Sashe 37
Tattalin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
TATTALIN SO 4**3 . Yarinka lallaminta yana jijjigata kamar karamar yarinya, harta koma bacci, sannan ya mike ya tafi. Be dade da jan motarsa ya tafi ta farka da wani gigitaccen ciwon baya da mara, ta farka tana salati, ta matsa kararrawar kiran talatu shiru bata shigo ba ta tuna fa ashe tun dazu ta tafi gidan yarta. Ta taso a hankali tana dafe da kugu, tana salati ta fito babban falo. Mansura tana zaune tana kallo, ta jiyo salatinta da nishinta, ta juyo tana kallonta, ta tabe baki ta juya taci gaba da kallonta. Zainab ta durkusa a gabanta ta daura kanta akan cinyarta, tana salati. Aunty dan girman zatin Allah ki taimaka min ki tallafawa maraicina, ki dubi girman Allah aunty kinsan abunda nakeji. Saita ji jikinta yayi sanyi, taji tausayin yarinyar ta tuna irin gigicewar dayi sanda tana nakudar Ahmad, da yanda yarinyar tai ta kuka. Ta juyo ta kalleta, ta murkususu a jikinta, ta dauki waya ta bugawa direban gidan, tace maza ya fito da mota. Ta taimakawa zainab din, saida suka shiga direba ya dauki hanyar asibiti data ke zuwa awo. Mansura ta fito da wayarta tana neman layin Aliyu amma bata sameshi ba, har suka isa asibitin, ana kokarin shigar da ita dakin haihuwa, ta samu lambar Aliyu ta shiga. Ringin uku ya dauka, hello! . Aliyu muna asibiti da zainab ba lafiya. Kafin ta karasa cikin kara yace mata what? Tayi saurin cire wayan daga kunnenta, don jin yana barazanar tsorata mata dodon kunne. Daga nan ya hawo motarsa ya nufo asibiti, ya tarar da ni'ima da sadiya dasu umma sunata zarya a kofar dakin data ke ciki. Yana zuwa bai tsaya ba ya banka dakin haihuwar tayi wujiga-wujiga tana salati, wata likita tana tsaye a kanta. A galabaice ta rinka miko masa hannu, tana cewa wayyo yayana zan mutu, yaya ka yafemin, yaya haka mamana tayi shiyasa ta rasa ranta. Yazo ya zauna a gefen gadon ya rungumeta, yana rarrashinta kiyi shiru zainab, kita addu'a Allah zai saukeki lafiya kinji? Ya rinka murza mata bayanta, yana karanata addu'o'i ya tofa a ruwa ya bata tasha. Taji ciwon ya lafa mata, ta bingire a jikinsa ta fara bacci, can wani gigitaccen ciwo ya farkar da ita, cikin lokaci kankani ta rikice da salati ta kankame Aliyu likitan tana taimaka mata, katuwar 'yarta ta fado fara tas da ita. Wata irin dariya Aliyu ya saka, tare da jerawa ubangiji kirari, yana nuna godiyarsa ga Allah. Ya dauki 'yar ya rungumeta, yanata aikin kallon babyn, likita tana gyara zainab, kamar wanda aka mutsina yayo waje da gudu yana kiran umma, mama, ummi, gaba daya suka yo kansa suna masu farin ciki. . Ummi ta karbeta, kai tubarkallah masha Allah. Su ni'ima da sadiya sai lekenta suke yi a hannun ummi, su naso su dauketa, amma Aliyu ya hana, wai kada a jagwagwalaa, ko ya manta suma sun a haihune. Likita ta fito cikin kalmar turanci take ce masa likita baka tsoro bebyn tayi mura ne, ka fito da ita take shakar iska? Aliyu yace ato ku kawota. Ya karbeta da sauri yayi cikin dakin da ita. Su umma duk suka bishi don ganin jikin zainab din. Zainab tana ganin su umma ta rufe idonta wai kunyarsu take ji, ni'ima da sadiya sunata yi mata dariya. Mansura kuwa tana tsaye a gefe tana mamakin irin murnar da Aliyu yake yi, kamar wanda bai taba haihuwa ba. Mansura ta fito daga dakin, don bazata iya kallon takaici ba. Ya wani zauna dirshan a gadon zainab din, jikinsa yana gogar nata, kamar zai rungumeta, sai wani dariya yake. Ta dauko wayarta ta buga, hello yaya saratu, yarinyar nan fa ta haihu yanzu, haba dan Allah meta haifa? Um du wannan iyayi da akeyi ta bige da haihuwar mace. Saratu tace "A me bambacin mace da namijin,kema ai yaya saratu kinsan mace da namiji akwai bambanci. . Ai namij shine magajin gida bare ahmad shekara takwas fa kenan, a hada da 'ya mace ta mintuna amma kinga yanda shida kannensa da iyayensa yanda suke ta wani murna da farin ciki. Saratu tace gaskiya mansura sai anyi miki uzuri, wannan hali naki sai an taimaka miki da addu'a, ni kinga bazan iya sauraran wadanan kananun maganganu naki ba, ta kashe wayar. A ranar aka sallamesu saboda mai jego da baby lafiyarsu kalau. Ummi itace a gun zainab. A ranar da dare saida ta kori Aliyu bangarensa, da asuba talatu ta girka garwa kan kuka gas, ruwan ya tafasa ta kwashe, ummi tayi wa zainab cikakken wakan jego, tana zillewa tana wash a haka aka gama. Zainab tana shiryawa ummi tana yiwa baby wanka talatu tana goge lokaci daya du suka gama. Me jego da baby sun fito dagwas shar dasu, gaba daya bangaren nata ya rikice da kamshi me rikita zuciya. Karfe takwas Aliyu ya shigo, ya durkusa ya gaida ummi, ya karbi babyn a hannunta, yace ummi zeey din tana ina? Tana daki. Ya mike da babyn a hannunsa ya shiga dakin , sai yaji kamshin da dakin yake yafi na ko ina dadi. Tana zaune a gefen gado ya shiga da dariyarsa, me jego kinsha kamshi. Tayi murmushi yazo ya zauna kusa da ita. Ta durkusa kasa, yaya ina kwana? Lafiya lau, yaya babyn ta kwana? Gata nan ka ganta. Ya dago zainab din ta zauna a jikinsa, zainab kinsan kuwa jiya da kyar bacci ya daukeni? . Zainab kinsan kuwa jiya da kyar bacci ya daukeni? Saboda me yaya? Wallahi tunani babyn nan tawa 'yar kyakywan nan ta zauna min daram a rai, tunda na taso ranar da aka haifeki, na ganki kika zauna daram a zuciyata, ban taba tunanin za a samu abunda zai kuma shiga zuciyata ya zauna min irin haka ba, sai gashi kin haifa min kyakyawan diyata da tafi komai shiga zuciyata. Zainab ta kalleshi cikin shagwaba tace, yanzu yaya kafi sonta dani? Yayi murmushi ya shafi fuskarta, yace ai ke dabance zeeyta, kaunar danake miki bata da misali, amma kinga bebyn nan tawa ma ta maye ruhina gaba daya. Zainab kin gama min komai da kika haifomin bebyn nan, bani da bakin da zan miki godiya, bani da abunda zan baki. Babbar addu'a da zan miki Allah ya miki tukuici da gidan Aljannah amin yayana. Bebyn ta dan motsa, ya balle marfin swan water, ya tsiyayo kadan a kofin azurfa ya bata tasha. Yace bata nononta tasha. Yaya wallahi data kama jiya, baka ji zafi ba. Yi hakuri ki bata a hankali zai daina zafin. Zainab din taba bata tana cije baki tare da cewar wash. Lallabata yakeyi yana cewa, yi hakuri zeeyta, tasha ta koshi, yauwa bata dayan. Da haka babyn tasha ta koshi, ya karbeta ya dorata a kafada, yana shafa bayanta har tayi gyatsa taci gaba da baccinta. Zainab ta dora kanta akan cikinsa, yana tambayarta me da me take so ayi shagalin suna? Suka jiyo karadin ni'ima da sadiya suna buga kofa yace su shigo. Suka shigo, sadiya tace yaya ka hade zeey din da bebyn du ka rikesu anan ga jama'a ga jama'a can sunata zuwa barka ba me jego ba beby. Yace nifa bana son yawan daukan nan fa, saboda shi yake kawowa yara ciwon jiki. A fitar da kan gadonta falon a sakata a ciki, a rufe da net din, du wanda yazo ganinta ya ringa lekata kawai, a ganta haka basai sun dauka ba. Ranar kwana hudu aka kawo kayan barka akwatuna shidda uku na beby akwatuna uku na mai jego fadan kayan da suke cikin akwatin bata lokacine. . Mansura ta mike fuu tayi bangare Aliyu, ta banko kofar dakinsa, babu sallama ta tsaya masa tsegege aka, yana kwance akan gado yana kallonta. Tace Aliyu nagaji da wannan rashin adalci naka, ni bazan iya zama ba, kana nuna min iyakacina, ka dubi uban kaya daka jibgawa zainab da jaririyarta, ni wallahi bazan yarda ba saide kome zai faru ya faru, ya daga mata hannu ki saurara kada kiyi min hayaniya aka, fita ki bani waje. Ta fito ta kwashi akwatunan daya bata ita da Ahmad tasa aboot din motar da ya bata da akwatunan ta tafi gidansu. Mansura tana isa gida, tasa kannanta suka shigo mata da akwatunan, iyayenta suna falo da saratu da hauwa, suka tareta da lafiya? Tace wallahi Alh na gaji da rashin adalcin mutumin nan, ka dubi 'yan kayan da ya bamu nida Ahmad, amma ita ya hada mata akwatuna shidda ita da 'yarta kuma ya bata irin motar da ya canja min. Saratu ta bude kayan tana gani, super da holland da les da material da shadda ganila ga takalma jaka da sarkar gwal. Akwatin Ahmad ma kananan kaya masu tsada, sai shadda da boyel masu tsada sun sha aiki, kala goma sha daya, ga takalma da huluna masu kyau da tsada, harda glas mai ruwan gwal suka gama gani, saratu ta rufe kayan, hajiya tace mun gani Allah ya saka da alkhairi, ubangiji ya kara buda masa. Mansura tace, hajiya nifa na taho gida, ku kirashi kuyi masa fada bazan iya zama da wannan rashin adalcin nasa ba.... Kafin ta rufe bakinta Alh ya wanke mata fuska da mari, hajiya ta rufeta da duka. Dabbar yarinya mara hankali, dazunan ya kawomin makullin mota sabuwa kar. Ya aikowa da mahaifiyarki katon injin kankara don ta rinka sana'a dashi shine kike kokarin tozarta kanki, da yake bakisan abun arziki ba, to du ranar da kika sake zuwa gidan nan kika kawomin karar mijinki, saina karyaki, bare kuma kiyo yaji, wannan kasheki zanyi murus har lahira. Fita ki bani waje, ya biyota tayi waje da sauri, . kananta suka mayar mata da akwatunan cikin mota, taja ta koma gida tana hawaye, fuskarta da yatsun babanta daya mareta. Tazo ta wuce ta babban falo tana kuka Aliyu yana zaune yana kallo, ko kallonta baiyi ba, ta wuce bangarenta. Ranar suna aka sawa jaririyar sunan maman zainab, suna kiranta da ihsan. Taron suna yayi kyau angama lafiya aka watse. Kyaututuka da zainab ta samu baza su lissafuba, daga kawayenta, abokan Aliyu 'yan uwa da abokan arziki, kayan kamar a bude sito dashi. Yaya ni'ima tace, kinsan kuwa yau shekarar ku uku cif da aure da yaya. Shida yayi alkawari saikin shekara uku