← Book details Waye Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 46 OF 84

Chapter fourty five: ta faru ta ƙare

Waye Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

Rabuwa sukayi kafin suka ɗauki jakun kunan su,suka fita, Aliyu has already arranged a car for them lokacin da suka fito drivern ya buɗe musu ƙofa greeting them politely, da can tare da Aliyu suke zuwa but things have changed tun wata ɗaya daya wuce da kansu suke zuwa makaranta a ƙafa. Politely Mahma tace '' mun gode Amma zamu tafi da kan mu ko Sam?" Jinjina kanta samha tayi,itama bata don shiga motar musamman ma saboda Aliyu yayi arranging,duk wani abu daya shafe shi bata so kusa da ita.
Kama hannun Samha Mahma tayi suka bar driver tsaye a wurin,cire hular kanshi yayi ya share gumin da ya tsatstsafo masa kafin ya mayar da hular ya fito da wayar shi daga aljihu yayi dialing ɗin number Aliyu bayan ya ɗauka respectfully yace '' yallaɓai yaran sun tafi makarantar da kansu '' daga can ɓangaren akayi magana kafin drivern ya jinjina kanshi ya ajiye kiran ya shiga motar yabar wurin.


Bayan sun dawo daga makaranta sun yi mamakin ganin chang xiao, Kallon kallo sukayi tsakanin shida Samha kafin Samha ta cire idon ta tayi hanyar ɗakin su her bag hunged lowly on her shoulders, bin Bayan Samha da kallo Xiao yayi jin footsteps ɗin Mahma yasa ya saita yanayin shi yaɗan rusuna ya gaida ita, tsayawa tayi tana yi mashi kallon tsatsaf, samun kanshi yayi da jin gumi na keto mashi ta ko ina,kaddai an gano shi! '' duk abinda zakayi kada ka kuskura ka shiga ɗakin mu and stay away'' tayi maganar cike da gargaɗi tana ƙara ƙaremasa kallo wasu shegun matsatstsun kaya ne jikin shi,she hates men who wear tight clothes '' to ranki shi daɗe'' Xiao yace yana ƙara rusunawa,barin wurin Mahma tayi tana ƙunƙuni cikin ranta,to her,koda ba'a kawo shi ba they could live on their own isn't Aliyu going to far? Tayi tambayar aranta tana tura ƙofar ɗakin su,har Samha tayi wanka ta canja kaya zuwa wani brown riga da wando irin street wears ɗin nan. Zaune take gaban madubi tana taje kanta with a distanced look on her face.
Mahma ta ƙaraso ciki ta cire takalmin ta da sock kafin ta faɗi saman gadon Samha that was neatly arranged tana faɗin '' nagaji wallahi,yunwa ma nake ji" tayi maganar tana yatsine fuska tana kallon samha ta cikin madubi with a dolly eyes, rolling ɗin idanun ta Samha tayi kafin ta miƙe tana faɗin '' zan dafa abincin ba sai kin roƙa ba'' dirowa daga saman gadon Mahma tayi tana dariya ta nufi Samha zata rungumeta, matsawa baya da sauri Samha tayi tana rufe hancin ta, cak Mahmah ta tsaya sai kuma tayi ɗan ƙaramin tsaki ta nufi hanyar toilet tana faɗin '' daɗin abun ma ƙamshin turare nake ehe'' ɗan ƙaramin murmushi Samha tayi Bayan shigar Mahma toilet ɗin,ƙara kallon kanta tayi cikin madubi,gashin ta har ya bushe ya sauko tsakiyar bayan ta '' zan yanke daga nan '' ta faɗa tana aunawa da hannun ta shoulder length kawai take son gashin.

Fita tayi daga ɗakin su zuwa kitchen completely ta manta da xiao dake gidan, shiga tayi ta kunna gas ɗin ta ɗauko frying pan ta ɗaura saman wuta, ta ɗauko noodles da ƙwai da sauran abubuwan da take buƙata.
Tunda ta fito daga É—akin su yake kallon ta, he has never had strong sexual urge towards anyone kamar ta ba. Bai san menene yayi drawing É—in attention É—in sa gare ta ba,but she effortlessly seduced him, maybe saboda yanda take É—aukan kanta ne? Or her sexy aura? Ko appearance É—inta ne he wasn't sure.
Ta wutsiyar idon ta samha ta hango shi yana tunkaro ta amma sai ta yi kamar bata ganshi ba,he holds no importance.
Tsayawa yayi daidai ita yana kallon smooth chocolate complexion ɗinta,lashe baki yayi ya miƙa hannun sa da niyar rungumeta yana faɗin '' sorry for your loss '' swiftly Samha ta kwashe albasar da ta yanka, ta matsa gefen da girkin ta yake avoiding his hug, kallon hannun shi dake sage a iska yayi kafin ya kalleta,wani irin irritation yaji yana taso masa amma sai ya danne.

Samha ta cigaba da aikin gaban ta kamar ba kowa wurin ita kaɗai ce,wani attempt yake ƙoƙarin yi ya jiyo footsteps a stairs hakan yasa stylishly ya fita daga kitchen ɗin kafin Mahma ta ƙaraso

Ganin Xiao ya fito daga kitchen yasa Mahma yi masa wani dogon kallo kafin ta shiga kitchen ɗin '' what was he doing here?" Mahma ta faɗa tana rungume hannayen ta a ƙirjin ta, kusan bayan minti ɗaya Samha tace slowly '' wa kenan?" Wuri Mahma ta samu ta zauna tace '' wancan wanda ya fita '' buɗe tukunyar abincin Samha tayi ta zuba albasar sannan tace '' i didn't notice '' daga haka bata sake cewa komai ba,itama Mahma sai tayi shiru kawai. Few minutes later Samha ta zubo musu acikin plate ɗaya ta kawo dining suka zauna su biyu suna ci, unlike da,there used to be four of them...the house looks and feels empty now. Bayan sun kammala cin abincin su Mahma tayi wanke wanke sannan suka dawo parlor suka zauna kusa da juna suna kallo


Da daddare Mahma tayi insisting sai sun jira Aliyu ya dawo kafin su kwanta duk da Samha bata so ba haka ta zauna tare da ita suna jiran shigowar Aliyu,har tara tayi ta wuce,goma tayi ta wuce har wurin ƙarfe ɗaya shiru ba Aliyu ba labarin sa

Jan Mahmah Samha tayi suka wuce É—akin su, daga nan kuma abin ya zama routine, kullum sai sun jira Aliyu but he never came

Tun suna da ran zai canja har sun haƙura,yanzu kaɗaicin yafi nada,and they only had each other. Komai tare suke wanda yaƙa ƙarama alaƙar su ƙarfi.

Shi kuma Aliyu yana ƙin zuwa gida ne saboda aduk sanda ya dawo gida memories ɗinsu na hunting ɗin sa, he was broken,he was in deep despair....

Xiao daya fahimci hakan sai yayi nufin sheƙe ayar sa, da farko ya fara zuwa ma Samha da lallami amma ganin yarinyar zata bashi wahala he resorted to violence. Kullum idan yazo sai ya daki Samha irin duka mai illatarwa sannan zai bar gidan cike da haushi da baƙin ciki, Samha bata ramawa bata kuma magana,duk abinda zai yi sai dai yayi amma bai taɓa cimma burin sa ba.
Idan ya ji mata ciwo sai dai ta shige bayi tayi treating É—in kanta in a way Babu wanda zai yi noticing .

Duk wannan abin da yake faruwa Mahma da Aliyu basu sani ba,don ita Mama tana shirye shiryen Junior WAEC ne At thirteen,hakan yasa ko an tashi sai ta zauna makaranta for extra lesson,da taso ta ƙi amma Samha tasa ta zauna'' i can take care of my self '' Samha take yawan faɗa ma Mahma
Babu yanda ta iya sai dai ta dinga zama lesson É—in through out her mind wandering to Samha.

Aliyu kuma he never cared Bai da lokaci it made them wondered shi bazai karɓi ƙaddara ba? Idan matar sa ce shi ai suma Uwar su ce,meyasa su suka iya karɓar ƙaddara Banda shi? Shi ba Musulmi bane? Me yasa yake denying ɗinsu fatherly love? Ba uwa ba uba,da wane zasu ji?

Tsaye Samha take bakin window tana kallon garin with a distanced look tunda ta dawo ake ta tsuga ruwa da sanyi amma ita ko sanyin bata ji,saye take da wata riga polo sai wando iya ka guiwa,ta yanke gashin ta kamar yanda ta ƙudurta hannayenta naɗe a ƙirjin ta tana ci-gaba da kallon yanda ruwan ke zubowa it made her wonder ko ya Mahmah zata coping?

Turo ƙofar yayi ya shigo,it was Cheng xiao fuskar shi ba annuri ko kaɗan daga gani muguntar yau sai tafi ta kullum. Dumm! Ƙirjin Samha ya buga,inda take ya iso ya sa hannu ya finciko ta yana faɗin '' yau daga ni saike kuma yau sai nayi abinda naga dama'' ƙwace hannun ta Samha tayi tana matsawa baya, kallon ta yake daga sama har ƙasa yana lashe baki,it made Samha want to puke 🤮!!

Gani tayi yayi ƙasa da wandon shi and kafin ta kauda kanta she has seen it, a grown man's private part,wani irin bugu zuciyar Samha ta fara irin na tsoro,tsoron da bata taɓa jin irin sa ba. Kauda kanta tayi tana faɗin ' hasbiyAllah' dariyar shaƙiyanci xiao yayi ya jawo gashin ta yana dunguna kanta a wurin wai tasa baki, Samha felt assaulted,her survival instincts kicked in,yana kokawar kai bakin ta sai tin wurin a matuƙar bazata yaji saukar wani irin kick daya sa shi yin tangal tangal kamar zai faɗi,dafe wurin yayi yana faɗin 'shiiiiit!!!' Saboda yanda zafin ya ratsa har cikin kwakwalwar shi, fuskar shi tayi ja,

Samha ta koma gefe ta tsaya zuciyar ta na cigaba da halbawa, tunkaro ta ya ƙarayi ya kwashe ta da wasu wawayen maruka guda biyu da yasa ta faɗi goshinta ya daki bed side table sai ga jini.

'' Ashhh '' Samha ta faɗa jin wani irin ciwo har cikin ƙasusuwanta, bata gama warke wa ba ya ƙara tunkaro ta yayi ball da ita ya sa ƙafar sa ya taka marar ta. For a heart beat she didn't move,jin wani sharp pain daya sa taji gaba ɗaya ta dena jin jikin ta,

Shi ko xiao sai huci yake,yau da gaske yake he has to fulfill his urge. Har ya yo kanta yaji anyi Horn abakin gate daburce wa yayi,yayi hanyar fita yana gyara wandon sa zuciyar sa na bugawa da ƙarfi,if he gets caught....

Samha ta daɗe kwance wurin ko ina na jikin ta na mata wani irin ciwo, after a while ta miƙe ta nufi toilet kamar yanda ta saba tayi treating ɗin ciwukan da taji, bayan ta gama ta kalli kanta ta mirror toilet ɗin,wai yau ita Samha taga na miji tsirara? And she was almost defiled! Baban ta bai sani ba no body knew,how? Dama haka maraici yake idan mutum bai da uwa? Cuz ta tabbata da Salamatu na raye No such thing will happen!
Idon ta ya kai saman pendant É—inta and she couldn't help but whisper '' I missed you Mom '' ajiyar zuciya ta sauke ta fara takowa Ahankali har ta kusa fita daga toilet É—in taji wani irin amai na taso mata,bayan ta tuna abinda ta gani,koma wa tayi da sauri tayi ta kwarara amai,bayan tagama ta kalli wurin É—an waro ido tayi ganin jini jini

Wanke wurin tayi ta fita,gado ta nufa ta kwanta tanajin wani irin feverish, karkarwa jikin ta ya fara,jawo blanket tayi ta lulluɓe zuciyar ta na ƙuna,she felt miserable she felt abused,she felt sick and assaulted....


WAYE SHI?(Behind the mask)By Autumn 17
Chapter 46 · 0% Book details