Sashe 25
Tattalin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da asuba yayi sallama da iyayensada iyalansa, jirginsu ya daga zuwabayelsa.Zainab suna tare da hajiya bata dawata matsala, hajita macece maibarkwanci da sanin ya kamata. Tai tanusar da ita yanda zata zauna damijinta, da yanda zata rinka yi masabiyayya.Ga 'yan gidansu su sadik, faruk, dahamza, sun riga sun saba hirarsu awajen hajiya, to dole wajen hajiyansuke tahowa nan gidan zainab dindon haka zainab take cikin nishadi,kullum tana ganin kamar a gidatake.Aunty sadiya ta sai musu littafankaratu, tunda ta karanta matar so,saita ji lallai itama tana so tayi huldada aunty hadizan nan, ko don tabata shawara ma kan nata auren,gaskiya zata nemeta dan ta samushawar wari da zasu tallafa mata garayuwar auren su.Ta jawo wayarta ta buga mata,ringin daya biyu ana uku ta dauka,"hello wake magana?Aunty hadiza bakuwace ina wuni?Lafiya lau."ya gida ya harkoki?Alhamdulillah.Aunty ina karanta wani littafi matarso, sai naji matsalar khadija, wallahinima ina cikin matsala.Matsala kamar ya ya? Mijin ne bayasonki? A'a yana sona, auren namu nenake ganin kamar na cin amana.Daga nan ta bata labarin komai dayanda akayi auren.Aunty hadiza tayi dariya tace, zainabkika ce sunanki ko?Tace, eh.Aunty hadiza tace Allah sarki gaki dasunan 'yata zeey auta, haba zainabkada ki bada mata mana akan watasaiki ki farantawa mijinki alhali bawaje daya kuke da ita ba.To ki saki jikinki ki farantawamijinki rai, du abunda kika san zaisashi farin ciki kiyi masa, ki kyautatamasa, abokiyar zamanki ki riketa dadaraja da mutunci, kada ki bari wataharkar raini ta shiga tsakaninku.Kada ki sake kiyi mata rashin kunyako ki wulakantata, yanda kike ganinmutuncinta da darajar a da, to kikara ninkawa akan na da din.Amma zainab na fuskanci ke yarinyace baki san komai ba, don haka zangyaraki, zan koya miki yanda akegyara jiki, na koya miki yanda akehada turare na ruwa dana wuta, fararhumra da baka da kulacca, hadinman gashi da zaiyi tsantsi da tsawo,ya rinka sheki da yana daukan ido.Sannan na koya miki yanda akehadin lallen kunshi wanda aketurarawa jiki yana kamshi, sai yayiwata biyu a kafarki bai fita ba.Tayi caraf tace, don Allah auntyyaushe zaki koya min? Wallahi inason kunshi da gyaran jiki, kumawallahi inason turarunkan nan masukama jiki da kama daki.To shikenan zainab, zan rubuto mikisu na turo miki.Yauwa aunty nagode, Allah ya sakada alkhairi. Don Allah aunty sainajiki.Uhm! Karki damu."to aunty, ki huta lafiya.To nagode.*** *** *******lawisa bayan kwana uku tazo,mansura ta tareta da murna, ya akayimutuniyar, kinje?Ai naje, ga abubuwa ya bayar ta fitoda kulle- kullentq,wannan gashi aruwan wanka zaki zuba masa,wannan ki barbada a shimfidar dazai kwanta, wannan kuma kiyi kokarikisa musu acikin abunda zasu ci.Gaba dayansu ita dashi zasu tsanijunansu, baza taba jituwa ba har saian raba auren."yauwa aminiyata nagode, gaskiyikinyi min kokari, amma kuma wanihanzari ba gudu ba kinsan Aliyubaya gari kuwa? Ta dafe kirji, ina yatafi?Yau kwanansa biyu da tafiyakaduna, jiya kuma sun tafi bayelsa,zasu yi sati hudu.Lawisa tace ba yanzu maganin zaifara aiki bama kenan, to da ita yatafi?Mansura tace, haba ina zashi da ita,tana can inda ya ajiyeta.To mu shirya muje gidan muci matamutunci, mu tsorata ta mu fakiidonta mu zuba mata maganin aabincinta ta tsane shi kafin ya dawo.Daya dawo ta burkice ta zuba masarashin mutunci, ke kuma saikiyi masaamfani dana wajenki, shima yatsaneta ya burkice ya saketa, kingashikenan mun samu aiki a saukake.Mansura tace, ai dole sai dai mu barisai ya dawo, don bata yanda zanyinaje gidanta.Saboda me? Lawisa ta tarinumfashinta.Ai hajiya kakarsu tana gidan.Lawisa tace ai kaji, munafukai kawai,wato har gadinta akeyi, ki nemi wajeki boye, kawai idan ya dawo din saiayi amfani dashi.To shikenan lawisa nagode**** *** ******da safe suna yin break sadik ya shigoda sallama, ya gaida hajiya sannanzainab ta gaisheshi, sadik yace hajiyakin gama mutafi? Don nayiwa likitawaya yana asibitin."hajiya tace, nagama mana, nida nakeshiri tun asuba. Zainab tace, donAllah hajiya zan biku asibitin, hajiyatace, waya gaya miki mace tana fitaba tare da iznin mijinta ba? To donAllah hajiya na buga masa wayar kigaya masa?Sadik yace a'a wallahi bazata gayamasa ba, ba mijinki bane ki gayamasa da kanki mana.Zainab tace, kai don Allah, yayasadik wai ina ruwanka ne? Don Allahhajiya kinji, kinga ni kadai zaku baria gidan shiru bazan ji dadi ba.Hajiya tace saika ce wanda zamushekara a can, naga dana gamaganin likitan nan zan taho ba indazan biya.Ta zumbura baki cikin shagwaba,nidai hajiya bazaki tafi ki barni nikadai ba, inma bazaku je asibitindani ba, to ku ajiyeni gidan yayani'ima, inku dawo saiku biyo ni mutafi.Hajiya tace banki taki ba amma farabugawa mijinki waya, abunda yaceshikenan.Sadik yace hajiya kema kin wanidaka ta tata, sai wani lallabata kikeyi, ki kyaleta ki taho mu tafi, hajiyatace ai dole.... [9:22AM, 05/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 2**18 Hajiya tace, ai dole na lallabata, mijinta amana fa ya barmin ita. Sadik haushi ya cika shi, don shi yana da wajen zuwa su kuma gashi suna bata masa lokaci. Sadik ya fito da wayarsa ya buga, can Aliyu ya dauka, hello sadik kun isa asibitin ne? Yace, wallahi zainab tana ta bata mana lokaci. Yaya Aliyu yace bani zainab din. Ya mika mata wayar. Tace hello, yaya, yace zeeyta ya akayi su hajiya basu tafi bane? Tace, don Allah don Annabi, yaya mu tafi tare na rakasu, tsoro nakeji ni kadai a gidan." haba zeeyta, ko zaki fita ai saina dawo mu fita tare, yaushe zan bari ki fita ni ina nan wani gaular ya kallar min ke. Yanzu ma munyi yanda zamu bullowa mutanen, damun gama zanyo miki waya muyi hirar mu har su dawo, yanzu ki bawa sadik wayarsa, kiyi wa hajiya bye-bye kice sai sun dawo, Allah ya kiyaye hanya, kinji zeeyta? Amma fa kada ki damu, kiyi hakuri kinji? Tace, to yaya na hakura. Yauwa zeeyta Allah yayi miki Albarka. Amin yaya." ta mikawa sadik wayar ya kashe yasa a aljihu yace hajiya mu tafi. Zainab ta rakosu har kofar falo da dariyarta, tana musu Allah kiyaye hanya. Hajiya taji dadi a ranta ta yaba hakurin zainab da biyayyarta. Suna fita tasa mukulli a kofar falon ta rufe, ta shige daki ta fada gadonta, ta jawo wayarta ta buga. Ringin biyu aka dauka, hello, aunty hadiza kiyi hakuri kada kiga na dameki. Lah haba bakomai wallahi, ai irinku muke so masu son gyara aurensu. To aunty dan Allah ki fara gaya min sirrikan turarukan. Kin shirya na fara gaya miki. Eh na shirya aunty (so wajen yanda ake hada turarukan na tsallake bt inkuna son yanda akeyi zan rubuta muku bayan mun gama). Zainab ta shiga tunanin irin nasihar da malamansu suke yi musu game da zaman rayuwar aure, ta tuna irin burin da suka rinka ci na yanda zasu kyautatawa mazajensu, to ita gashi yanda nata auren ya kasance mata, dole ta share komai ta rufe idonta ta nunawa mijinta kulawa ta musamman. Tun daga lokacin ta kasance bata bacci da dare, ta kara kusanta kanta ga ubangiji tana yawan yin nafilfili, tai ta kirari ga ubangiji tana rokonshi daya bata ikon yin biyayya ga mijinta, Allah ya tsaresu ya kuma karesu dukkan wani sharri da bala'i da zai tunkaresu. Allah ya hade kansu da abokiyar zamanta. Mijinta kuma, Allah ya karesu, aikin da suke yi Allah ya basu nasara, ya kuma dawo dasu lafiya. Kullum saita yi tashin dare tayi nafila da wa'yanan addu'o'in, hajiya ta rinka jin dadi tana kara karfafa mata gwiwa data ci gaba dayin hakan, hanya ce ta tsira, alamomi ne kuma daga mace tagari. Ta sake bugawa auntynta waya cewar, don Allah duk turaruka data lissafa ta hado mata, harda man gashi da turaren tsuguno na jiki dana dakuna. Aunty tace kada ki damu zan kawo miki harda hadin kayan itatuwa da zakiyi amfani dashi na karin ni'ima. Tayi 'yar dariya, tace kai aunty har kin bani kunya." kwana hudu a tsakani auntynta ta hado komai ta kawo mata. Cikin lokaci kankani zainab ta canja tayi wani irin kyau, fatarta ta goge sosai saboda turaren jiki data keyi, kamshi ya kama jikinta ko yaushe tana cikin kamshi mai dadi. Dakunanta kuwa duk wanda ya shiga baya so ya fito saboda fitinan kamshi da mutum yake shaka, gaba daya gidan nata kamshi yake mai dadin shaka, du saida ta dibarwa 'yan uwanta aunty sadiya da yaya ni'ima. Kwanci tashi ba wuya a wajen Allah, yau Aliyu satinsu biyar kenan a bayelsa, sunyi kokari su dawo a sati biyu da suka ce zasuyi to abun ya ci tura, gashi har sunyi sati biyar, yau da mangariba hajiya tana daki tana lazimi, don intayi sallar magariba bata tashi daga wurin sai tayi sallar isha. Zainab tana falo tana shan romon kaza da aka dafa mata da magangunan karin ni'ima, irin cikin kayan da auntyn nata ta hada mata. Wayarta tayi kara ta dauka, tace hello, yayana, kaki ka dawo yaya sai yaushene? Yace, au zeeyta kina so na dawo ne? Ina so mana, yaya nafi so ka dawo gida." to gaya min me kika tanadar min? Me zaki bani? Zaki shayar dani madarar soyayya? Kai dan Allah yaya ni bana son irin wannan maganar. To gaya min wani iri kike so? Tace nidai kawai so nake ka dawo to kin yarda in na dawo zamu rinka kwana gado daya tare na jiki manne a jikina, ina ririta ki inayi miki lallamin kauna? Tace don Allah yaya kabari. To shikenan tunda bakya so na dawo. Yaya inaso mana, yaushe zaka dawo? Yace insha Allahu yau saura kwana shidda na dawo, amma ki sani dana dawo zan yaye miki wannan hijabin kunyar, don ni take cuta." tace, yaya nidai don Allah saida safe." yace, au abin ma hakane, shikenan mu kwana lafiya. Da safe zainab take gayawa hajiya maganar dawowar yaya Aliyu saura kwana biyar, hajiya ta rangada guda tace, ina baiwar Allah nan data miki turarrukan nan tazo ta gyara minke, bani lambar wayarta na kirawota da kaina. Washe gari auntyn suka zo da aka fara gyaran amarya zainab, kwana uku ana gyaran jikin zainab, ranar kwana na hudu akazo akayi mata kunshi, akayi mata sarkar kafa data hannu. Ana gamawa aka wuce da ita salon, aka gyara mata gashi suka dawo gida, zanso kuga yanda wannan tauraruwar mata take. Saimun hadu a littafi na uku Sai night kuma😜😜😜 [9:16PM, 05/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 3**1 To yanzu mai kika shirya na tarar angon naki? Cikin jin kunya tace "aunty me kike ganin za ayi masa? Ina ganin