← Book details Tattalin So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 44

Sashe 22

Tattalin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ALLAH NE ya shirya aurenmu, kodai akwai haramci aciki?
Ta girgiza kai alamar a'a ya dagota, taso muje muyi break,
dura zan ringa yi miki bana son
zamanki da yunwa."
ya riko hannunta zuwa kan tebir din, yana bude abincin
yana shirin zuba musu, ta rike hannunsa,
ka bari yaya na zuba mana.
Yace, yauwa ko kefa, ai gwanda ki fara aikin lada." ta zuba
masa farfesun da soyayyen dankali
da kwai, ta hada masa tea mai kauri, ta tura masa
gabanshi.
Yace to sannu, muci." ta girgiza kai tace, bana jin yunwa."
yace, "kinfi so na miki dura kenan?
Ta hada tea kadan tana sha a hankali. Ya zuba
mata ido, shi yarinyar sha'awa take bashi, komai
nata a nutse cikin hankali da nutsuwa. Suna
gamawa ta kwashe kayan ta kai kicin. Shikuma
ya zauna akan doguwar kujera. Tazo zata huce
ta shiga daki, ya jawota ta fada jikinshi, yace
mata a kunnenta in zaki je kibar mijinki? Zo muyi
hirar soyayya, nine fa haidar dinki kin manta da
hirarmu da mukeyi mai dadi? Ta boye fuskarta.
Yayi murmushi wayarshi tayi kara, ya dauka da
sauri ya kara a kunnensa, ya rissina tare da cewa
hello, umma ina kwana?
Lafiya lau, ya jikin zainab din?
Yace, dasauki umma gata nan ma
ya nana mata wayar a kunnenta, ga umma zata
yi miki ya jiki.
Ta noke um-um, nidai kunyarta nake ji. Yace au
yau kunyar umman taki kike ji, bazaki amsa mata
wayarta ba?
Cikin sanyinta tace, hello, umma ina kwana?
Lafiya lau zainab ya jikin naki? Da sauki umma.
"kiyi hakuri zainab kinji, yanda nasanki da hakuri
da biyayya ki kara akan da, kada kisa kunya a
harkar aure, saita jawo miki halaka kinji zainab?
Cikin sanyita tace to umma, nagode, don Allah
umma ku daina wahalar da kanku wajen girki don
Allah umma kada asake kawowa zan girka da
kaina.
Anya zainab, ki bari ki kara hutawa mana ba zaki
iyaba akwai wahala. Tace bakomai umma zan
iya. To shikenan zainab Allah yayi miki albarka."
amin umma.
Ta kashe sannan Aliyu ya cire mata wayar daga
kunnenta, yace, "nifa kada kije ki kone ko ki
yanke, zaki ce zaki iya girki da kanki.
Tace yaya niba mace bace, ai dole nayi girki, zan
bar iyayenmu suna wahala ne? Ai saidai mu muyi
musu don su huta mu kuma samu lada ko? Ya
daga mata kai kawai saboda shi yana yabawa da
hankalin zeey din tashi.
Tace, yaya kaje ka gano aunty da Ahmad kaga
yasuka kwana? Au har korata kikeyi?
Tace ba haka bane yaya, gwanda kaje kaga yanda
suka kwana.
Ya gyada kanshi zanje, daganan zan wuce office
din daddy da Abba na gaishesu.
Sha biyu dai-dai ya fita ya nufi gidansa, yayi
sallama falon mansura tana zaune bata amsa ba.
Ya shiga ya zauna bata juyo ta kalleshi ba.
Yace yau bakisa su talatuwa sunyi shara da
wanke wanke ko ina kaca kaca haka? Tace, tunda
kazo ai saikai kasa suyi.
Ina Ahmad kinsa ankaishi makaranta daiko?
Tace nidai kada ka dameni, ka damu da
rayuwarsa meyasa baka tafi dashi can gidan naka
ba? Wai don Allah ko kunya baka ji ka riki yarinya
ka aureta yau ka kwana gado daya da ita har
wani abu ya faru a tsakaninku? Wannan abun
kunya da yawa yake, wallahi idona idon yarinyar
nan saina raunanata.
Ya daka mata wata irin tsawa data firgitata, yace,
wallahi ki kiyaye, du ranar da kika sake kika dora
hannunki akan matata saikin gane kurenki wallahi
sainayi maganinki. Bissimillah kije ki tabata.
Abunda yasa kenan nakasa bawa kowa auren
zainab, don kada wani ya cuceta, shiyasa na
aureta don nabata kulawa, sannan ke kuma kice
zaki daketa. Wallahi da sai kin raina kanki." ya
mike ya fice ya bar mata gidan, yayi office din
iyayensa.
Zainab kicin ta shiga, inda duk aka jere mata
kayan amfanin kicin kamar a turai, du wata
na'ura da zata dafa abu kota gasa abu cikin
sauki an sa mata aciki.(nan yanda za ayi
abincine nasan basai na rubuta ba)
Ta gama abinci ta shiga wanka ta dauro alwala,
tayi sallah tashafa mai, ta shafa farar hoda du da
ba wata kwalliya tayi ba saida ta kara kyau tasa
atamfa holan baka, dinkin karamine yayi das
ajikinta, ta fesa turaruka tanata kamshi.
Ta jona abun turaren wuta, mintuna kadan gidan
nata ya dumame da kamshi. Tana so taji
mutuniyar tata yayarta ni'ima, to bata tunda yaya
ya fasa mata wayarta batayi wata ba. Koda yake
bawa zai ba tunda shine me sayen?
Yaya Aliyu yayi parking motarsa ya fito a harabar
gidan, daddan kamshi daya ji yana tashi shiya
shaka ya ratsa masa zuciyarsa, saiya ji ya
sanyaya masa rai. Yayi murmushi ya shige ciki,
ya tura kofar falon ya shiga da sallama. Tana
zaune akan kujera ta amsa sallamar kanta a
sunkuye.
Yazo ya zauna kusa da ita, saita zame kasa ta
durkusa, "yaya sannu da zuwa." ya dagota ya
karata ajikinsa yace, "zeeyta meyasa baki taso
kin tareni ba kina oyoyo sannu da zuwa yaya?
Tace, "a da girmaba?
Wane girma kike dashi? Kefa babyna ce. Ta rufe
idonta, yaya kana sani jin kunya.
Zanyi kokari na cire miki kunyar nan dai ta daina
takura mana." don Allah yaya ka bari, ga
abincinka can a tebir." a lallai yau zanci girkin
amaryata, to taho muje ki bani. Ya riko hannunta
suka jere harkan tebir din, ta jawo masa kujera ya
zauna, tana bude abincin kamshi ya bugesa ya
lumshe ido.....

TA loda masa abincin ta rinka tura masagabansa, tasa
masa cokali, ta zuba masa hadinlemo data yi masa. Tace
yaya kaci mana." yazaunar da ita kusa dashi, ya debo a
cokalin yanufo bakinta, tace dn Allah yaya kaci, nasan
fabaka ci komai ba tunda safe. Nikuwa nasha ice-
cream."inbanda ke wa yake maida ice-cream abinci. Yabata
ta karba cikin kunya taci, shima yaci yceum-um carkwai,
waya koya miki girki haka?Tayi murmushi ta sunkuyar
dakai, ya rinka cinabinci yana santi, saigashi yaci dayawa.
Ta rinkamamaki ashe yaya yana cin abinci? Ita saita gaidan
aunty ta ajiye masa, idan yazo kokarinsayayi cokali biyu ya
ajiye.Intayi magana yace yakoshi. Saidai suyi ta ciye-ciye,
da yamma kuwa ya tafi gida yaci acan.Kodai daman rashin
dadi ne yake hanashi ci?Yana tafiya sallar isha ta rufe
dakinta ta kwanta,daya dawo ya taba kyauren yaji shi a
rufe, saiyakoma dayan dakin yayi kwanciyarsa.Da asuba
daya fito sallah ya buga mata, saidayaji motsin tashinta
sannan ya tafi masallaci.Yana dawowa dakinsa ya shige ya
koma bacci.Itama baccin ta koma, sai karfe takwas ta
miketa shiga kicin, tana gamawa ta kwashe komai tajera a
tebir, ta gyara kicin din ta share ko ina, taturare shi da
turaren wuta.Ta koma dakinta ta shiga wanka, tana fitowa
tashirya cikin wani jan les riga da siket, dinkinkaramine yayi
das ajikinta, sai kamshi take.Tana jera kayan kwalliyarta
akan madubi yashigo, ta durkusa da sauri tace yaya ina
kwana?Yace bazan amsa." ta marairaice, haba yayasaboda
me bazaka amsa min gaisuwata ba?Kinyi min laifi jiya kin
rufe min kofa." kayi hakuriyaya kunyarka nakeji.To zeeyta
me zanyi miki, na sani ke yarinya ce,nima ina tausayinki, ki
saki jikinki ba abundazanyi miki, rainonki zan tayi har sai
kinyi wayo,kada ki kuma rufe min kofa ina tsoro kada
waniabu ya sameki a daki ke kadai, gwanda munatare a
waje daya.Saiki yi kwanciyarki a gado, ni saina
kwantaakasa. Kinji zeeyta? Ta daga kai, kayi hakuriyaya
bazan kuma ba.To shikenan na hakura.Yaya ga break
can.Zeeyta harkin gyara waje haka kinyi wanka?Zainab aiki
yayi miki yawa, kodai asa umma tasamo miki mai aiki?
Haba yaya zan iya komai, wallahi malaminmu yagaya mana
du abunda kayi a gidan mijinka ladane, idan ka bawa wani
yayi maka, to shi yake daladan ba kai ba. Nikuwa yaushe
zan yardalahirata mu rinka rabawa da wasu?Ya gyada kai,
haka akeso zeeyta, mutum ya rinkaamfani da abunda yake
karanta.Akan tebir inda ta shirya masa break ya rinka
ciyana santi yana sa mata albarka. Saida yacidayawa ya
koshi yayi hamdala, yace zeeyta zokigaya min waya koya
miki girki ne? Naga a gidanauntyn naki bata fiya yi ba bare
nace gani kika yitana yi kka koya.Yaya a makaranta mana
ai har fanni koyon girkiakwai, shiyasa in mun tafi tun safe
sai shidda nayamma za a tashi. Yaya Aliyu yace ai
makarantartana da kyau, daddy baya wasa a harkar
ilimi."wayar tasa tayi kara, ya dauka yace, ke ina kikabar
mijin naki kika bugowa mutane waya dasassafe? Kayi
hakuri yaya, wallahi inaso injizainab shine na bugo a
taka.Ta gaisheshi. Ya mikawa zainab wayar, ni'imatana
jinta tace mutuniyar ya akai? Ina taso najiyo ki saina tuna
kefa kurmace yanzu tundabakida waya. Wai ya yayan ne,
komai ya faru ko?Zainab tace oho! Ke kika sani. Yaya ni'ima
inakika barshine?Yana kicin yana soya mana
break.A'uzubillahi, kiji tsoron Allah kina zaune mijinkiyana
kicin."ni'ima tace, ai shiya jawo, bashi ya dora mingajiya ba,
a wahale nake ba abinda zan iyayi. Aiya kuma shiga
kicin."ke yaya ni'ima wace irin gajiya ce da zata
hanakishiga kicin?Ni'ima tace 'a daga jin bayaninki
bakisankomaiba. Wai yaya kallonki ya tsaya ne haryanzu
baiyi miki komai ba?Tace "don Allah yaya ni'ima ki bari ni
bana sonirin wannan maganan.Zainab da wahala fa, nima
nasha wahala bare keda kike yarinya.Zainab tace don Allah
kidaina min irin wannanmagana, Allah zan ryfe
wayar.Ni'ima tace wai yaya na wajen ne koya tashi?Tace
mata, oho ke kika sani, ni dai ki bari banaso."to shikenan
naji matsoraciya, wata rana da kankizaki zomin da zancen
bazan saurareki ba.Tace, eh naji na yarda. Ta rufe wayar
tana dariya.Yaya Aliyu yace, me take gaya miki kike
cewabakya son ji? Gaya min ni."tace kai yaya nidai ba
ruwana. Ta tashi zatagudu daki ya rikota, zeeyta ba zaki
gaya minba,ni inason ji gaya min kinji.Ta boye fuskarta, don
Allah ka bari ni bazan iyaba. Wata wayar ce ta sake
shigowa, da yayi birisda ita saida yaga numbar mai
bugowan sannanya daga.Hello mansura ya akayi?
Chapter 22 · 0% Book details