← Book details Tattalin So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 44

Sashe 24

Tattalin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wadda tun tana yarinya baya kaunar ganinkukanta, yanzu
yaji hankalinshi ya tashi, sai yanemo mata komai take so
sannan yake samunnutsuwa, bare yanzu data zama
mallakinsa.Ya sanyaya murya can kasa kamar zaiyi
kuka,yace "zainab so kike ki daga min hankali ko?Bakya
son kwanciyar hankalina zeeyta? Ya kikeso nayi da
rayuwata? Zainab tafiyarki gidaawajena ba karamin tashin
hankali bane. Habazeeyta kiyi hakuri ki zauna agidan ki
rikeminamanar kanki da dukiyata da gidana. Yanzu inkika
tafi bakya nan gidan ai kango zai zama.Ya zauna dirshen a
kasa ya jawota jikinsa yanararrashi, kiyi hakuri zainab ki
kwantar dahankalinki ko na samu nutsuwar zuciyata.Zainab
yaki fa zamu tafi, ko muyi nasara ko akashemu . Tayi
firgigit ya dago kanta daga jikinsacikin razana. Tace yaya
mutuwa? Ya maida kantaya kwantar jikinsa. Yace kada ki
damu, ai hakamuke, nasara tana wajen ubangiji mun
dogaradashi zai karemu, cikin hukuncin ubangiji, Allahzai
bamu nasara akan abunda muka jeyi.kita yimin addu'a kinji
kada ki kuma damuwa.Ta dago kanta tace "yaya kayi hakuri
in na batamaka ka yafe min kaji.Bakomai zainab na hakura
na yafe miki ki dainadamuwa ki taimaka min da addu'a.To
yaya na dau alkawari zan tayi maka nafilfili daaddu'o'in
neman nasara. Yauwa kanwata,nagode. Bari naje gida
nawa su Abba da daddymaganar tafiyan, wa kike so akwo
miki ta tayakizama?Hajiya."yace, hajiya babba?Ta daga
kai. Yace babbar magana, bari na gayamusu, ai 'yar gatan
hajiya ce ke zata zo.Yana fita ta mike ta shiga kicin zata
tanadarmasa abunda zaiyi guziri dashi.Tana gamawa ta
shiga tayi wanka, tayi alwalatayi sallar la'asar, ta tsala
kwalliyarta da orangedin shadda, ta kafa daurinta tayi kyau
tanatasheki kamar ba ita bace tasha kuka dazu ba. Tajeta
bude jakar tafiyar ta zuba mishi kunshin ledamai kyalli guda
hudu, daya hadadden kek ne datayi masa mai kwakwa,
dayar kuma mitfy, dayarkuma kwallon kaza, sai soyayyen
cincin maisugar data ke dashi, ta dibar masa. Daya
kena'uroro sun zo mana masu saukaka mana aiki,shiyasa
nan da nan ta gama.Aliyu kuwa daya jewa iyayensa
maganar tafiya,nasihohi suka yi masa kamar yanda suka
saba,suka yi masa addu'ar samun nasara da
fatanalkhairi.Daya zo wajen hajiya yake fada mata
sakonmuniyarta, hajiya tace "Allah sarki, ai zainab cesaina
zo na tayata zama, yarinya mai hankali danutsuwa, ka gaya
mata ta kwantar da hankalintakana tafiya direba zai
kawoni."Aliyu yace yauwa hajiyarmu, kakarmu ta kanmu,ya
bata kudi mai yawa taita masa godiya, yabawa su umma
suma sukaita masa godiya da saalbarka.Ya amsa da Amin,
ya shige motarsa ya tafigidanshi, yana ganin gimbiyar sai
yaji hankalinshiya tashi daya tua tafiya zaiyi ya barta har
nawani lokaci.Ta tare shi tana murmushi tare dayi masa
sannuda zuwa, ya zuba mata ido da irin kallon nan
maibirkita kwanyar masoyi, ya nufi wajenta, ya
warehannunshi ya rungumeta yana sumbatarta ahankali
kamar zai hadiyeta.Du kunya da nauyinshi ya isheta,
kokarin zamewatake daga jikinsa amma yaki ya bata
damarhakan saima ya kara matseta ajikinshi.Sannan ya
zauna akan kujera yana shafa kanta,du ta noke ajikinsa
kunyarsa take ji sosai.Ya rada mata a kunnenta yaushe zaki
daina minkunyar nan ne Amma zanyi kokari na rabaki
dakunyar nan.ta rufe fuskarta ta zame daga jikinsa tana
maitsananin jin nauyin abunda ya fada mata.Yace baki bani
abinci bafa taso muje ki baniabinci yunwa nake ji.Da kyar
ta mike tayi gaba yana biye da ita harzuwa tebir din, ta
bude abincin kamshinsa yabugeshi. Malmala biyu ta cire
daga ledar sunataturiri ta zuba kan filet din tangaram, ta
zubamiyan cikan tagaran din ta zuba masa kunun aya,ta
rinka tura masa gabansa. A hankali tace kacimana.Ya
jawota ya zaunar da ita acinyarsa, yace waihar yanzu
kunyarce ne? Don Allah ki cire kunyarnan ki bani abaki.
Tace um-um, nidai bazan iyabadon Allah ka kyaleni.Ta mike
da gudu tai cikin daki, yabi ta da kalloyana murmushi, saida
ta shige ciki ya girgiza kaiya kama cin abincin yana mai jin
dadinsa sosai.Ya rinka shan kunun ayar nan da yaji
madararruwa yana santi.Saida ya gama ci, ya shiga
dakinsa ya fadatoilet, yaga ta tara masa ruwan wanka a
baho, yashiga yayi wanka ya fito.Ya shirya cikin kakinsa, ya
fito ya shiga dakinta.Tana zaune abakin gado tayi tagumi,
ya zaunakusa da ita ya cire hannun tagumin yace babukyau
ki daina, ya ciro sabuwar waya akwalinta yamika mata. Ga
waya zainab kullum zamu kasancetare awaya kinji.Ta daga
kai tace nagode.Ya fito da kudi masu yawa ya mika mata,
ungowannan kirike a hannunki ki rinka 'yan bukatunki.Ta
bude baki cike da mamaki, tace ai yaya kudinsunyi yawa,
me zan siya? Komai fa da akwai asito.Ta karba ta raba
kudin biyu, tasa masa rabi aaljihunsa, don Allah yaya ka
barsu wa'yannan masun isa nagode Allah kara budi.Yace
Amin nagode nji dadin addu'arki. Ya mikezainab zan tafi?
Ta dago kanta a sanyaye yayatafiyar zakayi? Sai kuma
hawaye. Ya dawo yazauna, ya jawota jikinsa, sai kuma ta
sakar masakuka......kawaisai tausayinta ya kamani na
tsaya da rubutun ina kallonsu

Bakwa komai
[9:20AM, 05/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 2**16 & 2**17

Ya dawo ya zauna, ya jawota jikinsa, sai kuma tasakar
masa kuka.Ya rinka rarrashinta yana lallaminta
kamaryarinyar goye dake jikin mamanta, kiyi shiruzeeyta
kiyi hakuri bazan dade ba zan dawo, mekike so na siyo
miki? Ta girgiza kai bakomai." yadago kanta yana share
mata hawayen, to kiyishiru bana son kukan nan, yana daga
minhankali.Ta hadiye kukan tana ajiyar zuciya, ya
rinkararrashinta yana lallaminta tare da dan
bubbugabayanta, sanyin iskar data rinka ji ta cikinkunnenta
shiya saukar mata da kasala jikinta yasaki kawai sai bacci
ya dauketa.Ya lallaba a hankali ya shimfideta, sadaf-sadaf
yafita ya shiga dakinsa, ya dauki jakar kayansa yafice ya
fada motarsa, ya sallami mai gadi yayiwaje da gudu ya
dauki hanyar kaduna.A zuciyarshi yana tunani zeey dinshi
saita tashitaga ya tafi.Kai zeey da rigima take, du ta daga
masa hankali,inba dole ba yaushe zai tafi wani waje ya
barta.Ya zari wayarsa ya bugawa hajiya,yace dan Allah
hajiya direba ya kaiki yanzu fanabar zeey ita kadai a
gidan.Hajiya tace ai kayana ma ake sawa a mota
yanzuzamu tafi.Yauwa hajiyata nagode. Ya kashe wayar.
Lokacindaya isa kaduna ya tarar da abokinsa faruk
yanajiransa, suka rungume juna, ya dakkowa Aliyutakardar,
Aliyu ya bude ya karanta yaji bayananda suke ciki.Aliyu ya
ninke yace to Allah ya taimaka mana.Faruk yace, bari na
karasa gida na barka kadanhuta kayi shirye-shiryenka.
Tafiyar asuba zamuyigwanda ka kwanta da wuri. Aliyu yace
badamuwa. Ya rakoshi wajen motarsa ya tafi.Aliyu ya shigo
cikin gida ya wuce dakinsa, yafada toilet yayi wanka yayo
alwala yayi sallah,yayi addu'o'insa ya shafa.Ya shafa
cikinsa daya ji yunwa ta fara matsamasa, yasan yayi
maraicin zainab ko don yandatake kula dashi wajen abinci,
yanzu dole saide yahada shayi yasha, don ya gaji bazai iya
fita gidanwani abinci ba.Gashi yaronsa maiyi masa girki
shima yaje ganingida bai dawo ba. Ya bude wayarsa ya
dannalambar zeey dinshi, ringin daya tayi ana biyu
akadauka, "hello yaya." saita sa masa kukanshagwaba. Ya
kama rarrashi, yi shiru yi hakurizeeyta, daina kukan gaya
min meye? Mene nezeeyta? Gaya min kinji babyna.Yaya
shine kayi min wayo kasani bacci ka guduko? Yaya kuma
kudin dana raba biyu na dau rabinace maka sun isheni na
baka rabin shine kaajiye min ko?Oh! Sorry zeeyta, bazan
kuma ba nadaina kinji,daina kukan kina tsiyayar min da
hawayenki maitsada a kasa, gashi bana kusa bare na
tsotse.Tace, ka gani zaka fara ko?To na daina, hajiya tazo
ko?Hajiya tazo tuntuni, suna falo ita da hamza dasadik
suna hira.Yace, yauwa ai nasan bazasu barmin ke
cikindamuwa ba zasu rinka zuwa suna tayaki hira. Keko dai
kinci abinci? Bana so ki rinka zama dayunwa fa, ki rinka cin
abinci sosai kinji?Tace, to yaya ai kaima baka ci ba.To ni
wa zai bani zeeyta? Yanzu ma zan jonahita na tafasa
ruwan shayi nasha, don yunwanakeji.Ya marairaice masa
tace, haba yaya da kanka?Yace to ya zanyi zeeyta, wa zaiyi
min? Tace yayaka duba cikin kayanka da akwai sako.Sakon
me?Um-um nidai bazan gaya maka ba, ka budeyanzu inka
kashe wayar."yace to.Ya kashe wayar ya jawo jakar kayan
nasa yanabudewa, yaga nadi-nadi na leda har kashi
hudu.Ya rinka warewa ganin abubuwan da suke cikiyasa shi
tsananin mamaki da al'ajabi, a yaushezeey tayi wannan
aikin? Kai wannan yarinyaubangiji Allah yayi mata albarka.
Hakika yaji dadita faranta masa sosai, ya daga hannunsa
yanayiwa Allah godiya. Allah na gode maka da
wannanbaiwa dakayi min nasamun nutsasiyar mace
maihakuri da sanin ya kamata.Ya ware komai ya rinka ci
cikin nutsuwa danishadi, saida yaci ya koshi yasha lemo
yayigyatsa yayi hamda ga ubangiji, yaita shiwazainab
albarka a zuciyarsa.Yayi waya gida ya sanarwa mahaifansa
ya isolafiya, ya bugawa mansura itama ya gaya mataya iso
lafiya, taba shi Ahmad sukayi hirarsu yanagaya masa
abunda zai sissiyo masa.Mansura ma ta karba ta gaya
masa abubuwandatake bukata, sukayi sallama. Yana kashe
wayarzeey dinshi ya sake bugawa.Tana dauka tace, hello!
Yayana ka koshi?Nakoshi zeeyta Allah yayi miki
albarka.Amin yaya nagode.Yace, wai zainab ba zaki rinka
gayamin sunayendana ji kin radamin ba, mazan jiya da
mazaje?Tace "kai yaya nidai ban zan iyaba, da dinma
danbansan kai bane ba.To yanzu me zaki rinka gayamin?
Honey ko myluv?Tace, kai yaya dan Allah ka bari.Yace, au
bazaki gayamin kalmar da zata sanibacci cikin nishadi ba?
Sai ya kashe wayar.Ta dafe kai tace kai yaya da saurin
fushi yake,toni yanzu ya zanyi masa? Ta dake ta bugamasa
wayar, ya dauka yace uhm! Ina jinki. Cikinsanyita tace yaya
fushi kayi? Don Allah kayihakuri kada ka kwana kana fushi
dani kaji.Yace to naji na hakura, amma saikin cemin I
luvu.Tace, kai yaya don Allah....Au bazaki fada ba?Saika ce
mai koyon magana ta fada da dai-dai, iluv u, tayi saurin
kashe wayar. Yayi dariya yanamaijin dadin hankalin zeey
din tashi dakuruciyarta.Da asuba yayi sallama da iyayensa
da iyalansa,jirginsu ya daga zuwa bayelsa....
Chapter 24 · 0% Book details