← Book details Waye Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 44 OF 84

Chapter fourty Three:when tragedy strikes....ƙaddara ta riga fata....

Waye Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 12 min read

The Nex day, Aliyu da Salamatu suka kai Samha da Mahmah har zuwa ACADEMY ɗin akayi musu register bayan sun cike foam ɗin. A maimakon su dawo gida kawai sai suka tafi wurin shaƙatawa,sun yi nishaɗi sosai kafin suka dawo gida lokacin wurin ƙarfe bakwai, wanka sukayi,sukayi sallah bayan sallar Isha'i kowa yayi retire zuwa gadon su. The next day kuma Samha tayi insisting sai an canja musu wardrobe,tana son tomboy out fits, Salamatu da kanta ta kai su shopping duk suka canja wardrobe kamar yanda samha ta buƙata, Mahmah ma ta canja kayan sawan ta from girly girl to a tomboy simply because tana son abinda Samha ke so.

Alaƙar su,su ukun ta ƙara ƙarfi inda a idon Samha Aliyu ya cigaba da zama kamar alien,idan har Aliyu na wuri Samha bata magana walwalar ta ma ɓacewa take babu wanda ya lura da hakan.
Shi kuma Chan Xiao sai ƙoƙari yake yaga ya samu damar da zai cika burin sa although it seems like there's none, Amma har ya rigada yayi deciding,idan yarinyar taƙi yarda kawai sai yayi mata fyade ya tsere simple as that.
Amma kafin nan ya fara shooting shots ɗin sa, Samha na tsaye kitchen tana zuba abinci yazo ya tsaya bayan ta,tun shigowar sa tasan shine sarai amma sai ta share ta cigaba da abinda take ,wani banzan kallo yake Binta dashi daga sama har ƙasa,duk da kuwa kayan jikin ta basu nuna surar jikin ta ba,lashe baki yayi kafin ya kai hannu holding her waist tare da faɗin '' let me help you '' yayi maganar yana matsar da hannun shi upwards yana shinshinar wuyan ta yayi nisa a sheɗanancin sa,when suddenly tayi amfani da guiwar hannun ta da ƙarfi hitting his rib cage,wani ihun azaba ya saki tare da yin baya ya dade wurin dai dai Aliyu na zuwa, '' Samha '' ya faɗa da ƙarfi a kuma tsawace yana zuwa inda xiao yake ya riƙe da yana masa sannu, Samha ko yi tayi kamar babu kowa a wurin ko batasan abinda ke faruwa ba.

Tambayar Xiao yayi abinda ya faru,xio yace '' cewa nayi ta kawo in zuba mata abincin shine ta dake Ni" Samha da taki abinda xiao ya faÉ—a bata ko juyo ba she was still nonchalant

Ran Aliyu ya ɓaci,'' ki bashi haƙuri yanzu!!" In ji Aliyu yana kallon Samha cike da fushi, kallon Aliyu tayi first,sai kuma ta kalli xiao dake murmushin nasara,

Ajiye abincin tayi ta zagaya su zata fita Aliyu ya finciko ta, saura kaɗan ta faɗi,riƙe hannun ta yayi gam yana faɗi a tsawace '' ki bashi haƙuri nace!!!!" Slowly Samha tasa idanun ta cikin na Aliyu tana faɗin '' Over my dead body '' zuciya ta ɗebi Aliyu ya wanka mata mari,her hair scattering over her face,share gashin Samha tayi daga fuskar ta ta kalli Aliyu dake huci amma batace komai ba,and her face was still expressionless, xiao sai daɗi yake ji, kamar ya ciji uwawunsa, '' for the last time apologize to him!" Aliyu ya faɗa yana ƙara damƙe hannun Samha '' I won't '' ta faɗa cike da taurin kai, wani marin Aliyu ya ƙara kai mata amma ko gezau sai gashin ta da ta ƙara gyarawa,ya ɗaga hannu zai mare ta for the third time Salamatu da ta iso wurin tayi saurin fincike ta daga hannun shi'' Haba Aliyu akan me zaka dinga dukar Samha?" Cikin fushi Aliyu ya faɗa mata abinda ya faru, kallon Samha da take kallon wani direction tayi kafin ta kalli Xiao dake kukan ciwo na ƙarya,she had alot to say Amma sai tayi shiru kawai taja hannun Samha zasu bar wurin Aliyu ya turje akan sai Samha taba Xiao haƙuri Nan da nan Salamatu ta hau suka fara exchanging words for me first time in forever, duk abunnan dake faruwa gaban xiao duk da da Hausa suke maganar amma yasan faɗa suke and he couldn't be anymore happy... Jan hannun Samha tayi suka bar wurin,ɗakin su Samha ta shiga Mahmah na bacci,zama Salamatu tayi tana duban Samha dake wasa da yatsun ta ga fuskar ta duk shatin mari, rungumeta Salamatu tayi zuciyar tana suya, bayan wani lokaci tace '' Why did you do it?" Kamar Samha ba zata yi magana ba can dai tace '' i don't like him '' Salamatu tayi mamakin jin abinda Samha tace '' me yasa baki son shi?"'' haka kawai '' Samha ta faɗa curtly Salamatu bata sake cewa komai ba,sai ƙara rungume Samha da tayi suka Cigaba da zama haka.

Bayan wannan incident akwai wanda ya faru,xiao yaga Samha da ruwan zafi da gan gan yazo ya tare ta yana ƙoƙarin kai hannun sa jikin ta, bada gangan ba ruwan suka ɓare jikin sa ya saki ƙara, Aliyu na zuwa ba tambayar ba'asi he punished Samha severely, Babu wanda ya faɗa mawa, wannan yana ɗaya daga cikin dalilan daya sa Aliyu never had a space in her heart,a suna shi uban ta ne but In relationship they shared nothing as such.


Ranaku sun tafi slowly, acan makaranta Mahmah ta dena barin Samha ita kaɗai,they were always together duk da ƙawayen Mahmah basu son Samha tare da su,a duk sanda tazo zasu dinga hantarar ta and all,she was never bothered.

Sannan ta cigaba da zuwa therapy sessions É—inta,hakan yasa condition É—inta improved drastically,ga martial arts class É—in da aka sasu ta mayar da hankali tana koyo sosai da farko it was hard idan sun dawo gida Mahmah tayi ta complain kafin suka saba, kuma idan sun dawo gida soke times suna practicing da Salamatu

Sai kuma online islamiyya da akayi enrolling É—in su nan ma suna É—aukar karatun Addini.

Theres' was a happy family so perfect so
good,ko da yaushe suna cikin farin ciki. Alaƙar su wasu a strong one...

Amma farin ciki ko baƙin ciki baya ɗorewa ai

Tragedy struck lokacin da Samha ta kai shekaru bakwai da yan watanni, Mahmah kuma shekaru goma da yan watanni, birthday É—in su guda dama.

Wani Martial arts tournament akayi organizing a academy ɗin, Mahmah taƙi tayi participating itako Samha ta ƙuƙahe akan sai tayi participating,foam ɗin ta kawo gida taba Salamatu, signing Salamatu tayi sannan ta ba Aliyu shima yayi signing,bai samu dama ba sai weekend suna zaune shine Salamatu ta ɗauko zancen, only then did he remember. '' sorry na manta ne,Je ki ɗauko foam ɗin Mahmah '' da sauri mahmah tayi hanyar ɗakin su Aliyu,ita kuma Samha tuni ta daina kallon ta fara wasa da yatsun ta jin wai Aliyu ya manta. It hurts her deeply.... Mahmah ta kawo foam ɗin, Salamatu ta tashi ta tafi kitchen tana duba girkin ta,karɓa Aliyu yayi yana signing mahmaitace '' pa idan fa nima ina so inyi joining?" Kallon ta Aliyu yayi ya ajiye foam ɗin gefe ya jawo ta yana mata cakulkuli yace '' ai bazan bari ki shiga ba aji miki ciwo ga banza'' Mahmah na dariya saboda cakulkulin da yake mata tace '' Ai itama Samha zata iya jin ciwo meyasa baka hana taɓa?" Samha ta sauke idon ta daga kallon su jin abinda Mahmah tafa ɗa, yanzu she was more than convinced Aliyu baya son ta, wato ita Mahmah ba yaso taji ciwo amma ita ko ajikin sa ko? Yanda yake wasa da Mahmah just now she wished it was her,will that forever remain a wish?'' pathetic '' ta faɗa saman lips ɗinta kafin ta miƙe taje ta ɗauki foam ɗinta tabar wurin. Da kallo Aliyu ya bita for a while kafin ya ɗauke idon sa his mood changing.kitchen ta tafi ta ajiye foam ɗin a counter Salamatu ta kalleta da murmushi tace '' kina buƙatar wani abu Moon?" Girgiza kanta samha tayi ta zo ta tsaya kusa da Salamatu suka cigaba da girki, Salamatu nayi mata hira. Salamatu tayi mamakin yanda samha ke responding unlike da,da sai dai tace uhm'' ko 'a'a,.. daga hira abin yazama wasa har da dariya Salamatu tayi farin ciki sosai. Soon Mahmah ta biyo su and the fun multiplied.

Ranakun tournament ɗin na ƙara ƙaratowa hakan yasa Samha ta shiga intensive training mode, har da Salamatu suke practicing bayan Wanda suke a makaranta. Mahmah was always by the side ta taya su cheering.


Cikin yan kwanakin nan their familial bond was stronger than usual,so da ƙaunar juna su ya ninku.

Ranar tournament Samha da Mahmah suka sa kaya baƙaƙe,riga da wando gashin Samha anyi mata tsoro biyu ita kuma Mahmah tayi ponytail,sai Salamatu tasa abaya fara tayi rolling ɗin veil ɗin Aliyu yasa yadi baƙi.

Ushering É—in su akayi zuwa seats É—in su ita kuma Samha ta tafi changing room ta sauya kaya zuwa na martial arts.

Zaman su bada daÉ—ewa ba aka fara tournament É—in, lokacin da Salamatu taga irin dukar da mutane ke sha,saura kaÉ—an tayi withdrawing É—in samha,it looked for a while kamar samha bazata iya ba, shima dai Aliyu haka yake gani amma sai ta basu mamaki....

Bayan an gama tournament É—in aka kira su aka basu medals É—in su, Samha as the first was asked wata yima dedicating É—in trophy É—inta,
Kallon mutanen dake wurin tayi,it was crowded every body wanted to hear her response, kallon su Salamatu dake cikin crowd É—in tayi '' Go Moon go" inji Mahmah cheering up for her,all eyes turned to her Amma bata damu ba.

Slowly Samha tace '' I dedicate this to my Mom and sister,I love you both so much '' wannan maganar was definitely the hardest task Samha ta taɓa yi but it was worth it.wani irin farin ciki ne ya mamaye salamatu an indescribable one,ita ko Mahmah sai tsalle take tana farin ciki. Aliyu yaji wani irin sanyi yana ratsa ilahirin gaɓɓan jikin shi,ga wani ƙaton abu da ya tokare masa maƙoshi,ƙasa yayi da idon shi.

Hotuna akayi da Samha,akayi mata ita kaÉ—ai kafin aka kira familyn ta akayi musu duka tare.

Ko ɗaya daga cikin hotunan Aliyu bai yi murmushi ba,his thoughts were in disarray. Bayan sun gama, Samha taje ta canja kayan ta sannan suka bar wurin,wani wurin shaƙatawa suka tafi,cikin motar Salamatu da Mahmah kaɗai ke magana Aliyu yayi focusing yana driving ita ko samha as usual tana kallon waje. Salamatu tayi noticing ɗin mood ɗin Aliyu and ta ƙudiri yi masa magana.

wurin cin abinci suka fara shiga,suka yi ordering ɗin abinci Kowa da abinda yayi ordering it was an open place,bayan order su ta sauka Mahmah ta ja wayar Aliyu ta fara yi musu video askin everyone to say what's on their mind '' Hello guys mom and dad I love you both sooo much and special love to my other half Moon soyayyar da nake maki ta daban ce'' Mahmah ta ƙarashe maganar tana juyo da Camera saitin Salamatu murmushi salamatu tayi sannan tace '' Ina son ku, ina son ku sosai iyalina Allah ya bar mu tare '' da Ameen suka amsa su duka sannan ta juyo d a Camera dai dai Aliyu, murmushi yayi har dimples ɗinsa suka lotsa simply yace 'l love you all '' yana gama faɗar hakan Mahmah ta juyo da camera saitin Samha dake kallon wuri daban tana dariya tace '' Oyah ƙara faɗa mana abinda kika faɗa kan stage '' to their surprise sai suka ga Samha tayi wani murmushi mai kyau, sannan tayi ƙasa da idon ta kafin ta ɗago ta kalli Salamatu da ita ma ita take kallo tace '' Ina son ki sosai mama, you're the best mom in the world'' tayi maganar idanun ta kan Salamatu, murmushi salamatu tayi ta buɗe mata hannayen ta , miƙewa Samha tayi tazo ta rungume ta, slowly Salamatu tace '' I love you too my baby ''

'' this is cheating '' inji Mahmah dake video,shi dai Aliyu zaune yake by the side Bai ce komai ba gawani irin anxiety that was rising up within him, ta dawo gefen Mahmah tace '' I love you too fiye da yanda zan iya faÉ—a.'' abinda ta faÉ—a kenan kafin ta koma ta zauna,dariya Mahmah tayi tace '' Tough girl'' Salamatu tana lure da yanda Aliyu ke bin Samha da kallo,she feels relationship tsakanin Samha da Aliyu needed to be fixed ta ajiye aranta har idan Allah ya ara mata rai she will see to it.

'' kuje kuyi wasa'' Salamatu ta faɗa ma su Mahmah, miƙewa sukayi suka tafi play ground kamar sauran yara suna wasa, fita dashi da Salamatu sukayi zuwa wani secluded area, suna hango su Samha da kuma duk abinda ke faruwa a play ground ɗin, tsayawa kusa dashi Salamatu tayi ta riƙo hannun shi , kallon ta yayi nd she offered him a warm smile, Murmushin yayi mata shima kafin tace '' I know how you feel,Amma kada ka damu Samha will definitely warm up to you Ina Nan to make sure hakan ya faru'' kafe ta da ido Aliyu yayi, ƙaunar ta na ƙara ratsa shi,jawo ta yayi ya rungume tightly kamar zai mayar da ita cikin sa,'' ban san ya zanyi ba idan babu ke, I love you to the moon and back '' yayi maganar yana raba jikin su, riƙe fuskar sa tayi a tafin hannun ta tace '' duk soyayyar da kake mun kasa a ranka tawa ta ninka taka,'' ta ƙarashe maganar tana haɗe bakin su,it was a slow and passionate kiss. Tilting ɗin kansa yayi to deepen the kiss, after a while suka rabu ganin tana ta kusa faɗuwa yasa salamatu cewa su koma gida. Aliyu ya jinjina kansa sannan suka tafi play ground suka ɗauki su Mahmah bayan sun yi hotuna da yawa. Wani pendant mai shape ɗin Moon Salamatu ta sama Samha a wuyan ta tayi pecking ɗinta on her cheek, murmushi Samha tayi Itama tayi pecking ɗin salamatu. Kafin suka bar wurin,har sun shiga cikin mota sun zauna Salamatu ta tuna ta manta abu hakan yasa tace ma Aliyu ya jira take ta ɗauko,kamar Aliyu zai ƙi amma sai yayi parking buɗe ƙofar tayi ta fita tana musu bye bye,

Haka kawai gaban Aliyu ya bada wani duum, especially da ya kalli ƙaton titin da zata tsallaka, ƙasa haƙura yayi ya fito daga motar ya tsaya waje har sai da yaga Salamatu ta tsallaka sannan hankalin sa ya kwanta

Suma su Samha suka fito suka tsaya kusa dashi,samha maintaining a distance tsakanin su.

Dukan su suka zubama hanyar wurin ido ganin yanda motoci ke Kai kawo,ga Salamatu har yanzu bata fito ba, har Aliyu zai tsallaka yaje ya É—auko ta sai gata ta fito,dukan su murmushi sukayi, tsallakowa titin farko tayi, yanzu sun fi kusa she just needed to cross one more


Aliyu ya wani irin riƙe numfashin sa, all be wanted was to see her close to him, ga wani irin sanyi da jikin sa yayi, Mahmah sai waving take ma Salamatu,ita Samha tayi shiru idanun ta ƙyam akan Salamatu,ko numfashi ba tayi.
Salamatu sai kallon su take,sai kuma tayi murmushi ta ɗan ɗaga murya tace '' i love you all soooo much '' dum!dum! Dum! Aliyu yaji zuciyar sa na bugawa wata farar mota tazo ta wuce , Salamatu ta kalli side by side taga ba mota hakan yasa ta tsallako,Aliyu kamar yaje ya jawo ta,to him this is the longest journey to wallahi, Samha ta ƙara kallon pendant ɗin ta kafin ta kalli fuskar Salamatu dake murmushi, har Salamatu ta kawo tsakiyar titi when suddenly a stray car da ta sharo gudu a 360 tayi sama da ita,sai ga Salamatu gaban Aliyu, kwance malale cikin jini,farar abayar ta was soaked red with blood

Aliyu couldn't breathe for a heart beat Bai kuma motsa ba.....


WAYE SHI?(Behind the mask)By Autumn 17
Chapter 44 · 0% Book details