← Book details Tattalin So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 44

Sashe 5

Tattalin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

TA YAMUTSA fuska tana tsara mata abunda zata girka. Harta mike ta fara tafiya zainab tabita tasa mata dari biyar a hannunta, tsohuwa laraba tace, "auta me za a sayo miki? Tace a'a ki rike baki nayi. Laraba ta washe baki tana murna tana godewa zainab.
Yaya Aliyu ya shigo, da sauri zainab da ni'ima suka yi masa sannu da zuwa tare da gaishe shi. Ya wuce bangarensa. Mansura ta kwalawa talatuwa kira, tazo da saurinta. Mansura tace, "ki hadawa Aliyu abinci kikai bangarensa."
zainab kanta data ke yarinya tayi mamakin abun, bare ni'ima data fara zama budura. Sun san haka bai kamata ba, don ba haka ake yi a gidan su ba.
Wata mata ce da goyon 'yarta ta fita da hayyacinta kamar almajira, ta durkusa tana gaida mansura. Mansura ta hade rai tana ya musta, da kyar ta amsa gaisuwan matar.
Ni'ima da zainab suka gaishe da matar, zainab tace kwanto yarinyar, bata da lafiya ne? Matar tace "wallahi zazzabi ne da amai da kashi na hakori." yayinda take kokarin sakkota. Zainab ta mika hannu zata karbeta, mansura tayi karaf tace "ke zeey auta yarinyar ba lafiya kokarin daukarta kike? Saita yo miki amai ajiki." zeey tace to kije ki sai mata magani ta sha mana.
Matar ta girgiza kai cikin yanayi na tausayawa, tace, "aiba kudin ne, magani har dari tara da hamsin, banida kudin dazan sai mata, kudin yayi yawa, ko dari da hamsin bani da'ita bare har dari tara da hamsin." zainab ta bude jakarsu ta zaro gudan dubu daya ta mikawa matar, "ungo kije kisai mata maganin." matar ta karba bakinta yana rawa.
Mansura tace, "ke zeey kudin wa kika samu kiketa rabarwa haka? Zainab tace daddy ne ya bamu da zamu zo ko zamu sai wani abun.
Mansura tace to shine kike rabar da kudi baku sai komai ba." zainab tace aunty ai muna da komai me zamu saya? Ba gwanda mu bayarba." matar nan dai tanata sawa zeey albarka harta fice ta tafi.
Ni'ima ta fuzge jakar daga hannun zainab, ta bude ta leke bakomai aciki, ta harareta to kin rabar mana da kudin, to yanzu dame zamu sai ice-cream din? Ni shiyasa wallahi bana so nabar kudin mu a hannunki, du saiki rabarwa da mutane mu ki barmu haka. Nidai kawai kirinka bayar da iya naki, kada ki kuma bayarmin da nawa kudin."
zainab tayi murmushi, tace "haba yaya ni'ima, abunki ai nawa ne, zan iya iko da komai naki, Allah ya bamu rai da lafiya, muna da kudi a gida, ko an bamu ma tarawa muke yi idan bamuda abun siya. To ga masu bukata saimu hanasu." ni'ima tace, "to amma ai bakya bayar du ba, ai kinsan zamu sai ice-cream."
zainab tace bakomai yaya ni'ima, zaki ga Allah ya bamu wasu, don ranan malaminmu yace, "anaso mutum ya rinka ya waita sadaka, saboda tana juyar da bala'i.
A zamanin annabi sulaiman (a.s) akwai wani mutum a gidansa akwai wata katuwar bishiya, tsutsuwa tayi 'ya'ya akai. Sai wata rana matar ta gaya wa mijinta cewar, ya hau kan bishiyar nan ya debo musu 'ya'yan wannan tsutsunwar zasu ci suda 'ya'yansu.
Mutumin nan ya kwaso 'ya'yan, suka gashe shi, shida matarsa da 'ya'yansa suka cinye. Sai tsunsuwar nan takai karar wannan mutumin gurin annabi sulaiman (a.s), shikuma yasa aka kirawo mutumin yayi musu tsakani da wannan tsuntsuwar, mutumin yayi alkawari bazai sake ba.
Ana haka sai wata rana matar nan ya kuma gayawa mijinta ya hau bishiya ya kuma debo musu 'ya'yan tsunsuwa, mutumin yaki, yace "annabi sulaiman ya hana shi ya sake dibar mata 'ya'ya." sai matar tace kana ganin annabi sulaiman zaiyi maka wani abu danka kwashe 'ya'yan tsunsuwa, alhalin shima me shagaltuwane da mulkinsa? Matar dai tai ta rudarsa har ya hau ya debo.
Sai tsuntsuwar nan tasake kai kararsa wajen annabi sulaiman, annabi sulaiman yayi fushi, ya kirawo shaidanu guda biyu, daya daga gabas daya daga yamma. Yace sutafi kan bishiyar nan su zauna, idan mutumin nan ya sake zuwa wajen 'ya'yan tsunsuwar nan su rike kafafuwansa su watsoshi kasa.
Shaidanu suka je kan bishiya suka zauna. Shikuma mutumin ganin ya debo wa'yancan ba ayi masa komai ba, don haka sa wannan karon ma ya sake komawa domin ya debo 'ya'yan. Har ya taka kafarsa zai hau, sai yaji almajiri yana bara a kofar gida, saiya umurci matar nan data bawa almajirin nan wani abu. Sai matar nan tace bakomai awajenta.
Sai mutumin nan ya dawo ya samu lomar abinci ya bawa almajirin nan, sannan ya koma bishiya ya debo 'ya'yan tsuntsuwar nan, saita sake dwowa ta gayawa annabi sulaiman, sai yayi fushi mai tsanani, ya kirawo shadanun guda biyu daya tura kan bishiyar. Sai suka ce bamu saba maka ba, muna kan bishiyar koda yaushe, lokacin da mutumin zai hau kan bishiyar sai wani almajiri yayi bara ya koma ya bashi lomar abinci, sannan ya dawo ya hau. Zamu kama shi kenan sai ubangiji ya aiko da mala'iku guda biyu, daya ya kamani ta wuya ya jefar dani inda rana take bullowa, daya yakama abokina ya jefar dashi inda rana take faduwa.
To kinga dalilin sadakar da yayi ya kubuta daga sharrin shaidanu. Aliyu yana daga dakinshi yana jinsu, ya sake jinjina hankalin autarsu, yasan hakika akwai bawar da Allah yayiwa autarsu na musamman.
Ya fito daga dakinshi.
Chapter 5 · 0% Book details