← Book details Tattalin So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 44

Sashe 35

Tattalin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Hadin manta ta dauko tana shafa masa a hankali,shikuma
yana wani lumshe ido don ji yake kamartafiyan tsutsa take
yi masa.Ta gama shirya shi cikin kananan kaya, ta
shafamishi turaruka kamshinsu ya gauraye, suna fitarda
kamshi mai dadi.Ta leka fuskarsa tana murmushitace
yayana kayi kyau.Ya jawota jikinshi yana jin wata nutsuwa
da farinciki du sanda ya rungumi zeey dinshi, don hakako
yaushe yake so yajita manne dashi. Du sandayaje kano
abunda yake wahalar dashi kenan.Babu irin wannan
tarairaya daga wajen mansura,babu irin wannan tattalin
son, da daddan kamshi,babu irin girke-girken da zeey dinshi
take shiryamasa.Yace zeeyta Allah yayi miki albarka, zeeyta
mekike so nayi miki yanda kike faranta min nimazanso inta
faranta miki.Gaya min me kike so?Yaya so nake naje gida,
naga iyayenmu da 'yanuwanmu.Ki kwantar da hankalinki
zeeyta zaki je kano dandazu da safe da zan taho, umma
suka tafi kaini'ima asibiti, dazu ina ofis suka yo min waya
tahaihu.Ta wani doka tsallen murna ta rukunkumeshi,yaya
ni'ima ta haihu? Yayana meta haifa?Ta haifi danta namiji
yana nan kato akace.Wayyo yayana gobe zamu tafiyadan
bugi bayanta kin fiya zumudi zeeyta.Aikin nawa fa wa zaiyi
min.Sai karshen sati zamu tafi muje ki bani abinci.Ta gama
zuzzuba masa komai ta tura masagabansa du da sanyi a.c
saida tadau mahuccitana dan fifita masa abinci wai don
kada yakonashi.Ta dauki wayarsa ta lalubo sunan ni'ima
tadanna, ringin biyu ni'ima ta dauka, tace helloyaya.Ihun
zainab taji tanata murna, yaya ni'ima kinsama mana
baby.Ni'ima ta kyalkyale da dariya, ni kada ki kashemin
dodon kunne, yaushe zaki zo autamu?Sai karshen satihaba
zeey har sai kin kwana hudusanan zaki zo, kiga babyn naki?
I, wallahi to ya zanyi. Kinsan bazan iya tahowana bar
yayana ba shi kadai anan, dole saikarshen satin mu taho
tare.To shikenan zeey kin san kawai ni na matsu dana
ganki ne, tun safe gidan nan cike yake damutane.Kowa
yazo sai yace ai yanzu zeey kam zata zotunda na
haihu.Auta mun matsu fa da muganki.Tace wallahi nima
yaya ni'ima kuna raina.Tun sanda yaya zai taho inaso ya
taho dani donna ganku sai yakisaboda makaranta, bakomai
autarmu sai kunzo.Kafin tace wani abu, Aliyu ya karbi
wayan yakashe.Ya jawota cinyarsa taho kici abinci.Ya fara
bata ya taba cikinta "yaushe zaki baninawa babyn ne?Ta
langwabe a jikinsa nidai ba yanzu ba yayana.Nikuma yanzu
nake so zeeyta.Yaya da wahala fa, kana kallo wajen
haihuwamamana ta mutu.Ta saka kuka, yana rarrashinta
ya rinka radamata a kunanta, kada ki kuma yiwa mama
kuka,addu'a zaki rinka yi mata. Ki taya mama farin cikitana
aljanna ta manta da kacaniyar duniya.*** *** ****Ranar
jumma'a tun asuba zainab ta gama musushirinsu, tana ta
murna da doki, yana dawowadaga ofis kuwa, suka bi jirgin
shidda na yamma,harda talatu suka tafi, a filin jirgi
direbansu yazoya daukesu, taga an nufi hanyar gidanta.Ta
kalleshi tace yaya ba gida zamuje ba, tundayaya ni'ima tana
can? Yace a'a saimun je gidakin huta. Tayi shiru kawai bata
ce mishi komaiba.Suna zuwa gidan taga komanta fes, yana
ajiyeinda ta barshi, yaushe rabonta da gidanta
tsawonwatanni, amma babu wani kura ko datti a gidanga
kamshinta na nan ciki. Ko du sanda yaya yazoyana zaman
gidan?Sallah suka yi ya hau kan kujera ya mike,
yanalumshe ido son yayi bacci. Tazo ta zaunaajikinshi ta
dan marairaice masa, yaya don Allahka tashi muje gidan
yanzuya bude ido daya yana kallontazeeyta bazaki barni na
danyi bacci ba? Kayihakuri yaya yanzu aunty sadiya tayo
min wayanace mata mun sauka yaya gaba dayansu fasuna
gida sun hallara, don Allah yaya mu tafi.Ya mike tsaye tashi
mu tafi.Tace yaya kayi hakuri idan ranka ne ya baci,haba
zeeyta ba raina bane ya baci,watanni da kikayi ba kiga 'yan
uwa ba ai nasandole kiyi zumudi,ya kamo hannunta ya
dagota, taso mu tafi.Suna shiga gidan wani ihun da suka sa
suka zosuka rungume zainab kowa murna yake yi, dafarin
cikin ganinta.Hajiya ta rinka taba jikinta tana cewa,
"Aliyuwankan inji kayi mata? Suka sa dariya, zainabtace
hajiya me kika gani?Kin canja kinyi kyau, kin kara fari,
gashinki yakara tsawo da baki.Kinyi bul-bul dake.Aunty
sadiya tace in a hanya muka hadu, ai bazamuyi saurin
ganeki ba.Yaya ni'ima tace autarmu, hutu ya kara
samuwada jin dadi.Zeey anya kina cin abinci kuwa?Du
yanda akayi daga madara sai youghot sai icecream dasu
cakulet, cimar hutu dai da jin dadikina kwance komai sai
anyi mikizeey auta canjawar taki tayi yawameye sirrin, ko
yayanmu yayi ajiyane?Tace ke kika sani, ina babyn namu?
Du nafidokinshi da murnar son ganinsa.Ta dauki baby fari
tas, kato dashi, ta rungumeshitana jin kaunar yaron.Ta
rungumeshi tayi dakin Abba, umma ta tashi dasauri ta
rungumota tana cewa 'yata zainab najidadin ganinki, kin
kwantar da hankalinki kinyikalau dake.Abba yace "yaki
zonan 'yata.Umma ta tafi da ita gaban Abba, ummi
tacemasha Allah dana ya iya kulawa ta musamman,Wai
zainab saita samu kanta da jin kunyarsu.

Wai Zainab sai ta samu kanta da jin kunyarsu, tarinka sun
kuyar da kanta, ta kasa dago kaitakallesu.A hankali ta bude
bakinta ta gaisheshi, yarinyarta kra birgeshi da shiga
ransa.Ta gaishe da umma da ummi, Aliyu yana kasagefen
kafar Abba yana mamakin irin kunyar dazainab take ji, du
yanda ta matsu tazo ta gaiyayensu, amma ta kasa sakewa
yanzu.'yata zainab ya zaman abuja, ince dai ko
bawatamatsala?Tace bakomai Abba.Yauwa zainab haka
nake sonji, Allah yayi mikialbarka.Amin Abba.Ta ajiye masa
turaruka manyan kwalabe masutsada yaita juyasu yana sa
mata albarka.Ta ajiye umma da ummi nasu harda humra
dakulacca, suma sukai godiya suna sa mataalbarka.Da kyar
ta iya mikewa rungume da jariri tayibangarensu.Ta tafi
gaban babanta ta zauna, yana lazimi, yayisaurin sallamewa,
yana murmushi.Zainab haka kika koma.Tayi murmushi,
babana naji dadi da nazo naganka lafiyanka kalau.Kullum
kana raina Babana, ina wuni?Lafiya lau zainab kin
kyautamin da kika kwantarda hankalinki.Gashi kinyi kalau
dake.Mama ta fito da fara'arta tana yi mata sannu dazuwa,
ta gaisheta ta bata tsaraban turarukan, babawa mahaifinta
kamar yanda ta bawa Abba.Sukai godiya suna sa mata
albarka.Ta mike baba bari na koma wajen su
yayani'ima.Yace to zainab.Ni'ima tana kwance a gado,
aunty sadiya tanaamsa wayar mijinta, tana gaya masa
zuwanautarsu, yace ai yana kan hanyar zuwa daukanta,ya
ga yanda zeey dinta suka koma.Ni'ima tace gaskiya zainab
kin canja da yawa,lallai ruwan aure ya karbeki.Zainab tace,
me kuma ruwan aure?Sadiya tace, ai kinsan ita bata
sanshiba, yaya maitausayinta ne, saita cika shekara ashirin,
sannanzata fara sani ko?Zainab tayi murmushi tace ku kuka
sani. Suka samata dariya, ta zauna suka fara hiran
yaushegamo.Aliyu ya shigo dakin ni'ima da sadiya suka
gaisheshi.Yazo ya zauna kusa da zainab, ya dauki babyn
dayake jikinta, ya rinka sumbatarsa yana yabayaronya
kalleta, zeey tashi mu tafi gida, tayi kasa damurya tace don
Allah yaya ka bari na kwanaanan.Yace ya za ayi na barki, ki
kwana anan nakigidan fa?Yaya bafa a gidan zaka kwana
ba, kafi so kabarni ni kadai na kwana.Kafin yayi magana
tes ya shigo wayarsa, wayartana hannun zainab saita bude
tes din, tunda tagaba lambar mansura bace, ta karanta tes
dinkamar haka.barka da zuwa yallabai, naji labarin
saukarka,kaida madam,ka iso lafiya?Kirjinta yayi wani irin
mummunan bugawa,gabanta yana fadi ta dafe kirjinta tana
haki.Yayi saurin cewa lafiya zeeytah?Meya faru?Ta
sunkuyar da kanta, ta dafe kanta da hannunta,ya ciro
hannun ya daga kanta, yace, zeeyta meyafaru?Ta
marairaice hawaye nason zubo mata, taceyaya wacece
tayo ma tes yanzu?Yace tes me akace acikin tes din?Ta
mika masa ya karanta, ya ajiye wayar, yacegaskiya ban san
ko wacece ba, don ni banma sanlambar ba, bare nasan
wacece tayo tes din.(page nan ya balle).Ranar suna sai da
yamma aka fita hotel da zaayi fatin sunan.Jama'ar suna yi
musu murna samun karuwa jaririda aka samu yasa masa
sunan babansa anakiransa da hanif.Suka zauna a
kwataccen wajen da aka tanadarmusu, gaba daya wajen
anyi shiru sabodaaddu'ar da ake yi. Sannan wani hadadden
motarAliyu ya sawo kai.Hankalin mutane gaba daya yayi
kan motar, zubaido kawai suke yi suga isasun da zasu fito
dagacikin motar, du da dai wasu sun san motar waye,suna
isa wani soja ya fito daga wajen tukin, yabude dayan
bangaren na baya, sannan ya budedayan bangaren.A tare
suka fito Aliyu da zainab kamar taurari,gaba daya
kamshinsu ya cika wurin, suka jerosuna tafe suna hirarsu
da dan murmushi, dukawajen saida suka birgesu, tare da
basu sha'awa.Banda mansura data diririce ta dabarbarce,
itatambaya ma take wacece wannan take manne damijinta?
Saida yayarta saratu ta rikota ta mayarda ita kujerarta ta
zaunar da ita, tace ki kula kisaisaita hankalinki, kada kiyi
wata gigiwa anan,don kada ki manta abunda Aliyu ya miki
akanzainab, kinsan ya gaya miki zai iya yin
komaiakanta.Sannan mansura ta kawo ajiyar zuciya,
yanzuwannan zainab ce, 'yar da nake kiranta dagidahuma
itace ta koma haka, ta waye?Aliyu ya cuceni daya barni a
kano, saidai ko nimaya mayar dani abuja, ko kuma ayi du
wacce zaayi.Saratu ta tabe baki, tace sai kiyi kin manta
sandaya koraki gida, yanzu kuma naga alamar kina soki
yanke igiyar aurenki, me wannan cikakkiyarmata 'yar
kwalisa 'yar gayu, don rabu dake mezai dameshi.
Chapter 35 · 0% Book details