← Book details Tattalin So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 44

Sashe 20

Tattalin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

LAIFI ne kince nayi kuma na baki hakuri basai ki yafeni ba."
niba wani wallhi, ai kasan ka zalinceni, haka kawai saikoyo
aure bakamin kayan fadar kishiya
ba, kuma baka canjamin kayan daki ba." yace kiyi hakuri,
idan nagama ginina wanda zan
hadeku waje daya saina canja miki, kayan fadar
kishiya kuwa ga akwatuna biyu can da kudi dubu
dari suna dakinki na ajiye miki."
sannan tayi shiru tana Allah-Allah suje gida taga
irin kayan da yake cikin akwatunan. Suna zuwa
gida shiya bubbude mata akwatunan ta gani,
kaya masu kyau da daraja da tsada, kala goma,
super, holland,leshi, shadda,ingila, diamond,
takalma uku, mayamayai da turaruka da
sauransu.
Ta zumburi baki tace ita kala nawa kayi mata?
Yace, "ba abinda ya shafeki bane wannan, tace
dama mana kace haka, kaci amanata na rike
yarinya ta gama sanin sirrina ka aureta." ya daga
mata hannu yace, "ki rinka yiwa bakinki linzami,
tun kafin nasan zan hadu dake nake son zainab,
tanada shekara daya aduniya mamanta ta bani
ita. Shiyasa lokacin da mamanta ta rasu na dawo
da ita gidana gabana don nasa ido sosai akanta
kada wani ya hure mata kunne. Yayi ficewarsa ya
barta ta dora hannunta aka tana zunduma ihu.
Ranar lahadi akayi wuni ni'ima taci kwalliyarta,
tna cikin kawayenta sunata hotuna da bidiyo.
Zainab kuwa tana cikin dakin hajiya tana
kudundune tanata aikin kukanta, sadiya ta shiga
ta dagota, "haba zainab wai miye hakane, yanzu
du kaunarku da yaya don an aura miki shi kike
kuka irin haka?
Tace, yaya sadiya aunty mansura fa marikiyata
ce, kuma saina juye na zama kishiyarta."
to meye ba haka Allah ya shirya ba. Ta lallabata
tayi wanka, ita ta shiryata ta dandasa kwalliya
cikin wata dakakkiyar galila da akayi mata dinkin
bubu, ta aikatu da surfani ta nada mata dan
kwalin shaddar kamar nadin gwaggwaro.
Tasha gwal tanata sheki, ta fito da ita zuwa
babban falo, mutane sai guda suke suna binta,
maroka kuwa sai wasata sukeyi. Sadiya ta fito da
kudi tana watsa musu, ta zaunar da ita. Ni'ima
tazo ta rungumota tana cewa, "haba my sister ko
kefe. Kawayenta du sunzo sun zagayeta ana yi
mata shekiyanci, bata iya cewa komai sai
hawaye.
Jikinta kuwa ya dumame da zazzabi, aunty
sadiya ta bugawa Aliyu waya, yana dauka tace,
"hello yaya, dama cewa nayi zainab ce ba lafiya
take fama da zazzabi, shine nace ko zaka bari a
barta a gida inta samu sauki akwota? Yace dan
Allah gafara can, inkun ajiyeta a gidan me zakuyi
mata inbanda ku dameta da sannu-sannu. Kunga
ku kawo min matata na bata kyakyawan kulawa."
tace "a yaya haka za'ayi?
Yace ku bata waje ta kwanta ta huta kada kusa
mata ciwon kai, bana so kudameta da hayaniya."
'yan wajen suka sa ihu da dariya.
Zainab kuwa ta dafe kai data ji yana sara mata.
Da daddare akayi jerin gwanon motoci, sai aka
raba jama'ar biyu, rabi zasu kai zainab da
kawayenta rabi kuma zasu kai ni'ima da
kawayenta.
Ankai ni'ima janbulo kabuga, gidanta babba mai
kyau ita kadai abunta, zainab an kaita nasarawa
G.R.A gidanta mai kyau zaman mutum daya,
fadan kyaun gidan bata lokacine. 'yan kawo
amarya sun zagaye ko ina kowa sai santin gidan
yake. Da yanda aka tsara komai, gashi ba wani
babba bane tsarin turai ne komai, 'yan kawo
amarya zasu tafi zainab ta kankame aunty sadiya
tana kuka.
Sadiya ta rasa yanda zatayi mata saboda yanda
taga jikinta yana karkarwa, yayi zafi zau, zazzabi
ne mai zafi. Sadiya tayi mata dabara tace "zauna
anan na samo miki magani da ruwa a kicin.
Ta zaunar da ita a bakin gado ta fice da sauri
tana kuka, bata ankara ba taji gidan shiru alamar
kowa ya fashe kenan. Ta dora kanta kan filo taci
gaba da zubar da hawaye, kanta yanata sara
mata, ta dora hannunta akanta ta dafe shi.
Aliyu yayi sallama cikin sanyi muryarshi, du da
tasan muhimmacin sallama amma saita kasa
amsawa, saboda wani irin rudani data shiga, itace
yau da yaya Aliyu a daki daya, daga ita saishi a
matsayin matarsa ta aure. Ko ina auntyn nata?
Yanda dai taji anata zugugun gidan tasan ba
gidan da auntyn take ya kaita ba. Yazo ya zauna
a bakin gadon, ta zame kasa tace, yaya ina wuni?
Ya dagota "lafiya lau zainab ya taro? Tayi shiru
tana sheshshekar kukanta. Yace zainab kiyi
hakuri nasan bakya sona, kada kiga na takuraki.
Zainab tsananin kaunar da nake miki bazan iya
bawa wani aurenki ba, saina ga kaman zai cutar
min dake. Kiyi hakuri zainab kidaina yawan kuka,
bana so ki jawowa kanki matsala, a sannu a
hankali wata rana zaki soni, kinki zeeyta?
Ni jininki ne dan'uwanki ne, ki daina damuwa
akaina kinji babyna."
yana dan bubbuga bayanta na rarrashi, ya shafa
cikinta, "kinga cikinki kwalam kina zama da
yunwa, bana son zamanki da yunwa kada olsa ta
kama minke.
Ya jaeo ledar kusa dashi yana zaro katon nadin
takarda, gasassun kaji ne guda uku, sai robobin
youghot da ice-cream, ya yago naman zaisa
mata abaki ta kauda kai, cikin sigar rarrashi yace
kinga, "kinsan bana son gaddama, ki karba kici."
ya rinka bata tana ci, a zuciyarta kuwa tunani
take yi, wai dama yaya Aliyu zai iya rarrashin
mutum da lallabashi haka? Yau babu wannan
fadan da hargagi na yaya,..
Chapter 20 · 0% Book details