← Book details Tattalin So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 44

Sashe 44

Tattalin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Aliyu yace, um-uhum? Har yana kwarewa, yace dazu da mangariba fa munyi waya da zainab, amma bata gaya min ba. Ya dauki wayansa ya kira zainab ringin daya ta dauka, yace zeeyta me yake damun babana? Wallahi yaya zazzabine, inaga dai awon hakorine, don yanata amai ya daka mata tsawa da gaske bashida lafiya kenan, amma baki gaya min ba? Yanzu me kika yi masa ina kika kaishi? Tace ba ko ina? Ya doka mata tsawa kina haukane ki barmin yaro da ciwo? Dif ya kashe wayar ya bugawa hamza, "hamza maza kaje gidana ka dauki arfat ka kaishi asibiti. Yanzu nan zanyiwa doctor waya. Yana kashewa ya mike yana zagaye falon, hannunsa goye a bayansa, yanata busar da huci. Ya sake buga wayar yauwa doctor za a kawo maka yarona. Ai gashima sun iso. Yauwa dr ka kulamin dashi sosai likita yace kada ka damu, zan kula sosai. Yauwa nagode. Yana kashe wayar ya kalli mansura ke ki hada abunda zaki hada, da asuba zamu tafi. Ta kalleshi cikin mamaki ba cewa kayi sai nanda kwana shidda ba? Ya girgiza kai bazan iya ba, bansan wane hali yarona yake cikiba. Karfe tara na safe suka shigo gidan ba wanda yasan da zuwan su. Gidan a gyare, mansura tayi bangarenta, Ahmad ya biyo Aliyu bangaren zainab. Zainab tana zaune cikin kwalliyarta tana ta kamshi. Umma da mama da ummi sunzo tun bakwai na safe duba arfat, yana hannun ummi tana bashi magani ta dabara, Aliyu yayi sallama, zainab ta bude baki cikin mamaki a ranta tace jiya da sassafe ya tafi. Kallo daya yayi mata ya dauke kai, tace yaya sannu da zuwa. Ya daga mata hannu kawai, Ihsan ta taho da gudu ta rukunkumeshi ya dauketa yana sumbatarta. Ya durkusa yana gaida iyayensa, ya ajiye Ihsan ya dauki arfat, yana duddubashi yayi tsaki, yaro jikinsa du ya saki, babu kuzari, babu wani karfi. Ummi tace sharrin amai ai yafi ga haka, ya dauki maganganun yana dubawa ya fice dashi a kafada. Yace musu, umma bari na maidashi wani asibitin. Ihsan ta biyo shi a guje, Abba zanje, ya riko hannunta suka fita Ahmad ya shiga da gudu ya fada kan cinya zainab, ta rungumeshi amadina tare kuka taho da aunty? Umma tace me gidan saukar yaushe? Sannan ya kula dasu, ya nufi wajensu yana dariya, ya gaishesu ya fice da gudu ya nufi bangaren mansura, yana gaya mata su umma suna nan dole tazo ta gaishesu, tayi musu barkar haihuwar zainab. Tare da tambayar ya mai jikin? Suka ce da sauki. Zainab ta dan rissina aunty ina kwana? Ta dago ta kalleta, a zuciyarta tace wai wani irin kyau da kullum kamar kara mata sabuwar halitta ake. Ashe ba rayuwar abuja ce tasa ta wannan kyaun ba? Ko ina take kyan nan bazai gushe ba. Zainab ta sake maimaitawa aunty ina kwana? Firgigit tayi ta amsa lafiya lau. Ta ttashi ta fita daga dakin. Ummi ta bugawa Aliyu waya, lafiya kuwa mukaji shiru? Aliyu yace bakomai ummi sun canja masa magani ne, sun kuma sa masa karin ruwa, yana karewa zamu taho. Tace to shikenan yanzu mu zamu biya muga jikin nasa, sai mu wuce gida. Suka yiwa zainab sallama suka tafi zainab ta mike ta shiga kicin ta dafa musu wannan, ta soya wacan wai duk kokarinta ta faranta masa taga yayan nata yana fushi da ita. Sha biyu dai-dai suka shigo, abun mamaki Arfat ya ware, yanata wasansa da dariya. Zainab tayi kwalliya ta daukan hankali, tana ta zuba kamshinan nata mai dadi, ta tareshi yaya sannu da zuwa. Ya kauce ya barta a tsaye ya wuce ciki, ya shimfide arfat ya shiga wanka, ta dauki arfat tanayi masa wasa yanata dariya, tasa masa nono a bakinsa yasha ya koshi. Ahmad ya shigo aunty mami naga sun dawo, Ihsan tana gurin mama kawo arfat din. Tace gashinan Amadina. Ya daukeshi, kai aunty mami kin iya haihuwar turawa, masu kyau, ni dadi nakeji naga kannena masu kyau haka. Tayi dariya, Allah Amadina, zoka kaiwa mama abinci kazo kuci kaida Abbanku. Yace to aunty mami rikemin kanina yanzu zan dawo. Ya dauki ya tafi, ta saka arfat a ruwa, ta sake masa wanka, ta canja mishi kaya yanata kamshin hoda ta sashi cikin kekensa na zama. Aliyu ya fito ya nufi arfat, ya daukeshi, Abbana ya jikin? I luv u Abbana, ta zauna kusa dashi, yaya barka da dawowa ga abincinka. Bana ci. Haba yaya don Allah kayi hakuri meyasa bazaka ciba? Ki kyaleni kawai zeey kin batamin rai, ki barmin yaro da ciwo ki ki yimin waya, to da ya mutu saidai na tarar da gawa kenan? Ya tsaya bakin taga yana kallon Ahmad da ihsan suna ball. Via #Justice_Hamzat [8:13AM, 07/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 4***16 Ya tsaya bakin taga yana kallon Ihsan da Ahmad suna ball a harabar gida. Yaji dadi a ransa, zainab ta taso ta daura kanta abayansa tana magana, cikin sanyinta. Kayi hakuri yayana ka gafartamin naga baka dade da tafiya ba, kuma ka barshi lafiya lau, saina kasa gaya maka, ina gudun tashin hankalinka. Saina rasa ya zanyi da yaron, ga talatu ta tafi duba jikarta ba lafiya, na rasa ya zanyi dashi, ni nasan bazan iya fita bada izninka ba, shiyasa kawai nasa yaron a gaba ina kuka. Yaya ka yafe min, bada niyya nayi hakan ba. Ya juyo ya rungumeta yana share mata hawayen, yaji tausayinta, ya juyo da ita ya rungumeta yana rarrashinta. Shikenan naji, ya isa daina kukan, na hakura muje ki bani abincin. **** *** ****** da yaje gida yake cewa Alh yana so zai rubuta takardar neman alfarma a dawo masa da ofis dinsa kano, saboda ya zauna cikin danginsa da iyalansa. Alh yace wannan shawara tayi daidai, tunda ka fara tara iyali dole ka zauna a waje daya, ko don kulawa da ilimin 'ya'yanka ma. Hakan akayi kuwa baisha wata wahala ba, wajen amince masa, aka bashi ofis a kano. Ga harkokin kamfaninsa komai yana garawa yanda yake so. Zaman mansura da zainab babu irin kyara da wulakanci da cin mutunci da mansura bata yiwa zainab, amma zainab saita kwantar mata da kai tana binta a sannu, bata kuma bari Aliyu ya sani, bare yayiwa mansura fada, ita dai zainab ta dage da gayawa Allah basu zaman lafiya. Cikin hukuncin ubangiji kuwa, Allah ya amsa addu'arta. Ta shiga falon mansura arfat na biye da ita, watansa sha biyar yanata yawonsa ko ina, amma bata yaye shi ba. Tace aunty zanje dubo jikin hajiya, ga arfat nan kafin Ahmad da Ihsan su dawo islamiyya. Har zata fita, mansura tace ke dawo ki dauki danki. Zainab tayi murmushi tace dana ko danki aunty? Ai kin fini karfi akan 'ya'an nan dani dasu du mallakarki ne. Mansura tace wai 'ya'yanki da kike turowa su wuni a bangarena ke kina naki bakya tunanin na cutar miki dasu, kona dakesu, ko nayi musu wani mugun abu? Zainab tace haba aunty na dade fa da sanin halinki, tun ina 'yar shekara takwas nake hannunki, da kina da mugun abu dani zaki fara yiwa. Aunty kina da kirki da hakuri kullum dauriya nake yi, har nake iya hada ido dake. Amma ina mai jin nauyi da kunyar aure miki miji danayi. Tasa kuka. Mansura ta taso ta rungumeta, kada ki damu zainab na dade dayin nadaman irin abubuwan da na rinka yi miki, don kin auri Aliyu wanda wauta nayi da son zuciya, tun fil-azal Allah ya rubuta ke matarsa ce, to ya zanyi da wannan rabon? Tunda kika haifi Ihsan Allah ya cusa min kaunarta a raina, haka arfat gani daya nayi masa naji kaunarsa ta ratsani. Kiyi hakuri zainab da abunda nayi miki. Ta rungumeta, wayyo aunty dan Allah ki bari ban taba rikonki da komai a raina ba, na yafe miki aunty nima ki yafe min. Na yafe miki zainab. Aliyu ya fito daga daki yana yi musu tafi, yace nagodewa Allah da kuka hade kanku, ga cek na milyan biyar-biyar kuja jari. Suka yi tsallen murna suka rungumeshi, suna masu yi masa godiya. Sun hade kansu bame jin kansu, tare suke harkar business dinsu. Dubai zuwa kano suna harkar gwala-gwalai, mansura ta samu ciki ta haifii 'yarta mace. Ansha murna da bidiri, akasa wa jaririyar Ikram, Ihsan du tafi 'yan uwanta murnar zuwan Ikram don gani take yanzu ta samu abokiyar shawara. A tsakanin mansura da zainab baka iya gane 'ya'yan, don gaba daya sunfi zama bangaren mansura. Aliyu kullum yana cikin godiyar Allah. Kamar yau da kullum nima da nake cikin godiyar Ubangiji. TAMMAT BI HAMDULILAH.

Sai wani jikon kuma @Khadija Idris ringing
Chapter 44 · 0% Book details