← Book details Tattalin So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 44

Sashe 2

Tattalin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

MAMAN ta bata kaza daya da youghot guda uku, ice-cream guda uku, gashi nan saii tafi gidan hajiya ki hadu keda 'yan uwanki mata da mazan tunda suna can kuci, wannan kuma in na nashiga wajen su hajiya cin abinci maci acan."
zainab ta dauki ledar tayi bangaren wajen hajiya, ta shiga da sallamarta, ni'ima ta tarota tana dariya tare da cewa, "sai 'yar gidan daddy, me kika samo mana.
Tace, "ai bazaki ciba tunda kika sa aka sani cinye abinci." tace haba yi hakuri 'yar kanwata, kinsan tsakaninmu bata baci."
sadiya ta karbo kayan tace, bawanin kunyi fada da ita dani take shiri." gaba daya suka hadu suna cin kazar da youghot din da ice-cream din. Ahaka Aliyu ya shigo ya sami kujera can nesa dasu yana duba jarida. Zainab tasa jummai mai aikinsu ta dauko mata jakarta ta islamiya tana son yin hadda, don gobe malaminsu yace su zo masa da haddan Arrahaman izu bakwai.
Ta bude Qur'ani ta bawa hajiya, tace hajiya rikemin nayi hadda, gobe malam yace muzo masa da hadda, du wanda bai iya ba zai sha bulala.
Hajiya ta rike mata Qur'ani ta fara karanto Arrraman cikin kwararen larabci irin wanda ake koya musu a islamiyasu, da yake tana da zakin murya, gashi ta iya fitar da kowane harafi, ta iya rera karatun da kome kake yi in kaji saika tsaya ka saurareta.
Aliyu ya lumshe ido yana mai jin dadin karatun nata, a ransa kuwa fassara suran yake yi yana fasalta mata 'yan aljannan da Allah ya yiwa rahama. Tana kaiwa karshen suran tace Alhamdulillah, na haddace a kaina."
hajiya tace "barakallahu fik, kin wuce dukan malam." hajiya tace shiyasa nake sara miki mutuniyata
shagwabarki bata damuna tunda akwai ki da kwakwalwa mai kyau, du abunda aka gaya miki kya dauke shi a kanki.
Sadik yace "iyayi dai da neman suna wai ita ace mata mai ilimi."
zainab tace toh ilimi karyane? Ai ilimi shine kan gaba a rayuwar dan Adam. Ilimi lallai ne mace ya kasance tana kula dashi, ilimin addinin ta da kuma ilimin rayuwa.
Misali, bari na baka misali da kowanne. Ilimin addini don tasan yadda hukunce-hukunce sallah, tsarki, jinin al'ada, jinin biki da dai sauransu.
Ilimin rayuwa kuwa, don kanta ya waye ya kasance tasan abunda yake faruwa a duniya, koda ta sauraron ko radiyo, kada ace mace bata san sunan gwamnan garinsu ba, ko shugaban kasa. Kinga akwai karancin wayewa a wajenki kenan.
Ilimi wani abune da yake karawa mutum daraja, Allah mai girma da daukaka yace "Allah ya shaida lallai babu abun bautawa da gaskiya sai shi." kuma mala'iku ma'abota ilimi sun shaida yana tsayar da adalci mabuwayi mai hikima. Kaga saboda muhimmacin ilimi a wannan aya, sai Allah ya ga hada shaidarsa data mala'iku da kuma ta masu ilimi.
Ashe du wanda ba malami ba, ba kuma mai neman ilimi ba, toh bai cika cikakken mutum ba. Haka kuma annabi ya fada acikin wani hadisi, "duk wanda Allah yaso shi da Alkhairi, saiya fahimtar dashi Addini." haka kuma yana cewa, "neman ilimi farilla ne akan kowane musulmi namiji ko mace.
Kuma Darajar farko idan ance ilimi shine ilimin addinin musulunci,sai kuma ilimi na rayuwa, kamar su ilimin likita, injiniya, siyasa, mu'amala da dai sauransu.
Daraja da kimar 'ya mace tana karuwa gwargwadon yadda ta kula da iliminta, kamar kuma yanda darajar da kimarta take lalacewa a wulakance sakamakon yanda taki yin ilimi."
mace ta gar itace wadda kunya bata hanata neman ilimi, ilimi na addini kona rayuwa. Ka duba ka gani, nana Aisha matar manzon Allah (S.A.W) du da yarinya ce karama, domin har annabi ya bar duniya shekarunta sha takwas ne, amma tayi gwagwarmaya da maza wajen haddace hadisan Annabi (S.A.W), domin itace ta hudu a cikin mutane bakwai da suka fi kowa haddace hadisai annabi acikin sahabbai.
Kaga wannan yana nuna kulawar mata da ilimi kenan.
To kada kuma yi min zargin son gwaninta ne yake sani yin karatu, a'a inason yin koyi da nana Aisha ne, don nima inaso na zama mace ma wadatatcen ilimi.
Hajiya tace Allahu akbar, Allah ya baki ikon yi.
'yan'uwan suka sa mata dariya, tare da cewa sai auta.
Aliyu yarinyar yaji ta burgeshi, ta kara shiga ransa sosai, yanda take da kyakyawar kwakwalwa ya kamata abarta tayi ilimi mai zurfi don ta zama wani abu gaba. Iliminta ya amfani sauran al'umma.
Washe gari yaya Aliyu sammako yayi ya koma kaduna bakin aikinsa. Cikin hukuncin ubangiji sai ga mama da ciki, don ita harta fitar da ran sake haihuwa, to ta ga zainab shekara bakwai harda wata uku. Sannu a hankali hajiya tana matsawa aliyu da maganar aure, shifa ya gaya mata bashi da lokacin da zai tsaya duba matar da zai aura, ita tace "to ta nemo masa, don ita tanada lokaci.
Du da akwai gidan makocinsu Alh haruna, 'yar gidan mansura ita take mutuwar son Aliyu, du sanda yazo tai ta shige da fice kenan a gidan, ayi masa soye-soye na kayan dadi akawo masa, amma baya kulawa saidai kannensa su cinye, hajiya ta zuba tukuici.
Duk yanda mansura taso taja ra'ayinsa don ya sota, ya rinka sauraranta bata isa ba, ko kallonta ba yayi saboda miskili ne.
Ita kuwa hajiya taga tayi tayi dashi ya samo matar da zai aura ya kasa, suka nema masa auren mansura.
Chapter 2 · 0% Book details