← Book details Tattalin So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 44

Sashe 10

Tattalin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kwakwata dazu bata ganshi ba, don ita inta na tar da Ahmad bata tunanin komai sai yanda zata kula da yaronta. Ta durkusa ta mikawa Aliyu shi, ta gaisar da Aliyun ta mike tayi dakinta itama ta shiga wanka. Tana fitowa ta goge jikinta da tawul, ta zauna gaban madubi tana kalkale jiki. Zainab tun tana karamarta 'yar iyayi ce da son kwalliya, gata da son kamshi, da kudinta ma sayan turaruka take yi bare yaya Aliyu yana sai mata, hakama Abbansu ko daddynsu suna bata. Ta tsara kwalliyarta cikin wani fine les mai fulawoyi, bashida nauyi, riga da siket ne filet, ta kafa daurin dan kwalinta daya kara fitowa da kyanta, ta fesa turaruka sai kamshi take zubawa. Ta fito falo har yanzu Aliyu yana zaune yana lallaba Ahmad da yayi barci, tace yaya yayi barci kawo shi naje na shimfede shi. Ta dan marairaice masa cikin shagwabarta tace.... Next episode by 6pm via #Justice_hamxat [1:26PM, 04/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 1**16 TA DAN marairaice masa cikin shagwabarta, tace don Allah yaya kabarni naje gida. Yace meyasa kike so ki koyi karya ne, ba inaji ni'ima tayo miki waya zakuje gidan biki bane? Tayi kasa da murya cikin shagwaba tace, wallahi yaya ba gidan biki zanje ba, aina gaya mata bazan jeba, tunda ban gaya maka ba. Daman su hajiya zan kaiwa Amadina su ganshi." ya gyada kanshi, "kuje direba yana waje sai ya kai ku." tayi murmushi, yauwa yaya nagode." ya gyada kanshi ya jingina da kujera yana ta kallonta, tana ta hada fidar Ahmad ta ruwa data madara, da dan fulas dinshi na ruwan zafi, ta debo masa kaya kala biyu da pampas guda biyu ta zuba acikin jakar goyonshi. Wannan page ya dan samu matsala yayi baki kwanci tashi ba wuya, zainab ta zama budurwa, tana da shekara goma sha bakwai, yanzu tana aji shidda a sakandare. Zainab kyanta ya kara fitowa, tana da iyayi da kwainane, akwaita da tsabta dason gayu, don du wata saita je salon, bata gajiya da kunshin tafin kafanta ko zanen fulawa ta lalle. Ta fiya sanyi magana da marairaita; saiki zata sangarta ce da shagwaba tayi mata yawa. Idan tana magana mace ma burgeta take yi bare namiji, akwaita da iyayi da yauki da yanga. Abinda yafi fisgar maza da hura wutan sonta a ransu, inhar zata shiga waje saita samu maza masu sonta. Amma bata iya tsayawa ta sauraresu, domin tana tsoron yayanta, tana gudun abunda zai bata masa rai, bata so tayi masa laifi. Don waya ma ya hanata rikewa, sai wata rana data je gida Abba ya bata wata mai kyau, amma ta rinka dari-dari da tsoron gaya masa. Sai Ahmad ne ya dauka da gudu ya kai masa yana gaya masa Abbanshi ya bawa aunty maminshi waya. Saida ya mata gargadi sosai akan in ta sake yaji ta bawa wani saurayi numbar wayarta sai ranta yayi mummunan baci, don haka take kiyaye wa. Ni'ima anzama babbar budurwa sosai, tana karatun diploma har ansa mata ranar aure har ma ankusa bikin. Aunty sadiya tanada 'ya'ya biyu, hafiz da sajida. Mansura kuwa tun daga Ahmad bata sake haihuwa ba, tace dama saiya shekara biyar, toh gashi yanzu ya shekara biyar din. Zainab yarinya mai hakuri, ga hankali da nutsuwa, tana da kwazo, don tayi saukar qur'ani yanzu ta juya hadda. Yau asabar tana tasowa a daga islamiya ta ware kitson kanta tana son zuwa salon, harta fara tunanin ta yanda zata tambayi yayan nata fita, bata son yayi mata fada. Zainab tayi murmushi tace don Allah aunty gayawa yaya zanje salon. Tace "bazan je inda yake ba munyi fada." tace haba aunty, don Allah kije ki lallabashi ki bashi hakuri, ki tambayo min nidai na tafi. Ta tabe baki tace hakuri? Hakuri fa kika ce? Don ya kara wulakantani." zainab ta kalleta cikin mamaki, Ahmad ya fito da gudunshi da hijabin nata a hannunshi yana cewa "aunty mami gashi mu tafi kinji. Tace jeka gayawa Abbanka cewar zanje salon. Dai-dai lokacin Aliyu ya shigo, Ahmad yaje ya rike hannunshi yana gaya mishi "Abba inji aunty mami wai zamuje salon. Ya dago kai ya kalleta, "saida kika dauki mayafin tafiya sannan zakice a gayamin." ta durkusa cikin marairaice warta, tace don Allah yaya kayi hakuri, tun dazu nake jiran fitowarka, ba mayafin tafiya nadauka ba." ya gyada kanshi kuje Allah kiyaye. Tace yaya na gode. Ya bawa Ahmad kudin salon din, suka tafi direba yakaisu. Suna yin fakin a gaban shagon salon din, suna fitowa daga kanta da zata yi karaf idanuwanta suka hade dana wani dan kyakyawan saurayi daya zuba mata ido, tayi saurin kawar da kanta, taja hannun Ahmad suka shiga ciki, a gurin suka wanke mata kai suka gyara mata shi, suka yanke mata farce, suka goge mata kafa, du da karfa tata sumul take kamar ta jarirai. Ta fito da youghot da biski ta bawa Ahmad don kada yaji yunwa. akayi mata kunshi kunshi sarka a hannu da kafa, nan da nan ta canja ta kara yin kyau kamar tauraruwa. Tana fitowa daga wajen idanunsu suka sake haduwa, yayi mata murmushi ta dauke kanta da sauri, ya taso ya tari gabanta. Yace "don Allah ki taimakamin ki saurareni ki gaya min inda gidanku yake nazo na sameki a gida." ta mika masa katin yayanta, tayi saurin shigewa motar direba yaja suka tafi. Saurayin nan ya sumbaci katin data bashi yana mai jin dadi da farin ciki haduwarsa da wannan beb din. Suna tafe tana tunanin saurayin data gani, gaskiya ya hadu, itace da tsayawa yau harda bawa saurayi katin yayanta, wyarta ce tes ya shigo, tayi mamakin waya turo mata tes. To kodai ni'ima ce? Ta bude tes din, bakuwar lambace bata san mai lambar ba, ta fara karanta sakon kamar haka. "i 've been lucking 4 a chance to tell u my message, i luv u." mamaki ya kamata bata ankara ba ta kuma jin shigowar wani sakon, ta bude ta fara karantawa. This secret has been in my heart enough now i want to make it. Ta bude dayar da suka shigo tare, i told you that i want u to be my wife" a'a wannan wane irin kalamomi ne masu rikitar da zuciya, waye wannan? Ta sake dubawa ta maimaita karantasu gaba daya. Ba suna to waye wannan? Ita dai tasan ba wanda suka hadu dazu bane, donshi bata bashi lambar wayarta ba. Kuma tasan ba wani namiji data bawa lambar wayarta, to ko waye? Next episode by 9pm via #Justice_hamzat [1:26PM, 04/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 1**17 Har suka karaso gida zuciyarta tana cike da tunane-tunane, waye wannan? Meyasa ya boye mata kanshi bai fadi sunanshi ba? Ahmad yayi barci, ta saboshi akafada ta kwantar dashi kan kujera. Mansura ta kalleta tace ammafa kinyi kyau, saide kin dade." ta zauna tace "hum! Kedai ki bari aunty, saurayi fa nayi a wajen, kuma harna bashi katin gidan nan, ina tsoro kuma kada yazo yaya yayi min fada. Mansura tace a haba wane irin fada kuma? Ai yanzu kin wuce wannan ajin. Don ma keba wayayyi bace kanki a duhu yake, amma yanda kike kyakyawar nan gaki danyar budurwa shine dai-dai fara wankar samari, toke sai rashin waye wa, kullum kina like a gida, idan zaki fita ki zurma hijabi saika ce gyatuma. Don Allah ki waye. Tace, to aunty wai ya kike so nayi ne, wace iri ne ce wayewar? Haka dai ta ringa ce mata tanasa matsatsun dinki ita kuma zainab tace ba haka Allah yace ba, ka waye akan addininka shine wayewa, aunty sadiya ce ta shigo da sallama da kanwar mijinta yasira, a'a auntyn mu barka da zuwa. Zainab taje ta rungumeta, tace yasira rabon goron harda aunty kuke yi ne? Tayi dariya tace to ya zanyi tace da ita za'a kawowa zeey autarsu na fati. Zainab tace fati yasira, anya zan dai zo miki yini, yaya bazai barni naje miki fati ba. Sadiya tace haba don Allah, ke bari zakiyi yasan zakije? Kice masa gidana zaki zo, ni'ima ma nan zata zo saimu tafi tare, nayi muku ankon fati da gwagwaronsa, harda takalmi set din kayan." zainab tasa ihu, "sai auntyn mu, kedai kina son fito da 'yan kannenki. A to inbanyi muku ba wa zanyi wa, ku kenan fa kannen nawa mata, ai dole na gyaraku. Mansura tace, "ai wannan autar taku saikin dage mata don taki wayewa, kullum kanta a duhu yake. Sadiya tana dariya tace ai laifin mijinki ne, bakina kallo yke takura mana auta ba, ki rinka hanashi kin barin ta da yake ta sake. Mansura ta kama baki tace rufamin asiri da yayanku, idan nayi magana tawa ce take yin zafi, ranar jumma'a wato ranar fatin, mansura ta shigo dakin zainab tace, "bazaki je ki fada masa maganar fatin ba saiya fito? Tace don Allah aunty gaya masa." tace kinsan in ni na gaya masa cewa zaiyi inason koya miki yawo. Ta mike bari naje, aunty kiyi min addu'a Allah yasa ya barni." tace "to Amin." yana shirin fita mansura ta kawo masa jakarsa, zainab ta fito ta durkusa tace "yayana. Bai kulata ba yace "uhm! Ya akayi? Yaya dan Allah zanje gidan aunty sadiya? Me akeyi a gidan? Bikin kanwar mijinta ake yasira, shine nake neman alfarma dan Allah yaya kabarni naje. Ya daga kai kada ki dade. Tace to yaya nagode." yana fita ta tafi gidan sadiya, direba ya kaita. A can ta tarar da ni'ima suka rugume juna suna murna. Kinyi sa'a 'yar uwa ya barki." kinganni dai, yayan namu ne sai a hankali. Amma yau ba laifi fuskar tasa a sake take. Hu! Aunty wannan material din fa? Tana daga su tana yaba kyansu. Tace Abban yasir ne ya kawomin su tsaraba, amma naga sun zo akaya zan sai muku. Yauwa auntyn mu kina burgemu fa. Suka gama tsra shirinsu na zuwa fati, wani hadadden material ne da aka sake fito da kyansa da wani dinki mai kyau. Gaba daya su ukun sunyi kyau amma ba kamar zeey da kamar don ita aka yoshi. Suna bayan motar sadiya da mijinta suna gaba. A gidan fatin suka bi bayan amarya da ango suka rakata har mazauninta. Yaron sa'adu bori yanata kida da waka 'yan mata sunata rawa daga baya aka tsaya da
Chapter 10 · 0% Book details