← Book details Tattalin So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 44

Sashe 26

Tattalin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

ayi masa girkin zamani. Karfe nawa yace miki zasu iso? Tace, karfe hudu zasu iso gida. To gobe saiki tashi da wuri sai kiyi masa satisfishal din girke-girke, dakko littafi da biro na koya miki wasu girke-girken. Ta dakko da sauri ta rurrubuta mata wasu, tayi mata sallama ta tafi. Da safe tasa aka turo mata mata guda biyu 'yan aikin gidansu don su tayata aiki. (zan wuce wajen grike-girken nan). Ta gyara tebir din ta shimfida leda me cin bakin les da adon fulawoyi, akan tebir din ta jera saitin filas din akai guda uku, daya farar shinkafa, daya jalof din makaroni, daya miyar kaji. Sannan ta jere saitin tangarayen nan guda biyar, daya soyayyan kwai cikin nama, daya kuma samosa, daya spring rolls, daya kuma gasasshen nama me romo ta dasa fulawa a tsakiyar tebir din. Su jimmale suka gyara mata gidan suka share ko ina, suka goge yana ta zuba kyalli. Hajiya data ga yanda aka gyara tebir din aka cikashi da kayan abinci, ta rinka gyada kai tana murmushi, tana cewa ma me cikin zani yanda zaiyi da wannan kayan abincin. Ko giwa ne shi ai ba zasu ciyu ba awajensa. Hajiya tace, jimmale tunda kun gama kunci abinci, ku zo mu tafi tare daku. Zainab ta rike hajiya ta marairaice mata, don Allah hajiya kiyi zamanki kada ki tafi." hajiya tace, ke baki da kai ne, yanzu sadik suka gama waya dashi jirginsu ya sauka ya za ayi na zauna har ya sameni? Haba hajiya ki zauna mana mu duk ba jikokin ki bane? Hajiya tace, uhm kyayi kya gama jummale ku shige muje. Zainab tace, hajiya ai baki cinye abinciccikan naki ba. To taya zan iya cinye wannan girke- girken haka? Jimmale kwashi ki saka min a mota, in munje gida naci." zainab ta rike hajiya tana kuka, hajiya tace, to ai ke kinga halinki, bakya so kenan inya kuma tafiya inzo in zauna miki ko? Tace a'a hajiya inaso, don Allah ki dawo, tace to zan dawo, amma sai kinyi shiru, kije ki shiga wankan. Tace to, ta tafi dakinta ta shiga toilet ta fara wanka, hajiya dasu jimmale suka yi saurin tafiya kafin ta fito. Yaya Aliyu kuwa karfe uku suka sauka da abokansa su bakwai da faruk, usman, hafiz, Anas, Amir da bashir sai Aliyu na bakwai. Gaba daya suka ce, sai sun biyo Aliyu sun gano amarya tunda yayi aure su suna nesa, bai gayyacesu ba. Yace, to kuma ba sai ku bari sai wata rana kwazo ba, sai yau mun dade bamu ga juna ba, ina dokin ganin 'yar kanwata kuma saiku bini ku katsemin hanzari? Usman yace, kaji zancen banza, yana wani kanwarsa wa ya sani ma ko tuni ya gama aiki? Faruk yace tun yaushe kai ma kasan rawar kan nan da yake yi kasan ba haka kawai bane, ya dandani zumar amarci. Aliyu yace, don Allah ku bari ita fa karamar yarinya ce, wallahi yanda nake son zainab nake tausayinta, bazan iya yin abin da zata wahala ba, aini rainonta zanta yi sai nan da wasu shekaru. Gaba daya suka sa masa dariya suna tafa hannu, tare da cewar, maji magani, faruk kaine na kusa dashi ka bamu labari. Ita kuma mansura tana ta shiri ita da Ahmad suka shiga mota, suka shiga mota sukayi filin jirgi tarar Aliyu, suna isa filin jirgi suka hangoshi cikin abokansa, Ahmad ya tafi da gudu yana kiran daddy! Daddy." Aliyu ya juyo da sauri ya daukeshi ya rungumeshi suna dariya su duka biyu. Mansura ta karaso inda suke tana dariya tace, barka da sauka, Aliyu yayi dariya ya riko hannunta ya sumbata, barka dai uwar gida sarautar mata, mun sameku lafiya. Lafiya lau." ya nuna mata abokansa du da dai tasan wasu daga ciki, ta gaishesu suka amsa cikin fara'a, suka rinka tsokananta mun biyo ango zamu ga amarya. Tayi dariyar yake tace, so ni ba zaku je nawa gidan ba, sai gidan amarya? Suka ce a'a mu mun isa? Ai sai mun fara zuwa gidan uwar gida tukun. Tayi dariya tace, to kun fitar da kanku." gaba daya suka shiga motoci suka yi gidanta. Zainab tana fitowa wanka tayi sallar la'asar, gaba daya gidan ta turareshi, sihirtaccen kamshin jikinta kuwa sai tashin fitinanun turarukanta yake yi. Dai-dai da gashin kanta saida tayi masa nashi turaren. Ta saka sabuwar super acikin kayan lefenta. Tayi kyau sosai, fatarta tayi wani sulbi da santsi, sai wani shnin take, tana wani daukan ido, ta lika kati ajikin kofar shigowa falonsu, dole du wanda zai shiga falon sai ya gani. Katin me kyau ne, yanata kamshi fari me fulawa, anyi rubutu da hausa da ruwan gwal, ga abinda yake jiki. BARKA DA DAWOWA YAYANA INA TAYAKA MURNA DA SAMUN NASARA AKAN ABUNDA KUKA JE. tana lika wani katin akan tebir din data jera kayan abinci taji tsayuwar motoci, taji gabanta ya fadi, ta runtse idonta ta karanto addu'o'i na yiwa Allah godiya, da isowar yayanta lafiya. Ga abunda yake jikin katin tebir din kamar haka. GODIYA ME YAWA TA TABBATA GA ALLAH DAYA DAWO DA YAYANA CIKIN IYALANSA LAFIYA. tayi saurin shigewa daki, yaya Aliyu daya taho da tawagar abokansa akafar falo yaci karo da katinnan, ya kalli abokansa sukayi dariya tare da jinjina masa. Suna bude falon fitinan kamshinan ya dakesu, gashi ya hade da sanyin A.C sai ya rinka feso musu kamshi mai dadi. [9:16PM, 05/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 3**2 & 3**3
Chapter 26 · 0% Book details