Sashe 1
Tattalin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
[8:06AM, 04/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO-1 PG-1 Kanal Aliyu Gwarzon jarumin soja kenan, Alhaji Yahuza shi ne mahaifinsa, matansa biyu da 'ya'ya biya. Hajiya Habiba ita ce uwargida, da 'ya'yanta uku. Aliyu shi ne babba, sai Sani da Sa'adiya. Sai Hajiya Talatu me 'ya'ya biyu, Ni'ima da Hamza. Dukkaninsu kansu a hade ya ke, da ya ke sun sami tarbiya sam babu yan ubancin nan bare nuna banbanci a junansu. Alhaji Safiyanu kanin Alhaji Yahuza ne, uwarsu daya ubansu daya, matarsa daya Hajiya Saude, da 'ya'yansu uku, maza biyu Faruq da Sadiq, sai karamar su mace mai suna zainab. Babban gida ne kowanne da bangarensa, gaba dayansu akwai kyakkyawar dangantaka da son juna a tsakaninsu. Mahaifiyarsu Hajiya Babba, ita ma a gidan ta ke bangarenta daban. Dattijuwar arziki ce me addini da ibada, ga ta da kokarin zumanci, du inda ta ji dan'uwanta wanda ko kaka dangantaka ta hada su, sai ta jawo shi jikinta ya ci arzikinta da na 'ya'yanta. Hajiya kyaftin kenan dattijuwar arziki, ko yaushe jikokinta suna tare da ita tana hada kawunansu, tana yi musu nasihohi da tattausar murya, ta rinka yi musu tarihin Annabawa da abubuwan da ta san za su karu dasu, su kara samun fahimta ko da a makaranta ne.
[1:15PM, 04/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 1**2
Yace, kai hajiya, kin matsanta min da maganan auren nan, wai ke bakya kishina ne?
Tace ni ai indai akan wannan ne banayi, ka samo min abokiyar zama, idan kuma kai bazaka iya ba ni na samo maka."
hajjaju kenan, za'a nemo in Allah ya yarda. Tace dakai wani ne saika samo a hadaka da 'yar uwarka sadiya, tunda kaga ansa rana data yi candy za'ayi aure insha Allahu."
yace kai hajiya, kedai kina son hada sabgata da yaran nan so kike su rainani ne?
Tace, "ai kaji sha'anin naka, sai son girma kamar gyambo, yo meyesa baka nemo tuni kayi ba? To bari kaji na fada maka, ko ka nemo yarinyar da kake so ayi auren kafin bikin sadiya, ko kuma ayi auren lokaci daya da sadiya."
ya mike yana dariya, "hajaju kenan, kin taba ji anyiwa namiji auren dole? Tace za a fara shi kuwa daga kanka."
hajiya dai da gaske take lamarinta, don ta matsu taga Aliyun yayi aure, tana so ya kara samun daraja da mutunci a gun iyayenshi, saboda Aliyu yaro ne nutsatse mai hankali da nutsuwa, yana da biyayya. Du abunda iyayensa suke so shi za yayi.
Du da karancin shekarunsa yanada halin ya kamata, shiyasa ya zama abokin shawarar iyayensa.
Karfe shidda na yamma direba ya kwaso 'yan makaranta tun safe. Da yake zainab a firamare take, karfe daya ake tashinsu, to saita shiga lesson na awa daya, karfe biyu take fitowa sannan antashi su sadiya da ni'ima da suke 'yan sakandare. To sai suyi sallah direba ya kawo musu abinci suci, sai kuma shiga islamiya data ke duk a cikin makarantar. Karfe hudu zasu fito sallar la'asar, suyi dan ciye-ciyensu su kuma komawa aji, sai karfe shidda za'a tashesu suyo gida.
Yau direba yana tsayawa zainab ta bude ta fito tayi bangarensu, kicin ta nufa don tasan mamanta tana kicin ita da 'yan aikinsu don gudanar da girkin dare.
Hajiya saude ta tari 'yarta da murna tana cewa, "sannu da zuwa auta." ta rungumeta suna dariya ta cika uwar tata ta nufi firiji tana cewa, wallahi mama yunwa nake ji." ta bude firij tace kai mama ina vanilla ice-cream dina?
Mama tace a'a zeey bana son rigima, ba tun jiya kika gama shanye naki ba?
Tace "to mama bana sa ragowar dayan a firij ba." tace to ai kuwa dashi sadik ya tafi makaranta da safe.
Zainab tanajin haka ta yarda jaka ta hau tsalle da ihu tana kuka, "wallahi saiya biyata ice-cream. Faruk da sadik suka shigo duk da goyon jakunan su, suma nasu direban ya dauko su, don makarantar matan daban ta mazan daban aka sakasau.
Tace "wai ice-cream dinta tasa a firij waye ya daukar mata a cikinku. Faruk yace "mama ai sadik ne ya tafi dashi makaranta."
sadik yace ai banaki bane ragowa ne na dauka da zaki kama yiwa mutane kuka."
tace "to bani nasa shi a firij ba kaje ka dauka min ba, wallahi sai biyani abuna." taci gaba da kukanta tana tsalle. Aliyu yana dakinsa ya ringa jiyo ihunta, ya shigo da sauri yana cewa lafiya?
Me akayi mata mama? Tace rigimar data saba ne kawai, ice-cream ne du sunsha roba dai-dai, ragowar daya ne wai ta dauka tasa a firij shikuma dan uwan dayan abokin yin nata ya dauke ya tafi makaranta dashi ya shanye, shiya kawo wannan rikici nata." ya daka mata tsawa, "tashi zaune." ta mike a razane tayi daki da gudu. Dai-dai lokacin ni'ima take shigowa take cewa "wallahi yaya ko abinci bata ci a makaranta ba sai youghot me sanyi ta rinka siya tana sha wuni guda, yaya sadiya tai ta mata fada ta kwace youghot din ta siyo mata meat pie da yambos, saida taga zata daketa sannan taci.
Aliyu yace a'a ba akai muku abinci bane?
Tace, "ankai mana mana, bata cin abinci sai kayan zaki dana sanyi take sha."
ya kwada mata kira da karfi, "zainab kina ina? Ta fito daga falon da sauri ta rabe a waje daya. Yace maza ni'ima shiga kicin ki zubo mata abinci ina zaune ta cinye shi.
Ni'ima ta zubo mata abinci ta dire a gabanta, Aliyu ya daka mata tsawa dauki ki cinyeshi. Taja filet din ta fara cin abincin, tsoronsa take ji sosai, don tasan baya wasa.
Yace ki cinye shi du idan kika rage ko kaka nida kene. Ya juya ya fita, ya sami direba a waje ya bashi dubu biyar, yace yaje bakori ya siyo masa ice-cream da youghot masu sanyi, da gashashiyar kaza guda biyu." ya wuce dakinsa. Zainab kuwa tana zaune tana kuka tana tura abincin, saida ta cinye tas sannan ta tashi tayi daki ta kuka, me aikinsu ta bita tana rarrashinta, ta hada ruwa a baho, ta cuda ta sannan ta kyaleata ta karasa wankan da kanta ta dauro alwalar sallar magariba, tana cikin shiryawa taji sallamar direba da yake kaisu makaranta. Mama ta amsa masa, ya shigo ya durkusa yace, "gashi mama inji yaya Aliyu, na zainab ne.
Maman ta karba tana budawa, tace "Aliyu kenan, ai shine ma ja gaban sangartar da zainab, don daman can shiya koya mata irin wannan cimar bata damu da abinci ba, gashi ta fara girma abu yana nema ya zame mata jiki.
ta kwala mata kira, ta fito da sauri tana cewa "mama me yayan ya kawomin. Ta tura ma kayan, gashinan 'yar lelen yaya. ta fito ta kama dubawa, robar yght guda shida, ice-cream guda shida, gasassun kaji guda biyu, ta dauki robar ice-cream da nono dai-dai ta saka a firij, tace wlh mama kada ki bari sukuma daukar min.
surayya
[1:16PM, 04/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 1**3