Sashe 43
Tattalin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ofis sai dare zai dawo da ya gama abunda yake yi bacci zaiyi don gudun kada ya makara. Bata da lokaci na samun hira dashi ko magana dashi, gashi ba wanda ta sani, kuma baya barinta fita ko ina. Kokari me aiki tazo tayi mata gama abunda take yi ta fice. Abun duniya ya isheta, bata da wani aikin yi sai kallo, sai dai idan ta gaji ta kwanta ta dauki waya ta bugawa iyayenta da 'yan uwanta. Da abokanan arziki suyi ta hira dasu. Take gayawa yayarta saratu matsalarta dake damunta, kawai inba babu dama kice ya dawo dake gida, ba gwanda zaman ki acikin dangi da 'yan uwa ba. Ko wani abune ma ai inkin ga danginki kyaji sauki. Tce to bari inya dawo daga ofis nayi masa maganar zuwana tunda gobe jumma'a zai zo to sai anjima kya bugo naji yanda kuka yi dashi sukayi sallama kowacce ta ajiye. Karfe takwas na dare Aliyu ya shigo saida ya kammala du abunda zaiyi ya zauna. Tace Aliyu. Yace um hum, inajinki. Tace gobe inaso in bika naje gida. Yayi mata wani irin kallo, yace zancen ne baki gaji dayi ba. Na gaya miki keda gida ba yanzu ba. Tasa kuka, wannan wane irin al'amarine, kai baka da lokacin da zaka zauna a gida Ahmad sai yamm yake dawowa, ana biki ana suna da mutuwa amma bazaka kaini naga gida ba? Yace itama wacce kike kishi da ita tana nan din kika bambareta ke kika dawo, itama haka take zaune. Kuma baki ga ina yawan kaita gida ba, saita shekara, don haka wlh kema saikin shekara sannan zakije gida. Ta dora masa hannu aka ta kurma masa ihu wayyo na shiga uku, baya son jin kukan dan haka ya tashi daga falon ya koma daki ya kwanta. Ta zauna a falo taci kuka saida ta gaji dan kanta tayi shiru. Ta tashi ta koma dakin ta rabe kusa dashi ta kwanta, tana ajiyar zuciya ya jawota jikinsa, baki daina kukan nan kina so kanki yazo yana ciwo ko? Tace ko meye ai kaika jawo min, nagane bansan abunda yasa baka kaunta ba, iya bakin kokari dai inayi maka don na kyautata maka, kuma kai baka so kasani farin ciki, kafi so kaita ganin raina a bace. Yace mansura inkika fadi haka bakimi adalci ba, tun kafi na auri zainab naso na mayar dake kaduna wajen aikina, kika nuna min baki da ra'ayi, ashe don na dawo da zainab wajen da nake aiki har kyace nayi miki rashin adalci? Kika je kika hadani da kawuna, wanda shine mahaifin yarinyar nan, ya rinka min fada akan bana miki adalci. Yasa aka bar jikarsa da 'yarsa aka taho daku. Makarantar Ahmad mai tsada yaron nan yana ganewa, kika sa aka rabashi da makarantar, aka canja masa wata, gashi nan saida suka maidashi baya, saboda karatun nasu ba iri daya bane. Sannan yanzu kuma kice min zaki koma kano ki rinka min wasa da makarantar yaro, ni da ke waye mijin? Ko ina tsoronki ne, bare a fara cemin mijinta ce? Don haka keda zuwa gida saikin shekara, anwa suma Ahmad hutun shekara. Se kuje. *** *** *** Ranar wata jumma'a yake ce mata mansura zan kai tsawon sati uku fa a gida ban dawo ba. Ta dafe kirji saboda me? Yace. Lokacin da sakanni din cikin zainab ya nuna ya kusa, kinga dole na zauna kusa da ita, don kada haihuwar tazo mata bakowa tayi masa wani irin kallo saboda in haihuwar tazo kai zaka cire mata ciwon? To wllh bazan dauki wannan rashin adalcin ba. Ko mu tafi tare ko kuwa kayi kwana ukun ka ka dawo. Ya daka mata tsawa, ki rinka sanin irin kalmar da zaki fadamin, ko kuma zan bar matana da tsohon ciki ne kullum ina farga bar halin data.. [8:09AM, 07/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 4**14 Kina tunanin zan bar matana ne da tsohon ciki, nazo na zauna anan kullum ina fargabar halin data ke ciki? Kinyi kuskure nasan darajar da, da haihuwa, bazan iya kwatanta miki yanda nake kaunar 'ya'ya ba, ya'ya na daban suke a zuciyata. Ki kiyaye abunda kika san zai tabamin 'ya'yana, koda harara ce wllh saina dauki mummunan mataki akai, ya fice ya barta. *** **** **** Ranar talata, ranar kwanan Aliyu hudu a kano, cikin dare zainab tana rungume a jikin Aliyu yana lallabata. Cikin baccin taji an mintsineta, ta farka firgigit, tana salati Aliyu ya mike a rude, yana tayata salatin, saida suka kai karshe sannan yace mata menene zainab? Yaya ciwo, Abban Ihsan wayyo ka taimakamin, ya rungumeta yana rarrashinta, tare da lailaya mata bayanta, tare da busa iska kadan2 a kunnenta har bacci ya dauketa, ya shimfideta yasa kayansa da sauri ya fito mata da nata kayan. Ya dauki Ihsan ya kaiwa talatu ita. Yana dawowa dakin ya samu zainab ta farka da wani azababben ciwo tana ta murkususu. Yayi saurin rungumeta sannu zeeyta, ya salube mata rigar baccin yasa mata kayanta, ya dauketa zuwa mota. Da kyar suka karasa asibiti, tana ta salati tana murkususu, gashi tana jikinsa ya lafe da hannu daya. Suna isa asibiti likitoci suka karbeta, mintuna goma sha biyar da shiganta dakin kukan beby ya cikawa Aliyu kunne, wani farin ciki da murna suka baibaye shi. Ya daga hannu sama yana tayiwa Allah godiya, saiya ga hakan ma baiyi masa ba, yayi alwala ya shiga masallacin asibitin yayi nafila raka'a biyu ta nuna godiyarsa ga ubangiji. Ya nufi dakin da zainab take, sun gama gyarata ita da jaririn fes dasu, kamar ba ita ta haihu ba. Ya karaso da fara'arsa, sannu zeeyta Allah yayi miki albarka, nagode zainab, ya dauki jaririn fari sol dashi ya rungume dan yana jin wata irin kaunarsa tana ratsa shi. Yace zainab yanzu wannan yaron ma nawa ne? Zainab nagode, kin kawomin Alheri cikin gida, kin sadani da farin ciki mara yankewa zainab 'ya'ya rahama ne, inason 'ya'ya da yawa, zeeyta ki daure kita haifo min kinji? Ya shafi kanta. Tace yaya haihu ta uku, amma sai sambatu kake yi, kamar wanda bai taba yi ba? Yace, zeeyta kin san kuwa yanda nake son haihuwa? Inaso naga na tara 'ya'ya da yawa, naga na hada family kamar mutum guda arba'in ace du nawa ne. Ta bude baki, A yaya arba'in fa kace kana sha'awar kara aure kenan? Yace um-um du ke zaki haifamin da auntynki. Tayi dariya yaya ai sunyi yawa, ba zamu iyaba. Zaku iya tunda kuna tare da gwarzon namiji. Ya dauki waya ya buga gida, karfe uku na dare ya fada musu albishir din haihuwa. Da sha daya na safe aka sallamo su ta taho gida da tawagar 'yan uwanta. Saida suka dawo gida Aliyu yayiwa mansura waya, yake gaya mata zainab ta haihu a daren jiya tace "me kuma ta haifa? Yace kyakyawan , sankacecen dana fari kal dashi me kama dani sak dana miji. Gabanta yayi wata irin mummunan faduwa, dakyar ta iya cewa Allah ya raya. Suna gama wayar, ta bugara yayarta saratu, take gaya mata abunda ya faru, tace kin gani kin cuci kanki da yanzu kina da 'ya'ya hudu ko biyar dole du abunda zata haifa a bayan naki suke, yanzu kuwa fa ba gashi harta fiki ba? Tace na shiga uku yanzu ni ya zanyi, kina gani a abujan ma nayi ziyartar asibiti yafi guda nawa, likita yace mahaifata normal ba abunda ya sameta, a shirye take ko yaushe zan iya daukan ciki. Amma har yanzu shiru babu labari. Kedai ki samu ki lallaba shi ya barki zuwa sunan nan, sai musan abunda za muyi akai, don dole sai an hada da rokon Allah. Ranar kwana biyu da haihuwar tayiwa Aliyu waya tace zasu zo wajen suna. Yace a'a aina gaya miki sai kun shekara zaku zo dan bazan yarda ki cutar min da ki rinka yi masa wasa da karatu ba. Tasa masa kuka, ni gaskiya ba yarda da abinda ka shirya yi wanda ba kaso in gani shiyasa kawai zaka hanani zuwa. Du abunda naga damar yi kin isa ki hanani ne? Karki manta fa da na samu, zan iya kyautar da abunda na mallaka don nuna bajinta, da godiyar Allah bisa kyautar mutum da yayi min. Kema ga key din mota sabuwar kira, ta yayi na baki, ki hada da dayar sun zama biyu, albarkacin wannan haihuwa da akayi min. Tasa kuka banaso bana farin ciki da kyautar da kayi min, ka barni ni kawai nazo naga abunda xa ayi. Ya kashe wayar yayi murmushi kawai ya girgirza kai. An sha shali ranar suna, a ranar kuma aka aiko masa da takardar karin girma, a ranar Aliyu yayiwa 'yan uwansa bajinta kanansa su hamza dasu sadik da faruk yayun zainab, ya basu gidajr guda hudu a jere da aka gama ginasu, yace su nemo matan aure, ya fito da keys na gidaje kanana ya bawa sadiya da ni'ima, yace gashi kuma kwasa 'yan haya. Ya bawa Abba da daddyn zainab mukullayn gidansu da aka gama. Tsawon wata uku basa cikin gidansu suna na gidan zainab data zauna aciki. Haka ya rinka bin 'yan uwa da dangi yana musu alheri, aka radawa jariri sunan Abbansa, suna kiransa Arfat. Aliyu yaje da kansa ya bawa maihaifin mansura key din gida mai kyau. Du abunda akeyi mansura tana samun labari ta waya, hankalinta atashe yake don ita gani takeyi bari da dukiyarsa yake yi kamar zata kare. via #Justice_Hamzat [8:10AM, 07/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 4**15 Rayuwa ta mike, jin dadi da kwanciyar hankali sun saukar musu, basu da matsalar komai Arfat yayi bul-bul dashi, fari sol kyakyawa. Watan arfat hudu dai-dai wannan lokacin ne kuma mansura suka cika shekara a Abuja. Ranar litinin da yamma mansura, tayi masa maganar zuwansu gida, yace su fara shiri saura kwana shidda su tafi. Tace kayi mana alfarma mu tafi jibi, kaga saura kwana bakwai bikin yaya saratu, ma fara shirye- shiryen da zamuyi. Ya girgiza kai kwana shidda na fada miki in kinje kwayi shirin da zaku yi. Taso tayi magana ganin ba fuska ta zumbura baki ta bar wajen. Da dare suna cin abinci da Ahmad mansura tana gefe daya tana kallo Ahmad yace, Abba dazu fa da ina waya da Ihsan cikin maganarta tace min arfat bashida lafiya. Cikin sauri