← Book details Waye Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 62 OF 84

Chapter sixty one: WAYE SHI....

Waye Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 12 min read

The slap landed Amma ba'a fuskar Samha ba, A tsakiyar bayan Ahmad... Suna tsaka da faɗa batareda kowa yayi noticing ba ya shigo da kayan sports ɗinsa wanting to take a rest..just for him to see an tarar ma Samha, zuciyar sa ta ƙuntata ganin abinda ke faruwa ganin Hajiya Saude ta finciko Samha ya ɗauka raba faɗan zatayi ashe she had other plans,tana ɗaga hannu zata sauke shi a fuskar Samha ya ƙaraso with a speed he didn't know he had ya ƙwace samha hugging her tightly sai marin ya sauka tsakiyar bayan shi, parlorn yayi shiru Saboda ƙarar saukar marin and upon whom it landed aka shiga kallon kallo, Lumshe idonta Samha tayi hot tears streaming freely, itama batasan dalilin da yasa take kukan ba,she had wanted to anyways...jin ɗumin hawayen ta a ƙirjinsa in a gentle voice yace '' You' okay my lady?" Jinjina kanta samha tayi batace komai ba, there was so much *pandemonium* in the parlor,su Azeezah suka fara kukan munafinci wai Samha tayi musu duka sannan tasa musu ƙaiƙai a shimfiɗa, lumshe idon ta samha tayi hugging him tighter, zuciyar ta na raɗaɗi at the same time she found home...she found peace in his embrace, Ahmad ya fara stroking gashin ta forgetting everything else not seeing anybody else... just Shi da Samha...

Su Hajiya suka shiga lallashin su Azeezah, itako Azeezah da Sultana Babu abinda yafi ƙona musu rai irin ' my lady ' ɗin da Ahmad ke kiran Samha da kuma yanda yake kareta,their tears were genuine..it comes from a heart burning with jealousy...

Wani yunƙurin Hajiya Saude ta sake yi zata kamo Samha wai ta dake ta, '' touch her and you'll see the worst of me!!!" Ahmad ya faɗa with clenched jaw a kuma tsawace,wani irin fushi na consuming ɗinsa, Hajiya saude da duk sauran dake wurin sai da suka tsorata, Hajiya Saude ta kasa komai '' Wannan abu da kuke wallahi bai daceba! Sai ku dinga fifita bare akan naku it's not fair!" Umar ya faɗa yana harare harare kamar wata mace
A fusace Ahmad ya juyo yana kallon shi yace '' You called her an outsider?" Dum! Umar yaji gaban sa ya faɗi,cire Samha daga jikin sa Ahmad yayi holding her hand yace '' Listen you all..'' ya ɗan dakata yana kallon kowa cikin su, su Azeezah suka ɗago jajayen idon su suna kallon Ahmad yacigaba da faɗin '' Samha is not an outsider because I love her! Inason ta and duk wani wanda yayi ƙoƙarin musguna mata then just know that faɗan dani akeyi! And who ever tries to Touch what's mine Wallahi wallahi saina ɗan ɗana ma mutum azabar da har ya koma ga mahaliccin sa they won't forget!" Slowly Samha ta ɗago jajayen idon ta suka shige cikin na Ahmad that were filled with love,wani irin weakness taji washing over her at the same time soyayyar sa swirling with full force a zuciyar ta, hawayen da suke bin kuncin ta Ahmad yakai hannu ya share sannan yajata suka haye upstairs

Mutanen parlorn couldn't move for a heart beat,sun bala'in yin mamaki jin abinda Ahmad ya faɗa and the way he swore to deal with duk wanda yayi ƙoƙarin taɓa Samha, Azeezah ta saki ƙara ta zube wurin tana murje murje sultana ta ruga da gudu sai ɗakin ta, Hajiya Saude ta duƙa tana mata magana amma Azeezah ko ji batayi,yan maza yan uwanta Hajiya Saude tasa suka ɗauke ta zuwa ɗaki...
*******

Suna shiga ɗakin Ahmad Samha ta fashe da matsanancin kuka, harda shaƙuwa da jan ajiyar zuciya, duk yanda Ahmad yaso ya lallasheta taƙi ji, jawo ta yayi pining her with his body batareda yasan abinda yake ba yashiga sumbatar ta, Samha was stunned...jin saukar lips ɗinsa anata, his mouth was warm,his lips soft.. tenderly Ahmad ke sumbatar ta as though she were a baby, his hand firmly holding her small waist,his tongue exploring her mouth, Samha ta lumshe idon ta accepting this foreign feeling,ji sukayi su biyun jikin su ya mutu, Lumshewa da idon shi ya fara yi and yanda yake jin jikin sa made him break the kiss ba shiri ya matsa baya His heart beating wildly,ya kalli Samha da taken nan wani irin bacci na fisgar ta gani kawai yayi ta haye gado ta kwanta without saying a word, wata irin nadama yaji tazo masa lokaci guda,he wasn't like that...

********
Gumi ne sharkaf a goshin ta sai motsi take her lips muttering *incoherent* words mafalkin da ta saba ne, amma na yau was more vivid, Amreesh be kwance cikin jini shaɓe shaɓe,ga wani mutum Nan da batasan koshi waye ba yana dariya wuƙa riƙe a hannun shi,itako on the other hand ɗaure take saman wata kujera, sai ihu take tana kiran Amreesh da idon sa ke lumshe but he wasn't responding...ɗago mutumin Amreesh yayi ya soka masa wuƙa
'' Amreesh!!!!!" Salmah ta kira da ƙarfi tana tashi zaune saman gadon duk zufa ta wanke ta and she was still naked, gashin ta ya watse she looked like a mad person, not minding babu kaya ajikin ta ta duro daga gadon ganin bata ga Amreesh ba,wani irin sharp pain taji Amma bata damu ba tayi ƙofa har zata buɗe ƙofa ta hango Amreesh yashe a ƙasa his hair covering his face,he wasn't wearing a single cloth,rufe bakin ta tayi jin kuka na ƙoƙarin taho mata,da sauri ta ƙarasa inda yake ta ɗago kanshi placing it on her chest ta shiga kiran sunan shi ganin baya responding yasa ta rungume shi crying incessantly, buɗe idon shi da sukayi jawur yayi gasping for air kafin ya fara tari, ciro kanshi daga ƙirjinta tayi staring at his face that looked reddish hawaye na cigaba da zirara daga idon ta '' baki gajiya da kuka Mahee Uhm?" Amreesh ya furta da shaƙaƙƙar murya, ƙara fashewa da kuka tayi hugging him tighter kamar tana tsoron in tabar shi za'a ƙwace shi, shima hugging ɗinta yayi stroking her hair with a trembling voice yace '' I'm sorry Mahee, I was inconsiderate of your feelings forgive me '' yayi maganar so much guilt eating him up ga azababben ciwon kan daya sako shi gaba,har bai gani da kyau '' it's okay,just...just don't.. just don't ever leave me pls!"tayi maganar wasu sabbin hawaye nabin fuskar ta '' Bazan taɓa barin ki ba Mahee!" Amreesh ya faɗa barely above whisper... Sun daɗe zaune a wurin kafin suka shiga toilet sukayi wanka,sukayi sallar zuhr da Asr... Amreesh yace ta kwanta zaije ya dafa musu Abinci amma taƙi tace sai dai suje tare, with no choices suka tafi tare landline ɗin wurin Amreesh yayi amfani dashi ya kira Ahmad ya sanar dashi they're off for two days...
****
Samha ce zaune beside Ahmad duk wayar da sukayi da Amreesh a kunnen ta,cije leɓen ta na ƙasa tayi.. ji take kamar tayi kuka, wuyan ta ta murza inda pendant ɗin ta yake kaiwa ada in tasa, and she does it even now da babu pendant ɗin when she misses home badly.. when she misses her parents,ƙara danne leɓenta tayi da haurunta trying so hard not to cry... Ahmad na lure da ita slowly ta miƙe batare da ta kalleshi ba tace '' can i sleep here for the night? Bazan iya Bacci Ni kaɗai ba" Share hawayen da suka zubomata tayi sannan ta fita daga ɗakin zuwa ɗakin su, tasha kuka har ta gaji tana tsaka da kukan Ahmad ya turo ƙofar ya shigo da sauri ta fara ɓoye fuskar ta cikin pillow pretending to sleep...

Kallon ta Ahmad yake hannayen sa zube cikin aljihun wandon sa his lips pressed tightly together alot of things swirling in his mind, Matsawa yayi gab da gadon yana ƙara ƙare mata kallo kafin ya ja blanket ya rufe ta, ya daidaita Ac'n with a sigh ya zauna bakin gadon ya miƙe ƙafafun shi ya jingina kanshi da headboard ya kashe wutar ɗakin... Tun Samha na tsammanin zai tafi har bacci ya kwashe ta..


The next day koda ta farko bata ganshi ba,wanka tayi,tayi Sallah yasa wata Abaya brown color tayi combing gashinta, ta shafa turare ,duk wannan tanayi babu walwala a fuskar ta abu guda kecin ranta meyasa mahma bata faÉ—a mata ba? Ita tama lura tunda tayi aure, their relationship became somehow koda yaushe Mahma wasu busy with her husband bata da lokacin ta, Ajiyar zuciya samha ta sauke trying to suppress kukan dake tasomata,

Juyowa tayi eyes filled with tears and behold! Idon ta ya shige cikin na Ahmad that were slightly reddish, saye yake da riga da wandon brown yard,gashin sa yasha gyara sai ƙyalli yake,his lips reddish and full, yayi bala'in kyau, ga ƙamshin da da ya cika hancin ta, hannun shi riƙe da breakfast,ƙasa Samha tayi da idon ta her tear flowed,da sauri ta juya masa baya but he had seeing it... Ƙarasowa yayi keeping the breakfast on the bed side yazo ya tsaya bayan Samha folding his hand a ƙirjinsa yace '' Still crying my lady?" Girgiza kanta samha tayi don idan tayi magana her voice will betray her,'' Toh inga fuskar ki'' yayi maganar yana juyo da ita, ƙasa tayi da kanta refusing to meet his gaze,duƙawa yayi slightly yana leƙa fuskar ta da sauri ta kalli gefe her lips trembling tace '' ka rabu dani pls..'' she said with a trembling voice, ji Ahmad yayi zuciyar sana ciwo, crossing the space between them he embraced her ta ɓoye fuskar ta a ƙirjinsa ta fashe da kukan da yafi wanda tayi jiya,bayan ta gama Ahmad yasa handkerchief ɗinsa ya goge mata fuskar ta,ya zaunar da ita ya bata breakfast ɗin da kanshi,bayan ta gama ya buɗe wardrobe ɗin ta ya ɗauko mata mayafin abayar ta ya yafa mata, holding her hand suka fita daga ɗakin jiki a sanyaye Samha ke biye dashi, ma'aikatan yaba plates shida Samha suka fita leading ɗinta yayi into his car bayan ta zauna a front seat ya zagaya ta shiga ɗayan side ɗin yatada motar suka bar gidan, through out the drive Samha was gloomy shima Ahmad baice komai ba untill they arrived in some orphanage, fitowa yayi ya buɗe mata ƙofar itama ta fito,tafiya kaɗan sukayi sai ga zugar yara sunzo da gudu sun rungume Ahmad, dariya Dr Ahmad yayi hugging them back,nan Ahmad ya fara dariya hugging them back, unknowingly Samha tayi murmushi tana kallon su in awe, nuna masu ita yayi suka zo itama suka rungumeta, suna gaida ita, Manyan orphanage ɗin ne suka biyo bayan yaran suna gaida Ahmad Samha ta tsaya daga gefe tana kallo, she was just in awe yanda ake girmama Ahmad, leading ɗinsa sukayi ciki, juyowa yayi beckoning Samha to come along, takowa tayi ta tsaya kusa da Ahmad suka shiga tafiya with the rest of the ppl,wurare da yawa aka nuna musu a orphanage, Samha was delighted duk wani baƙin ciki da ta kwaso ji tayi ya washe, ga wasu yara da sukayi surrounding ɗin Ahmad suna drawing duk sun ɓata masa jiki da paint,itama sai ga wasu sun zo da kayan su wurin Samha murmushi Samha tayi ta karɓa guiding them on how to draw, juyowa Ahmad yayi yana kallon Samha dake drawing ɗin sun set over an ocean sai ga wata ƙaramar yarinya zaune saman bench a kusa da ocean ɗin tana kallon sun set, idan mutum ya kalli hoton zai gane yanayin wanda yayi drawing ɗin da kuma abunda aka zana ɗin,it all screams loneliness...yeah, she was lonely...Yan yaran suka zauna with excited eyes suna kallo sai tsalle suke cuz drawing ɗin yayi musu kyau sosai, Juyowa Samha tayi idon ta ya haɗu dana Ahmad, murmushi mai kyau ta sakar masa which made his heart mealt,
'' Kana sonta ko?" Wani yaro da yayi noticing yanda Ahmad ke kallon Samha ya tambaya yana jan hannun rigar Ahmad, Murmushi Ahmad yayi holding the kid yace '' Alot...i love her alot..'' jinjina kanshi yaron yayi ya tashi daga jikin Ahmad wurin wani vase dake drawing room ɗin ya isa ya ciro wata flower me kyau, Ahmad na kallon shi,dawowa yayi ya ɗauki paper da crayon ya ba Ahmad karɓa Ahmad yayi yana binsa da kallo, whispering yaron yayi masa,Ahmad ya rubuta abinda ya faɗa with a smile on his face bayan ya gama ya karɓa yaje wurin Samha ta miƙa mata tareda flower,karɓa Samha tayi with a smile tace '' thank you '' gyaɗa kanshi yaron yayi kafin ya nuna Ahmad yace '' shi yace in kawo maki '' ido suka haɗa da sauri ta cire nata, unfolding the paper it read '' I love you My Lady,will you marry me?" Samha felt so shy,ta ɗago idon ta ta kalli direction ɗin Ahmad their eyes collided, wani irin Abu take ji a tsakiyar zuciyar ta especially ganin yanda yake flashing his expensive smile.... Ƙara ƙasa tayi da kanta feeling super duper shy,ga wani excitement that was tugging at her heart
*******

A ɓangare Salmah da Amreesh kuwa, soyayya taji da gani mai wuyar mantawa suke nunama juna, kullum suna manne da juna ba aikin fari bare na baƙi, they were always together,at the back of her mind as much as take ji kamar suyita zaman su nan suka ɗai,ta damu da son ganin Samha and wanting to know how she was,duk lokacin da ta tuna dacewa bata ko gaya ma Samha she was going out ba she feels guilty... aside from that nothing else

Kusan kullum sai sun shiga surrounding forest É—in wurin, Amreesh nada wasu hunter clothes su da su shiga cikin dajin like real hunters,she really loves the days they spent in this place just su kaÉ—ai... Har sukayi kwana biyu...

Doguwar rigar material jane saye a jikin ta dake ɗauke da adon flowers black and red,sai akabi flowers ɗin da stones, rigar ta mata kyau sosai yafa mayafi fari tayi packing her hair into a bun, ƙafafunta saye da takalmi masu stripes,it turned out Amreesh yayi niyar kawota nan wurin since few days don haka ya tsara komai ya siya musu kaya and all they'll need ... fuskar ta babu kwalliya sai almond eyes ɗinta da ta shafa ma kwalli da ya ƙara musu kyau making them appear more sexy and gorgeous..tsaye take bakin motar tana jiran Amreesh, taɗan yi nisa cikin tunani taji tsayuwar mutum gefen ta,ɗago daradaran idanun ta tayi ta sauke su akanshi and bloody hell!!! Saura kaɗan idon ta su zubo tsabar yanda ta waro su baki sake...


Fitowa yayi daga cikin gidan locking the door, yayi shigar jan yadi da akayi ma aikin embroidery na maza,and kayan sun bala'in yi masa kyau, sai ƙamshi yake zubawa gashin sa yasha gyara it was curled down wards, his cat eyes looking very sharp, fuskar sa har wani glowing take ga wani kyau na musamman Daya ƙara, hannunsa saye da wani expensive wrist watch black color ƙafafun sa cikin Black colored sandals, tafiya yake kamar baison taka ƙasa his eyes searching for her, hangota yayi tsaye wurin mota tana magana da wanda bai san WAYE SHI ba,ji Amreesh yayi his heart wasn't accepting it,ɗan ƙara sauri yayi don yakai wurin kafin ya isa har mutumin ya bar wurin WAYE SHI?....


WAYE SHI?( Behind the mask) By Autumn 17🍁 🍁
Chapter 62 · 0% Book details