Sashe 40
Tattalin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ga takalma jaka da sarkar gwal. Akwatin Ahmad ma kananan kaya masu tsada, sai shadda da boyel masu tsada sun sha aiki, kala goma sha daya, ga takalma da huluna masu kyau da tsada, harda glas mai ruwan gwal suka gama gani, saratu ta rufe kayan, hajiya tace mun gani Allah ya saka da alkhairi, ubangiji ya kara buda masa. Mansura tace, hajiya nifa na taho gida, ku kirashi kuyi masa fada bazan iya zama da wannan rashin adalcin nasa ba.... Kafin ta rufe bakinta Alh ya wanke mata fuska da mari, hajiya ta rufeta da duka. Dabbar yarinya mara hankali, dazunan ya kawomin makullin mota sabuwa kar. Ya aikowa da mahaifiyarki katon injin kankara don ta rinka sana'a dashi shine kike kokarin tozarta kanki, da yake bakisan abun arziki ba, to du ranar da kika sake zuwa gidan nan kika kawomin karar mijinki, saina karyaki, bare kuma kiyo yaji, wannan kasheki zanyi murus har lahira. Fita ki bani waje, ya biyota tayi waje da sauri, kananta suka mayar mata da akwatunan cikin mota, taja ta koma gida tana hawaye, fuskarta da yatsun babanta daya mareta. Tazo ta wuce ta babban falo tana kuka Aliyu yana zaune yana kallo, ko kallonta baiyi ba, ta wuce bangarenta. Ranar suna aka sawa jaririyar sunan maman zainab, suna kiranta da ihsan. Taron suna yayi kyau angama lafiya aka watse. Kyaututuka da zainab ta samu baza su lissafuba, daga kawayenta, abokan Aliyu 'yan uwa da abokan arziki, kayan kamar a bude sito dashi. Yaya ni'ima tace, kinsan kuwa yau shekarar ku uku cif da aure da yaya. Shida yayi alkawari saikin shekara uku sannan zai kusanceki, sai gashi shekara uku tazo da 'yar diyarku ko? Zainab tace ke kika jiyo, ni ba ruwana. Suka sa mata dariya. *** ***** kwanci tashi rayuwa ta mika, zainab tuni sunyi arba'in, harta koma abuja, taci gaba da karatunta. 'yar diyarta saida daddynta ya nema mata tsari sosai, saboda kyan Ihsan du wanda ya bude baki, sai yace hu! Wannan yarinyar da kyau take. Ihsan watanta shidda kenan tayi 'yar kubibi abun sha'awa da 'yan hakoranta biyu abakinta, tayi sabo da Aliyu du sanda ya dawo gida, yana tare da ita, don haka data ganshi tana bayan talatu zata rinka zillo. Ya karbeta ya rungumeta, yana murnar ganinta... via # Abdul azeez muhammad Ina 'yan gidan nan kowa ya fito ya bani Happy sallah nah [8:05AM, 07/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 4**8 Ya karbeta ya rungumeta, yana murnar ganinta, yasata a gaban mota, yaita yawo da ita. Tanada wata takwas ta fara takawa, dadi ya ishi Aliyu, komai ya gani sai ya siyo wa ihsan. Ihsan tana sanye da dan jeans din dogon wando da 'yar riga yalo ta dan kama mata jiki, anyi mata indomie akanta, ansa mata kananan ribon yalo. Da takalminta yarinyar tana ta kamshi, tana tura 'yar motarta a falon, tana binta. Aliyu yayi sallama ta taho da gudu tana cewa Abba! Har tana kokarin faduwa. Ya sureta ya rungumeta ta Abba. Zainab ta fito cikin kayataccen kwalliyarta ta kananan kaya, ta sake komawa yarinya sharaf, saboda hutu ya kara samuwa. Ta taryeshi ta rungumesu gaba dayansu yana me jin farin ciki, da nishadi a zuciyarsa. Ta karbi jakansa ya zauna kan kujera yana rungume da ihsan, zeey ta cire masa takalman kafarsa da safa ta cire masa kakin jikinsa, ta barshi daga shi sai ves da gajeren wando. Ihsan tanata tsallenta a jikinshi. Zainab ta kai masa kayansa dakinsa. Ta dawo ta dauke ihsan, tare da cewa, daga Abba yaje yayi wanka. Ya shirya ya fito cikin kananan kaya suka nufi tebir, sai da suka gama cin abinci suka nutsu, suna kan kafet suna wasansu, Aliyu ya daure ido da farin kyalle yana bin ihsan da rarrafe, tana gudu tana dariya. Zainab ta taboshi yayi saurin juyawa baya, yana lalume zai kamata, ta zille dayan gefen tanayi masa dariya. Ta rankwafo gabansa taja masa hanci, tayi saurin zillewa, yakai hannunsa bai kamata ba, zata gudu yasa mata kafa ta fado kansa, yayi saurin shafa kanta yauwa na kamaki. Tace "a wlh ban yarda ba wayo kamin. Ihsan ta fado kansu tana gwarancinta, gaba daya suka sa dariya. Ya bude idonsa duk suka zube kan kafet din suna maida numfashi. Tace Abban Ihsan, yace na'am maman Ihsan. Tace don Allah tunda na gama diploma, kafin na fara karatun digiri, muje gida kano mu huta, yaya rabona da gidan tun bayan arba'in din Ihsan. Wallahi inason zuwa gida. Yace haba zainab du fa sati ina zuwa, kuma ina gaya miki sakon gaisuwar da suke yi miki. Ga waya kullum kunayi kuna hira dasu kuna jin dadi, ko yaushe fa kuna tare dasu a waya. Ta langabe masa tanayi masa magiya, Abban Ihsan don Allah kayi hakuri ka amince mana muje, wallahi suna son ganin Ihsan, sunce hotunan ta baya gamsar dasu, yaya kada fa Ihsan ta tashi bata san dangita ba. Yace "I gaskiya hakane da wannan ku shirya wannan satin zamuje tare. Ta rungumeshi tana mai cike da murna da farin ciki, nagode yaya Allah ya saka da alkhairi, ubangiji ya kara maka budi da son zumunci. Amin zeeyta. Ranar da suka sauka 'yan uwa sunyi farin ciki sosai da ganinsu, kowa sai daukan Ihsan yake yi. Ahmad ya rungumesu, yana cewa barka da zuwa aunty mamina, nagode da kika kawomin 'yar uwata. Ta shafa kansa Amadina naji dadi dana sameka lafiya ka girma ka kara wayo da hankali. Gidan nasu ya kasance kullum a cike saboda 'yan sanda zuwa. Ranar da suka yi sati biyu da zuwa sukayi wanka sukayi kwalliya ita da Ihsan, ta shiga motarta ita da Ihsan da kanta tajasu zuwa gidansu. Ihsan tana da shekara biyu kenan, amma wayonta da surutunta saika zata tayi shekara hudu. Ni'ima ce ta sake haihuwa, suna gidan sunan Aliyu yayo wa zainab waya, Ihsan tanata rigima ta hanata amsa wayar, yanata yi mata fada wai ta shiga cikin jama'a da ita zafi ya dameta. Y kashe wayar mintuna kadan ya isa gidan ni'ima, ya yowa zainab waya yace ta fito ta kawo masa 'yarsa. Ihsan tana ganinsa ta rungumeshi, tana murna, Abba ka daina tafiya kana barina in ban ganka ba kuka zanta yi. To na daina Ihsan dita, dake zan rinka zuwa ofis ko? Ta daga kai. Yauwa bebyna. Yai tafiyarsa da Ihsan din sai mangariba ya koma gida, Ihsan tana rungume a jikinsa tayi bacci. Mansura tayi sallama, ta shigo ya amsa mata sallamar yace ina Zainab? Tace, kajika da wani zance, motata daban tata daban zance taho mu tafi ne, tare dai muka fito daga gidan ni'ima, ban san yanda akayi ba nura tsohon saurayinta yasan ana suna, sai ganinsa mukayi a zaune akan motarsa yana ganin zainab ya kama washe baki, ta tsaya suna gaisawa nikuma nayi tahowata. Yayi wata irin zabura ya mike yana huci, dai-dai lokacin da zainab din tayi sallama ta shigo, a fusace yace mata daga ina kike? Cikin sanyita tace yaya wace irin tambayace wannan? Kafin ta karasa maganan ya dauketa da mari, tuni ta dafe kuncin nata, ta wani durkushe a kasa saboda gigitaccen zafin marin. Ya nunata da yatsa uban waye ya baki damar tsayawa da nura, har ku gaisa dashi? Kanta yana sunkuye, tana jin haka da sauri ta dago kanta ta kalli mansura, tace aunty kiji tsoron Allah, wai me na tare miki a doron kasa ne kike so kiga kinsani bala'i? Ya kamata ku sani wannan duniyar ba matabbata bace. Aunty idan kin kashe aurena da yaya me kikayi tunda dai kinsan dole a gabanku zanci gaba da zama, har lokacin da zangama idda na samu wani mijn da zan aura, kuma duk matsalar data faru dani dole ku zan kwaso na gayawa. Aunty duk matan arziki bazata bari mijinta yayi fushi da ita ba, ni gashi kinsa ran nawa mijin ya baci dani, yana fushi dani alhalin bada hakkina ba. Via #Justice_Hamzat [8:05AM, 07/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 4**9 kiyi hakuri aunty, gaba kike dani, kuma ke auntyna ce, bazan taba bari wani batanci ya shiga tsakaninmu ba, amma dan Allah ki rinka jan mutuncinki da girmanki. Tace, yaya kayi hakuri, amma ban aikata abunda kake zargina dashi ba, rabona da nura tun ranar da ka koreshi, ko labarinsa ban sake jiba bare na ganshi. Ta mike tsaye zata nufi dakinta jiri ya kwasheta, tayi baya zata fadi, Aliyu yayi saurin tareta ta fado hannunsa, ta shide, numfashinta ya dauke a gigice sukayi asibiti, saida likitoci sukayi ta gwaje-gwajensu, suka jona mata karin ruwa ta farfado, sai dai takoma bacci. Mansura kukan nadama takeyi, tana bawa Aliyu hakuri, shi bakin cikin marin da yayiwa zainab yafi komai daga masa hankali. Likita ya shigo yace, yallabai saika kula da madam sosai, ka daina bata mata rai, don tana da karamin ciki na wata biyu a jikinta. Wani irin farin ciki ne ya lullube zuciyar Aliyu, ya rinka dariya yana nuna farin ciki da godiya ga Allah. Mansura ta rinka mamakin irin farin cikin da yake yi, wai yana son haihuwa haka amma bai hanata planin din data keyi ba, du da dai bashi yasa ta tayi ba. Amma ai wataran yana ji tayi waya asibiti, tace zato zo allura, bai ce mata komai ba, to me yake nufi da itane, ko bai dauketa wata tsiya ba? Tayi waje da saurinta, ta zaro wayarta ta bugawa yayarta saratu tana dauka tace, hello kinji yarinyar nan ciki ne da ita, kinga murnar da Aliyu yake yi kamar wanda akayiwa bushara da gidan Aljanna, yanzu dama mutumin nan yana son haihuwa ya barni inata faman planin. Au dama planin Aliyu ya saki kiyi shiyasa baki sake haihuwa ba tsawon lokaci? Tace wlh yaya saratu gaskiya ba Aliyu ne ya saniba, don na taba gaya masa zanyi tsarin iyali, yace ba ruwansa, kuma bada yawunsa ba, idan kuma nayi bai yafe ba. Ni kuma naga shi dan gayu, ga son ya huta, sai nake ga kamar tara 'ya'ya zai iya zame masa matsala, yaga baya samun yanda yake so watarana yayo min kishiya, sai duk da haka ban tsira ba. Amma tunda naji labarin zainab tana da cikin Ihsan, na daina planin din, amma gashi harta haihu ta kuma samun wani cikin, ni kuma ba