Sashe 42
Tattalin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
mijinta kusa da ita. Ya kuma hade kansu da mijinta da kuma abokiyar zamanta, ya kuma kare su daga sharrin mahassada da makiya. Ihsan ta farka da kukanta tana kiran dadynta, bata ganshi yau ba ta taso ta kwanta abayan zainab tana kuka, tana cewa aunty mami ina Abba na, ki kaini wajen Abba kinji aunty mami. Zainab tana kan addu'a tana hawaye tana jin ihsan a kwance a bayanta tana kuka. Ya dade da shigowa yana tsaye yana kallonsu, tsananin tausayinsu ya gallabi zuciyarsa. A hankali yae ya durkusa a gaban ihsan ya shafa kanta, ta dago ta ganshi, ta fada jikinsa tana dariya Abba na ina ka tafi ka bani? Ya rungumeta sosai yarinya ta rinka ajiyar zuciya ya rinka shafa kanta. Tayi lamo a jikinsa har tayi bacci ya shimfideta ya dawo wajen zainab. Yace yanzu zainab haka zakiyi min kiki sakin ranki ku rinka shiga kunci keda ihsan. Keda zaki rarrasheta amma ke kina kuka ita tanayi, a haka kike so na tafi na barku, taya zuciyata zata samu nutsuwa, bayan nasan bakwa cikin kwanciyar hankali. Kayi hakuri yaya wlh ni ba haka bne, ni abunda ya daga min hankali naga har sha dayan dare baka dawo bane, yaya ba dole na damu ba? Yaya ina kaje ka kai sha daya baka dawo ba? Yayi murmushi yace ina zanje kuwa, ai kinsan bazan iya fita wani waje a wannan lokacin ba, ina falon saukar baki muna lissafi da su sadik yanzu nan suka tafi. Tayi murmushi ya kamo hannunta zo muje na kwanta kada na makara. Da safe ya fito falo shida zainab yana dauke da ihsan, sunci kwalliya kamar masu shirin zuwa fati, sunata murmushi da fara'a ke ba kyace da wani kunci a ransu ba mansura suka shigo falon ita da Ahmada sunci kwalliya tana taunar cingam, Ahmad yayo wajen zainab yana cewa aunty mami mu tafi gaba daya. Ta shafa kansa kada ka damu yarona idan mun gama shirinmu zamu biyoku, inkaje ka kula da karatunka, kaga za a canja maka makaranta saika kula sosai. Yace to aunty mami naji. Mansura ta kallesu ta tabe baki, takaicinsu da bakin cikinsu ya isheta, wato du yanda taso ta kuntatawa zainab donta ga bacin ranta, yarinyar taki nuna damuwarta. Har mota ta rakosu, Aliyu ya mikowa zainab ihsan ta karbeta, ya shiga motar suna daga musu hannu, direba ya fara jan motar tana tafiya, Ihsan ta kwala wata gigitaccen kuka tana zamewa daga jikin zainab. Motar tana kokarin fita daga get Aliyu yacewa direba ya tsaya, ya fito da sauri ya karbi ihsan ya rungumeta, ta rinka cewa Abba jani. Yaya to ku tafi da talatu, ta taho da ita. To shikenan turo talatun. So kuyi hkr wllh banda lpia ne [8:08AM, 07/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 4**12 To shikenn turo talatun. Ta shige gida da sauri talatu ta fito ta shige gaban mota kusa da direba, ihsan na kwance jikin babanta, yana lallashinta Ahmad yana tsunkuninta suna dariya. Mansura takaici ya cikata, wai me zainab take yiwa Aliyu ne da yake musu irin wannan kauna? Kafin su karasa airprt Ihsan har tayi bacci. Suna fitowa daga mota talatu ta karbeta, ta koma motar direba yasu suka tafi. Mansura kanta ya kwance da ganin gidansu na abuja, du da dai na kano da suke ciki yafi shi girma da kyau, amma tsarin wannan din ya burgeta sosai, kamar gidan turawa. Tuni Aliyu ya fice cikin sauri ya nufi ofis. Mansura da Ahmad sun zagaye ko ina, bangare daya ne a kulle, ta tabbatar wajen zainab ne, tunda bai bude musu ba. Sai dare Aliyu ya dawo abun haushi ga yunwa ga wahala, amma yana zuwa ya tarar da mansura da Ahmad du sunyi yaushi, wai yunwa suke ji basu ci komai ba. Ya hauta da fada dan me ga kayan abinci nan bata girka ba? Tace ai babu gas kuma ta masa waya taji ta a rufe. Yace baki bude jakunan da akwatina da muka zo dasu kin jere kayan ba? Tace ai bata yi komaiba, yayi tsaki matsalarki kenan har yau baki san yanda zaki kula dani ba. Ya tashi da kanshi ya bude kayan ya fito da soye-soyen da zeey ta musu, dambun nama, kec, meat fy, samosa, cin-cin da wainar shinkafa, da sinasir da fukasau da soyayyen miya. Kawai sai mansura tayi turus, lallai zainab tayi nisa wajen siye zuciyar Aliyu, ita yaushe tayi tunanin haka ma bare tayi, abu daya tasan tana da yaji. Aliyu yasa Ahmad ya shiga kicin ya dauko filet da cokala, ya bawa Ahmad shima ya diba. Yaja gefe ya fara ci, yace wa mansura ki debi abunda zaki iya ci, ki zuba ragowar a firij. Ki debo mana ruwa da lemu tunda komai sai ance kiyi. Ta zumbura baki, ta tashi tayi yanda yace, ta zuba nata abincin ta zauna tana ci. **** ***** **** zainab ta shiga damuwa sosai, na rashin tafiyarta, tana son zaman kano saboda iyayensu da 'yan uwansu. Amma gaskiya tafi son zaman abuja, saboda tafi kusa da mijinta, tasan halinshi tasan damuwarsa. Tasan yayanta mai son a kula dashine wajen cikinsa da biya masa bukatarsa to tasan auntynta tun tana ita kadai ta riga tayi sakaci da hakan. Ta kalli Ihsan data gama rigimar neman abbanta tayi bacci. Ta mike ta shiga toilet ta dauro alwala tazo ta kama nafila tana musu addu'ar neman zaman lafiya a tsakaninsu da cikawa da imani. Tana shafa taji nutsuwa ta saukar mata, taji zuciyarta wasai, babu kunci ko damuwa. Tahau gadonta ta kwanta, wayarta kamar jira take tahau burari, ta dauka da murmushinta, tace "hello gudan raina, ya kake? Ina auntyna da dana? Yayi wata irin sanyanyar ajiyar zuciya, yace rayuwata ina Ihsan dina tayi bacci kota nata rigimar nemana? Um-um ta hakura tayi bacci. To saka min naji munsharinta don na tabbatar da lafiyanta. Tasa a wayar a hancin Ihsan, yaji numfashinta yana sauka a hankalo, tasa a kunanta kaji ko? Um Alhdllh naji bebyna kalau take. To ya dan bebyna baya tare da matsala ko? Kinsan tunda nayo miki waya mun sauka, to tun daga lokacin ban samu kaina ba sai bay isha inata aiki. Cikin tausayawa tace, wayyo yayana, ka wahala, sannu yayana, koda yake ai ka huce gajiyar yanzu dan nasa aunty ta gasa ma jikinka da ruwan zafi, kuma tayi maka tausa, nasan gajiya ta gudu sai wacce zaka sake dauka yanzu ko yaya? Yace, don kinga bana kusa kika samu bakin gaya min haka ko? To bashi du ranar dana dawo na ware gajiyar akanki. Tasa dariya tace yaya kayi hakuri bazan kuma ba kaji? Yace nasan ranki ya baci sosai rashin tahowarmu tare. Amma don ki kwantar min da hankali kika dake, kika nuna min bakomai kina goyon bayan nayi adalci a tsakaninku, don kina so ranar lahira na tashi cikin maza salihai, masu adalci a tsakanin matayensu, baki nuna son zuciya ba. Tace yaya dare fa yayi, kada mu shiga hakkin auntyna, yaya saida safe. To Allah ya tashemu zeeyta. Kwana hudu ranar jumma'a da azahar ya baro ofis ya taho yayi shiri, ya taho kano. Zainab kuwa tana cike da doki anata yi masa girke-girke da soye2 da lemuka. Taci kwalliyarta ita da Ihsan. Ihsan tana cikin 'yar shimin riga ruwan hoda me adon les, a kirjin da hannun rigar sai dan jeans ga dan takalminta me madauri kasansa na glass, yarinyar tayi kyau matuka. Tanata tsalle2 ta acikin motarta a harabar gidan, motar Aliyu ta shigo yana ganin Ihsan yaji zuciyarsa ta cika da farin ciki da annashuwa direban bai gama tsayawaba da motar ya bude ya fito da saurinsa Ihsan tana ganinsa ta kama dariya, tana dago masa hannu da cewar Abbana! Abbana ya dauketa ya kankame yana murna, ya jiyo da daddan kamshi sahibar tasa ya daga kai yana kallonta tana masa murmushi, ya dago mata hannu ta taho ta shige jikinsa, suna dariya yayi mata kyakyawar runguma yasa hannunsa a mararta, ya rada mata a kunanta ya bebyna? Ta rangwadar da kai lafiyarsa lau sai maraicin Abbansa da yayi. Ya rada mata ai gani nazo zamu kasance dashi na tsawon awa biyar. Ta kwace jikinta tana dariya, "a nifa yaya ba haka nake nufi ba. Yace ai kin manta da bashina da kika ci ta waya? Tasa dariya niba ruwana. [8:09AM, 07/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 4**13 Tasa dariya nidai ba ruwan ga 'yarka nan me shegen wayo tana jinka. Ya sumbaceta yace Ihsan din Abba yarinyar tayi dariyarta tace Abban Ihsan, gaba daya suka sa dariya suka fada cikin gida yana rungume da iyalansa. Suka zube a falo, ina Amadina. Yana can ya fara zuwa makaranta yau. Ta rinka cire zare masa kayn jikinsa ta barshi daga shi sai gjrn wando taja hannunshi zuwa toile inda ta hada masa ruwan wanka. Yana fitowa ta tareshi da tawul ta goge masa ruwan jikinsa, ta shiryashi kamar karamin yaro, ta rikoshi zuwa tebir. Yana cin abincin yana zuba mata santi, zainab kici gaba da tallafin rayuwata, kina min tattalin so, kada ki barni naje kasa don kece farin cikin rayuwata. Ta taso da sauri ta rungumeshi, ta hada bakinta da nasa, tana yi masa hot kiss da ya rikitashi, yake kokarin mantar dashi a wacce jiha yake. Ta cika shi tasa bakinta daidai kunnensa, i luv u yayana, i care 4 u, life iz gud. Ta rikitashi da kalamanta inda ita kuma ya rikitata da soyayyarsa, tuni ya manta da batun cewar abinci fa yake ci a falo. Sai da ya samu nutsuwa shi kadai ya rinka yiwa kansa dariya, zainab kuma abun ya bata kunya. Ta fada dakinta ta shiga toilet, shima dakinsa ya shiga ya fada toilet. *** *** ***** Rayuwa mai dadi zainab tana zamanta cikin kwanciyar hankali, bata da damuwar komai tana cikin danginta da 'yan uwanta, kowa yaso ganinta zai zo gidanta su wuni suna hira, amma ita bata fita ko ina, sai dai in fitar ce ta kama dole. Sai dai in Aliyu yazo du inda take son zuwa zasu je tare. Mansura kuma tana abuja, amma du abun duniya ya isheta, saboda bata saba da zaman kadaici ba. Ahmad in ya fice tun safe ya tafi makaranta sai yamma zai dawo. Haka Aliyu tun safe zai fice