← Book details Waye Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 23 OF 84

Chapter twenty one: the punishment

Waye Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

Idanun Samha sun wani ƙara girma kallon tsakanin bulalen da kuma waɗan da ke riƙe dasu, damn!! Gara tayi ta kanta yanzu ba lokacin zama heroine bane, da'ace babu waɗannan sheɗanun abubuwan a hannunsu, perhaps da ta tsaya sun kece raini, amma yanzu.....

Ganin sun kusa cimma ta yasa samha tattare doguwar rigar ta, ta kwasa da gudu suma ganin haka yasa sun fara Binta a 380

Ita Samha abun gabaki É—aya dariya ma yake bata,wai itace zaratan yan mata guda bakwai ke bi da bulala da zummar zasu zane ta,

Sun ƙara yin nisa sosai da hostel har sun fara gajiya, itama Samha ta gaji it has been long since she ran like that, ƙarƙashin wani bishiya ta tsaya tana haki,suma iske ta sukayi suna Faman haki

Zee ta miƙe tana nuna Samha da bulalar ta, tace '' dan ubanki yau zaki yi bayani,shegiya mayya'' Lucy ma tace '' wato harda su sa Adrian yayi confessing yana sonki ko? Zaki gane kuren ki''

Maryam da su Ameerah ma sai tofa albarkacin bakinsu suke suna zagin Samha tare da threatening É—in ta akan yau sai da wata ba ita ba.

Samha ko sai kallon su take tana ƙoƙarin ɓoye murmushinta,just now tayi diverting ɗin sune daga inda mutane suke,saboda idan ta fara basu tarbiyya (kashi) kada arabasu.

Bayan sun gama jawabin su,they expected that Samha would look scared but to their dismay sai suka ga Samha ta ƙyalƙyace da dariya

Sai da tagama sannan tace '' toh ku Yanzu Saboda jakanci shine zaku wani biyo NI har nan wai zaku buge Ni Ko?" Sai da tayi maganar suka fara noticing Ashe sun yi nesa da makaranta.

Sun kusa shiga daji, kallon kallo sukayi ma juna sai kuma Maryam tace '' perfect yanzu zamu ci ubanki la'ada waje'' wani kallo Samha tayi ma Maryam kafin ta kalli sauran

They all looked angry kamar zasu haɗiye ta,jin jina kanta tayi tace '' zee, kinsan na taɓa faɗa maki,ki faɗa ma ƙawayen ki su dena shiga what's in between me and you idan ba haka ba i will break their bones and their will be no evidence to support cewa nice na karya su ko?'' Samha tayi maganar da murmushi a fuskar ta, idanun ta har wani ƙyalli suke

Zee da su Lucy suka kalli juna obviously maganar ta ta basu tsoro amma suka dake after all Sarkin yawa yafi Sarkin ƙarfi, Samha taci gaba da faɗin '' yau ne ranar''

Amarachi tace ''baki da hankali,ki kalli yawan mu ki kalle ki ke kaÉ—ai and you're still making mouth ''

Zeenah tace '' ku ci ubanta '' tana faɗar haka dukan su,suka yo gaba, da sauri Samha tayi tsalle ta riƙe wani reshe (branch) daga bishiyar da suke ƙarƙashi,
Ta ɗaga ƙafafun ta, ta halbe Ameerah dake gaba a fuska, Ameerah ta saki ihu tana dafe fuskar ta
Ga baki É—ayan su they were momentarily stunned

Hakan yasa Samha ta diro,sannan ta jawo Zee ganin hakan yasa sauran fara shaulo bulolin su, Samha tayi amfani da zee' a matsayin shield

Maimakon bulalar ta samu Samha sai ta dinga samun xee,
Zee sai ihu take tana faÉ—in '' kutsa ya, wayyo Allah na'' bulalar ta kai mata karo wallahi, fuskar ta tayi ja,

Tura ta Samha tayi,zee tayi gaba ta faɗa ma sauran dake bayan ta,dukan su, su bakwai sai gasu a ƙasa

Samha tayi amfani da wannan damar ta ɗauki bulolin da suka zo dasu, kafin su iya miƙewa, Samha ta fara basu tarbiyya

Sai ihu suke ƙwalawa azo a taimake su, but they were far from the school
Samha tace '' Sarkin yawa yafi sarkin ƙarfi,true ,but In this case Sarkin ƙarfi yafi Sarkin yawa'' Samha tana magana tana bugun su ta ko'ina duk sunyi jage jage da hawaye

Wayar ta, ta ciro ta É—auke su hoto making sure fuskokinsu sun fito tayi captioning ''#school belles beating to a pulp by the unknown " sannan tayi posting a school blog anonymously

Ta gama bugun su ta tsaya tana kallon su one by one sannan ta tuntsire da dariya tace '' next time ku sake biyoni,ku baku san da cewa Ni ɗin nan i love fighting so much, Saboda daga karshe nice a sama,kunga yan......'' kalamanta sun katse lokacin da ta hango mr giant (Mr kanya) yana doso inda suke,waro ido tayi tace mr giant na tafe fa,hankalin su Zee ya matuƙar tashi, he has punished them once yanzu kuma basu marmarin ya sake hukunta su.... Ƙoƙarin tashi suke su bar wurin Samha tace '' ai bazai yiwu ba'' tana gama faɗin haka,ta ɗauki bulolin ta ƙara masu atleast biyar biyar,sai ihu suke,ganin mr kanya ya kusa ƙarasowa

Ta maza ta sama kowa bulalar sa a hannun sa, idan kagan yanda tayi musu zaka É—auka faÉ—a sukayi da juna.

Kafin mr kanya ya iso wurin,samha ta shige cikin dajin ta yanki hanyar da zai maida ita makaranta directly.

Su xee ko ba abinda zuciyoyin su suke in ba tafasa ba. The girl is a devil's incarnate,sun yi nadamar biyo ta.instead of beating her to a pulp they got beaten up

Mr kanya ya ƙara so wurin yana kallon su sternly yace'' what's going on here?" Da sauri suka miƙe daga jikin juna dan har yanzu suna yanda Samha ta barsu ga wani azababben ciwon jiki da suke ji. Zee ce tayi masa bayanin abinda ya faru,
Wani irin kallo yayi mata from head to toe sannan da Muryar ban tsoro yace
''You're very stupid,do you think I'm a fool? Duk yawan kun nan riÉ—a riÉ—a da ku,kuce wai wata karamar yarinya ta duke ku har haka? Toh ina yarinyar?"
Maryam tace '' wallahi...''
''shut up ur dirty mouth '' mr kanya ya daka mata tsawa,dukan su saida suka tsorata
Yace '' wato iskancin ku ya kai ku bar makaranta Ku zo nan kuna faÉ—a ko? Lafiya tayi muku yawa'' dukan su a tsorace suke, yanzu gudun su Yace zai basu punishment duk sunyi tsuru tsuru da ido, Kathy, Lucy da zeenah jikin su da fuskokinsu sunyi jaa ga shatin buloli, that because su farare ne.

Mr kanya ya gama ƙare masu kallo kafin yace '' your punishment is,zaku cika drum ɗin nan dake back yard for a whole week '' zaro idanu sukayi suna kallon juna, akwai nisa daga tap zuwa drum ɗin and it's huge
Kathy tace '' Sir please don't.....'' yace '' your punishment is multiplied '' a gasp escaped their lips suka kalli Kathy with accusing eyes
Tayi ƙasa da kanta. Mr kanya yace '' zan rufe idanuna idan na buɗe su nagan ku anan, You will serve for a month straight '' yana gama faɗar hakan ya rufe idanunsa da sauri suka fara gudu, every part of them itch....
Bayan ya buÉ—e idanun sa mr kanya yabi bayan su da kallo, apart of him believing what they said..... But no evidence

***********************
Koda Samha ta koma É—akin su it was 7 30 Ashe hanyar da ta bi nada nisa, Ra'esah da fateemah suna kallon ta sukace daga ina rule breaker? Dariya sukayi su dukan su kafin Samha tace '' wani aiki ne ya tsayar dani amma yanzu an gama '' tana gama faÉ—ar hakan ya shige toilet

Na'ema dake kwance saman gadon ta,tabi Samha da wani tsinannen kallo she really hates the girl, Ina ma zata samu ko da one opportunity ne..... Bada daÉ—e wa ba Samha ta fito, alwala tayi yazo tayi sallah tana nan zaune har aka kira sallar isha'i suka yi Sallah banda Na'ema. Bayan Samha ta tambayi meyasa bata yi Sallah ba tace '' mind ur business '' Jan bakin ta Samha tayi shiru

Fateemah ganin tense atmosphere ɗin hostel ɗin tace '' muje cafeteria'' miƙewa sukayi da hijabban da suka yi Sallah suka nufi cafeteria

Suna tafe suna wasa not minding dare ne, sanyi har ya sauko ga taurarin da suka ƙawata sama, the view was amazing

Ra'esah ta nuna wani tauraro mai haske tace ''Samha kinga wancan tauraron?" Samha da Ra'esah suka kalli inda take nunawa suka ce su basu ga komai ba saida ta ta nuna musu sannan suka ce sun gani,
Ra'esah ta dafe ƙirji tare da sauke ajiyar zuciya ta ce '' thank God ''
Dariya suka sa su duka kafin tace
'' ako da yaushe ina ganin kine kamar tauraron da yake haskawa yake kuma haskaka wanda ke tare dashi Samha,i never liked anyone the way I like you " Ra'esah ta ƙare maganar tana riƙe hannun Samha,itama Fateemah tace

'' Yes samha,you're a shield that protect us from the storm, , U give us courage Sam, Muna matuƙar ƙaunar ki"

Jawo su Samha tayi, and engulfed the three of them in a hug cike da ƙaunar juna kafin Samha tace '' nima ina ƙaunar ku sosai, I can't stand if something were to happen to you''

Sun daÉ—e a haka kafin suka rabu,
Fateemah tace '' aga wa zai riga kaiwa'' aiko suka kwasa da gudu suna rige rige.

Banko ƙofar cafeteria ɗin sukayi dukan su, suka zube ƙasa suna dariya, kowa ya zuba musu ido giving them weird looks especially saboda hijaban su,no one wears that...

Su dai su Samha ba abinda ya dame su, miƙewa sukayi Ra'esah tace '' na riga'' ''wai ma na riga'' haka sukai ta gardama har suka samu wuri suka zauna, Samha taje counter ta karɓo musu abinci.
Kowa ya maida hankali yana cin abinci some are busy chatting
Samha ta karɓo abincin kenan ta kawo daidai wurin table ɗin wasu, ɗaya daga cikin yaran dake zaune a table ɗin ta saita ma Samha ƙafa ji kake' gwain gwain,tim!!" Duk abinda Samha ta karɓo ya kife ita ma Samha ta faɗi

Wurin ya É—auki shiru,all eyes on Samha da kuma yarinyar da ta taÉ—e ta, sai wani ciccin magani take
Da sauri su Fateemah suka zo suka miƙar da Samha suna kakkaɓe ta
'' kin ji ciwo?" Fateemah ta tambaya idanun ta na cikowa da hawaye, Ra'esah looked worried, girgiza kanta samha tayi sannan Samha ta kalli yarinyar

Calmly tace '' baki ga kin ture Ni ba?" Yarinyar ta miƙe ta hayayya ƙo ma Samha da faɗa tana zagin ta sannan tace'' wallahi dan kinga kina ma mutane su ƙyale ki Ni in kin min cimaki uba zanyi'' sakaka Samha tayi tana kallon yarin yar, suma su Ra'esah sun yi mamakin jin yanda yarinyar ta wani bi tana zagin Samha ta zubda habaici...

Over all mutanen cafeteria suma sunyi mamaki ,abinda ya fi basu mamaki the fact that Samha batace komai ba, dan sun san ba'a mata ta ƙyale.sai murmuring ake, a tunanin su ko Samha ta tsorata ne saboda yarinyar da ta taɗetan tana da tsawo ga ƙiba,in fact Samha ta bata suna 'giant number 2' dama tasan yarinyar

Ra'esah da fateemah suka ja Samha suka bar wurin ita kuma yarinyar ta É—auka tsoron ta suke sai cigaba da tujara take.
Wani Abincin Fateemah ta karɓar musu, suka zauna suna ci suna hira kamar babu abinda ya faru, itako yarinyar har lokacin taƙi yin shiru ƙawayen ta sai zuga ta suke

Soon sai ga dark flames sun shigo, sanye suke da wasu orange É—in riguna da jeans dukan su, wurin yayi shiru kamar ba kowa wurin. Kusa da table É—in su samha suka tafi suka zauna, Ra'esah da fateemah became tensed banda Samha.

Bayan sun shigo sai gasu Lucy da zeenah su bakwai suma sun shigo, the atmosphere in the cafeteria became even more tensed

Saboda yanda suke kallon Samha kamar zasu cinye ta É—anya, itako yi tayi kamar bata San da ko É—aya daga cikin groups É—in a wurin ba.

Table É—in dark flames su zeenah suka zauna so their were eleven of them in total

'' hi guys '' matan suka gaida mazan,da wani jin kai su kuma suka amsa abinci aka kawo masu,suna ci suna hira tsakanin su time to time suna kallon table É—in su Samha Hauwa a fakaice tace '' the fight is not over '' Samha tasan da ita suke,she smirked she likes it, she doesn't want the fight to be over not yet

Fateemah da Ra'esah tuni suka yi shiru suka cigaba da cin abincin su duk a takure kamar sauran É—alibai
Samha tace'' naga nawar in koma gida wallahi '' Ra'esah tace '' ai an kusa fara jarabawa '' Fateemah tace '' za mu yi kewar ki Sam ''
Samha tace '' xamuyi exchanging É—in address, ya Ahmad zai kawoni mu gaisa '' da gangan Samha ta kira Ahmad dan taba zee haushi and she succeeded

Maganganun su,suka ci-gaba da yi while dark flames low key low key suke studying É—in Ra'esah da fateemah, suma yaran suna da kyau

Lashe bakin su sukayi exchanging knowing glances,idan Samha taƙi samuwa there are other alternatives....


WAYE SHI?(Behind the mask)By Autumn 17
Chapter 23 · 0% Book details