← Book details Tattalin So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 44

Sashe 3

Tattalin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Surayya Abubakar
[1:16PM, 04/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 1**4
SUKA nema masa auren mansura. Alh
haruna mahaifinta yaji dadi, inda yace a
hade sa ranar data yaya sadiya ayi biki
gaba daya."
da mansura taji wannan labarin kamar ta zuba ruwa a kasa tasha don zumudi da
murna. Shikuwa yaya Aliyu ya hakura ne
ya yarda don bashi da yanda zaiyi, tunda
iyayensa da kakansa sunfi karfinsa.
Yaya sadiya sunyi candy a ranar suka yi
fatin candy, kawayenta da 'yan makarantar sun shayin hotuna harda
bidiyo caset don dai tarihi. Sun kakkarbi
adireshin junansu da lambobin waya,
don dai su rinka tunawa da juna suna
sada zumunci a junansu.
Satinsu biyu da candy yaya sadiya ta fara rabon katin bikinta. Inda itama mansura
ta ke raba nata katin bikin ga kawayenta
da 'yan uwa.
Haka yaya Aliyu anbawa sani ya kai
masa katunan can kaduna, yanata
rabawa abokan aikinsa da abokan arziki. Ranar alhamis akayi kamun mansura,
ranar jumma'a akayi kamun yaya sadiya.
A ranar yaya Aliyu ya dira daga kaduna,
da wasu tawagar abokanan nasa da yayi
musu masauki a daya daga cikin gidajen
iyayensu. Washe gari ranar asabar akayi daurin
aure, gaba daya ankon galila shadda
suka matsa, da hadadden dinki yi mata
na aikin saa. Du ita suka sa, saida akaje
gidan su mansura aka dauro auren yaya
Aliyu, sannan aka daura auren yaya sadiya, daga nan maroka suka shiga
busa da kade-kade, su Alh suka shiga
rabon kudi ana watsawa maroka kudi.
Haka abokanan yaya safiyanu mijin
sadiya, sukai ta watsawa maroka kudi.
Karfe hudu dai-dai aka shirya walima, kawayen yaya sadiya da kawayen
mansura, abokanan yaya Aliyu da
abokanan yaya safiyanu, du sun ci
kwalliya ta kece raini, hadaddun 'yan
mata gogaggu, wannan ta wace wannan,
wannan tana wace waccan, sun sha ado da kwalliya.
A harabar gidansu akayi da yake
farfajiyar katuwa ce, an kafa rumfuna
aciki an zuzzuba kujeru farare acikin
rumfar.
An ware gunda Aliyu da mansura, safiyanu da sadiya zasu zauna.
Anyiwa wajen ado da fulawoyi da roba
balan-balan, an wadata wajen da amare
da angwaye, sunyi kyau kamar fulawa
aka dasa dan kyau.
Ni'ima 'yar shekara sha hudu ta fara zama budurwa, domin makerin budurci
har ya fara kerata. Tayi kyau ta ratso
cikin tsakiyar filin gurin da lasfika take, ta
dauki lasfikar tace, "ansuturillah." ta fada
sau uku, jama'ar sai kowa sukayi shiru
suka zuba ido. Ni'ima ta kalli inda iyayenta suke taga
daddyn zainab da Abbansu, shigarsu iri
daya. Haka iyayen su mata duka su ukun
shiga iri daya suka yi.
Ta kalli jama'a taga kowa yayi shiru ya
nutsu ya zuba mata ido. Saita ce "muyi salati ga annabi." gaba
daya suka ce (s.a.w)." bayan an gama
karantawa tace, "ya shafi sha biyu, Allah
ya shafe du wata fitina da zata kunnowa
ma'auratan nan." gaba daya akace
ameen." bayan angama tace Ayatul kursiyu kafa
uku, Allah ka karemu ga mugun ji, mugun
gani, sharrin mutum dana Aljan, da
sharrin duk wani abunki.
Allah ya basu zaman lafiya, Allah ya basu
zuri'a dayyiba saliha, Allah yasa anyi wannan aure a sa'a.
Ta cika da fatiha, ta daga hannunta tana
addu'a ana amsawa da Amin. "waman
yattikillah yaja'allahu makraja, wa
yarzurku min haisu lah ya tasiri, waman
tawakal alallahi fa huwa hasbun, innallaha baligul amri kadija'Allahu li kulli
shai'in kadira. Amin.
Yayinda kowa ya shafa.
Tace to Alhmdllh, jama'a muna yi muku
barka da zuwa, mungode da hallartat
taronmu da kuka yi don ku taya mu murnar auren 'yan uwan mu.
Bari na kira muku autarmu dan tazo tayi
mana 'yar fadakarwa kadan kafin
malaman namu da zasu yi wa'azizzikan
su gama karasowa, tace "zainab zeey
daddy bismillah." zainab 'yar shekara takwas ta taso cikin
nutsuwa tana murmushi daya karawa
fuskarta kyau, tana sanye da dan dan
datsetsen yelow les da yake ta walwali,
dambara-damran dutsuna ajiki kamar
madubi, tasa gwagwaro yelow, ta yafa dankwalin les din. Tasa fashion azurfa
mai yalayen dutsuna wuya da kunne, da
zobensu, tasa warwaraye suma yaleye.
Yarinyar tayi kyau sosai, tsarin kwaliyarta
kamar wata babba. Shiga iri daya sukayi
da ni'ima komai da komai. Ni'ima ta mika mata lasfikar suna yiwa
juna murmushi, yayinda masu hotuna
suke basu flasha, masu filet din dvd da
cd suke ta dauka, ni'ima ta koma wajen
zamanta, zainab cikin zakin muryarta
tace "Aslm 'yan uwa musulmi." gaba daya kuwa suka amsa mata da "wslm.
"hakika ina taya 'yan uwana murna da
wannan rana ta aurensu, Allah ya basu
zaman lafiya dauwamamme, yaya sadiya
da aunty mansura, yanzu Allah ya kaiku
wani matsayi da rayuwarku zata canja ba kamar sanda kuna gida ba. 1- abu na
farko da ake so 'ya mace ta gane ta
fahimceshi shine, hakkin mijinta akanta,
ta gane cewar miji shine shugabanta, ta
rinka jin hakan a ranta.
Saboda Allah ubangiji yace, maza masu tsayuwa ne da shugabanci a kan mata,
kuma maza suna suke da fifiko wajen
girma da daraja akan mata."
wadanan dalilai su zasu mace ta dinga
jin cewa, namij fa shugabane, kuma ta
dinga jin haka a jikinta, kuma tasan yana da hakki akanta, domin tasan bazata fita
ba saida izninsa, kuma duk inda zata je
saita san ransa bazai baci ba.
Manzon Allah (s.a.w) ya fada a cikin
hadisi ingantacce
[1:17PM, 04/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 1**5

YA fada acikin hadisi ingantacce, saboda girman hakkin miji akan matarsa, "da za'a umurci wani yayi sujjada ga wani, dana umurci mace tayiwa mijinta sujjda. Koda miji zai bukaci amfani da matarsa, ita kuma tana kan sirdin rakumi, to kada ta hanashi.
A wata ruwayar ta bukhari, manzo Allah (s.a.w) yace, "idan mij ya kirawo matarsa zuwa ga shimfidarsa ita kuma taki har ya kwana yana fushi da ita, to mala'iku zasuyi ta tsine mata har sai an wayi gari, bukhari ne ya ruwaito.
Idan mace ta gane hakkin miji akanta, kuma tayi masa da'a akan abinda ba sabon Allah bane, to hakan zai taimaka kwarai wajen gyara zuciyarta.
2- abu na biyu shine amana, anaso mace ta zamo mai amana bata cikin abunda ya shafi dukiyarsa, kuma bata ha'ince shiba akan karan kanta.
Ha'intar miji wajen dukiyarsa daukan wani abunsa batare da iznin sa ba.
Ha'intar miji aka karan kanta kuwa, shine ta bada kanta ga wani namiji. Ko kuma tayi kawance da mijin da banata ba. Du matar kirki bazata yi haka ba.
Toh macen kirki itace wadda bata ha'intar mijinta daga dukiyarsa ko kuma akanta. Salihan mata masu da'a ne ga mazajensu, masu tsare mutuncinsu ne da dukiyoyin mazajensu, basa ha'intar mazajensu alokacin da basa nan.
Manzon Allah (s.a.w) ya fada cewa babu yanda za ayi mace ta dauki wani abu a dakin mijinta ba tare da izninsa ba, to bai halatta ba,
sai sahabbai suka tambayi annabi cewa "ko abinci ne? Sai annabi yace "wannan shine mafi daraja acikin dukiyoyin mu, ba a yarda mace ta dauki abincin mijinta tayi kyauta dashi ba.

Kuyi hakuri plz yau bazan samu daman pstn ba, wannan wanda nadan soma rubutawa jiyane, amma gobe insha Allahu zanyi muku 3 times pr day, kuyi hkr
[1:17PM, 04/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 1**6
Chapter 3 · 0% Book details