← Book details Waye Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 30 OF 84

Chapter twenty nine: she's my wife

Waye Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 17 min read

Shigar Amreesh ɗakin yayi daidai da tashin Salmah zaune saman gado tana Faman haki kamar wadda tayi gudu ta jiƙe sharkaf da gumi idanun ta sai yawo suke a Kowane kusur wa na ɗakin jikin ta sai ɓari yake da sauri Amreesh ya ƙaraso tare da ajiye abubuwan dake hannun sa. Zama yayi kusa da ita holding her gently tare da gyara mata gashin da ya rufe mata fuska, kallon shi Salmah tayi da idanun ta da sukayi jaa kamar tana ƙoƙarin gane shi, '' Are You okay?" Amreesh ya faɗa caressing her face da sauri Salmah ta rungume shi jikin ta na cigaba da ɓari, haurun ta na karkarwa kamar mai jin sanyi. Shiru Amreesh yayi yana ƙara shigar da ita jikin shi itako sai ajiyar zuciya take saukewa tana ƙara ƙanƙameshi. Ɗagowa tayi after a while tana duba Amreesh all over tana shafa fuskar sa jikin sa and all where her hands could reach, riƙe hannun ta Amreesh yayi idanun sa cikin nata wondering what's wrong with her, miƙewa Salmah tayi tare da miƙar da Amreesh still checking everywhere on his body ɗaga rigar sa tayi ta duba cikin sa,sai kuma ta cire rigar duka tana cigaba da dubashi duk abinda take Amreesh bai hanata ba sai kallon ta kawai da yake sai da yaga zata cire wandon sa tana faɗin ''Are You okay '' sannan yayi azamar riƙe hannuwanta yet again yana kallon cikin idon ta, itama shi take kallo duk a firgice take kallon juna suke eye ball to eye ball kafin yace in a gentle voice '' what's wrong Mahee?" Ya faɗa yana shafa gefen fuskar ta fashewa da kuka Salmah tayi hugging him tighter than before shi kuma yana patting ɗin Bayan ta kuka take sosai kamar wadda akayi ma bushara da mutuwa, abun ya daure ma Amreesh kai cikin kuka tace '' promise me bazaka taɓa barina ba one day'' ta ƙarashe maganar tana ɗago kanta her reddish dark eyes into his ocean blue ones riƙe fuskar ta yayi yana goge mata hawayen tare da faɗin '' koda duk duniya zasu taru akan mu trying to separate us,I will stick to you like a bandaid,sai in mut..." Da sauri Salmah ta rufe bakin sa tana ƙara fashewa da kuka tace '' dan Allah kada ka faɗi haka, I can't live without you '' Amreesh bai san mai yake damun Salmah ba yana so ya tambaye ta but he will do that when she calms down rungumeta yayi on his bare skin kamar zai shigar da ita cikin shi

Sai ajiyar zuciya take sauke wa, É—aukar ta yayi ya ajiye ta saman gado zai mike ta jawo sa ya faÉ—o kanta tace '' let's stay like this Dan Allah '' ajiyar zuciya ya sauke sannan ya mirgina ya dawo da ita saman shi his hand wrapped around her yana gyara mata gashin kanta she looked disrupted. He so badly wants to know what made her behaved the way she did..... Bacci ne yayi gaba da su su biyu....


Can kitchen kuwa Samha da Ahmad tuni suka gama haɗa pizzar su,sai tsalle take kamar wacce aka biya wa kujerar Makka. Dr Ahmad yayi tagumi a counter yana kallon ta he had never seen her like that. Ganin yana kallon ta yasa tayi brushing ɗin gashin ta behind her ears ta zo kusa dashi ta tsaya sannan tace '' na gode'' tsayawar oven ɗin yasa ta juya da sauri ta isa wurin ta buɗe zata zura hannu ba tare da tasa gloves ba da sauri Ahmad ya riƙe hannun ta ɗago foxy eyes ɗinta tayi looking into his sleepy ones, hararar ta yayi sannan yace with cool voice '' ba kida hankali ne? Salon ki soye hannu ki ishe mu da raki ko?!" Ya ƙarashe maganar yana jawo ta baya turo baki Samha tayi tana kallo ya cire pizza that was smelling so nice it looked delicious. Serving ɗin ta yayi bayan ta dauko plate, ƙara ɗauko wani tayi yace '' wannan fa?" Yayi maganar cikin ɗage gira, ta waro ido tace '' idan naci,kai ma sai kaci!" Ta idasa maganar tare da serving cikin plate ɗin yace '' i don't eat junk food '' ta miƙa masa plate ɗin tare da faɗin '' sai ka fara yau'' ƙin karɓa yayi ta jawo hannun shi ta'aza masa plate ɗin ranta ya fara ɓaci. Ɗaukar nata tayi ta tafi dining. Ahmad ya bi bayan ta yana faɗin ' Attitude ' aransa

Tunda Samha ta fara cin pizza É—in take Santi,Dr Ahmad ya kasa cin wanda tasa mashi ya shagala da kallon ta,' the way her pink lips move, damn sexy I wanna have a...' zaro ido Ahmad yayi jin abinda ranshi ke ayyana wa,da sauri Ahmad ya dakatar da tunanin ya kauda kansa tare da faÉ—in '' astaghfirullah' Samha da taji abinda ya faÉ—a ta haÉ—e rai tare da faÉ—in '' dama cin pizza haramun ne bansani ba?" Tayi maganar visibly irritated

Ahmad baice komai ba ya tura pizza ɗin gefe ya miƙe, tsalle Samha tayi ta ɗane sa tana faɗin '' dan kai pa na katse Bacci na na wahalar da kai na nayi wannan abin mai shegen wahala shine zaka tafi baka ciba?" Ta ƙarashe maganar kamar zatayi kuka daskarewa Ahmad yayi yana ƙoƙarin kada yayi losing control yanda maganganun ta ke fitowa da kuma yanda zazzafan hucin ta ke dukan kunnen sa and Overall how her body felt on his? Da shaƙaƙƙar murya da yake jin tsoron kada ta gane yanayin sa yace '' toh sauka zanci'' da sauri Samha ta sauka ta koma wurin ta ta zauna Dr Ahmad ya ɗau kusan minti 3 batare da ya juyo ba, lumshe idanun sa da suka sauya launi yayi sannan ya juyo ya zauna avoiding her gaze. Samha ko ta tsare shi da ido waiting for him to eat.' she's too cunning ' ya ayyana aranshi

Daƙyar Ahmad ya samu ya cinye sannan ya miƙe ya bar wurin Samha ta bisa da ido sai kuma ta taɓe baki tayi clearing ɗin abubuwan da suka ɓata kafin ta wuce upstairs.....


02:39
Wayar Amreesh dake gefen gado ke ringing,a hankali ya fara buɗe idon sa ya kalli ceiling kafin ya lumshe su sexily ya kai hannunsa sa ya jawo wayar da ta riga da ta katse, Salmah dake kwance saman ƙirjin sa ya kalla wondering if she felt better


Sauke ta yayi daga ƙirjin sa ya gyara mata kwanciya ya rufa mata blanket Dan akwai sanyi yayi pecking ɗin cheek ɗinta

Wayar sa ta ƙara fara ringing,duban shi yakai ga caller ID ' Uncle T' shine rubuce a screen ɗin,kallon wayar Amreesh yake yana mamakin kiran me ake masa har wayar ta tsink...
Swiping yayi ya shiga call logs yaga missed calls from different contacts business da family cikin natsuwa yayi dialing É—in Uncle T'
Wayar na fara ringing aka ɗauka, kara wayar Amreesh yayi a kunne tare da lumshe idanun sa ya jingina da head board ɗin gadon daga ɗayan ɓangaren wata murya cike da fushi tace '' Shin kaga abinda ke yawo a media da kuma ƙasar baki ɗaya? Nace kagani? Did you know how ur actions affected us? Ashe dama shekara da shekaru ƙarya kake mana Muhammad? You will pay for it '' yana kaiwa nan ya katse kiran. Amreesh ya kalli screen ɗin wayar sa,sai kuma cikin rashin bawa abin muhimmanci ya ajiye ya miƙe ya nufi toilet. Fitowa yayi bayan yayi alwala ya kabbarta sallah bayan ya gama yayi adhkar ya nufi gadon zai tada Salmah tayi sallah idon sa ya sauka akan wani jan abu, yaye blanket ɗin yayi yana kallon jinin...buɗe idon ta da suka kumbura salmah tayi suka shige cikin na Amreesh, sai kuma ta yunƙura zata tashi she felt wet da farko ta ɗauka ko fitsari ne sai da takai idon ta wurin taga jini ne,zaro ido tayi sai kuma ta kalli Amreesh da shima abinda yake kallo ke nan fashewa tayi da kuka tana jan blanket ɗin tana ƙara rufe wa, yanda take kukan yasa Amreesh jawota jikin sa ya rungume batare da damuwa da cewa kayan sa zasu iya ɓaci ba.since she has turned to a cry baby cikin raɗa yace '' it's okay queen of tears,ba kya gajiya da kuka ne?'' ɓoye fuskar ta tayi a ƙirjin sa tace '' yi haƙuri ba da gangan bane''

'' it's okay this is a normal thing so ki daina kuka" yana gama faɗar hakan ya ɗauke ta suka shiga toilet wanka yayi mata da kanshi wata irin kunya ce ta rufe Salmah tayi ƙasa da kanta ta rufe idanun ta gam, Amreesh didn't tease her at all, bayan ya gama ya jawo towel ya goge mata jikin ta ya ɗauke ta suka koma ɗaki ya shafa mata mai ya gyara mata Gashin ta ya sa mata loose fitted gown ya fesa mata turare ya ajiye ta saman sofa ya cire bedsheet ɗin da ya ɓaci ya shimfiɗa sabo. Ita dai Salmah ta ƙasan ido take binsa da kallo yanda yayi mata komai kamar bata da lafiya ko kamar ita jaririya ce, she was embarrassed Amma wata irin ƙauna da son Amreesh ne ya ƙara cika zuciyar ta miƙe wa tayi tana taya shi a kunya ce, ɗaukar pillow Amreesh yayi ya jefa mata ita ma ta jefa masa just like that pillow fight begun sosai suke nishaɗi jawota Amreesh yayi yace '' You haven't eaten what do you want to eat?" Salmah tace '' bana jin yunwa but i will take tea'' miƙewa yayi ya haɗa mata tea mai kauri ya bata kaɗan ta sha tasa ya shanye sauran tana dariya, yace'' kin rama ke nan?" Yayi maganar yana waro ido Salmah ta rufe idanun ta tana dariya.

Samha ta koma ɗakin ta bayan ta gama tayi clearing ɗin komai Ahmad ya shiga ɗakin sa dafe da marar sa ya isa bakin gado ya jawo drawer ya ɓalli maganin jiya yasha sannan ya kwanta saman cikin sa yana lumshe ido, yanda yake azabtuwar nan,he has to stay away from Samha. Bazata dinga ɓallo masa aiki ba tana barinsa da jinya.

Yana kwance ahaka his phone rang batareda ya duba ID ba ya É—auka ya aza saman kunnensa yana lumshe ido " Ahmadu wato harda kai aka haÉ—a baki ana cin amanar mu ko? Wato kaima ka zama mutumin banza, kai da shi kun haÉ—a baki yana lalata da ya'yan Mutane kai Kuma kana supporting É—insa I'm so disappointed in you Allah kaÉ—ai yasan for how long this has been going on sai yau ya toni asirin ku" tunda aka fara magana Dr Ahmad ya tashi zaune,sanin wa ke maganar it was uncle Naseer, yanda yake magana a kausashe da kuma kalaman shi yasa Dr Ahmad ruÉ—ewa what's he talking about? Dr Ahmad yace '' kawu bangane abinda kake nufi ba" from the other end uncle Naseer yace '' oh baka sani ba? Ni zaka raina ma da wayau?" Kafin Dr Ahmad ya yi wata magana Uncle Naseer ya katse kiran
Da sauri yayi unlocking ɗin wayar sa messages begun popping up, harda latest News sakin wayar yayi ganin hoton Amreesh da Salmah anyi editing ɗinsa, Salmah sanye da pant G string irin wanda Turawa ke sawa idan zasu Beach sai bra da bata wani rufe ƙirjinta ba, Amreesh ɗauke da ita tayi wrapping ɗin ƙafafun ta on his waist hannun ta on his neck shi kuma ya ɗaga ta sama hannunsa wrapped around her waist suna kissing ɗin juna. Hoton Gaba kuma yafi na farkon muni.'innalillahi wa inna ilaihi raji'un '

Miƙewa Dr Ahmad ya yi ya fita jikin sa na tsuma, Amreesh ya gani tsaye gaban TVn dake nan parlorn sama shima yana kallon News ɗin fuskar sa unreadable,

Ƙarasowa Dr Ahmad yayi zai yi magana wayar Amreesh tayi ringing ɗaukar wayar Amreesh yayi tare da sawa a speaker '' Come home '' kawai aka faɗa aka katse kiran

Dr Ahmad kallon Amreesh kawai yake he could feel the drop in temperature


********ZAKEE MANSION


Wani irin katafaren gida ne gari guda mai ɗauke da golden gate side by side securiy ne, buɗe gates ɗin sukayi lokacin da motar su Amreesh ta ƙaraso, suna Faman faɗin '' welcome young masters '' driving Dr Ahmad yake eyes looking ahead Amreesh a gefen sa ya jinginar da kansa, shima dai bai san abinda zasu tarar ba amma yasan koma menene bazai ƙare da kyau ba. Bayan yayi parking ya fito ya buɗe ma Amreesh ƙofa shima ya fito, tare suka jera suka shiga katafaren MANSION ɗin Wanda kusan komai na ciki green and white ne, according to the residents,green represents nature kuma su suna son yanayi dan haka agidan ma akwai itatuwa of varieties of fruits. Gawani chandelier dake hanging high up, Babu single room down stairs sai dai upstairs kuma parts ne ba ɗakuna ba,parlorn ya haɗu sosai duk wani abun more rayuwa akwai a wurin ga daddaɗan ƙamshin dake tashi. Tun lokacin da su Amreesh suka shigo servants ɗin dake kai kawo suka tsaya suna ta Faman kwasan gaisuwa bowing slightly kan su ƙasa, bayan tafiyar su Amreesh daga wurin suka ɗago kawunan su suna ƙusƙus tsakanin su.
Wata corner su Dr Ahmad suka bi da ya sada su da main parlorn da ake family meeting.

Wani kata faren parlor ne wannan ya fi wancan girma haɗuwa da tsari. Gabaki ɗaya ahalin Zakee tun daga Manyan su zuwa ƙana nan su babu wanda baya wurin.

Old man Zakee zaune saman wata kujerar royalty it was made out of pure gold shima kansa kayan dake jikin sa represents royalty duk da ko su ba jinin sarauta bane, shi ba fari ba shi ba baƙi ba tsaka tsaki ne, fuskar sa mai cike da kamala da Dattaku ga kwarjini da haiba da Allah yayi masa, gefen sa Uncle T ne sai cika yake yana batsewa fuskar sa a mutukar murtuke Uncle Naseer shima gefen sa sai karkaɗa ƙafa yake kamar wata mace shima dai fuskar sa ba annuri, sai Uncle Ismael da yake nan kamar ba abinda ya dame sa sai kuma papa baban Amreesh da yayi ta gumi.
Ɗayan gefen kuma matan uncles ɗinsa ne zaune, Hajiya Saude matar Uncle T, Hajiya zakiyya matar Uncle Naseer Hajiya Turai matar Uncle Ismael sai Hajiya maleeka matar papa, kowace da abinda ke yawo aranta musamman Hajiya Turai da zakiyya da suka kasa ɓoye wa, they had alot to gain idan abinda ake zargin Amreesh gaskiya ne to ma ai gaskiya ne tunda gashi abu ya karaɗe ko ina and it's affecting their business.

Daga ƙasa kuma yan mata da samarin gidan ne, Kabir, yaƙub, Malik,Azeezah,maraƙisiyya, da Ummu yayan hajiya Turai ,sai saudat, Usman, haneef Umar,sadeeq yayan Hajiya Saude sai kuma mariya Ja'afar,Adam , yaseer, khaleel,Aymana da sultana yayan Hajiya zakiyya sai
Abdul Malik da Abdul Rahman yayan Hajiya Maleeka.

Abdul Malik É—an Uncle T,Abdul Rahman É—an Uncle Naseer,Umar, Sadeeq da maleek ya'yan Uncle Ismael, su suke taya iyayen su juya family business dukan su sa'an su Amreesh ne
Ga wani irin competition dake tsanin su babu Maison yaga dan uwansa ya wucesa kuma iyayen su basu kwaɓe su ba, amma cikin su Babu wanda ke ƙoƙarin cutar da wani dan hanashi samun cigaba. ra'ayin su baya taɓa zama ɗaya,abu ɗaya da ra'ayin su yazo ɗaya akansa shine tsanar su ga Amreesh Amma wannan ba su kaɗai ba kusan kowa agidan hakane banda granpa da papa, duk dashi papa duk sanda Amreesh yake nesa dashi zai ji yana matuƙar kewa da begen dan nasa amma daga sun zo face to face sai yaji kuma babu wanda yaƙi jinin haɗuwa dashi sama da Amreesh. Sai kuma yan matan gidan dake mutuwar son Amreesh da ko kallo basu ishe sa ba.
Tun tuni suka ƙagu da ya zo su ganshi ko zuciyoyin su zasu samu Salamah duk da wasu daga cikin su, Dr Ahmad shine Abin harin su. Sun kuma san gidan kowane daga cikin su amma they don't dare to go.

Ga baki É—aya palorn yayi shiru kowa ta ciki na ciki, granpa da kanshi yaga nawar su Amreesh su zo yayi kewar su musamman Amreesh

Turo ƙofar dr Ahmad yayi bakin sa ɗauke da sallama Amreesh biye dashi a baya duka aka yo masu chaa da ido.
Har suka samu wuri suka zauna Ahmad ya gaida uncles ɗin nasa duk da ba wani amsawar kirki suka yi ba. Shi ko Amreesh tunda ya zauna ya maida idanun sa ya lumshe yayi shiru kamar babu sa a wurin da ido suka bishi wani abu na tokare masu maƙoshi amma babu wanda yayi magana.... after a while granpa ya fara magana '' Muhammad mai zakace game da abinda ke ta yawo a kafafen sada zumunta?" Kafin Amreesh ya bada amsa Uncle T a fusace yace '' Yanzu Alhaji duk bayan abubuwan da ka gani you're still asking the ɗan iska? Tunda ya zo nan ya zauna tsabar iskancin da taɓarɓarewa waya gaida?"
Uncle Naseer ya karɓe da faɗin '' bar fitsararren ɗan iska bamu zai nuna ma ya girma ba? Da har zai zo ya zauna inda muke bai iya gaida mu ba! Ya je yana lalata yaran mutane ai dole idanun sa su buɗe'' Uncle Ismael dai bai ce komai ba haka ma old man Zakee duk da kalaman da suke faɗa akan Amreesh na sukar ranshi papa kuma ya yi ƙasa da kanshi, yana mai jin baƙin cikin abinda yan uwan nasa ke faɗa akan ɗan shi,he so badly wants to defend Amreesh yana so ya faɗa musu cewa ɗanshi bazai taɓa aikata abu makamancin haka ba amma ina! Words failed him. Yan matan kuma kowa ce sai cika suke suna batsewa suma basu jin daɗin yanda ake magana akan Amreesh infact they don't blame him sai ma yarinyar da aka kama su tare, a cewar su,she must have seduced him.
Yan samarin ma kowa ya cika da haushin Amreesh for the fact that saboda wannan scandal É—in, masu hannun jari a Zakee and sons company da yawa sun cire hannun jarin su aside from that dama sun tsane sa.

Hajiya zakiyya tace '' dama Ni nasan tunda aka ce yana da wannan cutar ƙaryan nasan ba gaskiya bane, ji dai yanzu it has been confirmed bin mata yake awaje '' Hajiya Turai tace '' dama pa? Abu jinin masu jajayen kunnuwa you can't expect any less '' Hajiya Saude ta taɓe baki tare da faɗin '' yanxu Ni ba wannan ba ma,baƙin painting daya shafa ma sauran yaran gida pa? Nan pa sai da aka tambaye sa idan aure yake so amma ya murje ido yace shi babu wacca zai aura acewarsa cutar bazata bari yayi mu'amala da wata ya mace ba amma ji yanzu?'' kowa sai tofa gubar bakin sa yake matan su da mazan su banda papa, uncle Ismael da old man Zakee da yayi shiru Yana kallon kowa, idan Ahmad yayi ƙoƙarin kare Amreesh su ƙundumo zagi su jefa masa shida Amreesh, accusing him if being an accomplices.
Duk maganganun da suke babu wacca tashi ga kunnen Amreesh,tuni ya ɗauki abinda zasu faɗa as back ground noise and unnecessary hakan yasa he blocked it, Babu amfani a wurin sa, aside from that lokaci ya basu idan har lokacin ya cika zai tashi yayi tafiyar sa ne,Dr Ahmad ya kalli Amreesh cike da tausaya wa da kuma ƙauna ga ɗan uwan nasa,and he was more determined to defend him
'' shegiyar yarinya itama da tarbiyya bata ishe ta ba,ko mai ya haÉ—a ta da wannan fitsararren? Oho!" Inji Uncle Naseer
" To waya sani ma ko yara nawa yayi hakan dasu? Yazo ya ɓata wa mutane suna,dama muna da maƙiya da abu kaɗan suke jira suyi ta ya maɗiɗi da mu yanzu kuma sun samu'' Uncle Ismael da yake shiru tuntuni ya faɗa cike da tsana ga Amreesh, su kuma sauran yan mazan sai Allah wadai suke da Amreesh basu da ikon magana tunda Manyan su na magana if not they had alot to say.

" Ni dai gaskiya na la'anci wannan yari...''

'' Uncle T'' Amreesh ya faÉ—a with a cold voice eyes expressionless yana kallon Uncle Taheer,duk wannan abin da suke faÉ—a bai yi niyyar tanka masu ba dama kuma suma hakan suka tsammata, Amma jin suna zagin matar sa yasa shi buÉ—e bakin sa, kowa dake wurin kallon Amreesh yake cike da mamaki banda Ahmad
'' be respectful when you talk about her '' yayi maganar idanun sa baƙi ƙirin, sai da gaban uncles ɗinsa ya buga basu kaɗai Bama,harda matan su that were making mouth
Uncle Ismael yace '' oh rashin kunya zaka mana akan wata banza karuwa Muhammad?'' kowa sai girgiza kai suke in disbelief.... Amreesh ya fara binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya tuni temperaturen wurin yayi dropping kowa ya fara zufa, duk da Amreesh nasu ne they Really are afraid of his ruthlessness ba yaran kaɗai ba harda iyayen su, zufa suka fara duk da sanyin Ac'n wurin. Tuni idanun Amreesh suka koma multicolored this Time around saboda emotions ɗinsa were in disarray bazaka taɓa sanin abinda ke yawo cikin sa ba.

Bayan yagama binsu da kallo with a dangerously calm voice yace '' dukan ku anan U have no rights to question what I do! I'm an adult not some teenager'' they were all stunned ga wani shegen kallo da yake binsu dashi, to them he looked nothing less than the devil suka cigaba da kallon sa cike da tsana

Uncle T yace '' ai maganar gaskiya akayi yarinyar karuwa ce ba komai ba does it hurt you?" Amreesh yace '' U don't disrespect her, she's my wife! Bakuma zan lamunci cin mutuncin matata ba daga koma wane ne'' yana gama faÉ—ar haka ya tashi ya fita.

Comment nd share pls


WAYE SHI?(Behind the mask) By Autumn 17
Chapter 30 · 0% Book details