Sashe 38
Tattalin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
sannan zai kusanceki, sai gashi shekara uku tazo da 'yar diyarku ko? Zainab tace ke kika jiyo, ni ba ruwana. Suka sa mata dariya. *** ***** kwanci tashi rayuwa ta mika, zainab tuni sunyi arba'in, harta koma abuja, taci gaba da karatunta. 'yar diyarta saida daddynta ya nema mata tsari sosai, saboda kyan Ihsan du wanda ya bude baki, sai yace hu! Wannan yarinyar da kyau take. Ihsan watanta shidda kenan tayi 'yar kubibi abun sha'awa da 'yan hakoranta biyu abakinta, tayi sabo da Aliyu du sanda ya dawo gida, yana tare da ita, don haka data ganshi tana bayan talatu zata rinka zillo. Ya karbeta ya rungumeta, yana murnar ganinta... [8:01AM, 07/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 4**4 Tabbas badan tasan zafin zuciyar Aliyu ba, ba zaiyi mata ta dadi ba, da sai ta barar da abincin. Fuu! Ta tashi tayi daki, kamar kububuwa, su kuwa basu kula da ita bama. Sati yana cika suka koma Abuja, Aliyu yaci gaba da rainon zainab da cikin da yake jikinta, taci gaba da zuwa makarantarta, Aliyu shi yake dada ganar da ita gun da ya shige mata duhu, don haka kwakwalwarta ta sake budewa, take da kokari sosai. Don ma yanzu cikinta yayi nauyi, wani abun yana yi mata wahala, tana daurewa ne, don saboda Aliyu kokari yake ya hanata zuwa makarantar, wai tana wahala. Ga hajiya tanata damunsa da waya ya kawo zainab ta haihu a gida, du sanda yazo wkend hajiya ta sashi a gaba kenan tai ta mita. Dole sai ya kawo zeey din ko kuma tasa a kawota, har abujan ta taho da ita. Yace hajiya kiyi hakuri, exam suke yi, yanzu saura sati biyu su gama, suna gamawa zan dauki hutun shekara saimu taho tare, tace to yanzu naji magana. Suna gama jarabawa kuwa, da sukayi hutun wata biyu suka taho gida kano. Du wata siyayyar haihuwa ta kayan baby da mai jego Aliyu ya wuce dubai zaiyo musu acan. Satinsa daya acan ya dawo ya tarar cikin zeey dinshi ya kara girma, don komai a wahale take yinsa, da kyar take daga kafa. Har baya so yaga ta tashi don sai yaga kamar ya ciro cikin ya dawo dashi jikinsa. Da ta tashi zai dawo da ita, menene ne, ina zaki? Yaya lemo zan dauko maka, ya kwantar da kanta a kafadarshi yana lallaminta kamar karamar yarinya, ki bari zan dauko da kaina, don Allah ki daina wahalar da kanki, ni nake jin ciwon ajikina. Sai kuma ta langwabe a jikinsa ta kama kuka ya rinka jijjigata, yana rarrashinta, ya rada mata a kunanta menene, gaya min me akayi miki? Yaya ba kaine kayi tafiyarka ka barni ba, har kwana bakwai?ya rinka shafa bayanta, shikenan yi shiru, bazan kuma tafiya na barki ba. Shikenan yi shiru kada kanki yazo yana ciwo. Mansura tazo kansu tana huci, tace, ai saika mayar da ita ciki, karewar shagwaba da sangarta, ko kuma ka sakata a jaka, ka rinka yawo da ita du inda zaka je. Kuma wallahi rashin adalci da ake yi min na daina yarda, bazan kuma zama anan ka dauketa ku tafi abuja ba, kana tura mata kudi kana kashe mata kudi acan, taci abunda du ranta yake so, ka kalli yanda kuka canja kamar masu rayuwa a turai. To wallahi ko mu rinka tafiya abujan gaba daya, ko kuma wananan intaje tayi watanni wannan ma taje. Ya daga mata hannu ya isheni, tunda ke baki iya sannu da zuwa ba, sai kananan maganganu kika iya. Ta tafi tana kunkuni a dakeka a hanaka kuka, nidai bazan yarda da zalunci ba, ko gware kuka yi kuka fito karewar 'yan uwantaka. Ta bar wajen. Aliyu ransa ya baci, ya rinka huci yana kokarin tashi, zainab ta sake langabewa ajikinsa, tana shafa kirjinsa, yayana menene dan Allah? Ka huce kada damu yayana. Da safe zainab tasha kwalliyarta da wata ganila shadda bulu tayi kyau, Aliyu ma yasha wata lallausar farar shadda, sai kyalli takeyi kamar boyal, sai tashin kamshi suke yi, kamshin da yake tsoratar da mansura, ta rasa wani irin kamshine dasu. Du da ya hanata yin komai amma ranar girkinta bata iya hakuri saita yi masa girki. Yau ma ita ta hada break din suna kan tebir din, shida mansura suna ci amma ita ta kasa cin komai. Aliyu yace zeeyta kici mana. Tace, yaya bazan iya ci ba. Nasa talatu ta gasa min hanta ita kawai zanci. Ya ajiye kofin tea din, yace, bakya jin dadi zeey, tun jiya ina kula dake, taso na kaiki asibiti. Tace, yaya bana jin ciwon komai bakina ne kawai ba dadi. Mansura ta tabe baki ta yamutsa fuska, tace kyaji da gulmarki, haihuwa dai ba abar wasa bace, in kin tsaya iyayi kyasha wahalarki ke kadai. Aliyu yace Allah zai rabata da wahala, lafiya lau zata haihu, na samu jaririn dana dade ina mafarkin samu. Mansura tace Allah sarki wane dare ne jemage bai gani ba? Ai sai daran mutuwarsa. Talatu tayi sallama ta shigo ta kawo mata gashin hantarta, Aliyu ya karba ya yanka yasa wa zainab a baki, ta rinka tauna tana yamutsa kamar mai cin magani. Shi kuma du ya damu, sai lallabata yake yi da taci, mansura kuwa ta kumbura tayi tim, haushi da takaici suka cikata. Ni'ima tayi sallama ta shigo tana dauke da yaronta hanif, zainab ta kama dariya, Oyoyo 'yar uwa naji dadin zuwanka, bani yarona naji duminshi. Aliyu yayi saurin karbarsa yana cewa, zeey ai bazaki iya daukansa ba, tubarkallah yayi nauyi. Aliyu ya rinka yi masa wasa yanata dariya, ni'ima ta gaishe da yayan nasu. Ta juya tana gaishe da mansura, ta amsa a ciki, ni'ima ta shareta don intana cikin wannan yanayin bada sauraronta. Ni'ima ta fito da atamfar super hollan da les masu kyau, tace zainab ga ankon suna mun fito dashi. Zainab tace yaya ni'ima har wani anko za ayi? Tace ke kada kimanta dan autarmu nefa da babban yaya, ai dole muyi abubuwan da zasu kayatar masa da taron sunan dan dangi (kuji ni'ima da tsokana) zainab ta debi kayan ta mikawa mansura, aunty ga ankon suba nan su yaya ni'ima sun fitar. Ta watsar da kayan ta doka mata tsaea, dan Allah can yimin shiru kwaji da munafuncinku, maga dai abunda za a haifa ko dan gwal ne ma gani. [8:02AM, 07/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 4**5 Aliyu ya dago kansa yayi mata wani mummunan kallo, ya rinka wani huci na bacin rai, mansura ta juya ta shige bangarenta. Aliyu ya mike zai bita zainab ta rikoshi ta marairaice fuska, kamar me shirin yin kuka, tace yaya don Allah kayi hakuri, kaji ka huce, bani break din zanci. Ya koma ya zauna, yayi ajiyar zuciya, ya rinka bata break din du da ba dadinsa takeji ba, amma ta daure taci sosai, don ta kwantar masa da hankali. A yangace tace, yaya na koshi, yayi murmushi, ai naji dadi ma da kika ci wannan din, hankalina har ya kwanta. Ya mike ya dauki makullin mota, bari naje ofis, na tabbatar da kayan da suka iso jiya, an gama jibgesu a sito. Ta mike a hankali ya riketa, kiyi zamanki ki huta, ta makale kafada, tace um-um nidai saina rakaka. Ta dauko masa jakarsa, suka jera suna hira cikin nishadi, suna murmushi, suna zuwa kofar falon ya karbi jakan yace, ta koma ciki, ta rinka daga masa hannu yana daga mata, har ya shige mota, ita kuma ta dawo falon, ni'ima ta mike suka yi bangarenta. Ni'ima tace wai ke zainab ke wacce irice? Ta rinka yi miki abu iri-iri bazaki dau mataki ba, kuma ki rinka hana yaya yi mata komai. Tace haba yaya ni'ima, Allah du abunda take yi baya sakamin bacin rai, ko daya a zuciya. Kuma in na mace zan ringa biyeta, ai kullum yaya bazai samu kwanciyar hankaliba, du inda yaje yana tunanin halin da gidansa yake ciki. Yanzu kuwa ko ina yaje hankalinsa kwance, yasan bazan saurareta ba, kuma dan habaici tai tayi mana, nasan ko giyar wake tasha bazata kai hannu ta dake ni ba. Hayaniya kuwa taita yi, wata rana zata gaji ta daina, dan karfe daya baya amo. Ni'ima tace hakane. Suka ci gaba da hirar abunda ya shafesu. **** **** ***** mansura tana shiga dakinta ta dauki wayarta ta bugawa tayarta saratu. Hello! Mansura ya akayi ne? Tayi tsaki hum yaya saratu, gaskiya matsalolin gidan nan sun fara isata. Tace menene kuma meya faru? Tace, um mutumin nan du ya wani rikice akan cikin yarinyar nan, saika ce wanda bai taba haihuwa ba, zaita lallbata tana wani yanga da yamutsa ga shagwabar tsiya (komai girman namiji wani lokacin yana son ana masa shagwaba), ta kama kukan gulma ya rikice yanata rarrashinta, sai kace wata 'yar kwai. Yarinya ina ganinta gidahuma kamar ba wayayyiya ba ina ganin bazata iya aikata abunda take yi ba, kinga yanda take zama dakyar ta tashi da dakyar amma du ranar girkinta, ita zata yi masa du wani abun da kanta. Kuma shima da yake munafikine, ranar girkina idan kuku yayi girkin iyakacinsa yaci cokali biyu, ko uku ya ture. Ranar girkinta kuwa ta sashi a gaba tana loda masa abinci yana ci yana santi tana dariya, sai yaci dayawa. Baki ga yanda yake daukin cikin nan ba, kullum addu'arsa da fatansa ta haihu lafiya inda kika san ba a taba yi masa haihuwa ba. Gashi ya mayar da Ahmad din irin makarantar dasu zainab din suka yi, bazai dawo ba sai shidda na yamma wannan ai zalunci ne. Gashi ya debi yayunta ya dorasu akan dukiyarsa, wannan kamfanin nasa fa a hannunsu yake, daya darakta daya manaja. Saratu ta katseta to ina ruwanki ba 'yan uwansa bane? To idan 'yan uwansa ne ni bazaiyi min kara ba? Kamfaninsa na motoci ya daura kannensa, da suke uwa daya uba daya da ni'ima su biyu da nasa kannen biyu. Shi kenan arzikinsa saide suci su isu? Ni banda nawa dangin kenan? Saratu tace kedai mahaukaciya ce wallahi, ki jawowa kanki abunda zai sakeki, kizo mu sake zama. Kina kallona gashi miji yaki samuwa, kuma kice yana yiwa danginsa banda naki. Kina ina ya dauki rabi'u da hamisu ya kaisu kamfanin nasa ya basu aikin yi. Ko kin manta da zaman banza suke yi. Gashi yana zuwa yana