Sashe 6
Tattalin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Surayya abubakar
[1:19PM, 04/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 1**8
YA FITO daga dakinshi, yayi gyaran
murya, ya ciro dubu biyar a Aljihunsa ya
mikawa zainab, yace "zeey auta ga kudin
ice-cream." ta rissana ta karba tana
godiya. Yaya Aliyu ya wuce ya sake fita. Zainab tace yaya ni'ima kinga abunda
nake fadamiki ba, inka bayar da kadan
sai Allah ya baka mai yawa." ni'ima tace
nagani, amma bani su nan kada ki sake
bayar mana." ita kuwa mansura a
zuciyarta cewa takeyi, "wannan yarinyar da shegen iyayi take. Wajen mangariba
suka isa gida. Bangaren hajiya suka nufa
sukayi sallar mangariba, zainab ta mike
tayi bangarensu, saita tarar da mamanta
kwance tana juyi. Ta tafi da sauri ta
rikota, tana cewa menene mamana, meya sameki? Maman tace banida lafiya
zaina, marata da bayana ciwo suke yi.
Nan da nan sai zainab tasa kuka tana
cewa, "mama tashi muje asibiti kinji?
Mama don Allah tashi mu tafi asibiti ko
kya samu lafiya. Maman tace da kyar, saboda ta fara
galabaita "zainab asibiti babu abunda
zasu iya yi min, Allah ne kadai zai bani
lafiya. Ki kirawomin hajiya da umma da
ummi, tayi cikin gida da sauri, du ta gaya
musu gaba daya suka taho, a lokacin Aliyu yana gidan. Maman ta galabaita
sosai, ko hannunta bata dagawa.
Umma tana ta hado kayan haihuwar a
dakin. Umma tana rike da maman, hajiya
tana mata tofi a ruwa a kofi, zainab din
taje ta rike maman tana jijjigata tana kuka, tana cewa mama! Mama!! Ki bude
idonki kiga hajiyan fa na kirawo miki ita.
Ki bude idonki kifa tofi take miki, don
Allah mama ki bude idonki kiga umma da
ummi., kefa kika ce nakira miki su, don
Allah ki tashi." ta kama jijjigata tana gwale mata ido, tana cewa mama!
Mama!!. Aliyu yace "umma ku kamata mu
tafi asibiti."
a lokacin Aliyu yaiwa abba da daddy
waya, suka ce to suma sun wuce
asibitin." a can suka tarar dasu Abban har sun riga zuwa, aka shigar da mama dakin
haihuwa, zainab sai kuka take yi, ta tafi
ta rungume daddynta tana kuka tana
cewa daddy kana ganin mama bata da
lafiya sun shigar da ita can, daddy kazo
mu bita. Ya rungumota yana rarrashinta, "kiyi
hakuri zainab, ki kwantar da hankalinki,
mamanki haihuwa zatayi. Ko bakya so
tasamar miki kanwa? Tace ina somana
daddy." to kiy shiru ki daina kuka,
mamanki haihuwa zatayi kinji ko? Kita yi mata addu'a kinji? Tace "to daddy
zanyi mata. Abba yace, hajiya su koma
da zainab gida a ar umma da ummi a
gurinta.
Abba ya taho da hajiya da zainab gida,
zainab sai kuka take yi, suna zuwa gida suna ni'ima da sadik su ni'ima suka tare
su da cewa ta haihu? Hajiya tace musu
a'a ta dai kusa. Du rarrashin da hajiya
take yiwa zainab ta kasa yin shiru, sai
kuka take yi.
Su kuwa can asibiti sun kasa samun nutsuwa, saboda jikin mama da yayi
tsanani. Wajen karfe uku na dare ta haifi
'yarta mace, su umma da ummi suka ta
hamdala suna yiwa Allah godiya.
Karfe bakwai na safe gaba daya 'yan
gidan sun hallara, ganin yanda jini ya tsinkewa mama, hankalin kowa ya tashi.
Daddy mijinta yana rike da ita yana
salati, yayinda likitoci suketa iya bakin
kokarinsu. Sunyi mata allura jinin ya
tsaya, du 'yan uwa sun zagaye ta, harda
sadiya amarya da mansura, su sadik da ni'ima du suna wajen. Zainab kuwa
hajiya ta janye ta suna falon dakin da
aka kwantar da maman nata. Saboda
kuka da zainab din take yi.
Ita kuma mama jikin nata yayi tsanani,
sai wasiya take bayarwa, sai cewa take cikin dakushashshiyar murya, "ina zainab
autata, ki kirawo min zainab dina.
Sadik ya fita da gudu yana kuka ya kira
zainab, ta taho da gudu ta rike hannun
maman nata ta jijjigawa, tana cewa "gani
mama, tashi gaya min abunda zaki gaya min, kinji mamana?
Ta kwantar da kanta akan ruwan cikin
maman nata tana kuka, maman data ke
fitar da nishi da kyar ta dora hannunta
kan zainab din tana shafawa, a hankali ta
rinka motsa bakinta tana karanto kalmar shahada 'yan uwa sunata amsa mata,
tana ta shakewa. Su sadiya da ni'ima
kuwa gaba daya sun rikice da kuka.
Can mama tayi shiru, hamza cikin firgita
yace, "ta mutu! Iyayen suka dauki salati
ga daya da hawaye, yayinda yaran suka cika daki gaba daya da kururuwar kuka.
Zainab kuwa tana yin baya ba'a ankara
ba ta sulale ta fadi kasa ba numfashi.
Aliyu ya sunkuce ta aguje ya shiga office
din likitan da ita. Likitan ya karbe ta da
sauri ya dorata kan gado yana kokarin ceto rayuwrta. Aka tafi da mama gida
akayi mata sutura aka binneta, kowa yaji
ciwon mutuwar mama. Mama mutuniyar
kirki me kawaici da hakuri, daddyn zainab
karfin hali kawai yake yi, domin yasan
yayi rashin da da wuya ya mayar da'ita. Don rashin hajiya saude ba karamin gibi
rayuwarsa tayi ba.
Anata amsar gaisuwa shikuwa sai yayi
jigudin yana tunani, ga 'ya'yanshi 'yan
mazan faruk da sadik suna manne da
jikinsa, yaran sun kasa manta mutuwar, sai dai kawai kada suna sharar hawaye.
Faruk shine sa'a ni'ima mai shekara goma
sha hudu, sadik kuma shekararsa sha
daya. Kwana daya da rasuwar mama aka
sallamo zainab suka taho, da yake ummi
ce a wajenta. Yarinyar tayi wata irin rama sai kace wacce ta dade da ciwo.
[1:22PM, 04/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 1**10
ABBAN yace "toh shikenan Aliyu, Allah ya tayaka riko." Aliyu yace amin Abba, nagode, Abban yace to ka gayawa daddyn naku? Yace "eh, saida na fara zuwa nayi shawara dashi tukunna."
yace, "to ai shikenan komai yayi dai-dai, Allah ya tayaka riko." ya amsa da Amin. Ya yiwa mahaifinsa godiya ya tashi ya nufi gidansu, ya gayawa kakarsu.
Hajiya murna tayi takara karfafa masa gwiwa daya rike 'yar uwarsa dakyau, ta hakane zumunci zai kara karfi a tsakaninsu."
don ita hajiya mace ce mai zumunci, tana so taga kan zuri'ar ta a hade, yayiwa hajiyar alheri, hajiya tanata godiya dasa masa albarka, ya fice ya nufi bangarensu. Ya tarar da umma da ummi a babban falo suna hira.
Yace musu, "ku hadamin kayan zainab da daddare zan zo na tafi da ita." gaba daya suka hada baki cikin razana suka ce, "zaka tafi da ita ina?
Gidana zata koma zan cigaba da rikonta.
Umma ta mike ta kama yi masa fada, " wato mu ka raina irin rikon da muke yi mata, shine zaka ce zaka dauketa saboda kafi mu sanin darajarta, ko iko zaka nuna mana akanta?
Yayi murmushi yace "kuyi hakuri, umma ba haka bane." iyakacin maganar kenan yayi musu shiru. Sun riga sun san bai fiya yawan magana ba, sai dai yayi atakaice. Inkin ji shi yana hira mai tsawo, to da iyayensa ne maza.
Ya mike yana ce musu, "umma bari na karasa gida." umma tace "saboda maganar tamu bata da amsa ko? Yayi murmushi ya dire musu kudi a gabansu, yace ummi kwasai goro." tace "to, mungode, Allah yayi albarka."
yana fita umma ta kama baki, tace, "ki gane min yaro, wai shi babba har ya fimu sanin abunda ya dace. Ummi tayi dariya tace "Aliyu kenan gadanga kusan yaki. Shifa zuwan da yayi yaga dazu bata je makaranta ba, gani yake kamar zamu kara sangartar da ita mu rika biyewa shagwabarta."
Aliyu yana isa gidansa yayi fakin ya shiga, a falo ya zauna yana karkade kafa. Mansura ta fito daga daki, tace "sannu da zuwa Aliyu, ga break dinka can, koda yake rana ma tayi kaine kayi fitar safe."
yace "nayi break a office din daddy bana tare da yunwa." yace kisa a share wancan dakin, zan dawo da zainab gidan nan zata zauna acikin dakin can.
Ta dafe kirji tace "haba Aliyu, ya zaka ce zaka dawo da zainab? Ai zaka takurawa rayuwarta. Don Allah ka kyaleta a gidanku, wannan shagwababiyar yarinyar in zamu iya da ita anan?
Ya doka mata harara yace ba shawararki nazo nema ba, idan zainab tazo kada ki barta ta zauna ki koreta."
tace, "haba Aliyu kai ka fiya zafin zuciya, daga 'yar wannan maganan saika hau tari, ba nufi na haka ba, ita da gidan wanta "ai ban isa na koreta ba." yamata shiru bai sake ce mata komai ba daman tasan ba zai sake magana ba, don ya fiya miskilanci, baya son yawan magana.