← Book details Waye Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 27 OF 84

Chapter twenty six: the cold treatment

Waye Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

𝑊𝐴𝑌𝐸 𝑆𝐻𝐼?(𝐵𝑒ℎ𝑖𝑛𝑑 𝑡ℎ𝑒 𝑚𝑎𝑠𝑘)𝐵𝑦 𝐴𝑢𝑡𝑢𝑚𝑛 17

𝐶ℎ𝑎𝑝𝑡𝑒𝑟 𝑡𝑤𝑒𝑛𝑡𝑦 𝑆𝑖𝑥: 𝑇ℎ𝑒 𝑐𝑜𝑙𝑑 𝑡𝑟𝑒𝑎𝑡𝑚𝑒𝑛𝑡


Kafin Na'ema ta gama warke wa, Samha ta cakumota tana huci tace '' Why did you do it?" Na'ema ta zaro ido cikin ina ina tace '' me nayi?" Tayi maganar ita ma tana cakumo wuyan Samha,ƙara ɗauke ta da wani mari Samha tayi cikin ihu tace '' Me yasa kika samin magani cikin abun sha?" Jin abinda Samha ta faɗa yasa kowa zaro ido wasu na rufe baki sai ƙusƙus ake, Dr Ahmad ya maida kallon shi ga Na'ema yanzu yake gane ita, she was the girl who was with them randa suka yi video call da Samha

Na'ema ta rama marin da Samha tayi mata, tace '' EHHH!!! I drugged you akwai abinda zaki iya yi ne? Na tsane ki Samha idan da za'a bani wata dama dana kawar dake'' wata shegiyar dariya Samha tayi sannan tace '' ai nasani, ba sai kin faɗamin ba,tun lokacin da kika wanko shegun ƙafafun ki,ki kazo wai kina so muzama ƙawaye i knew right then wani abu kike shirya wa, kuma haƙar ki bata cimma ruwa ba'' Samha ta ƙarashe maganar ita da Na'ema suna kai wa juna duka,kan kace me, har sun kai ƙasa suna tumurmusar juna, da sauri Fateemah da Ra'esah suka ƙaraso da wasu daga cikin yan hostel ɗin ana rabasu,sai an rabasu su sake ƙwace wa su cigaba,

Mutane sunyi mamakin jin abinda ya faru kenan duk ganin da suke kamar Samha ba tada lafiya ashe magani aka sa mata? Amma me yasa? Basu da amsa, Ƙara ƙwacewa Samha tayi suka haɗe da Na'ema suna cigaba da dukan juna kamar zasu kashe juna, mutane sai ƙoƙarin raba su ake amma abu yaci tura, ganin haka Dr Ahmad da yake tsaye wuri guda kamar an ɗasa shi ya matso ya finciko Samha holding her tightly sai ƙoƙarin ƙwacewa take amma ta kasa, su Ra'esah suka ja Na'ema gefe gabaki ɗaya wurin sai hayaniya ake

Ganin Samha tare da Dr Ahmad,kuma sannan abinda tayi nufin ya faru bai faru ba wani haushi ya ƙara turnuƙe Na'ema kawai sai ta dawo da faɗan kan Ra'esah,ta ɗauke ta da maruka har guda uku, Ra'esah ta dafe kuncin ta hawaye wasu na bin wasu,zaro ido mutane Sukayi, da sauri Fateemah ta saki Na'ema kafin ta ishi ishi ta kafta mata wani wawan mari

Faɗa ya dawo tsakanin Fateemah da Na'ema, Ra'esah ko ba abinda take in Banda hawaye ganin Na'ema ta kusa fin ƙarfin Fateemah Samha ta warce hannun ta da Dr Ahmad ya riƙe ta isa wurin, ta taya Fateemah wurin cin uban Na'ema sai da suka mata ligya mutane suka ƙara rabasu,this time around suka barta suka isa wurin Ra'esah dake kuka rungume ta suka yi su biyu ta ƙara fashewa da kuka she wish itama tana da ƙarfi kamar su ahankali Samha tace '' it's okay '' Fateemah tace '' ya isa haka '' suka cigaba da lallashinta

Mutane ko babu wanda yabi takan Na'ema da take nan kwance she couldn't move jikin ta sai ciwo yake sai ma Ra'esah da suka je suna lallashi...

Bayan komai ya lafa suka raka Samha har wurin motar su by then it was 3:39 dr Ahmad tuni ya shiga yana warming ɗin motar ya kuma kira Salmah ya faɗa Mata suna tafe,tayi mamaki but she didn't waste time ta shiga kitchen ta fara haɗa abincin tarbar ƙanwar ta.

Koda suka kawo bakin motar sai da Samha ta ƙara lallashin Ra'esah,

Ra'esah na kuka tace '' ba wai ina kuka ne dan ta mare Ni ba,kawai ina kewar kine Samha '' shiru samha tayi kafin ta jawo Ra'esah ta rungume sannan tayi ma Fateemah dake tsaye gefe tana kallon wani wuri saboda bata so aga hawayen ta alamar ita ma tazo,matsowa Fateemah tayi tana goge hawayen ta before she joined in the hug samha tace '' nima zanyi kewar ku sosai and take care of ur selves while I'm away '' jin jina kansu sukayi kafin su rabu, Samha tana share masu hawayen su.

Duk abinda suke Dr Ahmad na kallon su ta mirror, buɗe ma Samha seat ɗin gaba Ra'esah tayi Samha ta shiga, Ra'esah tace '' Brother in law Dan Allah wata rana ka kawo Samha gidan mu kaji?" murmushi Dr Ahmad yayi yace '' Yes Madam!" Murmushi Ra'esah tayi itama tace'' thank you '' Fateemah ta ƙara da faɗin '' and take care of your lady'' dariya suka yi ita da Ra'esah ita ko samha tayi ƙasa da idon ta, jinjina kansa Dr yayi, rufe musu ƙofa Ra'esah tayi sannan suka matsa baya bidding them a good bye kafin Dr Ahmad yayi reverse suka tafi, Fateemah tazo kusa da Ra'esah ta rungume ta '' it's okay Eysah '' tayi whispering

Share hawayen ta Ra'esah tayi sannan suka juya suka koma cikin makaranta.


Tunda suka É—au hanya babu wanda yayi magana,from time to time Samha ke satar kallon shi amma shi ko sau É—aya bai kalli inda take ba.

Jingina kanta samha tayi tare da lumshe idanun ta

After a while suka iso, yayi Parking ya fita ya buɗe Boot ya ɗauki akwatin Samha yayi ciki dashi, Samha tabi bayan shi da kallo kafin tayi ƙasa da idon ta,buɗe ƙofar tayi ta fito walking slowly ta nufi cikin gidan,sai kallon ko ina take everything has changed

Kafin ta ƙarasa ciki sai ga Salma ta fito hugging her excitedly,sai murna take, raba jikin su tayi tana kallon fuskar Samha dake ɗauke da fake smile tayi missing ɗin Salmah da gaske amma yanzu tana cikin damuwa ganin how coldly Dr Ahmad treated her. Yana ganin ke nan duk abinda ya faru laifin tane?

Salmah ta lura da yanayin Samha amma sai ta dauka Maybe ta gaji ne '' muje ki huta '' Salmah ta faɗa tare da riƙo hannun Samha suka shiga ciki, cire takalmin ta Samha tayi suka ƙarasa har ɗakin ta, koda suka shiga akwatin ta was there, fita Salmah tayi leaving her alone, ajiyar zuciya samha ta sauke sannan ta shiga bayi tayi wanka

After a while ta fito tana tsane gashin ta da yaƙara tsawo da cika, ɗan turo baki tayi tana ayyana zata rage gashin aranta, mai ta shafa tayi oiling ɗin gashin sannan ta buɗe wardrobe ta dauko wata rigar saƙa loose fitted ash color da wando palazo shima ash tasa, ta fesa turaren da ta ɗauko daga ɗakin dr Ahmad, murmushi tayi kafin ta ɗauko wani ɗan ƙaramin hijabi white tasa

Sallah ta fara yi kafin ta miƙe ta fito tana tafiya kamar wadda aka zarewa laka, karo suka ci da Dr Ahmad, ya ɗago ta daga jikin shi without looking at her kafin ya sauka ƙasa, tabi bayan shi da kallo wani abu na tsaya mata a wuya, har yayi wanka ya sauya kaya zuwa riga ja da jeans baƙi sai zuba ƙamshi yake. Ganin ya fita daga gidan gaba ɗaya Samha taji hawaye na shirin zubo mata, juyawa tayi da sauri ta koma ɗakin ta, ta tsaya bakin window ta ɗaga labule tana kallon Motar sa har ta fita daga gidan

Zama tayi bakin gado ta dafe kanta slowly tace '' ba laifi na bane, i didnt know'' hawaye na wanke mata fuska, zuciyar ta nayi mata wani irin nauyi

Tunawa da tayi Salmah zata'iya shigowa ta ganta yasa ta saurin share hawayen ta jawo akwatin ta tana ciro kayan tare da shirya su cikin wardrobe tana tsaka da shirya kayan wani abu ya faɗo, duƙa wa tayi ta ɗauka, agogon da ta siya ma Dr Ahmad ne,
Maida agogon tayi ta ajiye cikin kayan ta,ta ci-gaba da gyara wardrobe ɗin ta. Bayan ta gama ta koma ta kwanta ranta ƙuntace tana saƙe saƙe har bacci ya ɗauke ta.


09:00

Tun bayan da tayi Sallah take zaune wurin tana tunani, bayan taje ta dubo Samha taga tana Bacci ta dawo É—akin ta ta kwanta bacci yayi gaba da ita, mafalkin da ta daÉ—e batayi ba shine tayi yau, kuma na yau É—in yafi na koda yaushe munana, she felt so worried

Tana tsaka da tunani aka turo ƙofar tun kafin ya ƙaraso ciki ƙamshin turaren sa ya iso, ido suka haɗa bayan ya shigo ƙasa tayi da idon ta. Inda take yazo ya zauna yana kallon fuskar ta,ita ko sai wasa take da yatsun ta kafin tace '' Sannu da zuwa '' jin bai amsa ba yasa ta ɗago suka haɗa ido,ƙasa ta sake yi da kanta zuciyar ta na lugude,miƙewa yayi ya matsa gefe yana rage kayan jikin shi kafin ya shiga toilet

Ajiyar zuciya Salmah ta sauke ranta na mata wani iri. Bayan minti biyar ta miƙe ta nufi wardrobe ta ɗauko masa kaya ta aje kafin ta fita daga ɗakin


Ɗakin Samha ta nufa,samun ta tayi tana waya ƙarasowa tayi ciki ta zauna bayan Samha ta gama wayar tace '' ke dawa kike magana '' Samha na murmushi tace '' room mates ɗina, ashe Eysah na da waya amma bata taɓa nuna mana ba shine yau ta ɗauko ta kirani wai tayi missing ɗina'' murmushi Salmah tayi bayan taji abinda Samha ta faɗa, shiru yabiyo baya suna kallon juna Salmah tace '' Ni naga kin ƙara girma kin zama wata riɗeɗiya,how fa?" Dariya samha tayi tace '' Na ƙara girma ko na rame?" Salmah tace '' girma dai'' taɓe baki Samha tayi ta miƙe tana shafa cikin ta '' Acici '' Salmah ta faɗa kafin suka fito zuwa parlor


Amreesh was already there, É—ago kanshi yayi ya kalli Salmah for few seconds kafin ya maida kanshi ga Samha, É—auke idon shi yayi ya maida ga abincin gaban shi

Salmah taji wani iri a zuciyar ta, Samha dai,ko a slippers É—in ta, bayan sun zauna Samha tace '' ina yini'' '' Lafiya '' ya faÉ—a curtly yana cigaba da cin abincin shi, Salmah ta zauna kusa dashi tana kallon shi

He didn't even look at her, ita dai samha tuni ta zuba abinci ta fara ci, sosai abincin yayi mata daÉ—i.

Amreesh na gamawa ya miƙe ya nufi study room Salmah tabi bayan shi da kallo me kuma ya faru? Hawaye taji sun cika mata ido tayi ƙasa da kanta kafin taja cup ta zuba ruwa tasha badan tanajin ƙishirwa ba sai dan kada samha taga hawayen ta.

Samha ma dai ta tafi Tata duniyar tunani da sauri ta ƙarasa abincin ta, ta kwashe kwanukan zata wanke Salmah tace '' ki barshi zan wanke'' Samha bata saurare ta ba ta kwashe kwanukan tana faɗin '' tunda mijin ki ya bar wurin hankalin ki ya bishi, and I know you want to go to him tashi ki tafi kawai '' ta faɗi hakan tana idasa shige wa kitchen, Salmah ta daɗe zaune a wurin kafin ta miƙe walking slowly ta nufi ɗakin su,he wasn't there har zata tafi study room sai kuma ta fasa instead ta shiga toilet, bath tub tashiga bayan ta haɗa ruwan wanka ta sa duk turarukan wanka...

Haka kawai ta fara kuka ita ma batasan dalili ba,or maybe Amreesh treated her coldly? To Amma mai tayi da ta cancanci hakan? Bacci ne yayi gaba da ita a wurin

Bayan Samha ta gama wanke wanken ta fito ta kashe komai kafin ta nufi ɗakin ta, gado ta faɗa kafin ta jawo wayar ta tashi ga contact tayi scrolling har ta tsaya akan number Dr Ahmad ta daɗe tana kokonton ta kira shi ko a'a daga baya dai ta kira shi har yayi ringing ya katse bai ɗaga ba. Ƙara kira tayi nan ma bai ɗaga ba, ana ukun data kira sai taji switched off Nan tagane Ashe ƙin ɗauka yayi. Ajiye wayar tayi ta kwanta tare da jan duvet ɗin ta rufe har kanta. Tayi alƙawarin bazata sake kiran shi ba.

Ƙarfe ɗaya saura Amreesh ya shigo ɗakin,idon shi yakai kan gado bai ganta ba,ya ɗauka ko ta tafi ɗakin Samha,rufe ƙofar yayi ya nufi toilet,yana shiga ya hange ta a bath tub tana Bacci ɗan waro ido yayi,ƙarasawa yayi wurin ta ya tsoma hannun shi cikin ruwan har sunyi sanyi, cije leɓen shi yayi kafin ya miƙe tare da ɗaga ta ya ajiye ta ƙarƙashin shower ya kunna, yana bin ta da kallo tundaga fuskar ta zuwa ƙirjin ta idanun shi lingered on her chest,ba tare da yasa abinda yake ba ya kai hannunsa yana shafawa ɗayan hannun sa kuma riƙe da ƙugun ta, buɗe idanun ta tayi jin saukar ruwa, da farko ta ɗauka mafalki ne sai da taji ana taɓa ta idanun ta suka buɗe da kyau, ido suka haɗa da Amreesh da shima ya gama jiƙewa da ruwa,tsuke fuska tayi tare da ture shi, gallara masa harara tayi kafin ta ɗauki towel ta ɗaura ta fita daga bayin tana ƙunƙuni, Amreesh was stunned me yayi kuma? Kashe shower yayi ya cire kayan jikin shi, ya ɗaura purple towel ya fito daga bayen

Haryan zu Salmah ƙunƙuni take, matsowa inda take Amreesh yayi ya riƙo hannun ta,fisge hannun ta tayi a fusace tace '' ka dai na taɓa Ni! The body is mine...''
'' and you're mine '' Amreesh ya katse ta tare da fisgo ta ta faÉ—o jikinsa.


WAYE SHI?(Behind the mask) By Autumn 17
Chapter 27 · 0% Book details