wurin ya dakata da abinda yake waiting to see what happens next, murmushi Samha tayi kafin ta e

'' bayan kin rigada kinsan banda tarbiyya why seek for greetings from me?" Wurin yayi wani irin shiru,a loud silence, Kafin a fara exchanging glances,Dr Ahmad yayi ƙasa da kanshi yana murmushi,his lady wasn't from behind,a harzuƙe Hajiya zakiyya tace '' rashin kunya zaki min? Na lura kanki na rawa ko? Wallahi zan saita maki shi, kaji min shegiyar yarinya!"

Duk wannan maganganun da take babu wanda ya tanka mata babu kuma wanda yayi joining ɗinta,su Uncle Naseer da sauran mutanen kallo suke cike da mamaki, Azeezah idanunta kamar zasu huda Samha, Samha ko noticing batayiba ma, maraƙisiyya anxiously take jira taga fitowar Amreesh yet it seemed kamar bazai zoba.

Samha kuwa tayi da É—ai duniya batasan da Hajiya zakiyya ba sai Abincin da ta É—auki plate ta fara serving, kanta ta zuba mawa kafin ta kalli plate É—in Ahmad taga empty
'' What would you like to have?" Ta tambaye shi ba tare da ta lalle shi ba,'' duk abinda kike so my lady'' abincin da ta zuba ma kanta ta zuba masa

'' wato iskancin da kuka yi É—azu bai isa ba sai kun sake maimaitawa ku watsatstsu ko?" Hajiya Turai ce tayi maganar yanzu,and suddenly ta fara bada labarin abinda ya faru É—azu har dacewa wai Ahmad yayi kissing Samha, And the ppl present there the other time were supporting her duk da ba gaskiya bane.

Su Uncle Naseer suks fara balbale Ahmad da masifa,the dining room turned absolutely chaotic, Samha dai abincin ta take ci, tana lure da yanda Ahmad yayi pausing listening to each and every word why would she do so?

'' ku barshi yasha iska will You?'' Samha tayi maganar tana ajiye cokalin hannun ta with a sound tna kallon su a fusace, what the heck!
Hayayyaƙo mata sukayi and sai abin yazama cecekuce, once in a while take basu reply komai yawan maganar da zasuyi, a very hurtful reply, Ahmad ya dinga kallon ta ganin yanda take defending ɗinsa, her love Multiplying in his heart

'' What's going on here " Muryar Amreesh ta faso wasu wannan chaos ɗin,their heads turned to him, saye yake da kayan ɗazu sai baƙin wando daya ɗaura sama, hannun rigar ya tattare zuwa guiwar hannu,dogon gashin sa sai ƙyalli yake fuskar sa a matuƙar ɗaure,his dark Aura oozing and reaching them daga inda ya tsaya, ƙamshin turaren sa na dukar hancin su, Salmah tsaye daga gefen sa cikin farin hijabi,her hands holding his arms itama irin wandon jikin sa ne jikin ta...her almond eyes wide open tana kallon abinda ke faruwa

Tunda Amreesh yayi magana wurin yayi tsit,wanda da ace wani daga cikin su Uncle Naseer ne yayi Magana babu yanda za'ayi ayi shiru har haka

'' Here comes the devil'' Abdul Malik ya faɗa da murmushin ƙeta, Kafin ya kalli Abdul Rahman dake kusa dashi, Slowly idanun su ya sauka akan Salmah and hell man...

Ahankali Salmah da Amreesh suka ƙaraso dining ɗin,all eyes turned to them,wasu fuskokinsu baƙiƙirin, Especially maraƙisiyya,Saudat da mariya, ganin kyan Salmah ba ƙaramin baƙin ciki hakan ya musu ba, Khaleel ya kafe Salmah da ido ko ƙiftawa bayayi,hell man ina aka samo wannan beautyn? Abinda zuciyar sa ta ayyana masa kenan, kowa da abinda ransa ke raya masa and every body had their reactions

Seat ya jawo ma salmah like a gentle man,bayan ta zauna shima ya zauna, Hajiya Maleeka at this point ji tayi kamar zata fashe cuz what the hell?!!!

Gaida mutanen wurin tayi wanda bata wani samu amsawar kirki ba, '' You don't have to '' Amreesh ya faÉ—a yana kallon ta tenderly

'' wato kai kana disrespecting É—in mutane shine kake koyawa matar ka ko?" Inji Abdul Rahman, slowly Salmah ta sauke almond eyes É—inta akan shi,sai kuma ta kalli Amreesh da bai ko tanka ba, rather sai Abincin da ya far zuba ma salmah a plate É—inta, sai É—aya suka haÉ—a ido da pa dukan su suka wani É—auke kai kamar wasu enemies.

Nan danan aka fara habaici, both the parents and their kids, su Uncle Naseer dai basu ce uhm ko a'a ba

Ahmad yaji ranshi na mashi ƙunci jin yanda suke zagin Amreesh haka ma salmah, Samha itadai sai cikin ta take loda ma abincin because idan ana zagin mutum it's their choice suyi shiru ko su rama

Amreesh was unfazed da abinda suke faÉ—a sai da yaji Adam na faÉ—in '' I bet batasan Abinda ya aikata ba,idan ma anyi auren must have deceived her!" Yayi maganar smugly Yana shan juice É—in dake hannun shi

Amreesh ya wani daskare amma hakan bai nuna a body language É—insa ba, Ahmad ya kalli Amreesh

'' so tell us sister in-law,mai kika sani game da ɗan uwan namu?" Yaseer yayi tambayar cikin tsare Salmah da ido, kowa turned up to listen to abinda zata faɗa, Samha tayi ma yaseer kallon ƙasan ido kafin ta cigaba da cin abincin ta,
Murmushi Salmah tayi kafin ta kalli Amreesh sannan ta kalli yaseer cikin ido tana faÉ—in '' Nasan abinda ya kamata ace mata tasani gane da mijinta '' Yanda tayi maganar confidently yasa yaÉ—an ji a little *apprehensive*
'' Uhm interesting, kamar dame dame kenan?" Ja'afar ya jeho mata wata tambayar, Haryanzu Amreesh baice komai ba,but the anxiety within him was increasing,dan yasan akwai Manufar wa'yannan tambayoyi
'' Abinda nasani, it's personal ba sai ka sqni ba!" Dariya kusan dukan su suka kwashe dashi mockingly Abdul Malik yace '' oh, it's personal '' Salmah bataji daÉ—in yanda suka yi mata dariya ba, Samha ma taji haushi, slowly Salmah tace '' Ita wannan yawan dariyar amma dai kuna da ciwon hauka ko?" Tayi Maganar tare da É—age gira guda and she looked so freaking hot

'' Hey min..'' ta katse Abdul Rahman da faÉ—in
'' and mind your language! Tun tuni kuke disrespecting miji na, saying all sorts of things Bai tanka ba,don Ni Na faÉ—i hakan sai ka wani dinga hura hanta your ego was hurt? That easily!" Tayi maganar tana hararar su, Samha tayi murmushi haka ma Dr Ahmad while Amreesh yaji É—an sanyi aranshi but not for long saboda Kalaman Mariya yar hajiya zakiyya
'' i bet your dearest husband didn't tell you his little dirty secret!" Tayi maganar with a scowl, Salmah was a bit confused wani sirri kuma? Amreesh yaji kamar zuciyar sa stopped beating, Abincin da yake ci ya dakata na yan sakanni kafin ya cigaba,Mutanen table É—in seemed delighted Banda Pah da yake ji like be has failed as a father, Ajiyar zuciya ya sauke

''I bet idan tasani da ƙafafunta zata gudu after all wa zai so ya kasance da murd...''
''Aymana!!!!!" Dr Ahmad ya kira da ƙarfi kamar maƙoshin sa zai faɗi, idanun shi waje, Saida Aymana da sauran dake wurin suka razana,'' Mey kake wani kiran Aymana? Ba gaskiya ta faɗa ba?" Inji turai tana hararar Ahmad kafin ta cigaba da faɗin '' shi ɗin ba abinda aka kirasa bane? Ba maka...'' ta kasa ƙarasawa saboda kallon da Amreesh yayi Mata idanun shi turning black,yawu ya haɗiye tana rolling ɗin idanunta

'' har tsawon yaushe zaka cigaba da ɓoye gaskiya? Ko badaɗe ko bajima sai gaskiya ya bayyana incase idan ma ƙarya kaiwa yar mutane!" Cewar Hajiya zakiyya...and the whole place turned chaotic again,

'' koma menene na yarda da mijina and I love him the way he is!" Salmah tayi maganar with certainty,kowa yayi tsit yana kallon ta,dawo da kallon ta tayi kan mariya tace '' And the dirty secret kike magana akai...'' ta dakata tana kallon Amreesh da shima yake kallon ta yanzu holding his hand with assuring smile tace '' That's his personal life,duk abinda wani zai faɗamin idan har bashine ya faɗa min da kanshi ba then I will never believe it! Kuma every body has a past abinda ya faru was in the past na tabba and I'm his present and future Dan haka abinda ya faru a baya is none of my business so you all should calm down and give him a breathing space....'' tayi maganar a ƙufule sannan ta miƙe riƙe da hannun Amreesh suka bar wurin


WAYE SHI?(Behind the mask) By Autumn 17
Chapter 53 · 0% Book details