Sashe 21
Tattalin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
YAu babu fada da hargagi irin na yaya, sai wani ji
yake da ita. Lallai namiji kenan.
Ta kifa kanta a jikin gadon saboda yanda taji
yana sara mata kamar zai rabe biyu, yace zeeyta
mene ne? Ya dagota yaji jikinta zafi zau, yace, ya
ilahi. Yanzu zeeyta bazaki daina sama kanki
damuwa akaina bako? Ta rinka lumshe idonta
yana kokarin rufewa, saboda azabar ciwon da
kanta yake yi, Aliyu hankalinshi ya tashi, ya
kwantar da ita ya mike ya shiga kicin ya debo
ruwa awata a silba, ya taho da hankicif.
Ya kwantar da ita a cinyarsa ya cire mata rigar,
sai farar shimi mai kyau a jikinta, ya rinka tsoma
hankicin a ruwa yana goga mata jikinta. Sannu a
hankalin zafin jikin nata ya fara raguwa, ya bata
magani tasha, ya barta daga ita sai bes da siket,
ya shimfideta a gado ya mike ya koma kicin don
ya mayar da kayayyakin ciki, ya jere ice-cream
din da youghot din a firij, ya shiga dakinsa ya
fada toilet yayi brush, ya saka kayan bacci ya
koma dakin bayan ya rufe ko ina, ya tofe ko ina
da addu'o'i ya hawo gadon. Tuni ta dade da fara
bacci, ya dagota ya dorata akan kirjinsa ya
rungumeta, a zuciyarsa ya ringa jin wata irin
nishadi, wai yau shine rungume da zainab dinshi,
ashe zaiga wannan rana? Ashe wannan lokaci
yana nan zuwa gareshi? Yaso suyi sallah raka'a
goma sha biyu don nuna godiyarsu ga Allah, to
matsalar rashin lafiyar zeey dinshi hankalinshi ba
akwance yake ba.
Zainab ta dan motsa, ya rinka jijjiga ta yana
lallabta kamar yarinyar goye, da yake zazzabi ya
sauka baccinta take yi sosai.
Sai wajen asuba ta farka, tana jinta rungume
ajikin yayanta Aliyu du kunya ta dame ta, tana
kokarin zame jikinta daka nasa sai ji tayi ya sake
kankameta, dole ta hakura amma du kunya ta
isheta, ta kasa wani kwakkwaran numfashi.
Saida akayi assalatu sannan ya shimfideta a
gadon, ya rada mata akunnanta, "ki tashi kiyi
sallah ni zan tafi masallaci.
Ita kunyarsa take ji sosai, bata iya amsa masa
ba, ya fita ya nufi dakinsa ya shiga toilet ya
daura alwala, ya fita masallaci.
Ta mike tana mamakin yaya Aliyu, daman haka
yake? Tayi alwala tayi raka'atul fijir, ta tashi tayi
sallar asuba, ta gama laziminta ta daga hannu
sama tana addu'a, Allah ya basu zaman lafiya,
Allah ya hada kanta da kishiyarta yaya Aliyu Allah
ya kara buda masa, Allah ya bashi ikon yin adalci
a tsakaninsu. Ita kuma Allah ya bata ikon yin
biyayya ga mijinta.
Tana cikin yin addu'a yaya Aliyu ya shigo, sai ya
huce dakinsa. Tayi sauri ta shafa addu'ar ta
koma dakinta saita rufe kure kofofi, don ita a
tunaninta da wani ido zata kalli yayanta.
Daya taba kofar tata yaji ta rufe, sai yayi
murmushi kawai ya koma dayan dakin ya kwanta,
sai sannan ya samu bacci mai karfi ya daukeshi.
Karfe takwas ta tashi ta shiga wanka, ta shirya
cikin riga da siket na shadda ruwan goro dinkin
stayil ne, anyi mishi hawa-hawa kamar asabari,
an zuba dutsuna aciki yana ta walwali. Farar
fatarta tayi das aciki, ta hade kananan kalabar
kanta tasa ribon ruwan goro ta daure, ta feshe
jikinta da turare tana ta zuba kamshi.
Ta rinka jin ana kwankwasa kofar falon, taje ta
bude. 'yan gidansu ne hamza da sadik suka kawo
musu abun karyawa. Ta basu hanya suka shige.
Hamza ya kama tsokanarta, "amarya kinsha
kamshi, don Allah du kukan da kika sha jiya harda
su zazzabi amma kalleki yanzu shar dake kinsha
kwalliya.
Yace kin hakura kenan? Tace "ban hakura ba,
yanzu zan biku mu tafi tunda ku kuka fara zuwa."
sadik yace kibi su wa?
Na biku mana." hamza yace rabu da ita fade
take, ina zata iya zuwa, data sha bulalan Yaya.
Sadik yayi dariya, yace irin wacce tasha data yi
zance ba. Gaba daya suka sa mata dariya.
Tace to ya isa, tunda kun kawo aiken da akayi
muku kuzo ku tafi. Sadik yace zamu tafi bamu
gaisa da yaya ba? Tace to bacci yakeyi.
To ki taso mana shi mana.
Ya zan taso shi yana bacci aiba haka akeyi ba.
Hamza yace, "wati har kin fara rowarsa ko? Tace,
"kai ka sani.
Suka fice suna mata dariya. Ta bude taga
shiryayyun break din da akayo musu ta girgiza
kai tasan iyayensu mata ne zasu yi ba
'yan aiki ba.
Ta shirya komai a tebir, tuni ta gyara falon tasa
turaren wuta mai dadin kamshi. Daga bayanta taji
motsi, tasan Aliyu ne, saita kasa juyawa, a haka
ta durkusa tace, yaya ina kwana?
Sai shima ya durkusa ya dora kansa a bayanta
yace, "haka akeyin gaisuwa a juyawa miji baya?
Yace "zeeyta ya jikin, meyasa kika rufe min kofa
da asuba?
Du ya saukar mata kasala ta kasa wani katabus,
wai shi yaya baisan kunyarsa take ba, meyasa
yake yi mata hakane? Ya kama shafa
wuyantayana cewa "zeeyta zazzabi ya sauka ko?
Ta rasa yanda zatayi, du ya kanainayeta,
kunyarsa da nauyinsa ya isheta, gashi ta gaji da
tsugunan.
Ta zame zata zauna ya tallafota jikinsa a hankali
yana shakar ni'imtaccen kamshin jikinta,
muryanta can kasa cikin marairaita tace "don
Allah yaya ka bari, kunyarka nake ji.
Cikin kunnanta ya rada mata, kidaina jin kunya ta
nifa mijinki ne, kin taba jin inda mata take jin
kunyar mijinta? Kefa malama ce kinsan hakkin
miji akanki, kada kunyata tasa ki sabi dokokin
ubangiji, ki saki ranki ki saki jikinki.
[9:16AM, 05/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 2**11, 2**12 & 2**13