← Book details Tattalin So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 44

Sashe 8

Tattalin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Surayya [1:23PM, 04/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 1**12 ALIYU dan Allah zaka danyi min tausa? Yace nikuma me zakiyi min? Tace bakomai." yace to kyaleni bacci nake ji." ta ture masa kansa akan kujera, tace to dagani naje na kwanta." yau alhamis karfe biyu direba ya dauko zainab daga makaranta, saboda yau basuda islamiya, shiyasa basu kai shidda ba. Ta shigo tana jan jakartata, ta zube a falo tace "wash! Aunty sannu da gida, ya bybynmu? Mansura tace gashi nan dai yana ta min zillo. Aunty ki bashi abinci yaci yunwa yake ji, inya ci zai daina yi miki zillo." ai naci abinci zeey, kin zata ni irinki ce sai anyi min dura ina kuka? Zainab tayi saurin mikewa, bari na tashi kada ya shigo ya ganni anan ya kuma sani cinye abincin daya fi karfin cikina." tayi dakinta suna dariya. Da mangariba ni'ima tazo gidan, sukayi tsalle suka rungume juna suna masu jin dadin ganin juna, kamar ba dazu suka rabu a makaranta ba. Suka zauna a falo suna dariya. Ni'ima tace auntyn mu ina wuni, ya babyn namu? Lafiyarsa kalau gashi nan yana jinki." ni'ima tace zainab kinsan gobe ne fatin zara'u yusuf shidda na yamma, ya zamuyi wajen tafiya, don yanda muke da zara'u dole ne mu fasa fatin nan? Zainab tace, wallah yaya ni'ima ina so in rakaki, to amma ya zamuyi da yaya, dama ya tafine da sauki, to shi sai ranar littinin da safe zaiyi sammakon tafiya kaduna kan bakin aikinsa." ni'ima tace, "ai dolene ma kije zainab, tare fa nayi mana ankon fatin, har gwagwaron, har takalimin da not din iri daya ne. Kuma yanda zara'u take sonki, ke wallahi kin fiya tsoro, ba sai kice masa zaki zo gida ba sai muyi tafiyar mu ta gida." mansura tace amma ni'ima anyi saurin yiwa zara'u kawarki aure da wuri, shekararki sha bakwai fa? Koda yake daga ganini zara'un nan ta girmeki, Allah ne dai ya hada kaunarku." ni'ima tace shekara biyu fa ta bani, yanzu da ita fa zamuyi candy, wai mijin zai barta ta karasa a gidansa." to saurin na meye? Inji mansura, saura wata shidda fa kuyi candyn, da ya kyaleta ta karasa ba shikenan ba." ni'ima tayi dariya tace tsoro yake yi kada ayi masa kwace, tafiya samari daya wa." talatuwa ta shigo tana jera musu abinci, ni'ima ta bude jalof din taliya ce da farfesun kifi. Ni'ima tace zubamin jalof din kadan da farfesun." talatuwa ta zuba mata. Zainab kuwa farfesun kawai ta diba, ta debo musu fantar gwangwani a firij. Ni'ima tace, zainab wai ke wace iri ce? Ban taba ganin makiyin abinci ba sama dake, yanzu kuma inkinci wannan shikenan saida safe ko? Tace "a haba yaya zai taho mana da cake da icream. Ni'ima tayi tsaki tace, shikenan abincin naki." tace don Allah aunty ki rinka yi mata fada, shiyasa kullum gata nan kamar a busheta ta fadi. Mansura tace ai tasan karonsu da yayanku, saina shiga gaya masa tukunna." talatuwa ta dawo da tangaram a rufe, da gasasshiyar kaaza aciki da mansura tasa agasa mata. Ni'ima tace kai aunty ni aida nasan da wannan ai bazan ci farfesun ba, ba ruwanki aunty, abinda kike so kici shi zaki ci. Muma dai Allah ya aurar damu, ina daga kwance aita yimin komai." mansura tayi dariya tace, ke kuma abunda yake baki sha'awa kenan. Suka fara cin kazar suna hirarsu, zainab ta fara cire hannunta waita koshi, ni'ima da mansura kuwa har kashi saida suka taune. Ni'ima ta kwalawa talatuwa kira tazo, "gani. Kije ki gayawa direban gidan nan gani nan fitowa zai kaini gida." talatuwa ta fita da sauri. Ni'ima ta mike tana yafa mayafinta da jaka, zainab ta rike hannunta tace, "don Allah yaya ni'ima ki bari sai anjima kya tafi kinji? Tace a'a zainab gwanda na tafi, kinsan yanzu yaya yana kan hanyar dawowa gida, kada ya gane ni nazo najaki ya hanaki zuwa goben." tace to shikenan saina zo goben. Ta rakata har mota ta tafi. Sannan ta dawo ciki ta wuce dakinta, alwala tayi ta tayar da sallar ishsha. Aliyu ya shigo ya wuce dakinsa, sai da ya watsa ruwa ya dan shafa lotion a jikinsa, yasa kananan kaya, ya fito falo yana kallon tashar zee-aflam, suna wani tsohon film mai kyau. Mansura tana gefensa tana cin tufa, zainab ta fito daga daki ta durkusa a gabans, tace, yaya sannu da zuwa." ya amsa a hankali. Taci gaba da tsugunnawa tana so ta tambayeshi zuwa gida gobe ta rasa ta ina zata fara. Ya kula da ita yasan akwai abunda take so ta tambaye shi, don haka sai yaci gaba da kallonsa ya dauke kansa daga bangaren tana zaune tana zaune tana wasa da yatsun hannunta, tace "yaya. Yace "uhm! Ba tare da ya kallo taba. Saita yi shiru ta kasa cewa komai. Shikuwa yana jingine da kujera ya lumshe ido yana kallo kamar ma baisan da zamanta a wurin ba, ta sake cewa, yaya don Allah gobe zanje gida. Yace me ake yi a gidan? Tace bakomai. Yace to bazaki jeba." ta sunkuyar da kanta sai hawaye kawai itada bata da wahalar yin kuka. Mansura tace don Allah ka kyaleta taje." yayi mata shiru kamar baiji abinda tace ba. Mansura tace, ni tsiyata dakai kenan, sai ayi ta ma magana kayi shiru kana jin mutane kamar wani kurma. Ko motsi bayyi ba balle yasan dashi take. Zainab ta mike a hankali zata wuce daki, ya kirata "zainab." ta juyo da sauri tare da amsawa na'am yace "don nace bazaki jeba shine kike kuka? [1:23PM, 04/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 1**13 TA juyo da sauri tare da amsawa na'am. Yace "don nace ba zaki gidan ba kike kuka? Tayi saurin girgiza kai. Yace bakida baki? Tace a'a ta koma ta durkusa a gabansa tace, "yaya dama bikin kawar yaya ni'ima za'ayi, shine zan rakata." yace "to me ya hanaki ki gaya min gaskiya? Tace, "don Allah yaya kayi hakuri ba zan sake ba." ya jinjina kai. Tace yaya naje goben? Ya daga kai. Amma kada kiyi dare." tayi murmushi, "yaya nagode, Allah ya saka da Alheri." tamike ta shige dakinta tana murna. Da safe a makaranta zainab take gaya wa ni'ima yaya ya barta zata zo. Ni'ima tayi murna, tace "to ki taho da wuri dai. Bayan sun tashi daga makaranta, karfe biyar na yamma ni'ima ta bugo wayar mansura tana neman zainab. Zainab din tana karba ni'ima tace, "haba zeey, ki sauri kizo man biyar fa tayi. Zainab tace, "nayi wanka na gama kwalliya, yaya nake jira ya fita nasa kayana na taho. Tace baya barki ba ki fito ki taho kawai mu tafi. Tace mata, cewa fa yayi kada na dade, to kinga gwanda yasan ban taho da wuri ba. Tace eh to gaskiya hakane. Yauwa kingan shi can ma ya fitarsa, yanzu direba zai kawoni. Wajen fatin ya hadu, ango da amarya sunyi kyau kamar fure, sai walwali suke suna sheki. Ni'ima sai kaiwa da komowa take a matsayinta na babbar kawa, du inda tayi kuwa zaki ga idanuwan samari a kanta, saboda ni'ima ta zama budurwa kyanta ya kara fitowa, ga gwalli ga iyayi. Su masu sabis da aka dauka sunata kaiwa mutane abinci dasu swan, lemon kwali dana gwangwani. Jama'a suna cin abinci Ali jita ya saki kida, tuni zakin kidansa yasa jama'a suka fara kada kai. Amarya da ango suka shiga filin rawa, nan fa kawaye da abokan ango 'yan uwan amarya da 'yan uwan ango, aka shiga filin rawa aka rinka watsi da naira kamar ba a san zafin nema ba. Hankalin zainab ya tashi ganin har takwas na dare tayi, ta rinka damun ni'ima ta taho su tafi gida. Ni'ima tayi tsaki, waike meye hakane? Ki bari agama basa mu tafi ba. Zainab tace um-um yaya ni'ima, kinsan halin yaya, kizo mu tafi, ni'ima tace ke wallahi kin fiya matsala, saika ce wata matar aure, kita faman jin wannan tsoron, bafa abunda zaiyi miki. Tace um- um, nidai kizo mu tafi bana son bacin ran yaya, wallahi du saina ji na damu." dai- dai lokacin da Ali jita ya saki cashiyar karshe ni'ima ta riko hannun zainab suka fice suka shiga motarsu, direba ya kawo su gida. Saida aka sauke zainab sannan ya wuce da ni'ima gida. Yana zaune a falo yayi zaman nasa na kasaita kamar wani basarake, ya lumshe ido daga gani tunani yake yi, mansura tana kwance da littafi tana karatu, zainab tayi sallama ta shigo, mansura ta amsa sallamar tare da cewar "kun dawo? Tace mun dawo aunty." tace yaya sannu da gida." ya bude ido daya yace sai yanzu kuka ga damar dawowa? Bance ku dawo da wuri ba? Ta marairaice, "don Allah yaya kayi hakuri bazan sake ba." ya daga kai "shikenan tashi kije. Ta mike tana hamdala a ranta da abin yazo da sauki. Ranar littini da asuba Aliyu ya nufi kaduna bakin aikinsa, sai kuma ranar jumma'a da yamma zai dawo. Kwanci tashi asarar mai rai, cikin mansura ya shiga wata tara harda kwanaki, tana zama dakyar tashi da bisimillah. Ranar jumma'a da mangariba Aliyu ya iso, bai samu wata tarba ba, sai dai mansura ta langwabe masa bata da lafiya, sai kuka take yi masa. Shikoma du ya wani rikice, don shi kukan yaro ma baya so bare na babba. Ya kwasheta suka nufi asibiti, raki take yi da ihu tana murkususu acikin motar. Zainab kuwa sai hawaye take yi, tana cewa aunty kidaina ihu salati zakiyi. Tun a motar Aliyu yayi waya gidan su mansura da gidansu. Suna isa asibiti aka shigar da mansura dakin haihuwa, Aliyu yayi tagumi yana sauraron ikon Allah, yayinda zainab ta dukufar da kanta acikin gwiwarta tana kuka kasa-kasa. Tana tuna lokacin da suka kawo mamanta acikin irin wannan halin, wanda haihuwarce sanadiyar mutuwarta, 'yan gidan su mansura sun zo. Yart da kishiyar babarta. Can saiga ummi tazo, zainab ta tafi ta kankame ummi tana kuka, ummi ta rinka shafa kanta tana rarrashinta. Wani ihu da suka ji mansura tayi shine dai-dai da dan ya fado. Nurse din ta garzayo da gudu tazo ta kwantsama musu labarin haihuwa, tuni kowa ya washe baki ya daga hannu sama yana yiwa Allah godiya. Sun shiga dakin anata yiwa juna barka da yaba kyan
Chapter 8 · 0% Book details