← Book details Tattalin So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 44

Sashe 4

Tattalin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

BA AYARDA mace ta dauki abincin mijinta tayi kyauta dashiba saidai in dafaffe ne in tayi, gudun kada ya lalace, to sai a sadaukar dan gudun kada ya zamo almubazaranci. Shima idan miji ya dawo saiki sanar masa, ko gidanku zaki aika da abinci saiki sanar masa, bare ki bawa wani can daban. Wannan yana cikin cin amanar miji.
Manya mutane suka rinka mikewa suna yiwa zainab kyautar kudi, saboda yanda yarinya karama ta burgesu, Abba da daddy sai washe baki suke yi don jin kokarin 'yar tasu da kwazonta.
Mamanta kuwa tayi hamdala acikin ranta, tana mai jin dadin baiwar da Allah yayi wa 'yarta tun tana karama, kowane tebir mutum hudu ne a zagaye dashi, akayi umurni da masu sabis su fara rabon abinci, shinkafa ce fara da taliya itama haka, sai soyayyun kaji da gasashen nama, sai mitfy, samosa, sopringros, haka kowa za a tsira katon filet a dire a gabansa, mata masu wa'azi sun zo, wajen yayi shiru an nutsu ana cin abinci, yayinda aketa kwararo wa'azi akan zaman aure ga ma'aurata.
Washe gari akayi yini, ranar litinin akayi fati, a ranar kuma aka kai amare dakunansu. Burin mansura ya cika, yau ta auri gwarzon namiji cikakke, wato Aliyu.
Tasan sarai Aliyu miskili ne bai fiya
wasa da dariya ba, shi hasalima magana wahala take masa yi masa, don inzaka daka ta tashi sai dai kuyi ta zaman kurame dashi.
Aliyu mutum ne mai tsafta, dan gayu ne mai son kamshi, baya damuwa du tsadan turare zai saya indai kamshin shi yana da dadi. Aliyu yana ji da kansa, akwai iya jan aji, yana da tsananin iyayi da gwalli kamar mace, ya fiya kasaita da son girma kamar wani basarake.
Washe gari ranar talata gajiyar biki bata bar ni'ima da zainab zuwa makaranta ba. Tun asuba da aka tashe su suka yi sallah, suka sake komawa gado suka nade cikin bargo suna bacci. Karfe bakwai masu aikinsu sukayi ta tashinsu don su shiry su tafi makaranta, amma du sunki tashi.
Dole sai rabuwa suka yi dasu.
Karfe goma dai-dai Aliyu ya shigo gidan don gaishe da iyayensa. A farfajiyar gidansu mai gadi da direbobi suna ta risinnawa suna gaisheshi. Aliyu ya cewa malam idi direba, "ina 'yan makaranta , i ce kodai basu makara bako?
Malam idi yace ai basu fito ba, yau ban kaisu makaranta ba." a zuciye Aliyu ya shiga gidan, kafa kawai yasa ya daki kofar ta bude garam.
Ni'ima da zainab suka tashi a firgice, suna mitsike ido. Suna dago kai suka ganshi. Kafarshi daya akan gadon, dayar tana kasa, fuskar nan tayi kirtif da ita kamar bai taba dariya ba.
Zumbur suka mike suka diro kasa daga gadon, suka durkusa can nesa dashi, suka kama cewa "yaya ina kwana? Bai amsa musu gaisuwar ba, sai tambaya daya jefo musu cewar "meya hanaku zuwa makaranta? Gaba daya jikinsu ya hau bari suna in'ina da kame-kame abunda zasu ce, ya daka musu tsawa "ku tashi ku saka uniform dinku, ina jiranku a falo." suka mike da sauri kowacce ta nufi kwaba. Shikuma yayo falonsu yana tsaye. Mintuna kadan suka fito sanye da kayan makaranta da jakunkunansu a rataye, ya sasu a gaba har farfajiyar gidansu, ya kwalawa malam idi direba kira, ya taho jikinsa na rawa. Yace "daga yau du ranar daka kara kin kaisu makaranta abakacin aikinka."
malam idi ya rikice jikinsa yana bari, yace "kayi hakuri yallabai, wallahi ba laifi na bane sune basu fito ba." yace "daga yau idan kaga basu fito ba kayi min waya kawai ka gaya min. Yace "to yallbai." suka shiga motar direban ya jasu. Shikuma Aliyu yayi cikin gida. Zainab tace, "inbanda abun yaya, daga yin aure saika fito da sassafe. "ni'ima tace, "ai gwandake bangarenku ma na 'yan firamare ne, ni 'yar sakandare nasan wallahi sai an dake ni, daya kyalemu gobe basa muzo ba."
gidan Aliyu yana nan daga bayan gidansu ba nisa. Amma tunda aka kai mansura basu je gidan ba, saboda basu da wani lokaci sai dare, sukuma ba fita suka yi da dare ba.
Yau alhamis ana tashi daga boko gida suka yo, dan ba islamiya. Ni'ima da zainab tuni sun gama shiri, anko sukayi na wani dandatsesen material baki, ni'ima tana rike da hannun zainab suka tafi.
Suna zuwa gidan suka shiga, 'yan aikin gidan sai sannu da zuwa suke yi musu. Suka karasa babban falo inda matar gidan take, sukayi sallama, saida akayi musu izni sannan suka shiga. Mansura ta taresu da murna, a'a sai yau zaku zo, nayi fushi." suka rike hannunta suna cewa, "tuba muke aunty, kinsan kullum da makaranta.
Tace, "to amma gaskiya yau anan zaku kwana." suka ce wai kwana aunty? Ai baza a barmu ba a gida." tace haba don Allah, ya ya zasu hanaku kwana a gidan babban yaya." yayinda take kwalawa mai aikinta kira talatuwa, "na'am ranki ya dade, ta amsa da saurinta, ta durkusa a gabanta, mansura tace "bakya ga munyi bai ne baki kawo musu komai ba, nifa bana son shashanci, kirinka kula da aikinki fa."
talatuwa tace kiyi hakuri aunty. Ta fita da sauri ta shiga kicin ta hado musu lemuka da snacks taje ta durkusa a gbansu ta ajiye. Zata mike zainab ta bude jakarta ta dauko dari biyar ta mika mata. Talatuwa tasa hannu biyu ta karba tana godiya. Inna laraba tashigo ta durkusa a gaban mansura tana tambayarta hajiya me za'a girka?

Surayya Abubakar
[1:19PM, 04/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 1**7
Chapter 4 · 0% Book details