Sashe 9
Tattalin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yaron. Aliyu ya rungumeshi a jikinsa yana maiyi masa addu'a da fatan Allah ya raya shi. Washe gari da safe ka sallamesu kasancewar mai jego kalau da ita da babyn. Gidan ya cika da 'yan barka 'yan uwan Aliyu dana mansura. [1:24PM, 04/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 1**14 GIDAN ya cika da 'yan barka 'yan uwan Aliyu da 'yan uwan mansura. Sadiya ta taho tinkis-tinkis dana ta tsohon cikin, ni'ima da zainab suka rungumota suna murnar ganinta. Dakin mai jego sai kamshi yake. Kowa yazo barka zainab ce zata karbeshi da farin cikinta, ta dakko masa jaririn. Ko yaushe yaro yana rungume ajikinta, kamar kada ta bawa kowa." ranar kwana hudu aka kawo kayan barka a katuwar akwati, kayan jariri ne tsala tsala masu kyau, da dan jeans da shet na yara, takalma, safofi, fidoji, saitin shawul da tawul, barguna masu laushi. Kaya ne masu kyau da tsari duk 'yan waje. Sai karamin akwati kayan mai jego ne, turmin super holllan biyu, leshi biyu, shadda galila mai tsadar guda daya, kowanne da mayafinsa, sai takalma da jaka kala bibbiyu. Ya bawa ni'ima da zainab da sadiya super holland biyu su uku, ya karawa zainab da galila anyi mata haddaden dinki aikin sama mai tsalelen kyau. Da mangariba Aliyu yana dakinsa, mansura ta shiga da jaririn, Aliyu ya karbeshi yana murmushi, sai shafashi yake yana murmushi. A zuciyarsa kuwa godiya yakewa ubangiji daya bashi kyautar da duk duniya babu wanda ya isa ya baka kyautar da sai Allah. Mansura tace Aliyu nazone akan maganan shirye-shiryen suna. Yace uhm! Me da me zaku yiyyi? "inaso da yamma ayi walima, da daddare mu fita fati a daula hotel, sai bokitai da manyan robobi da kalanda, du za'a rarraba a wajen. Yace za'ayi komai amma banda fati." ta wani harzuko, haba don Allah don Annabi, wallahi ka fiya yawa, ya zaka ce ba za'ayi fati ba, alhali ni inaso na burge saboda kawayena zamu kakko makadi don kawata fatin, kuma zaka kawo min matsala. Yace albarka nake nemarwa 'ya'yan, bana so su taso akan harkar shaidanci. Ta mike ta kama masifa, kai dai kawai kana so ka wulakantani a gaban kawaye na, haka wai haihuwar fari dan kwaya daya amma bazaka saki kudi ayi bushasha ba, don kasan bakai kasha wahalar haihuwan ba. Ya daga mata hannu yace, ya isheni haka fita ki bani waje." ta fito tana kunkuni tare da bakaken maganganu. Ya dafe kai don jin kansa yana sarawa, mansura zata haddasa masa ciwon kai, shi baya son hayaniya. Ta dawo daki tana kunkuni da fadar maganganunta. Saratu yayarta tace, meye kuma? Mansura tace kinji wai baza ayi fati da kida ba. Saratu tace, ai wannan wulakanci ne, ya mayar damu kananan mutane bayan ni har na buga kati na fara rabawa? Lawisa kawar mansura tace, kawai inba zai bari mu tafi ta nan ba, ba saiki ce masa zaki je kiyi sunan a can ba, inyaso da daddare muyi tafiyarmu fatin, ai mun riga munyi dai ai shikenan." saratu tace ita wallahi jeki ce masa zaki tafi gida zamuyi sunan acan. Mansura tace wallahi yace na fice na bashi waje, idan na koma nasan halin zuciyarsa, sai ya iya marina. Saratu tace tabdi ya mareki? Ai kuwa wallahi daya mari aurensa. Lawisa tace, tunda kuwa kika nuna kina jin tsoronsa kinsha wulakanci iri iri. Nan suka hadu sukaita aibata shi, suna fadar maganganu son ransu. Zainab kuwa ranta ya baci, kawai saita sa kuka. Saratu da lawisa suka hau yi mata masifa. Kinji yarinya da munafunci, dan uwanki yayi ba dai-dai ba zaki hanamu fadane munafuka? Kiyi kukan jini bana hawaye ba." zainab ta mike tayi dakinta tana kuka. Lawisa ta rike baki, tace ahaka kike zaune da wannan yarinya mai miskilancin tsiya, har wani kuka take don anfadi laifinsa. Mansura tace kuma wallahi baki ga yanda yake takura mata ba, ni har tausayi ma take ban, don inyana gari bata da sakewa" saratu tace "ai wani irin mutum ne, shiko fuska baya saki don kada akawo masa raini." ranar suna dole mansura ta hakura da maganar fati, akayi taron suna da yamma akayi walima ta burgewa da bajinta, mai jego sai shiga take tana fita tasa wannan ta cire tasa wancan ta cire. Yaro yaci suna Ahmad, sadiya da ni'ima da zainab, les din da Alh ya dinka musu suka saka, da yamma a wajen walima suka sa super ta wajen Aliyu. Can jimawa zainab ta canjo da shaddar da Aliyun ya dinka ma, sadiya tayi mata daurin gwagwaro akanta, tayi kyau, kamar ka saceta ka gudu. Sadiya da ni'ima sun cancanja shiga, suma dai shadda ce amma kalar ta kowa daban. Sadiya ta rinka raba kalanda mai hoton zainab tana dariya rungume da jariri, kaandar tayi kyau kowa ya karbi kalandar ya kalla saiya yaba da ita. Haka su saratu da lawisa su kaita raba robobi da 'yan kananan bokitai. Da haka taro ya tashi lfy, kowa yana san barka. Kayan barka da atamfofi data samu, da rigunan jarirai kamar wadda zata bude shago. Ba ruwanta kibarta kawai take yi, taci mai kyau tasha mai kyau, ta hau gado ta mimmike ba ruwanta da harkar Ahmed, yana wajen masu rainonshi su zasu hada masa madara su bashi yasha, su bashi ruwa, idan ya koshi su goya shi. Shan nononsa sai lokaci lokaci, saidai idan ta jiyo kukansa ta kirawo 'yan aikin nata ta balbalesu da masifa, mai suke yi masa yake kuka? Suyi ta faman rantse rantse cewar, wallahi basu yi masa komaiba, sannan zata karbeshi ta bashi nono, tasa su goya shi suyi ta faman jijjiga har sai yayi barci. [1:25PM, 04/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 1**15 TASA su goya shi suyi ta faman jijjiga shi har sai yayi barci. Sai dai fa du sanda zainab ta dawo daga makaranta, tana yin sallah zata karbo ahmad daga wajen masu rainonsa, taita yi masa wasa tana tarairayarsa, tai tayiwa mansura naci da magiya dole saita karbe shi ta bashi nono ya sha ya koshi. Ahmad yayi wayo sosai, yayi mugun sabo da zainab, don har yafi ganeta akan mamanshi don zainab har ta iya yi masa wanka, ta shirya shi cikin kaya masu kyau, tasa mishi turare yaita kamshi. Har mansura taita sha'awarshi, abinda ita lalacinta da son jikinta bazai barta ta iya ba. Du da zainab din ba wani lokacine da ita ba, inta fita tun takwas na safe sai shidda na yamma take dawowa, idan sun taso data dawo gida inta ci abinci tayi sallah, tayi wanka tasa kayanta, saita dakko yaronta ahmad taita yi masa wasa tana lallabashi, har lokacin bacci ta kaiwa mansura shi ta bashi nono yasha ya koshi ta taho dashi dakinta ta kwantar dashi a gado, ta canja kayan barci tayi musu addu'a taja bargo ta rufe su, ta rungume ahmad a jikinta suyi barcinsu. Talatuwa data ke tayaa kwana idan ya farka cikin dare, ita zata dakko shi ta bashi madara da ruwa, tasa shi shi akafada ta jijjiga shi yayi gyatsa ya koma baccin shi, saita shimfida shi a gaban zainab ta rufe su. Itama ta koma baccinta du sanda Aliyu yazo weekend, yana kula da abinda yake faruwa da yaronshi da yake kokarin zama marayan karfi da yaji. Sun sha fada da mansura akan sakarwa masu aikin dansa data keyi. Yasha korota intaje kwana dakinshi, yace saita dakko mishi dansa. Saita rabu dashi ta tafi dakinta tayi kwanciyarta. A hankali ya fuskanci tsananin son da zainab take yiwa ahmad, ya gano zainab ce take kwana da ahmad ba yan aiki ba, sai ya samu nutsuwa a ransa, yayi wa Allah godiya, don yasan zainab tafi mansura tarbiya da sanin ya kamata, yasan danshi zai taso da tarbiya matukar yana tare da zeey autarsu. Yau asabar, Aliyu yana gida, zainab babu makarantar boko, wajen tara na safe tayi wa ahmad wanka a bahon shi, Aliyu yana kallonta yana yaba baiwar da Allah yayi wa yarinyar, 'yar da har yanzu bata cika shekara goma sha uku ba, amma tana da nisan hankali da tunani wanda 'yar shekara ashirin da biyar bata dashi, wato mansura. Ta gama yi masa wanka, ta nade shi a tawul tana yimi shi wakar data ke yi masa inyana rigima. Wayar falonce tayi kara, zainab ta daga tace "hello yaya ni'ima." daga can ni'ima tace yau ne fa yinin kawata murja sule, kizo da wuri muje." zainab tace don Allah yaya ni'ima kiyi hakuri, ba zan samu damar zuwaba." ni'iman tace saboda me? Zainab tace, yaya ni'ima wallahi ban tambayi yaya ba, kuma kinga yau nadan samu hutu ba boko, ina so na wuni da ahmadina, ba zan iya fita waje na barshi ba. Ni'ima tace kinfiya shirme zainab, ina uwarsa ko zaki zama mai rainonta ne? Ita ba unguwa take ficewa ta barshi ba, sai ke zaki zauna ki rinka yi mata wahala dashi? Tace "haba yaya ni'ima kada ki manta ahmad dana ne gudan jinina ne, don wallahi basu da maraba da abunda zan haifa, tunda dan yaya nane. Ina ruwana da halin uwarsa, tsarina daban nata daban. Kiyi hakuri wata rana na rakaki, kinji yaya ni'ima? Tace to shikenan auta, ba komai ki shafamin kan ahmad ki sumbace shi, kice masa inji momynshi." zainab tayi dariya tace, "to bar kiji ma nayi masa kafin ki kashe wayar." ta suabcin kumatun ahmad tace yarona momynka tace nayi maka, tana kuma gaisheka, inta dawo daga gidan biki zata zo ganinka." ta ajiye wayar tana dariya. Ta zauna ta gama gogewa Ahmad danshin jikinsa, ta shafa masa manshi, ta shafa mashi farar hoda, sannan ta daga wuyarsa da hammatarsa ta zazzaga masa, ta shafa masa kasan wuyansa da hammatarsa, tasa masa kwalli, tasa mai pampas, tasa masa farar ves, tasa masa safa da dan takalminsa, ta shafa masa turarensa. Shirin yaron yayi kyau, gashi yana ta kamshi. Ta dama mishi madararsa a fida daidai cikinsa, tasa masa abaki ya kama zuka, ya shanye tas, ta bashi dayan fidar mai ruwa a ciki ya sha, ta dora shi a kafadarta tana shafa bayanshi, yaron har yayi gaytsa. Ta dago shi tana yi masa wasa yana dariya, daga bayanta taji ance " bani yaron naki na taya ki raino." ta juyo da sauri tace "lah! Yaya yanzu ka shigo? Don ita