← Book details Tattalin So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 44

Sashe 41

Tattalin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

labari. Saratu ta daka mata tsawa tare da cewa, ke kika yiwa kanki, kin cuci kanki abanza a wofi. Ga dukiya nan yana samu kamar kasa, ita kuma taita tara masa 'ya'ya kya zama 'yar kallo ai, yanzu ma ya fara baki kujerar makka biyar, kin kawowa Alh, to gaba muka san me zaiyi mana, bare ace kin cika gidan da 'ya'ya, ni bazan iya sauraran takaicinki ba sai anjima. Ta kashe wayar. Mansura ta dawo dakin a sanyaye da ita. Zainab ta farka Aliyu yace sannu zeeyta. Ta dago kanta cikin sanyita tace yaya kayi hakuri dan Allah ka yafemin, wallahi ba wani namiji dana gaisa dashi. Kayi hakuri yaya zuciyarka ta huce. Ya shafa kanta zainab ki daina tuna wannan magana dakin san yanda raina ya rinka suya da tukukin bakin ciki, ina tuna ni na mareki da wannan hannun nawa sai nake tunanin irin hukuncin da zanyiwa hannun ko zuciyata ta huce. Zainab nayi abunda Allah ya hana, yanke hukunci cikin fushi. Zainab ba laifina bane, shirin mansura ne kawai don ta bataki awajena. Kiyi hakuri zeeyta. Tayi saurin sa hannu ta toshe masa baki tana murmushi, don Allah yaya ka daina bani hakuri, wlh na yafe maka, ka gayawa aunty ma na yafe mata. Babban jin dadi na da zuciyarka ta huce, bakayi fushi dani ba. Zainab jiyan ma bacin raine da zafin kishinki, wai har na mareki. Tace don Allah yaya kadaina tuna zancen marin nan, kaifa yayana ne, kayi min marin ne a matsayinka na wana, ba miji ba ko yayana? Mansura tana tsaye a gefe daya tayi shiru tana jinsu. Aliyu kamar baisan tana wajenba, bare zainab da bata san tana nan ba. Zainab tace, dan Allah yaya kayi hakuri kada kayiwa aunty wani abu, kasan dan adam ajizine, kowa zai iya kuskure kayi hakuri yaya ka yafe mata. Ya daga kai shikenan naji na yafe mata, mansura kawai saita juya ta fita daga dakin. Likita ya rubuta musu maganguna na karin jini da lafiyar dan tayin cikinta. A daren suka dawo gida wani irin tattalin so da sabuwar kulawa da yakeyi, kamar zai mayar da ita ciki ita kuma sai sangarta take zuba mai da shagwaba ga cikin nata mai tsurfa ne du daurewar data keyi, amma abu kankani sai ya daga mata hankali yasata amai. Hankalin Aliyu ya kasa nemansa akeyi awajen aikinsa, ga zeey dinshi bata cika lafiya ba. Amma dole ya dauketa su tafi Abujan, ta karasa warware wa acan. Yace wa zainab ki hada abunda zaki tafi dashi don jibi litinin zamu tafi. Yana fita yayi bangaren mansura, yace mata kiyi lis din du abunda zaku bukata, don jibi zamu koma abuja. Tace, kaida wa? Yace dawa muke tafiya? Tace, kana nufin wai da zainab din zaka kuma tafiya ne? Yace ya wuce wai. Ta mike tsaye tana tafa hannu, to wlh abunda bazai taba yuwuwa ba kenan, na gaji da yi muku gadin gida wlh, wlh bazan zauna ba, na gaji da rashin adalcinka, ka rinka kwasar wadanda kake so kuna tafiya. Ya daga mata hannu, tare da cewa ya isheni, kada ki kawomin maganar banza, haka nayi niyya baki isa ki canjani ba. Ya fice ya doka mata kofar, ta tabe baki dan rainin hankali zaka gane kurenka. Via #Justice_Hamzat [8:07AM, 07/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 4**10 Dan rainin hankali zaka gane kurenka, tauraruwar taka dole ka barta, ko kuma ka tafi damu gaba daya, don wlh bazan zauna ba, sai na bika. A bangarenta ya kwana da safe ya sake yi mata maganar ta bada lis din abunda zasu bukata. Tace masa saidai ka nemi lis a wajen zainab, don ni kaga akwatuna na can nagama shirin binka. Ya daka mata tsawa ke baki isa ki raina min hankali ba. Ga cek nan ki rubuta abunda kike bukata a karbo miki a banki, idan kinga zaki zauna ki zauna, idan kinga bazaki zauna ba to ki tafi gidanku. Ta dafe kirji ni zaka yiwa wannan wulakancin Aliyu? Ko kallonta baiyi ba ya fice ya bata waje, tana jin fitarsa itama ta shirya ta fice, gidansu Aliyu. Da suka gaisa da umma, sai tayi bangaren ummi ta gaisheta, sannan ta shiga bangaren su zainab, ta gaisar da maman sannan tace mata, don Allah daddyn zainab yana nan? Mama tace "I yana ciki. Tace don Allah mama inason magana dashi. Tace, to bari nayo masa magana. Ta mike shiga bangarensa ta gaya masa. Yace mansuran ta shigo, mansura ta rissuna ta gaisheshi, saita fashe da kuka daddy yace, lafiya menene, me suka yi miki, wani abu ne ya faru? Tace daddy wai dan Allah Aliyu yace zasu koma abuja da zainab, sai nace ya rinka kwatanta adalci a tsakaninmu, mu ma yaje damu abujan nan, shine ya hauni da fada wai bazamuje ba, anan yaga damar ajiyemu, in zan zauna na zauna, in bazan zauna ba na fice na tafi gidanmu. Dady yace subhanallahi, me yayi zafi haka? To kiyi hakuri ki koma gida kici gaba da shirinki, zai tafi daku kinji. Tace to dady nagode Allah ya saka da Alheri. Yace bakomai tashi ki koma gida. Ta fito tayi musu sallama ta koma gida. Dady yayi waya ya kira Aliyu, ya zo da saurinsa, yace dady gani. Bayan sun gaisa, yace haba Aliyu kaifa yaro ne, amma me halin manyan mutane. Haba Aliyu kada rudin duniya ya debeka, ka kaucewa fadin Allah, kazo kana fadawa halaka. Yata masa nasiha daga karshe yace to yanzu tunda bata amince ba, to an shiga hakkinta, don haka ka tafi da mansura abuja ka bar zainab anan kano. Aliyu ransa ya baci wato mansura kararsa ta kawo kuma tasan inda bai isa yayi musu ba. Yace to dady na tafi da itan. Yace yauwa ko kaifa dana, nagode. Aliyu ya taho gida ransa a bace saboda abunda mansura tayi masa. Magoronsa ya rinka daci na tukukin bacin rai, sai yaji zazzabi yana neman rufeshi. Ya shiga falon zainab ya zauna ya zuba tagumi zainab ta fito daga kicin ta ganshi, ta karaso gabansa da sauri tace lafiya yayana, meya faru, meya sameka kayi tagumi? Tasa hannunta ta cire mishi tagumin, ya akayi yayana menene? Ya danyi tsaki yace bana jin dadin jikina, ina jin dan zazzabi ajikin nawa. Oh! Sorry yayana sannu, ta dafashi tana lallaminsa kamar yaro. A hankali ta zame masa kayan jikinsa, daga shi sai gajeren wando. Ta shiga kicin ta kawo mishi ruwa mai sanyi, da lemu ta zuba a kofi tasa masa a bakinsa kadan ya iya sha saboda bacin rai. Ta debo ruwa a tasa ta dauko karamin tawul tazo ta rinka dangwalar ruwan tana daddana masa ajikinsa, yana lumshe ido a hankali ya fara jin yana watsatsakewa, saida taji jikinsa ya huce daga dumin, sannan ta bashi magani yasha. Ya kishingida akan kujera, ta rinka yi masa tausa, sannu a hankali yana lumshe ido tare da cewar wash. Bacci mai dadi ya ringa fisgarsa, ya kwantar da zainab ajikinsa ya rungumeta, bacci ya daukesu a haka. 50 min suka kwashe suna bacci, a haka zainab ce ta fara farkawa, ta runkura a hankali zata zame tabar jikinsa, ya kara kankameta, ya bude ido ya sumbaci lebenta, dariya, yayana ka farka. Tunda zaki bar jikina ai dole na farka. Yaya lokacin sallah yayi hudu saura. Ya mike da sauri, ta shiga toilet ta hada masa ruwan wanka, ya shiga yayi wankansa a nitse ya fito zuciyarsa wasai, ya manta da wani bacin ran mansura, yayi saurin sa kaya ya fita masallaci don sallar la'asar. Lokacin daya dawo daga masallaci ya tar zainab ta canja masa shiga ta kananan kaya, irin shigar da yake so. Ta tare shi tana murmushi, ta riko hannunsa suka wuce tebir don cin abinci. Ta rinka tattalinsa, tana bashi abinci abaki, sai kace yaron goye. Suna ci cikin nishadi da faranta ran juna, sai santi yake zuba mata, yana sata kyalkyala dariya. Tasa shi cikin farin ciki da walwala kwata2 ya manta da bacin rai da mansura ta dasa masa. Ya dauki waya bari na bugawa ni'ima ta kawo min Ihsan dita, bana jin dadi idan bana jin karadin bebyna. Zainab ta rike wayar don Allah yaya ka bari, tace saida daddare idan zasu zo yi mana sallama zasu taho tare. Yayi wani dif saboda yanda zuciyarsa ta buga da ya tuno fa bada zeey dinshi zai tafi ba. Gashi du ta hada kayansu da abunda tasan zatayi amfani dasu. Ta kula da halin da yake ciki, tace wayyo yaya don Allah kayi hakuri idan ranka ne ya baci bari na tura direba ya dauko maka ihsan din kaji yayana. Ta mike ya riko hannunta dawo ki zauna, ba fushi nayi ba, dani da ni'ima ai duk daya ne. Tace to meye yayana nafa duk ka canja? Yace kiyi hakuri zainab bada ke zan tafi abuja ba. Ta dafe kirji yaya me nayi maka, saboda me bazaka tafi dani ba? Ya kwanto da ita jikinsa. Via #Justice_Hamzat [8:08AM, 07/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 4**11 Ya kwanto da ita jikinsa yana rarrashinta, kiyi hakuri zainab ba a son raina ba, mansura ce ta kai karata wajen dady yace na tafi da ita. Tace shikenan yaya, saikun dawo Allah ya kiyaye hanya. Ta mike tayi cikin dakinta ta kwanta tana hawaye. Ya taso ya biyota, ya dagota "zeeyta menene fushi kika yi? Kiyi hakuri nasan dole ranki ya baci, amma ni nafiki cutuwa da rashinki kusa dani. Zainab kici gaba da shirinki, saimu tafi gaba daya, kinji. Ta tashi tace haba yaya ya zanki jin maganar mahaifana? Dady abunda ya fada gaskiya ne, hakan shine adalci yaya kuje Allah ya kaiku lafiya, zan tayi muku addu'a daga nan. Ta tashi ta shiga toilet shiru-shiru yana jiranta bata fito ba, ya dafe kansa tabbas yasan zeey dinshi fushi tayi, ya tashi ya fita daga dakin. Lokacin ni'ima da sadiya suka zo musu sallama, sannan Aliyu baya nan, zainab bata gaya musu cewar ba tare da ita za a tafi ba. Sai goman dare suka tafi, sunyi mamakin rashin dawowan yayan nasu gida da wuri. Sha daya na dare zainab ta kasa bacci, tana tunanin ina Aliyu ya shiga ne? Tayo alwala ta shimfida dadduma tana sallar nafila, tana addu'a Allah ya bata hakurin jure rashin
Chapter 41 · 0% Book details